Sashe 73
Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
Ko data gama abinci iya ita da yaran suka zauna sukaci,bayan sun gama tasa suka kwashe suka kai mata kitchen zata wanke,tana tsaye a kitchen din ta soma dauraye kwanukan ya shigo,ta waiwaya ta dubeshi ta dubeshi sai kuma ta dauke kai tana ci gaba da wanke wankenta
"Ni ban taba ganin ango irin wannan ba,ba abokai ba komai,ka dawo gida ka samu waje ka zauna?" Take tadin ita da zuciyarta,wanda harya iso bayanta dab da ita bata sani ba,kallonta yake hakanan qirarta da shape dinta yake daukan hankalinsa fiye da qima,saiya dinga tuna baya can da bai taba ganin komai nata ba,saboda a sannan ma'abociyar sanya hijabi ce,a lokacin da yake cike da buri da fatan Allah ya bashi kudin da zai aureta ya mallaketa a matsayin matarsa,yanzu gata a matsayin matarsa,amma wani abu ya ma rayuwarsu karan tsaye,saiya kauda wannan tunanin yace
"Ni ba za'a bani abincin ba?" Gocewa tayi gefe jin maganarsa dab da ita,da alama tsaye yake kenan a bayanta
"Ban dafa dakai ba" ta amsa masa tana ci gaba da wanke farantan ba tare data juyo ta dubeshi ba,shuru yayi yana dubanta,bata taba hanashi abinci ba sai yau,sai baice komai ba ya matsa gefe kusa da inda tukwane suke,ya dauki daya ya dauraye ya ya tari ruwa a fanfon dake kusa da ita,ya hada kayan qamshi ya dora ruwan shayi,ya jingina da jikin kwabar kitchen din yana kallon ruwan yana jiran ya tafasa,duk abinda yake tana kallonshi ta gefen ido,ta rugashi gamawa don haka ta fita tabar masa kitchen din,suna falon yazo ya wucesu da ruwan shayin,harya soma hawa saman saiya waiwayo yana dubanta,hankalin yaran duka nakan arewa24 yace
"Banfa ji haushi ba,wanda ma aka dinga bani a baya Allah ya amfana ko?" Ya qarashe maganar yana daga mata gira,kauda kai tayi yadda ta saba kaman bata ganshi ba,yayin dashi kuma yaci gaba da hawa saman.
Da yammaci suka sake gyare gidan tsaf suka cikashi da qamshi tako ina,har turarukan da bata taba amfani dasu ba sai ranar,kama daga na labule carfet da wanda kebin iska,sun gama kenan sai gashi ya sauko cikin shadda brown sabuwar qarr,kyau uya kyau yayishi,sai taga kamar wannan shigar ta musammance,duk da dama shidin koda yaushe cikin saka sabbin sutura yake,hakanan taji wani abu ya tokareta sanda suka hada ido ya dage mata gira guda,saita aje pillow din hannunta ba tare data bari ya iso inda suke ba ta shige kitchen,tana jinshi da yaran suna uncle kayi kyau,ya gama dan hirarsu dasu ya fice daga gidan bayan ya dauki daya daga cikin motocinsa.