← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 73

Sashe 50

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daidai lokacin da motarsa ke tsaye qofar gidan anty usaina wadda ta buqaci ganinsa a yau basai gobe ba,yana zaune cikin motar baikai ga yiwa mai gadi horn ba bare ya bude masa,ya tsaya ne amsa waya,dukka gilasansa a rufe suke ruf kamar yadda al'adarsa take yawanci idan yana cikin mota,bugu da qari kuma ma sabida iskar dayaga ta taso sosai,wanda yasan ba za'a rasa qura ba cikinta,gefansa ya kalla kamar wanda aka fisgi hankalinsa,sai yaga kaman itace ta wuce,yaci gaba da amsa wayar yana kallon bayanta,tabbas ita dince,amma me take har war haka duhun magariba ya mamaye gari bata koma gida ba,idanunsa suka ci gaba da kallonta har lokacin data dan bada tazara daga inda yake,yana shirin janye idanunsa yaga yayyafi ya soma sauka ta gilashin motarsa,yaso ya dake yaso ya dauke kai ya saka motarsa cikin gidan anty usaina amma saiyaji kaman umarni,a zafafe yace
"Oh god" yana zare belt din jikinsa,cikin zafin nama da kuma jin haushin kansa da kansa ya bude murfin motar ya fice.

Yana kuzari da halittar ba daya bace,hakan ya sanya cikin qididdgaggun taku ya cimmata
"Daga ina kike haka?" A nutse ta waiwayo tana dubansa sanda take gab da qarasa bakin titi,saita juya da niyyar ci gaba da takawa ba tare data amsa shi ba
"Wai sanda zaki fita ma kin tambayeni ne?,saboda tsabar rinton zunubi?" Kalaman sun mata ciwo,wato tun yanzu yake nufin xai mulkata kenan?,hakan yasa ta tsaida tafiyar tata ta juyo ta dubeshi
"Kai waye da don zan fita saina tambayeka?"
"Kinfi kowa sanin ni waye ai ba buqatar na maimaita miki,banason dogon zance wuce muje na taimaka miki na saukeki,amma kafin sannan idan kina da niqab ki saka a fuskarki kar mutanen unguwa su ganmu tare su zaci nima dan harka ne" ya kai qarshen zancan yana dage girarsa duka biyun,wanda hakan ya masa kyau ainun duk da fuskarshi a murtuke take,sosai kalaman suka fusatata wanda hakan ya sanyata ta juyo gaba daya ta watsa masa idanunta da suka sake budewa saboda bacin rai,hakan ya tilasta masa dan qanqance nashi idanun gami da damqe hannayensa dake zube a aljihu
"To hell with your taimako...Allah suturu buqui,har abada bana son taimakonka,sannan kuma aikin banza kake harara a duhu,da kake gudun kar a ganmu tare me ya kaika neman dauramin igiyarka,idan da gaske kake qyamata aiya kamata ka gujeni da gaske ta yadda ko qasa daya ba zaka hada dani ba bare inuwa daya,indai ka cika kai anwar ne ka aikata hakan" qaramin murmushi ya saki daya sake fitar da kyansa,ya dage dukka kafadunsa
"Ba zaki taba samun yadda kikeso ba,niba qaramin yaro bane bare kalamanki su tunzurani nayi miki yadda kikeso,abu daya kawai na sani shine,na riga dana biya sadakinki,saboda haka ina da power a kanki ko kinqi ko kinso...saboda haka ki wuce muje" dogon tsaki taja wanda ya ratsa kunnuwansa,sannan ta watsa masa harara ta juya taci gaba da tafiya,bai fasa binta ba shima har suka isa titi.

Adaidaitan farko data tsaida ya sallameshi da dubu daya yace yane abinsa,na biyu ma haka,na uku kuwa da yame dattijone yace masa baba kaje matata ce yaji takeson yi,na bata haquri taki haqura,nan yasa bawan Allahn ya tsaya yana mata nasiha,inda daga qarshe ya sallameshi da dubu uku ya amsa yana godiya,ta hudu kuwa ya samu sauayi maiji da tashen girma yaso masa gardama.kan saiya dauketa tunda itama tana son shiga
"Kana sha'awar xaman gidan kaso kenan?" Harya karkata baki zai masa diban albarka saiya nutsu ya qarewa shigarsa kallo,tun daga takalminsa,kayan jikinsa zuwa agogonsa,aibabu shiri yaja abun hawansa ya fece,bacin rai ya taru ya rufeta ruf sanda ta kalli titin ta ganshi fayau ba wani sauran abun hawa na haya kuma nan kusa,ta waiwayo zata gasa masa magana ko xataji sanyi,kadan ya rage fuskarsu ta gwaru,sam batasan yana bayanta ba a tsaye,da alama kuma duk tsahon lokacin kallonta yake,baya yaja yana bata fuska
"Ke baki da kunya ne?,akan titi kike neman ki rungumeni?,toki maida qwalamarki,ni ba naki bane" kawai saita fashe da kuka ba tare data shirya ba,saboda ya gama cutarta,bata ga wani kalma da zata fada masa ba wadda zata rama abinda ya gaya mata,minti biyu kacal ruwan sama ya soma sauka,ya kalli sama sannan ya kalleta
"A karo na qarshe nake gaya miki ki wuce mu tafi" baya taja saman wasu tayoyi da masu faci suka tashi suka barsu a wajen ta zauna,ta gwammace ruwan yayi mata koma meye data bishi kota shiga motarshi,ganin ta zauna dafa'an ya sanyashi juyawa ya koma cikin layin don dauko motartashi zuwa nan bakin titin dukda yadda ruwa yake dukansa.

Yana isowa wajen yaga tashinta cikin adaidaita sahu,qaramin murmushi ya sube masa,wato dama tana da taurin kai kenan?,saiya sake baiwa motar wuta harsai daya je daya side din na adaidaitan,ya tabbatar ta ganshi sannan ya barsu suka wuceshi,a baya yaci gaba da binsu har xuwa sanda yaga shigarta gida sannan ya karya kan motar ya koma gidan anty usaina.

Sanda ta shiga gida baqinciki da takaici ya sake cikata ganin yadda gidan har baqi yadan samu,hakanan ga kayan amsar lefe a kammale gobe kawai suke jira,hasina ma ba'a barta a baya ba,ganun zata saka mata ciwon kai da tsokanarta yasa tayi zarcewarta daki ko tsayawa a wajen batayi ba bare ta zauna,gaban mudubinta ta tsaya tana kallon yadda ta jiqe gaba dayanta,haushinsa ya sake cikata,taji kaman ta sake fashewa da wani kukan,duk shi yaja mata,da ta shiga adaidatan a lokacin daya dace da duk hakan bata faru da ita ba,haka ta ringa cire kayanta daya bayan daya ta daura babban towel ta shige bandakinta ta hada ruwa mai zafi tayi wanka. https://youtu.be/alR4jOvvQUc

*Alqawarin Allah*
3️⃣3️⃣

Washegari da wuri tabar gidan fiye da yadda ta saba fita,ko a kamfaninma masu gadi kawai ta taras,ta bude office dinta ta shiga ta zaun donko mai maita shara ma bata iso ba.

Sanda aka tashi ta tsaya tunanin inda zata,don tasan wala'alla dai dai lokacinne ma gidan yake a cike,yankewa kawai tayi ta tafi gidan oga rayyan,ba bata lokaci ta gayawa mai adaidaitanta ya wuce can da ita.

Sosai taji dadin zuwa gidan,a rayuwa gidan yana burgeta qwarai,yanayin mu'amalar jama'an gidan,nan wajen raihana ta zauna suka sha hira sosai,sai bayan sallar magariba sannan tayi haramar tafiya,nan ta cikata da turaruka tana cewa
"Gashi amarya,naji oga yace kin kusa shiga daga ciki,ki fara amfani da wadan nan kafin lokacin xan kawo miki na amare"
"Hmmm" kawai tace tana dan fitar da murmushin da baikai zuci ba daga fuskarta.

Tun daga harabar gidan zaka san cewa ansha baqi a gidan,bata yarda tabi ta qofar falo ba saita bi ta qofar baya tayi shigewarta dakinta,kayan hannunta ta aje ta rage kayan jikinta ta shiga wanka,bayan ta fito ta murza manta mai qamshi ta saka riga mara nauyi,ta ciro wayarta daga jaka kenan taga miscal din zunnurah,sai fuskarta ta washe da fara'a,ba bata lokaci tabi kiran,bugu biyu ta daga,abu na farko data fara shine guda ta sakar mata,bacin rai ya bijirowa shahidan,wato kiranta tayi donta tsokaneta kenan?,sai kawai ta yanke kiran,ta nufi gadonta ta hau ta kwanta rub da ciki tana lumshe idanunta,dai dai nan hasina ta turo qofar
"Au yaushe kika shigo?" Banza tayi da ita kamar bata ji ba,hakanan taqi bude idanunta,don tasan qarshenta itama tention xata qara mata kawai
"Shahida" hasina ta sake fada tana matsowa dab da gadon,ta dora hannunta saman filon tadan daka,sai a sannan ta ware idanunta tana dubanta
"Bacci nakeji,don Allah ki barni na huta" murmushi hasina ta saki
"Amma na miki jaje da zaki kwana bakiga kayanki ba wallahi,kallo ya barki" qur ta mata da idanu kafin taja qaramin tsaki ta maida kanta daya barin tana rufe idanunta,dariya ta sheqe sosai da ita sannan ta juya ta fice tana waqar amarya.

Da sauri ta diro daga saman gadon ta isa bakin qofar ta saka key ta kulle sannan ta sake dawowa ta kwanta,tana gyara kwanciyar tata tana mita ita daya gami da jan tsaki lokaci lokaci,rigingine ta kwanta tana kallon roofing din dakin,idanunta a kulle gam tanason tilasta kanta tayi bacci.

Haka aka dinga mata knocking tana ji ta share,donko hasina yau saidai ta kwana wani dakin amma ba nata ba,kadaitaka kawai yau take da buqata.

Sai sha daya da wani abu na dare sannan bacci ya soma fisgarta,qarar wayarta yasa ta bude idanunta ahankali kan wayar dake aje saman cikinta,ta daga wayar tana dubawa,lambace babu suna,kaman ba zata daga ba sai kuma ta daga kana ta kara a kunneta gamida yin sallama,can qasa taji an amsa sallamar har bata tantance muryar waye,shuru ya ratsa da wasu sakanni
"Nuradden" ta canki sunan
"Shahida,na rasa ta ina zan fara koyawa kaina haquri dake" idanunta ta lumshe tana jin bacin rai na ratsata
"Kayi haquri noradden,duk ni na jawo mana komai,da ace banyi jinkirin hanaka zuwa gidanmu ba da guni hakan duka bata faru ba"
"Ki tayani addu'a kawai,Allah ya yayemin,don ba lallai bane na daina sonki" daga haka wayar ta katse,a sanyaye ta ajiye wayar ta mirgina daya barin nata,harga Allah bata tausayin kanta kamar yadda take tausayin nuradden din,ya riga ya fada da yawa,ta kuma son ciwo da radadin soyayya,musamman a sanda ka rasa abinda kake tsananin so ka kuma saka ranka dashi,a hankali kalamanshi suka fado mata,baya neman yaradarta,bata cancani ta rayu cikin farinciki ba ta zabi wanda takeso,zai aureta ne don ya nuna mata ya isa,lebanta na qasa ta cije tana rarrabe maganar da abinda yake nufi,auren manufa zaiyi da ita kenan?,zaiyi ne don cimma wani boyayyen nufi nashi?,lallai zata nuna masa yayi ganganci,akwai banbanci tsakanin da da yanzu,ta jima ahaka tana saqa abubuwa da yawa tare da tunawa da al'amura masu yawa kafin bacci yayi nasarar saceta.
Chapter 50 · 0% Book details