Sashe 52
Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gidansa ya soma isa ya bude sashensa ya shiga,ya aje kayan hannunsa,bandaki ya shiga ya tara ruwan wanka mai dumi ya sake wanka sannan ya nemi abinci yaci ya qoshi,wardrobe dinsa ya bude ya zabi kayan da yaje gani sun dace da irin wannan lokacin ya sanya,ya tsaya gaban mudubi yana taje kansa gami da kallon kansa yadda kayan suka amsheshi,tuna abinda ya faru tsakaninta da muhsin yayi,saki yaja,wato ita mai taurin kai ko?,har yau bata kallon laifinta sai wani take dorawa alhakin faruwar komai ba tare data duba nata laifin ba,aikawa yaso yi direct inda dole ta karba saqon,amma hkanan yaji yana son yaje yaga hawayenta ya takaleta ya kuma tsone zuciyarta,saiya aje cumb din yana daura agogon fata sannan ya zauna ya daura takalmansa ya feshe jikinsa da turare ya dauki key din motarsa ya fito.
A hankali yake tafiyar kaman bazaije ba,karon farko da zai fara zuwa gidan anty zubaida kenan,yadan yi nauyi a hanya hakan yasa bai isa ba sai qarfe shida mintina hamsin suka rage kenan a yi sallar magarib.
Maigadin gidan anty zubaida ne ya iso ya bashi hannu don suyi musabaha,cikin tantama yadanyi jim don yana ganin bai kamata suyi hannu da hannu ba
"Mu gaisa mana abokina,bakason ladar ne" da sauri ya miqa masa suka gaisa
"Inason magana da wata yarinya shahida a gidan nan ne" cikin washe baki yace
"Au,kaddai kaine angon?" Murmushi kawai yayi sannan ya sake cewa
"Idan ka shiga matar gidan zaka sanarwa zuwa na,sannan ka turomin faruqu ko haidar"
"Toh...toh" ya fada yana juyawa zuwa ciki.
Sanda saqon kiran ya sameta tana daki tana shiryawa bayan ta gama mitar wankan turaren da anty zubaida ta kafa nata dokarshi,turaren na nata dadi da qamshi amma tuna dalilin yinsa ke qona mata rai da dagula mata lissafi,tsaki taja sanda huda ta gaya mata ana kiranta,ta shiga mita
"Wai wanne irin kirane da baqi haka tun dazu ba za'a bar mutum ya huta ba?,haka kawai kana zaman zamanka daada ta tada zaune tsaye cak,ni wallahi na gaji da wadan nan abubuwan,daga wannan sai wancan?" A haka ta shirya ta zari hijabi ta fito
"Baqon na waje ai" anty zubaida tace da ita sanda taga ta tsaya ta mata turus,haka ta juya ta fita kaman zata fashe.
Faruq ta soma hangowa cikin dakin saukar baqi na gidan baki na motsi da alama hira yake zubawa,harara ta zabga masa duk da bai ganta ba,a haka ta isa ta yaye labulen,tare idanunsu suka sauka cikin na juna,yawun bakinta ya tsaya kowannensu na kallon dan uwanshi ba tare daya dauke ido ba,gani yayi kamar ba ita,fatarta ta sake sauyawa kyanta kaman an matso shi,qamshinta ya soma cika wajen,shima kwarjini taga yayi mata,shigar ta amsheshi,yayi kyau ya sake zama cikakken mutum da hankali da ilimi suka ratsashi,ita ta soma janye idanunta,ranta a hade tsaf ta taka zuwa ciki tana duban faruq,saiya miqe,anwar yace
"Zan nemeka kafin na wuce kada kayi nisa"
"To yaya" ya fada yana ficewa,sai da taga fitarsa sannan ta zauna hannun kujerar dake a dab da bakin qofar fita,tanason tsareshi da ido donta karanci me ya kawoshi amma batasan me yasa takejin rashin qwarin gwiwa ba,ta maida idanunta kan tafin hannunta tana murzawa ba tare data ce masa uffan ba,hakan ya bashi damar kafeta da ido,ya soma kallonta tun daga yatsan qafarta zuwa saman kanta,yana jin wasu tagwayen abubuwa na fada cikin zuciyarsa,daya nason yaqar daya gami da rinjayarsa,inda daga qarshe dayan yayi galaba,saiya runtse idanunsa yabar kallonta saboda wani bacin rai dakeson shaqeshi,kullum kwanan duniya yana son sasautawa kanshi,yana son ya daina ganin baqinta da baqin abinda ta aikata,yana son abinda idanunsa suka gane masa da hotunan daya gani su bace daga idanunsa ko zai samu salama da rangwame amma hakan ya faskara,sai komai yayi kaman zai goge saiya sake dawowa sabo fil a ransa.
Walwalar da yake jin kaman zata samu a ruhinsa ta dusashe,sauran faragar fuskarsa ta bace bat.
Zaman kurame ne yaci gaba da wanzuwa tsakaninsu harna tsahon wasu mintuna,sai daya gama zamanshi don kanshi sannan ya miqe,cikin wani taku ya isa dab da ita ya tsaya akanta,kana ya ranqwafa gefanta har tana iya jiyo qamshin ya aje envalope din hannunshi,ba tare daya dago ba yace mata
"Baki iya gaisuwa ba saikace a gidan mashaya inda kowa yake ogan kanshi,karki tsammaci xaki gidana da wannan dabi'ar ki tsira,ga saqon da muhsin ya kawo miki daxu kika maidashi nina dawo dashi,idan kin isa karkiyi amfani dashi yadda ya dace kiga yadda zata kaya mana nidake,tunda na fahimci cikin halayen da kika koyo kala daban daban harda taurin kai ko?,good....inason wannan sabon halin naki,idan kin tashi gayyatarki karki sake ki kwaso min tarkacen 'yan maye,ko tarkacen qazaman tsaffin samarinki" daga haka ya dago yana shirin wucewa zuciyarta taje iya wuya,ta kasa daurewa
"Idan ba haka bafa?,me zakayi?" Ta fada a tsiwace cikin fushi da fusata,saiya sake dawowa gabanta ya tsaya,ya dubeta na wasu mintuna sannan ya saki murmushi
"Ki aikata din sai kiga sakamakon" miqewa tsaye tana masa kallon tara saura kwata sannan tace dashi cikin salo na masifa dake cin zuciyarta
"Baka isa ka sakani abinda banyi niyya ba,baka isa komai ba idan ma kana tunin ka isa" murmushi ya sake saki wannan karon mai sauti,yadan buga qafarsa sannan yace
"Ko a haka aka tsaya ai inga irin tawa isar ko?,hukuncin da zan miki ba isata kawai zai nuna miki ba,izzar aure da izzar anwar namiji"
"Namiji shine zai tsaya takara da abokan adawarshi ya kuma samu nasara,ba wanda zai wafta koya biyo ta bayan gida ba,koya taka wani tsani don kaiwa wannan bigiren,ka daina batawa kanka lokaci wajen kiran kanka da namiji,ba namiji bane kai saidai mata maza" idanunsa ya qura mata qir sanda take maganar cikin dakiya da rashin nuna tsoro,hakanan bilhaqqi da gaske,ganin takai aya saiya soma takowa inda take tsaye,ta tsaya cak don ganin iya gudun ruwanshi,saidai harya iso gab da ita bai daina takowa ba,hakan na nufin zai hade gap din dake tsakaninsu kenan,don haka ta soma ja baya ga zatonta zai tsaya amma ina,bai barta ba sai daya tabbatar ya hada bayanta da bango,qafarshi dake saye da takalmi saman tata qafar wanda yana iya jin zafi zafi na tudun takalminsa daya take mata qafa,kusancin dake tsakaninsu yayi yawa,tana iya ganin fuskarsa tarwai wadda kyau ya cikata gamida iya gyara,idanunsa sai suke juye mata irin na anwar dinta na wancan lokacin sak,janye qwayar idanunta tayi gabanta na bugawa da sauri da sauri,tsoro da fargabar me zaiyi mata na shigarta,saitaga ya daga hannu kaman yana shirin marinta,ta runtse idonta da sauri tana wassafa me zata masa ita bayan ya gama marin nata,ji tayi yaja baya da sauri cikin kaushi yace
"Sai na saki kinyi nadamar lafazinki,tsautsayi kuma yasa bakiyi yadda nace miki ba" daga haka ya juya da sauri sauri ya fice daga dakin,cikin hanzari ta daga murya
"Idan ka isa ka tsaya mana ka dakenin kaga yadda akeyinta" gab da zai fice ya waiwayo yace
"Aiba a gidan syrup muke ba" kalmar ta tsaya tana fassarawa,take wani abu ya cushe mata maqoshi,cikin qanqanin lokaci hawaye ya ballewa idanunta,tana jin zafi a zuciyarta duk sanda yayi wani lafazi dazai iya tuna mata da abinda ta aikata a baya,sulalewa tayi ta zauna a wajen,ba shakka ba'a bari a kwashe duka,shaye shaye ashe wani tabone da tambarinsa bai barin jikin maishi?,koda kowa ya manta ba'a rasa burbushi,ta jima a wajen tana jin ciwo kala kala kafin ta miqe ta fice daga dakin,ko kallo envalope din basu isheta ba bare ta dauka.
A falo anty zubaida tace ta tsaya ta duba dinkunanta na biki wanda ita batasan ankai bama,don ko kayan har yau bata kalla ba bare ta gane me takeso a ciki har tayi tunanin kaiwa dinki?,bata cikin yanayin da zata iya zama cikinsu saboda haka tabawa anty zubaidan uzurin kanta na ciwo zata duba zuwa safiya da haka ta wuce dakinta.
Washegari sun fito da anty zubaida zata koma gidan gyaran jiki tanata kumbure kumburenta da mita cikin ranta na yadda aka takura mata ba gaira babu dalili faruq dake sharar dakin da uncle hisham ya sakashi sabida zaiyi baqi ya fito da envalope din yana miqawa anty zubaida
"Anty wannan a dakin na gansu,kaman na anty shahida ne don jiya na gansu a hannun uncle anwar" hanu tasa ta karba sannan ta waiwaya tana duban shahidan
"Me yasa kika barsu a dakin?,abinda kikayi dai dai kenan?" Saita langabe kai,ita abun goma da ashirin,komai tayi batayi dai dai ba,saita saka hannu kawai ta amsa suka wuce,suna shiga mota ta kasa daurewa ta saki kuka tana kife fuskarta saman cinyarta,anty zubaida batace komai ba saidai ta dora hannunta saman bayan shahidan,saida tayi kukan na wani lokaci sannan anty zubaida tace mata.......*Alqawarin Allah*
3️⃣4️⃣
"Abubuwa da yawa da mukeso muke qwallafa rai a garesu ba alkhairi bane ga bawa,kiyi qoqarin rage wannan kaifin qiyayyar kamar yadda annabi yayi umarni saboda kada ta juye miki zuwa soyayya mai zafi daga baya,kiyita addu'a Allah yasa abinda zai faru dake ya zama shine mafi akhairi a rayuwarki duniyarki da lahirarki" da ire iren wannan nasihar suka isa wajen gyaran jikin.
Anty zubaidan ita ta karbi envalope din ta bude taga abunda ke ciki,saita amsa ta aje tana jiran hasina tazo ta raba cikin 'yan uwa,don shahidan a yanzu bata da wata qawa banda zunnurah da take sokoto,tunda abun ya faru gaba daya ta cure qawa daga tsarin rayuwarta,saidai gaisuwa kawai ta mutunci,sabida card din bashi da wani yawa sosai,da alama dinner ce da akayi selecting iya adadin mutanen da zasu shiga.
🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍