Sashe 36
Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sanda ya turo qofar lokacin saddam ya miqe yana fadin
"Bari na samo miki wani abun,na fuskanci kaman yunwa kike ji" bata iya amsa mishi ba yayin da sukayu clashing da nuradden sanda yake shigowa,suka kalli juna saddam ya sanya kai ya fice nuradden ya bishi da kallo,sai daya bace masa sannan ya dauke idanunshi ya qaraso yana rufe office din idanunshi a kanta
"Waye wannan din?" Ya tambayeta kai tsaye,tasan akan wa yake tambaya saita saki murmushi
"Abokin aiki,aiki muka gama dashi yanxu" dan shuru yayi kishi na cinsa,ji yayi kaman ya maqure saddam din sabida ya karanci irin kallon da yakewa saddam din shima irinsa yake masa,kansa kawai ya jinjina yana qarasowa
"Kin kashe wayarki kin tsammaci bazan iya laluboki ba duk inda kika shiga ko?" Boye dariyarta tayi,batasan ya dagota ba
"A'ah,kasan idan ina aiki banason yawan amsa waya,dalili kenan daya sanyani na kashe" inda ta tashi ya koma ya zauna yana kallon office din nata,kaman yadda ya saba burge jama'a shima ya burgeshi sosai
"Sannunka da zuwa" saiya kalleta
"Allah yasa har zuci" qaramar dariya ta saki
"Da ba har zuci ba da tunu na koreka ai" maimakon ya amsa saiya jefo mata wata tambayar
"Wanne babban baqo haka kukayi a companynku yau?" Dan tunani tayi kadan sannan tace
"Gaskiya ban sani ba,saboda ba bangarena bane" kishi yakeji sosai da fargabar kar shahidan ta subuce masa saiya sanya idanunsa cikin nata sanda take za a wata kujerar da take kallon tashi
"Haka manyan mutane ke zuwa wajenku?" Kafada ta dage
"Wajensu dai,abune mawuyaci ni nasan zuwansu ko fitarsu,tubda ba sashe na bane saidai idan wata matsala da buqatar zuwa wajena ya zama dole"
"Ina kishinki shahida" cak ta tsaya tana kallonsa,kalamansu sunyi shigen kama dana juna,ya tuna mata dashi dole saboda yanayin yadda yayi furucin,hakan ya sanya ta miqe kawai ba tare data samu abun fada ba
"Kinsan sonki yake?" Ya jefa mata tambayar sanda take bakin dan qaramin fridge dinta tana ciro masa ruwa da lemo,saita waiwayo tana dubanshi,murmushi ya qwace mata
"Wani abu makamancin haka bai taba shiga tsakanina dashi ba,kar ka saka komai a ranka,kai kanka shaida ne na wace shahida,abu mai sauqi ne samun hanya zuwa zuciyata kai tsaye har haka?" Maganar tata ta bashi qwarin gwiwa,sai yayi shuru yana nazarinta,harta dawo ta aje masa lemon da ruwan a gabanshi,yayin dashi kuma ya dire mata ledar daya shigo da ita
"Ga abinci nan,inajin kamar kina da buqatarsa shi yasa dana tsaya naci nayo miki naki takeway din,don nasan ko xuwa nayi nace kizo muje muci taren ba zuwa zaki ba" ya fada cikin jefanta da magana,tasan yana jin haushin hakan,ita kuma ra'ayine sam bata dashi,sabida haka tayi murmushi kawai,ko yanzun ma ba zata iya cin abinci yana kallonta ba shina ya sani,amma duk da haka saiya soma bude mata ledar yana cewa
"Kiyi haquri yau dai daya kici a gabana,saimu tattauna abinda ya kawonin,kada lokacin break dinki ya qare na shiga haqqin company",bai gama budewa aka sake bude qofar aka shigo,dukansu suka maida hankali ga qofar,saddam ne hannunshi dauke da ledar gidan abincin dake daura dasu,wanda shahida tafi order abinci acan,fuskarsa cike da murmushi ya nufosu kai tsaye ba tare daya dubi nuradden ba ya iso gabanta,dora abincin yayi saman na nuradden daya bude mata yace
"ga favourite dinki nan", wani abu ne ya takorewa nuradden wuya,ya daga kai ya kalli saddam cikin fushi
"Wanne irin rashin hankaline malam?" Dubansa saddam yayi
"Da akayi me?"
"Ta yaya zaka shigo kai tsaye ba tare daka nemi izni ba,sannan ka samemu zaune zata ci abinci ka dora wata ledar a sama?" A dage saddam yace
"Matarka ce?"
"Koba matata bace ina zaton tare ka ganmu" cikin halin ko in kula yace
"Auto da sauqi abun,kaga kenan allurar cikin ruwa ce,mai rabo ka dauka" ran nuradden saiya kai qololuwar baci,hakan ya sanya shahida ta dubi saddam
"Banason tashin hankali saddam,meye haka?" Baison nuradden ya gane cewa bai taba furta mata kalmar soba bare ya sake samun qwarin gwiwa,hakan ya sanya ya dubeta
"Ba manufata na bata miki rai ba,sai anjima" ya juya ya fice.
Sosai yake jin babu dadi cikin ranshi,saiya dubi shahidan
"Shahida...tsorona da fargabata ta sake daduwa,inajin har cikin raina bani da tabbas idan har baki amsa min cewa ni kikeso ba kuma ni xaki aura ba" gaba daya sai lissafinta ya nemi dagulewa,batason ta dauki alqawarin da zai zame mata ciwo ko nauyin da wuya ta zaiyi wahala ya iya dauka,saboda haka cikin sanyin murya da kwantar dakai tace
"Tsoron meye haka nuradden,ka kwantar da hankalinka don Allah".
Duban nafisan yayi fuskarshi a hade" me kikayi haka kenan?,me yasa tun farko baki duba lafiyar atm din naki ba saida kika gama siyayyar?,bayan kinsan accnt din aya samu matsala sai xuwa gobe zai soma aiki?"langabe mishi kai tayi
"Please anwar...don Allah kayi magana da mai kamfanin gaba daya,na tabbatar ka sanshi tunda naji kace bakason yasan ka shigo kamfanin,tunda ka bada rabin kudin yanzu zai amince ka aiko da saura idan ka koma office,Allah wannan sarqar nasha wahala na dade ina nemanta,kuma kanaji suma sukace dsign dinta kadai yayi saura,ba lallai idan na ajeta naje na dawo na sameta" idanunsa ya lumshe kaman bazaice komai ba,haka kawai yakejin kasala tunda ya tashi yau,hakanan zuciyarsa da jikinsa sam babu dadi,baice komai din ba ya fita daga wajen da kanshi ya taka zuwa sashen biyan kudi,suka tarbeshi don tunda ya shigo kamfanin suka gane waye,hakan ya sanya suketa nan nan dashi,daya daga cikin ma'iakatan ya yiwa magana yana son ganin rayyan
"Ranka ya dade,oga bai shigo ba,amma babu damuwa zaka iya ganin rahama" dan shuru ya sake yana fidda wayarsa daga aljihunsa ya duba lokaci,sannan ya lalubo wata number ya kira,bata shiga ba,duka lambobin rayyan din basa tafiya,saiya sake kiran wata number din,ba jimawa aka daga,ya ambaci adadin kudin da yake buqata ya gaya masa inda zai kawo masa
"In sha Allah yallabai ina hanya" daga haka ya maida wayar aljihunsa
"Ai...ranka ya dade basai ka zauna jira ba,rahaman kawai zaka yiwa bayani shikenan zata shigar ne cikin kundin bayanan shiga da fitar kudi na kamfanin" lokaci ya kuma dubawa,shi kansa baison zaman,saboda jiransa da ake,banda ya riga da yayiwa nafisan alqawari kuma baison rashin cika alqawari da baiga abinda zai zaunar dashi har haka ba
"Ba damuwa,bani number din office din"
"To ranka ya dade" ya fada yana gaya mishi cikin sauri kai tsaye ba tare da an sanar da mai office din ba saboda sanin wayeshi baida buqatar sai sun hadashi da mai masa iso,a nutse ya juya ya soma takawa
"Ina zaka?" Nafisa dake addu'ar Allah yasa su gama lafiya su fita lpy karya hutsance mata ta tambaya
"Ki jirani" kawai ya fada yanayin gaba.
Kallon number office din yayi sosai sannan yaja da baya ya kalli qofar,ya dora hannunshi saman handle din ya tura a hankali wanda hakan ya sanya basuji alamun bude qofar ba. *zafafa biyar na kudine,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina da buqata ki tuntubi wannan number*
07067124863
*ko kuma*
09032345899
*Alqawarin Allah*
2️⃣4️⃣
"Hankalina bazai taba kwanciya ba idan ba ganinki nayi a gidana a matsayin matata ba...shahida" ya kira sunanta yana miqewa zuwa gabanta,gab da ita ya zauna akwai kusanci sosai tsakaninsu,tanason sake ja baya ta kasa,ya saka hannunshi cikin aljihunsa ya ciro zoben rannan daya siya ya bata tabar masa abinsa cikin mota,ya bude gidan xoben ya ciroshi
"Ki yarda mu qulla wanna yarjejeniyar tsakanina dake yanzu yanzu shahida,ita kadaice zata dan kwantar min da hankalina" bata ankara ba ya kama yatsanta yana ci gaba da roqonta,wani abu anwar yaji ya dakar masa tsakiyar kai,yayu yunqurin juyawa ya fice daga office din salin alin kaman yadda ya shigo,saidai ya gagara haka,ji yayi kaman an kafeshi idanuwanshi a kansu,ya gaza daga qafarshi bare ya juya ya fita din,da hanzari shahida tace
"Sakemin yatsa nuradden...basai ka saka..." Bata qarasa kaiwa ba ya soma zura mata zoben,bansan ya akayi ba,baisan ta yaya ba ya tsinci kanshi da furta
"Stop it!" Cikin tsawa da hargagu,idanuwanshi na sauya kala,wanda yayi sanadiyyar rashin shigar zoben yatsanta,dukkansu waiwayawa sukayi don ganin waye,ga tsammanin nuradden saddam ne ya dawo,amma sai yaga bashi bane,matashin saurayi ne da shekarunsa suka tasamma talatin da biyar,mai kyau kwarjini da cikar zati tsaye yana dubansu,idanunshi qyar kan nuradden din,yayin da idanun shahida ke kanshi,mamaki yaso daskarar da qwaqwalwarta,me yake nan?,me ya kawoshi?,yazo ci mata mutunci ne?,koko yazo tozartata cikin mutane ne kaman yadda yayi mata wancan karon,anya ma shine kuwa?.
Idanunsa har yanzu nakan nuradden suna kallon kallon har zuwa sanda ya soma takowa zuwa cikin office din hannayensa soke a aljihunsa,cikin wata izza da taqama,qarfin gwiwa da qarfin halin da sam baisan yana nunashi ba muraran.