Sashe 24
Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin qaramin lokaci taji anwar din ya wanke mata a rai tas,ya sire mata,ya fice mata daga ruhinta,taji zata iya rayuwa babu shi,taji abune mai sauqi hakan,saidai baizo mata da sauqi ba yadda ta tsammata,ta share darare da yawa bata samu bacci ba,ta ga wuninnika da darare masu tsaho da tsauri cikin rayuwarta a wannan lokaci,ta cika bangon dakinta da shafukan littafanta ta kalaman qarfafa kai da qarfafa gwiwa akaran kanta,ta siya littafi tayi rubutu mai tsaho da yawa kan rayuwarta har kawo bigiren da yau take kai,ta tattara duk wani abu da zai iya tuna mata da anwar ta ajesu waje daya,ta shiga tsara yadda rayuwarta zata kasance nan gaba,tun saga lokacin ko masoya ta gani sai taji tana tausayinsu,musamman mace idan taga ta zura jiki da yawa.
Bayan umma ta fita takaba uncle hisham shi ya karbi ragamar daidaita musu duka al'amuran gidan,sannan suka yanke shawara dashi shahida zata koma hannun anty zubaidan,tunda har yanzu bata gama daidaita ba,saidai cikin kaso dari an samu sauyi na kaso shida,rabata da unguwar da duk wani tsohon memory dinta zai sake taimakawa wajen saita tunaninta,da wannan suka dauke shahidan ta koma wajensu.
Makarantu daban daban anty zubaida ta sakata wanda zata qaru ta fanni da dama,wasu na koyon harshen larabci wani na koyon turanci bawai don bata iya ba,a'ah saidon ta maidata busy sosai wanda hakan zai sanya bata da lokacin zama ma ta tuna wani abu mara dadi daya faru da ita a baya,tayi hakanne kuma kafin wata shekarar ta zagayo su nema nata admission saboda wannan shekarar ta qwace mata.
Rayuwarta ta soma samun sauye sauye,kullum kwanan duniya saitayi kukan dabi'ar shaye shaye data ta taba tsintar kanta a ciki,kullum sai tayi nadamar sanin fiddausi a rayuwarta,sai tayi nadamar sakin jiki ga duk qawar data kutso rayuwarki sama taka,abune mak wahala da idan ka sake ka jefa kanka da wuya ya fice daga rayuwarka salin alin ba tare daya haifar maka da nadama da danasani ba,bai kuma bar maka qatoton tabo ko baqin fenti a rayuwarka ba,ta godewa Allah da yayi gaggawar fiddata tun batayi nisan da ba zata ji kira ba kamat yadda tagani ta kuma ji labari da yawa akan wasu,wanda ta shiga bincike ne akai bayan ita Allah ya tsamota,gefe daya kuwa yaqi take tuquru da kanta game da lamarin anwar,wata irin tsana da bata taba tunanin tanawa wani dan adam ba ita ke taso mata,duk wani abu da yayi mata da yadda ya dubu qwayar idanunta ya gaya mata magana,fiddota daga gidanshi da sauransu,uwa uba hotunan yarinyar da yake gaya mata ya sake ya sauyata a madadinta,kullum qoqarin goge duk wani tabo ko abun tunawa daya barwa rayuwarta take,tanason ta nuna masa ta kuma nunawa duniya she can survive without him,tana son watan watarana yaga cewa shi din ba komai bane da ba zata iya rayuwa babushi ba.
*Cikin rashin kunya murjewar ido dajin wannan karon dai dai take da kowa,zata iya karawa da kowa,a shirya take ta rabu da kowa saboda shi,bata jin akwai abinda ya isa yayi mata hijabi tsakaninta dashi,koda waye,koda mahaifiyarta data haifeta,koda mahaifinta da yayi silar zuwanta duniya*
*"Allah ya isa ban yafe ba duk wanda yayi silar rabani da Zamab,ko wayeshi bazan taba yafe masa ba wallahi, dan an haifeka ai ba halittarka akayi ba, kai ma babu wanda yayi maka auren dole, haka a addinance babu inda Allah yace ayiwa mace auren dole"*
*kalaman da suka fito kenan kai tsaye daga bakin Basmah zuwa ga mahaifinta Ya Mu'allim tana dubanshi kai tsaye ba kunya ko rusunawa*
_SAKI RESHE KENAN littafin da zaizo muku daga jarumarku haziqar marubuciya HAUWA A USMAN JIDDERH_
*WANNAN WACCE IRIYAR DIYACE HAKA?,ME YAKE FARUWA ME KUMA YA FARU?,DON JIN CI GABAN WANNAN LABARI DAKE QUNSHE DA BADAQALA,SAKIN RESHE DA SAGEGEDUWA ZAKA BIYA NAIRA 300 KACAL TA WANNAN HANYA,BA TARE DA BATA LOKACI BA ZA'A SADAKA DA WAJEN DA ZAKA SAMU NAKA*
Hauwa Auwal Usman
GT bank
015325259310
*saiki tura shaidar biya zuwa ga wannan number*
07020489340
*katin waya kuma xaku tura 300 ta watsapp ta wannan number*
07020489340
_kar ayi babu ke,maza garzaya ki nemi naki_🏃🏾♀️🏃🏾♀️🏃🏾♀️🏃🏾♀️🏃🏾♀️ https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos
*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karkiyi sharing,idan kina da buqata ki tuntubi wadan nan numbers din*
07067124863
*ko kuma*
09032345899
*Alqawarin Allah*
1️⃣7️⃣
Daga gefan anwar kuwa yaso barin garin ne gaba daya,saboda yadda garin yayi kishi zafi,yaji ya tsani komai,bashi buqatar duk wani abu daya sani,yana buqatar baqon muhalli,anty husaina ce ta kafe kai da fata kan bata yarda ba,ganin yadda ya dage kan son tafiya din ta sakar masa kuka,wanda ya sanya dole ya haqura shima yaci gaba da zaman.
A wannan lokacin da nafisa taga dama tazo mata,taso ta gabatarwa da anwar kanta ne gaba gadi,taso anwar ya dawo cikin gidansu da zama qarqashin abbanta,ya bashi gida mota da kuma jari suyi aurensu,saidai yadda labari da halayyar anwar tazo mata ta tabbatar da cewa aikata hakan babban kuskure ne da zai janyo kwabarta tayi ruwa,wanda daga qarshe suka gama shawara da mima kan yadda zasuyi.
Alhaji abba kabara mahaifin nafisa mutum ne mai yawan taimako da samawa matasa ayyukan yi,yana da kamfanoni hakanan yana da shagunan da yake sanya matasa a ciki,duk matashin da yayu shekara guda riqe da amanar shagon ba tare da an taba kuka dashi ba alhj abba yakanyi masa kyakkyawar sallama ta hanyar bashi jari mai tsoka,wani lokaci ma bai duba da abunda aka samu a shekarar,zamanka a shagon iya karantarshi da amanarka kawai ya nuna idan ya baka jarin ba zasu salwanta ba,wasunsu kuma yakan daukesu ne ya kaisu kamfaninshi,musamman masu takardun makaranta,dalili kenan sanya sanya ta samu abban nata
"Uhmm...ya akayi nafi?" Cikin nuna yanayi najin kunya tadan sadda kanta
"Abba dama...dama" sai tayi shuru
"Dama me?" Ya tambayeta yana sauke medical glass dinsa
"Akwai wani marayan matashi ne,abba yana da amana da duk halayen qwarai,ya kammala karatunsa baida aiki,abba yana shan wuyar rayuwa sanadiyyar haka,idan na masa magana abba da kaina bazai karbi duk wani abu ba,amma idan kaine da kanka abba zaifi amsar duk wani taimako" shuru ya danyi yana nazarinta
"A ina ke kika sanshi?"
"Abba...a unguwarsu qawata yake,ita take bani labarinsa,na tabbatar zaka yaba da halayenshi hakanan zaka tabbatar daya cancanci taimako" kai yake gyadawa sannan yace
"Ba damuwa,ki turamin adress dinshi,zamu fidda sanarwar daukan ma'aikata a kamfanina zansa a duba takardunshi sosai"
"To Abba Allah ya qara budi" amin ya fadi yana daukar jaridarsa yaci gaba da dubawa,yayin da nafisan ta fita cikin farinciki da walwala.
Randa aka kira anwar aka shaida masa sunan kamfanin da sukeso duba takardunsa yayi mamaki qwarai,don iya yawon neman aikinsa bai taba bi koda ta titin da kamfanin yake ba,don bai taba sama ranshi cewa zasu daukeshi aiki ba.
Qarfe taran safe na ranar da zaije kamfanin ya gama shirinsa ya fito yana kulle gidan yaga mota tsaye a qofar gidan,horn aka danna mishi kana aka jawo motar zuwa gabanshi
"Daga kamfanin alhj abba ne akace muzo mu daukeka" ya kalli motar sosai yaga tambarin kamfani jiki,hakan ya sanya ba musu ya bishi suka shiga.
Sam bai kula da itaba ashe tana zaune a bayan,sai daya waiwaya suka hada idanu ta sakar masa murmushi,sam bai ganeta ba,ita ta soma gaidashi sannan ta gabatar mishi da kanta a matsayin diyar alhj abba,mamaki day ayayi na wanne matsayine dashi da har za'azo har qofar gida a daukeshi cikin motar kamfani shi da za'a yiwa alfarmar bashi aiki,bashi da amsar wannan saboda haka shuru shi yafi masa,yana jin nafisan na bashi labarin abubuwan da suka shafi kamfanin kamar ma an daukeshi aikin ne,shidai nashi kunne ne,don yanzu baya ga anty husaina baya jin dadin hira da kowacce diya mace,hasalima bayaso su rabeshi.
Bisa jagoranci da shigewar gaban nafisa ya gama komai cikin kamfanin,aka kuma bashi babban gurbi wanda ko a mafarki bai taba tsammata ba,koda wasa bata nuna ita ta roqa masa wannan alfarmar ba saboda tasan ba wani abu bane cikin aikinsa yaqi amsar aikin gaba daya.
Lokaci kadan da fara aikinsa alhj abba ya tabbatar da duk maganar da nafisa ta fadi a kansa,yana da gaskiya yana da amana,hakanan yana da aiki tuquru,baya taba saba lokacin zuwa kamfani hakanan lokacin tashi,gwara ma lokacin tashin idan akwai wani aikin da kamfani zaici gaba yakan sarayar da lokacin nashi ya gabatar dashi,dalilin kenan daya sanya alhj abba da kanshi ya danqawa anwar qaramar motar hawa mai azabar kyau da tsada irin wadda bai kawo zai mallaketa ba nan kusa,sannan ya nemi daya dawo cikin gidanshi da zama,wanna ne kuma ya bawa alhjin haquri,saboda yadda nafisa ke shishshige masa sam baya masa dadi,yana karanta mata ne da daga mata qafa kawai saboda girma da darajar mahaifinta,motat ta sauqaqa masa sauran ayyuka da zuwanshi ma kamfani gaba daya,hakanan ya dinga barin motar a wani garage dake farkon layinsu wanda masu abun hawan da basu da muhallin ajesu suke ajewa a nan su biya wani abu ladan ajiyan.
A sannan rayuwa ta soma mishi kyau,koma ya soma canzawa,kama daga sutura cima da sauransu,anty husaina ma kanta canji ya soma zuwa mata,a wannan lokacinne nafisa ta kasa shanye halin ko in kula da anwar ke nuna mata,duk wata alama da ake nunawa mutum ya gane ana sonshi ta nuna mishi amma a banza wai an mintsini kakkausa,hakan ya sanya tayi qundunbala taci alwashin sanar mishi wata rana da abbanta ya gayyatoshi cin abincin dare gidan.