← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 73

Sashe 10

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anwar dinne ya soma cewa"Kamar yadda kika sani na gaya miki daxun cikakken suna na sannan kuma ni maraya ne,na rasa mahaifina da mahaifiyata da qannena guda biyu duka rana guda" zaro idanu shahida tayi cike da mamaki da tausayi tana duban anwar
"Eh rana daya,sanadiyyar hatsarin mota da sukayi a hanyarsu ta dawowa daga qauyenmu"
"Wayyo....Allahu akhbar" ta fada fuskarta na nuna tsantsar tausayi,qwalla na cika idanunta,tausayin anwar ya kamata,rayuwa ba uwa ba uba ya zata kasance kenan?
"Mu biyu muka rage a gidanmu,ni da yayata kaman yadda na gaya miki,yayata nada aure tun kafin rasuwar iyayenmu,yanzu haka tana gidan aurenta ni kadai na rage ina rayuwa a gidanmu,maganar gaskiya shahida zan gaya miki ba boye boye a tarayyarmu,saboda ina fata Allah ya shiga lamarinmu,niba mai kudi bane,bani da komai sai abinda Allah ya tsagamin,karki tsammacin samun rayuwa mai tsada,kyauta mai tsada ko nauyi daga wajena irin wanda samari sukewa 'yammatansu,indai kina ganin tafiyarmu akwai matsala,duk da tsananin soyayyar da raina ke miki zan iya haqura na barki da muradinki" kai take girgizawa,sam a batajin zata iya rabuwa da anwar,qaunarsu dashi daga Allah take,wata qauna ce mai qarfi data kama dukkaninsu cikin qasa da kwana bakwai,tasan cewa ba qaramin lamari bane a tsakaninsu
"Ni dinma ba wata bace,kaman yadda kake gani rufin asirin Allah ne da dukka bawa yake qarqashinsa,ina addu'ar yadda muka hadu Allah ya tabbatar damu a haka" sai data fada kuma taji kunya ta kamata,sun d'an jima kadan suna hira ita dashi,yana bata labarin abinda yake karanta yanayin makarantar da dai sauransu.

Qarar wayarsa ce ta sa ya dakata da abinda yake gaya mata,ya ciro wayar daga aljihunsa yana duba mai kiran,gabansa yadan fadi,don sam zuwansa wajen shahidan ya mantar dashi abinda ya tunkarosa,neman mudin rigestration,hausawa suka ce mai kurmin ido da wuri yake fara kuka,haka yake duk sanda suka soma exams tun a lokacin yake fara fafutukar neman kudin,wanda tunda ya soma karatu haka yake,Allah gatan bawa ne,sai yake bashi kafin lokacin da za'a rufe,saidai wannan karon yana fargaba,saboda ganin yadda rayuwa ta sake cudewa,fadi tashi ya yiwa mutane yawa,babu ta sake samun gindin zama a rayuwar al'umma.

Saida aka sake kira ya sami ya daga da sauri,don babu ko ficika a layin nashi
"Ina zuwa in sha Allahu" kawai yace ya latse wayar ya maida aljihu,miqewa yayi tsaye hannayensa cikin aljihun yana duban shahida qasa qasa,ta masa kyau qwarai,bai taba ganin macen data masa kyau kaman shahida ba,komai nata mai kyaune,tun daga yatsun qafarta har kanta,dauke kai yayi da sauri yana kwabar kansa daga kallon qurillar da yake mata sanda ta dago kai tana dubanshi sanda taga ya miqe
"Allah ya taimakeki zan tafi" ya fada yana qawataccen murmushin daya sake fitar da sigar kyansa,
"Allah ya tsare hanya...na gode"murmushi ya saki
"nine da godiya,yau an shayar dani irin abinda nake ji abokaina na fada....zumar soyayya.....dama haka take?,haka akeji?" Dora tafin hannayenta tayi saman fuskarta ta rufe tana murmushin jin kunya,yayin da ya zuba mata idanu yana kallon zara zaran yatsun hannunta da suka dauki hankalinsa,ya sauke sassanyar ajiyar zuciya cikin ranshi yana roqon Allah daya sanya yana kammala karatunsa ya shiga cikin sahun daliban da suke samun aiki da wuri,don a yanzu jikinsa har ya soma sanyi da irin kyan daya lura shahida nashi,irin matan da masu kudi ke rububin samu su aure,Allah kada ya sanya shahidan ta subuce masa,ubangiji yasa rabonsa ce,da ya gama dacewa nan gidan duniya,tunanin daya dinga yi kenan har sukayi sallama ya wuce.

Koda yaje inda ake kiran nasa ma ba wani biyan buqata ya samu ba,kudin da yake nema bai samu ba,amma sai sam baiji wata damuwa can ba wadda ya saba ji a baya duk sanda yaje neman kudin registration dinsa bai samu ba,wannan karon darensa cika yayi fal da tunaninta da begenta,ya dinga juyi saman katifarsa,ya danna wayarsa yana zargin kansa me yasa bai karbi number wayarta ba?,sai kuma ya saki murmushi daya tuna koya karba dinma ina yaga credit din kira?,da gaka ya lallashi kansa yana addu'ar Allah ya kaimu gobe lafiya.

Tun daga wannan lokacin wata iriyar soyayya mai qarfi ta shiga tsakanin anwar da shahida,dukkan tunaninsa nata ne,duk wani motsinsa shahida na ciki,tuni labari ya kai kunnen anty usaina,kallon anwar din kawao tayi tana mamaki,tunda suke dashi bai taba kawo mata zancan wata yarinya ba,hasalima koda da tsokana tayi masa zancan budurwa tabe baki yake sannan yace
"Uhmmmm,anty kenan,anata kai wa yake ta kaya?,yanzu kojin labari kikayi ina kula wata ba zaki tsawatarmin ba?,a wannan yanayin da muke ciki anty mu tsira da rayuwarmu ma,indai ina da abun kula budurwa na kasa baki ba shakka bani da wani amfani a rayuwa" tunda har taga yadda anwar ke muradin shahida sai batace komai ba,tunda haka ta faru tasan cewa soyayya ce tayi masa mugun kamun da bai zata ba
"Su anwar manya,ashe an fada tarko" dariya yayi yana shafa kansa
"Anty,shahida ta dabance,na soma sonta a sanda babu tsarin soyayya a rayuwata gaba daya,tana da hankali da kamun kai yarinyar,anty koke na kawowa shahida kika ganta zaki sota,fatana kawai Allah ya dubeni dana kammala karatun nan na samu aiki,na kula dake anty na kuma samu damar auren shahida" damuwar qaninta tata ce,su biyu suka ragewa juna a duniya,anwar irin mutanen nan ne jajurtattu,duk da bashi dashi,duk da shima neman dafawar wani yake amma indai ya samu ko yaya samun yake saiya tuna da ita,akwai sabo sosai a tsakaninsu,ba wanda ke iya boyewa wani wani abun,sun zama iyayen juna abokan shawarar juna
"Kullum fatana kenan anwar,ina maka addu'ar wahalar da kakesha a rayuwarka ta zame maka alkhairi dajin dadin da har iyayenmu dake kwance a kabari xasu ji dadinsa"
"Allah ya amsa anty"
"Yanzu ya ake ciki da kudin resgistratin dinka?" Ta fada bayan ta aje masa shinkafa kwano guda da wake rabin kwano,wanda aduk sanda ta samu budi take bashi ya samu ya sauya kalar cimar da yake ci,duk da itama ahalin ni 'yasun take,amma haka suke raba wuya da dadi tare,kamar yadda idan shi dinne ma hakanne,duk da yana qoqarin boye mata wasu abubuwa da dama amma takan fuskanci wani abun koda bai gaya mata ba da bakinsa
"Muci gaba da addu'a,in sha Allahu kafin sannan Allah zai kawo"
"Allah ya dafa mana don isar annabi"
"S A W" ya qarasa mata,daga haka ya miqe,saita kwance bakin zaninta,yasan me take da nufin yi saboda haka ya dakatar da ita
"Ina da hamsin dina da zan hau mota,bar kudinki" kai ta daga tana kallonshi,tanason karanto gaskiyarsa ko akasin haka,don ya saba gaya mata haka,qarshe kuma dabawa yake a qafa har gida duk da tazarar dake tsakaninsu saboda bashi dako sisi,ganin haka saiya juya da sauri yana mata sallama,bai tsaya saurarenta ba ya fice.

Yana tafe a hanya tunani fal ranshi,shi daya idanunsa sun kada sunyi ja,fatansa da addu'arsa Allah ya bashi abinda zai sakawa anty usaina dashi,tunanin shahida daya fado masa a rai shiya dauke duk wani radadi dake ransa,har ya murmusa shi kadai ba tare daya san ma yayi hakan ba,ya dinga tuna wuninsu na yau,yana zaune daga shagon balarabe kamar yadda ya saba yana more kallonta,lokaci lokaci sukan hada ido su sakarwa juna murmushi,wani kallo da yayi mata ya sanya man abincin dake hannunta ya kware duka cikin botikin shinkafar,kunya ta kamata yayin dashi kuma ya dinga mata dariya,har a hanyar komawarsu gida ya dinga tsokanarta kan ashe raguwa ce ita bai sani ba?,anya idan anyi aure zata iya dauke soyayyarsa kuwa?,kunya ta sakata guduwa ta barshi da botikin,sai mubina ce ta shigo dashi,wannan tunanin na shahida shi ya hanashi jin nisan tafiyar,har ya iso gida,sai yaji kamar baiyi tafiyar komai ba,bai zauna ba ya kunna risho dinsa ya dora shinkafar,sannan ya tube kayanshi ya shiga wanka saboda idan ya fito yaji dadin duba karatun jarrabawarsa.

Cikin wasu 'yan qididdigaggun kwanaki qalilan wata iriyar alaqar soyayya mai qarfi ta qullu tsakanin shahida da anwar,wata iriyar soyayya mai ban mamaki da daure kai,zaka rantse da Allah sun doshi shekaru masu tsayi tare,kowannansu yayi amanna da d'an uwanshi,kowanne ya yarda cewa rayuwarshi ta d'an uwanshi ce,baqincikin dan uwanshi nasa ne haka farincikinsa,wuya da dad'i basujin zasu iya rabasu,qaddara kuwa sun jima dayi mata magiyar kada ta shiga tsakaninsu,komai nasu ya zama iri guda,tunanin da wannan yake a mafi yawancin lokutta zaku samu irinsa dan uwanshi yake,tamkar tare aka haliccesu haka sukeji,tamkar zuciya daya aka halitta musu su biyun kowanne bari daya na cikin jikinsa na aiki,anwar kullum kwanan duniya shike rakota gida,bayajin an halicci wani uzuri a duniya da zai iya hanashi rakota gida,yakan xauna a rumfar balarabe yana hangota cike da kishi,duk wani motsinta yana kan idanunshi,baya samun nutsuwa ko sukuni har sai ta kammala ya tattara mata kayanta ya kaita gida,da ace yana da iko da tuni ya hanata zuwa wajen,kishi yakanyi kamar xai halakashi duk sanda take zaune tana rabon abincin,daga bisanima da yaji bazai iya jurewa ba shike amsa ya zubawa kowa,itama a nata bangaren tanajin shine karsashinta,duk motsi d'aya idan zatayi saita daga kai ta kalli qwayar idanunshi take samun salama,tana jinsa har cikin jini da jijiyarta,zata iya sadaukar da komai dominshi,saidai tana mamakin yadda ko sau d'aya bai taba zuwa ya karbi abincin da take rabawar ba kamar yadda sauran mutane ke amsa.

Bangare guda kuma bai taba gaya mata yanayin wahalar rayuwar da yake fuskanta ba,tadai san cewa bamai qarfi bane,hakanan yanayinsa ya tabbatar mata da cewa shi din mai wadatar zuci ne,don bata taba jin wani qorafi daga bakinsa ba,ko nunawa kasawa ko gajiya a fuska da jikinsa ba gaba daya,hakan kuma ya sake burgeta dashi,ya kuma sake saka mata qaunarsa.
Chapter 10 · 0% Book details