← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 73

Sashe 69

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Bazaiyiwu ba anwar,ka tashi kawai kayi tafiyarka" cewar alhj abba,don harga Allah bayason su xama sila na yiwa anwar din dole,wani tashin hankali ya saukowa nafisan,ya ga qoshi ga kuma kwanan yunwa tana shirin yi?,me yasa abban nata zaiyi mata haka?,girgixa kai anwar yayi cikin qarfin hali
"A'ah abba,ba za'ayi haka ba,nafisa qanwa take a gurina idan da kara da kawaici,abinda ya wuce ya riga daya wuce tunda ta gane kuskurenta,Allah ya yafe mana gaba daya ya kuma kiyaye gaba" murna farinciki kaman ta taka rawa a gabansu,saidai yanzu ba lokacin hakan bane,sake kwantar dakai tayi sosai ta sake neman afuwa gamida nuna tsantsar nadamarta,itakam hajiya bilkisu miqewa tayi ta fice tabar falon,tana jin ciwo cikin zuciyarta sosai duk lokacin da nafisan ke roqar soyayya,ta rasa wacce irin diya Allah ya bata?,zataso ace nafisan ta auri wanda shi yake mutuwar sonta ba ita take mutuwar sonshi ba,ta rasa meye matsalarta meye damuwarta?,ba kalar saurayin da bata dashi wanda kowa neman yardarta kan ya aureta yake amma sam ita ta qwallafa rayuwarta kan anwar,eh anwar ya isa mutumin da za'aso a zama mata a gareshi,amma duka hakan a ganin mummyn xaifi kyau idan har shine yazo da kanshi ya nemi hakan.

Tunaninsa ne ya dinga kasuwa kashi kashi,abinda ya faru yanxu cikin gidan alhj abban,tabbas shi shaidane kan irin son da nafisan ke masa wanda sautari hakan yakan bashi mamaki qwarai,karbar aurenta da yayi yasani shi kadaine abunda zaiwa alhj abba ya saka masa dimbin alkhairin da yayi masa da kyautatawa a rayuwa,da yadda yake kallonshi tamkar danshi,saidai ko daya zuciyarsa babu nutsuwa ko jin dadin karbar da yayi,bayajin wani daidaito ko daya kan batun nafisan,duk da agefe guda ya sani yana da buqatar kulawar mace,amma,ta yaya wata zata sanyo kai cikin rayuwar gidan alhali ga yadda take?,ta yaya zai kawo gyara?,tuninsa ya sake tafiya kan hotunan dake aje har yanzu suna yankawa gami da qona zuciyarsa duk daqiqa ko sa'a daya da zata shude,duk lokacin da idanunsa suka kai kai,yaha shahidan tsirara tare da wani sai yaji kaman mai shirin haukacewa,duk sanda ya kallo hoton yaga shahidan rungume qirjin daya daga cikin masu saida kayan maye sai yaji dama makaho ne shi,Allah ne kadai da qarfin addu'a suka sashi ya rayu har yakai bigiren da yake kai a yanzu.

Sassanyar ajiyar zuciya ya saki sanda yake kashe motar shi,ya daga hannunsa ya kira maigadin,cikin girmamawa ya qaraso
"Baqi indai ba 'yan uwa bane na jiki duk wanda yazo kace musa bama nan"ya qarashe maganar cikin muryar dake nuna jiki da zuciyarsa duka babu qwari
"To ranka ya dade" ya wuce ya koma bakin qofa yayin da shi kuma ya fito,ya dinga takawa a hankali zuwa cikin falon.

Shuru yake kaman koda yaushe,saidai ya hangi abinci a shirye saman dining,hakanan yayi sha'awar xama a falon,idonsa kan wata tasha da suke nuno fasahar zamani da qere qere,suna wani shirin kan na'ura mai qwaqwalwa,tsohon mintuna idanunsa nakan allon talabijin din,wani bayani da baqon nasu yakeyi ya dauki hankalinsa matuqa,yadda ci gaban xamani yazo da sauye sauye,yadda za'a qirqiri abu a idanunka kaga haka yake,amma da za'a sanyashi a na'ura sai kaga abun ba haka yake ba,tsahon minti ashirin yana bayanin wanda yayi matuqar daukan hankalinsa.

A hankali tunaninsa ya karkata ga abunda zuciyarsa keson tuna masa tun daxun,saiya miqe da hanzari ya soma haurawa saman cikin sassarfa,bai tsaya ko inaba sai bakin safe din nashi,cikin sauri ya tsugunna,ya soma saka lambobin sirrin ya budeshi,envalope din ya ciro kaman ko yaushe ya zazzage hotunan ciki duka suka fado
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya furta kaman yadda ya saba sanda yake binsu da kallo daya bayan daya,duk sanda zai gansu yakanji kaman duniyarshi sama ta kona qasa ne,kullum yanajin kamar ranar ya soma ganinsu,saiya zauna sosai zuciyarsa na fata da kuma burin samun mafita,xuciyarsa ta cika da fatan dama ace ba haka bane,dama ace ba ita bace,dama ace ba shahida bace a jiki shine bai ganin dai dai duk sanda zai kalla,saiya sake gyara zamanshi sosai,ta ina zai fara?,bashi da wani qarfin sani ta wannan fannin,idan kuma yi masa za'ayi duk duniya bayajin akwao wani mahaluki da zai iya bari yaga hotunan,koda mahaifiyarshi data haifeshi ce inda tana raye.

Sake miqewa yayi da sauri saboda tunawa da yayi da makarantar computer da sa'ida ta mishi xancan ummi ta musu register xasu fara zuwa,idan bai manta ba ta gaya mishi akwai online classes da special classes da za'azo har gida a koya maka,system yayi nufin kunnawa,sai yaga kamar ba zata masa sauri ba,ya ciro wayarshi daga aljihunsa ya kunna data sannan ha fada google ya soma rubuta sunan makarantar,bai manta sunanta ba saboda kusan ma'abocin siyayya ne a shagonsu na yanar gizo wato www.rahamalls.com,bakin gado ya koma sannan ya rubuta sunan makarantar *RAHA COMPUTER INSTITUTE* ,cikin qaramin lokaci ya samu dukkan bayanai,kuma tsarin ya gamsar dashi,ya dauki number dake cikin bayanan ya kira.

Cikin sanin daraja da mutuntaka tadan adam ya sake samun bayanan da yake buqata,cikin abinda bai gaza awa guda ba yayi register dasu da komai da komai,ajiyar zuciya ya sauke sanda komai ya kammala,ya duba agogo yaga lokacin daya kwashe,ya miqe a hankali yana fidda kayan jikinsa,ya sauya wasu marasa nauyi,wando iya gwiwa sai jallabiyya daya fitar ganin lokacin sallah ya kusa,ya shiga bandaki ya daura alwala,sanda ya fito wayarshi na ruri,gab da zai isa gareta ta katse,saiya duba mai kiran,nafisa ce,miscal na shida kenan daga sanda ta fara kiransa zuwa yanzu,sai a sannan ma zancan ya dawo masa,ya duba saqon data tura masa wanda na godiya ne da kuma ya yaje gida,aje wayar yayi ya isa inda magungunansa suke ya cira yasha,sannan ya fesa turare ya qarasa bakin gado ya dauki jallabiyyarsa ya saka,hakanan yakejin kaman wani nauyi ya ragu daga zuciyarsa.

Cikin mamaki ta dubi table din sanda ta fito daga dakinta,taji kaman ya shigo amma bataga alamun hakan ba,kaman zata share sai kuma taba hakan bai dace ba,kodon jikinsa takega ya kamata ta duba,idan lafiya lau shikenan babu buqatar sake damuwa ko saka ido.

Zai fita ita kuma zata shigo,kusan lokaci daya suka murda handle din,baya tadanja kadan bayan ta dubeshi ta dauke idanunta,sai taga kaman ya fada kadan daga jiya zuwa yau da kuma fitar daya sakeyi da dawowarsa,ganin alamun fita zaiyi sallah saita juya ta soma sauka tana cewa
"Sannu da zuwa"
"Yauwa" ya amsa yana tsaye cak yana dubanta sanda take sauka din,yanajin kaman ya rintse ido ya bude yaga duk abinda ya farun da wanda ke faruwa a mafarkine,bai taba kwana ya kwatanta a ranshi ko sau daya rayuwar zata iya zuwa musu da wannan salon ba,dai gashi lokaci daya komai ya canza,komai ya tabarbare,komai yazo da cikin wani bahagon yanayi.

Karon farko tun bayan rabuwarsu dayaji wani abu mai kama da tausayi tausayi akanta saboda tuna cewa nan gaba kadan nafisa xata shigo gidan a matsayin kishiya a wajenya,ya tuna yadda mata ke komawa duk sanda zance makamancin haka ya shiga kunnensu yatuna yadda nafisa ta birkice a sanda labarin wanzuwarta qarqashin inuwa guda ya shiga kunnenta,a sannanma bata zama qarqashin ikonsa na,basu taba kwana qasan rufi guda ba,inaga ita?,duk da bashi da tabbacin cewa zataji wani abu ko zata damu,saboda dukkan dalilin dake sawa mace tayi hakan babushi tattare da ita.

"Kidan samu kifi ki dafaminshi idan ba damuwa,zanje sallah na dawo" ya fada cikin laushin murya wanda har hakan yaso bata mamaki,saita juyo tana kallonshi,suka hada idanu ta sake dauke kai ganin yadda ya kafa mata idanu,taji kallon nata har cikin jikinta,sai taba baiken kanta data sanya kaya irin wannan ta zauna haka ko mayafi babu bare hijabi,amsa masa tayi da to tana ci gaba da sauka daga benan,har sai dayaga bacewarta sannan ya sauko shima yawuce masallacin.

Sai data soma shiga daki ta samu dan qaramin hijabi ta saka sannnan ta wuce kitchen din har yanzu tana mamakin irin salon da yayi mata magana dashi,ta ciro kifi ta gyarashi,ta kauda wancan tunanin na farko ta fada tunanin yadda zata sarrafashi ta yadda zai dace da yanayinsa,wani gashi ta tuno mai kama da romo romo da takanga anty xubaida bayi,ba bata lokaci ta soma hadashi,wanda cikin mintuna qalilan ta kammala,qamshi kuwa ya cika gidan ko ina,ta gyara komai a kitchen din ta gogeshi sosai yadda ta saba sannan ta fito don barin kitchen din.

Tunda ya dawo yana falon a zaune yana shaqar qamshin kifin har cikin zuciyarsa,da mamaki tadan dubi sashen da yake din,don iya zamanta a gidan batace ga sanda ta ganshi zaune haka sosao cikin falon ba,kamar yasan da tsaiwarta shima ya waiwaya yana dubanta,yabi hijabin jikinta da kallo,shima hakan yayi masa don tamkar gata tayi masa,baisan me yasa takeson ta zame masa tamkar wani maganadisu ba ko mayen qarfe aduk sanda ya ganta?,baisan me yakeson sauyashi haka ba,bayan a baya yasan bai damu da dukka shigarta ba,amma cikin abinda bai gaza sati biyu ba yanason sauyawa gaba daya?. *Alqawarin Allah*
44
Chapter 69 · 0% Book details