Sashe 14
Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A nutse cikin sallama ya shigo ta daga kai a hankali ta kalleshi saboda ita kadai tasan yadda tayi missing dinshi,shi dinma idanunshi na bisa kanta ji yake kamar ya shekara dari bai ganta ba,amma duk da haka saiya gintse saboda tuno ganinta da yayi da wani,daya daga kujerun falon ya samu ya zauna suka gaisa da anty amina sannan ta soma tambayarsa
"Wai me ya hadaka da shahida?,duk ka firgitamin diya?"
"Ta firgitani dai anty...bakiga har rama nayi ba?" Murmushi anty aminan ta saki,yadda sukeson junan nasu na bata sha'awa,bai boye komai ba ya gaya mata sannan ya dora da cewa
"Wallahi anty wani irin kishine dani,ina da matuqar kishi kan abinda nakeso,ranar dana ganta wallahi anty ban iya bacci ba"
"To kayi haquri mr kishi....bari kaji me ya faru" ta shaida masa kamar yadda shahidan ta gaya mata,nannauyar ajiyar zuciya ya saki yana jin kaman an sauke masa qaton dutse daga zuciyarsa,sai a sannan ya sami salama
"A rude nake anty,shahida ba ruwanmu bace mu talakawa,hankalina a tashe yake kada wani ya qwace min ita"dariya ya baiwa anty amina sosai har sai data dara
"karka damu anwar,shahida taka ce in sha Allah,yo shahida muka bata wani bakaiba ai inajin fiya fiya zata sha ta mutum" sosai anty amina ta baiwa shahidan kunya,har sai data diba a guje ta shige dakin anty aminan,shima ya miqe ya fice yana dariya.
A dakin ta taddata ta dubeta
"To laila majnun,saikije ku sameshi tunda na kashe case din,saiki kula a gaba"
"Na gode anty amina ta"
"Eh kyace haka mana tunda na dawo miki da hasken rayuwarki ko?" Dariya ta tuntsire dashi sannan ta miqe ta zura hijabinta ta fice.
Yana tsaye a soron gidan amma qofar fita yake kallo,tadan tsaya kadan a bayanshi,a jikinsa yaji tana wajen saiya juyo a hankali idanunsa zube fes a kanta,takowa yayi har sai daya rage tazarar dake tsakaninsu sannan ya tsaya,a hankali cikin wata murya dake cike da mayen so yace
"Nayi kewar wannan kyakkyawar fuskar,wannan ruhin ya hana ruhina samun barci bare ya samu salama,na cika da fargabar cewa na rasa hasken idaniyata,ashe abun duka ba haka bane" sosai kalamanshi suka sanyaya mata rai cikin daqiqu kadan,tayi qas da kanta tana fidda murmushi
"A'ah dago kanki sosai don na samu qwarin gwiwar fada miki albishir din danaso yi miki tun rannan mai mota ya korani"
"Don Allah ka daina zancan mai motar nan honey haba"
"Na daina" ya fada yana murmushi
"Na samu aikin kamfani Allah ya taimakeki...wani maqocinmu ne ya sama min,kwana goma sha biyar zan dinga aikin kwana,kwana goma sha biyar aikin wuni,zasu dinga biyana albashi duk wata dubu sha biyar" sosai fuskarta ta washe da fara'a tana jin farinciki na ratsata,tana jin burinsu ya soma daukar hanyar cika,rasa inda tsoma ranta zatayi har sai daya tsaya yana kallonta cikin mamaki,sun jima a soron gidan anty aminan kafin ya sanyata ta tattaro kayanta tazo su wuce gida,napep ya tsaida musu har qofar gida,sanda suka sauka ta zaro kudi zata biya ya harareta ya ciro daga aljihunsa ya biya,dariya kawai tayi,ko yaya idan yana da kudi ko iyakarsu kenan jikinsa baya yarda tayi masa hidima da kudinta,nan ma sun dan jima kafin suyi sallama ta wuce gida shima ya wuce.
Cikin taimakon Allah ya soma zuwa aikinsa,saidai babban qalubalen daya soma fuskanta shine na rashin kudin mota,tafiya ce mai nisa tsakanin unguwarsu zuwa kamfanin haka yake niqar gari ya tafi,duk da cewa ya saba tun sanda yana makaranta amma tafiyar bata kai ta makaranta nisa ba,sai kuma abincin da zaici shima saiya dawo zai jiqa kwakinsa yasha musamman idan aikin dare yayi zai dawo da safe,duka wannan bai dameshi ba tunda yasan cewa komao lokacine,hakanan bai yarda shahida ko anty usaina sun sani ba saboda baiga dalilin da yana namiji zai dinga daura nauyi wa mata ba,a haka ya cinye watanshi guda,saidai kafin cikar watan ya fada yayi baqi,hakan ya sanya shahida ta sanya ayar tambaya a kanshi.
Ranar daya amso albashinsa yazo da daddare,duka ya zube mata albashin nasa yana dubanta
"Me zanyi dashi honey?" Ta fada bayan ta gama saka musu albarka
"Inason ki dauki iya abinda ranki yayi miki,a matsayin albashin mijinki na farko" kai ta girgiza tasan ko tace masa a'ah cewa zaiyi bata isa ba saiya dauka,saboda haka tasan maganinsa.
Da fari ta ware wasu kudaden tace wannan kudin kayan abinci da zai siyo ya dinga dafawa yana tafiya dashi kamfani,ta sake ware wasu tace ya sake dinka kaya kala guda duk wata zai dinka kala daya,ta sake ware wasu tace ya riqe ya kashewa ne,sannan ta cire wani abu a ciki tace wannan ya kaiwa anty usaina ita yafi cancanta ta sanya albarka,next month kuma idan ya sake amsa to ya fara ajiya saboda lalurorin yau da kullum,duk sai data gama kasafin ya cakude kudaden waje daya sannan yace
"Qurun qus kin gama tatsuniyar taki?,toni ba haka nakeso ayi ba,da safe me mike ci idan zaki makaranta?"baki tadan cuno
"Kome meye ya samu"
"Good" ya fada yana cire wasu kudi ya aje
"Indomie da qwai nakeson ki koma ci" idanu ta zaro tana kallonshi baki bude
"Honey...me kake fada ne?"
"Abunda kunnuwanki suka jiyr miki.....wannan kuma kudin kashewarki na wata gud....."
"Kaga...don Allah ka tsaya ka daina wannan lissafin mana" nan sa'insa ta kaure tsakaninsu,da qyar ya yadda da nata lissafin bayan ta masa alqawarin wata na gaba ta yadda za'a sata cikin kasafin,saidai duk da haka yayi cancel kudin kashewarsa ya bata dole ta amsa saboda ya kafa mata sharadi.
Koda ya kaiwa anty usaina ma itama cewa tayi ba zata soma amsa yanzu ba,ya aje wajensa zata masa magana idan lokacin daya dace yayi,haka ya dawo dasu ya miqawa shahida
"Shikenan...zan saya banki na dinga tara maka,duk sanda kake da buqata saika amsa" washegari kuwa ta sayi bankin ta zuba masa harda kudin daya bata,ta nuna masa sannan ta roqeshi
"Don qaunar da kakemin kada kace a'ah,za'a tara ne ka siya abun hawa ko keke ne,ko baka fadimin ba nasan tafiyar qafa kake" da qyar ya amince da shawararta,donshi a son ranta tayi hidimar gabanta kawai dasu.
Wata hudu cif da fara aikinsa komai ya soma tafiya babu laifi,ta wanni fannin abubuwa da dama sun soma sauqi,cikin godiyar Allah da yadda da cewa komai lokaci ne.
Cikin haka aka fitar da ankon bikin umaima,wadda take cousin ce a wajenta,ranar data kawo musu ankon wuni tayi a gidansu,har dare tana nan,sanda ta tashi tafiya anwar yazo shahidan na wajensa,mubina ce ta rakota tana nanata mata idan ta tashi dawowa ta kawo mata alawarta,qarasawa tayi wajensu shahidan tana mata sallama daga bisani tace
"Ina zuba ido saikinzo siyan ankon,kuma wlh baki isa ba ba wani daya da zaki duka biyun zakiyi"
"To ummata" ta fada tana hararta,don batason ta tada zancan a gaban anwar din,sun riga da sun gama maganar su tun cikin gida,da haka sukayi sallama umaima ta wuce.
"Wai ina bankin nan kuwa?"
"Yana cikin gida"
"Idan yana kusa daukomin shi idan yana kusa" bata ce komai ba ta shige gidan ta fito dashi,bankin qasa ne ya amsa saiya sakeshi ya fadi take ya fashe kudin ciki ya bayyana,baki ta bude tana zaton itace bata bashi dai dai ba ya riqe ya fadi haka,sai taji yace
"Yauwa yayi dai dai,tayani qirgawa" cikin mamaki ta duqa ta soma tayashi hada kudin,bayan sun gama hadawa ya miqa mata yace ta irga,cikin murna da mamaki tace
"Da gaske ne kudi wawayene....ban zaci zasu kai haka ba wallahi" murmushi shima ya saki,walwalar da take kawai ta isheshi farinciki
"Kije ki sayi ankon ko kala nawa ne,saura kiyi dinki,idan ba zasu isa ba kiyimin magana" ranta ta ba'ta sannan tace
"Me kake fada ne?,kudin keken naka zaka bani kace nayi anko bayan sunkai kudin keke sabo harda canji?,kuma ma tuni umma tace zatamin daya abba guda daya"
"Duk bansan wannan ba....abinda kawai na sani shahidana zata saka kaya kamar yadda kowacce mace zata saka...kada kice zakimin musu indai baso kike raina ya baci" kaita duqar
"Allah ya baka haquri" dole ta fidda kudin ta sayi ankon kala biyu mayafi da abun daurawa,cikin sati uku suka shiga hidimar biki amma hakan bai hanata ganin anwar ba,shima hakan ya masa dama tunaninsa rashin ganinta.
Ranar da za'ayi dinner tun safe suna gidan kwalliya,qarfe biyar da rabi na yammaci ya kirata yazo ganinta tana ina,itama yana ranta don jiya basu samu ganin juna ba basa unguwar kwata kwata suna can aikin snacks,ta kwatanta masa gidan kwalliyar,ya gane gidan saboda cikin anguwarsu ne.
Sanda ya iso tuni an gama mata tata,zata wuce kuma gidan bikin ta saka kayanta kafin a soma dibansu zuwa wajen da za'a gudanar da shagalin.