← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 73

Sashe 58

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaman dirshan yayi qasan tiles din dakin,zuciyarsa na masa zafi tun bai fito da hotunan ciki ba,ya daga ya zazzagesu duka suka zubo,dai dai sanda wani abu ya tokare masa maqoshi,idanunsa suka soma sauya launi zuciyarsa na suya,haka ya dinga daga hotunan daya bayan daya yana kalla abinda ya jima baiyi ba donko sashen da suke ajiye bai fiya son kalla ba,kowanne hoto yayi a qalla minti biyar yana qare masa kallo kamar maison sanin dai dai lokacin da aka daukeshi,haka ya gama kalla baiga wani abu da zainuna akwai kuskure koba dai dai ba game da hoton,kowanne ya fito tas ya fita kar hakanan komai na jikin shahidan ya bayyana baro baro,gudun zuciyarsa yaji ya sake daduwa kansa ya soma daukan dumi,haka ya janyo envalope din ya soma maidasu ciki jin alamun hawan jininsa na neman tashi,yasan shiya jawa kansa daya kalla hotunan,amma hakanan kawai yaji kaman an tsunkulinsa kan ya jawosu ya duba,saiya miqe a daddafe ya shiga bandakinsa ya saje daura alwala ya fito ya tada sallah.

Kamar yadda ya saba kafin ya idar sanyi da nutsuwa sun saukar masa,ya daga hannu yayi addu'a sosai sannan ya shafa,saman abun sallar yaci gaba da zama,kwanan da baiyi ba kenan kan gadonshi a darensa na farko cikin gidan aurenshi,sai akan abun sallar ya kwana,wanda bai sake farkawa ba saida ya rage mintuna kadan a tada sallar asuba sannan ya sake wata alwalar bayan yayi wanka,ya bare wata jallabiyyar ya saka bayan ya feshe jikinsa da turare masu sanyi da taushin qamshi.

Har zai fice saiya tuna da ita,ya tabbatar haqqinsa ne ya kula da addininta,koma meye a yanzun tana wuyanshi,saboda haka ya sauya akalar tafiyar tashi zuwa sashen dakunanta.

A sannan itama ta farka tana gefan gado tana shirin shiga bandaki ta sauya audigar jikinta taji knocking,tasan ba kowa bane saishi,tana ji amma tayi banza kaman bata ji ba,saida yayi a qalla wajen sau goma sannan tadan ja gyaran murya kadan,hakan yasa ya gane ta tashi sai kawai ya juya ya fice zuwa masallaci.

Sanda ya dawo kashe wayoyinsa yayi baki daya ya haye saman gadon sosai bayan ya cire jallabiyar jikinsa daga shi sai gajeran wando,ya kwanta dai dai saman gadon yana sauke gajiyar da jiya bai samu saukewa ba.

Duk da gajiyar datayi qarfe tara saura taji baccin ya fita a kanta,saboda haka ta miqe ta fada bandaki ta tara ruwa mai dumi sosai tayi wanka ta dawo cikin dakin ta shirya cikin atamfa riga da zani simple mara ado,bayan mai sai powder da kwalli kawai data zizara a fuskarta,tayi daurinta sosai ta feshe jikinta da turare,dakin tadan kakkabe tayi goge goge ta sake shareshi ta dame gadonta sosai,sai a sannan ta bude qofar dakin nata tabi 'yar hanyar data sadata ta falon.

Daga tsaye take sake kallon falon,sai yanzu ta sake ganin kyau da tsaruwarshi,komai yayi mata perfect daidai da ra'ayinta,ta daga kanta ta kalli saman wanda da alama anan dakunan baccinsa suke,saita tabe baki ta juya zuwa qofar da kitchen take,can dinma komai yayi mata a tsare,gidan gaba daya babu fariyar kashe dukiya hakanan babu qaranta,karon farko tun bayan da suka sake haduwa da yayi wani abu data ji abun ya burgeta,duster ta dauko ta dawo falon shima ta saitashi yadda takeso,daga nan kitchen ta shiga,store dinsu babu komai a ciki,amma taga kayan tea da qwai,saboda haka ta tafasa shayi mai kayan qamshi ta zuba a flask,sannan ta fasa qwai ta soya,sai a sannan ta tuna da ledar jiya,ta kyabe baki ko tabata batayi ba bare ta duba meye a ciki,saita debi ruwan zafin tasha,sannan ta fito da flask din da wainar ta jera saman madaidaicin dining dinta mai kyau wanda keda kujera shida tana cewa
"Ba don halinka ba" saidata aje sannan ta koma dakin,ta janyo ledar ta duba,kayan qwalama ne irin na kowacce amarya daren farko,kazar ciki kawai ta cire ta koma da ita kitchen,ta sake mata dan hadi cikin kayan qamshin da aka kawota dashi ta jona ovean dinta ta sake gasata da kyau sannan ta cireta taje ta hadata da 'yan uwanta saman table din,ta gyare wajen ta juya ta fice,bata tsaya a falon ba ta wuce dakinta don tana tunanin ba zata rasa abunyi ba a ciki.

Cikin baccinsa ya soma jin qamshin kazar da take gasawa,bai gama farkawa ba wayar muhsin ta tadashi,ya farka yana ware hanci yana shaqar qamshin wanda yasa tsohuwar yunwarshi motsawa,saida kiran ya katse ya sake shigowa sannan ya samu damar dagawa
"Haba malam,da ba zaka daga kiran nawa ba wato tunda mun gama namu aikinko?"
"Kai bakasan haqqina ka dauka ba?,ina tsaka da baccina ka tadani?" Murmushi mai kama da dariya muhsin ya saki
"Lallaikam,su bacci manya,ai dole kayi bacci tunda ka mallaki abinda rai keso ruhi ke muradi,barcin shekara shida zakayi ai...."
"Wannan ne dalilin kiran daka yimin?" Ya katseshi gami da jeho masa da tambaya kai tsaye
"A'a a'ah,so nake ince maka ka haqura hakanan fito muje gaisuwar surukai,idan muka dawo ka dora daga inda ka tsaya"
"Ban fara bama bare na dora shaqiyyin banza,ni zaka yiwa iskanci?,dadin abundai aiba haram bane ko?" Dariya ya qyalqyale da ita
"Dama waya ce haram ne?,banda kai dakeson haramtawa kansa,kayi sauri ka fito don Allah don nikam bazan shigo gidanku ba"
"Kai ka sani" ya katse wayar ya ajeta gefe sannan ya yaye bargon da yake lullube dashi ya sauka daga gadon ya shige toilet.

Tsaf ya shirya cikin manyan kaya,yayi masifar kyau daka ganshi ango xam,saidai babu wata walwala ko qyallin goshi da hausawa ke fada.

Har yakai bakin qofar falon xai fita saiya tuna da ita,ya sake komawa ya doshi qofar dakin nata,sau hudu yana knocking bata amsa ba sannan bata bude ba duk da tana jinsa,ganin lokaci kaman zai qwace saiya juya ya fito,idanunsa suka sauka kan dining ya hangi flask akai,ya qarasa ya bubbude yaga meye a ciki,hankalinsa ya kwanta da alama taci abinci kenan,dama damuwarshi ya sauke nauyinta daga kanshi,kada ya fita ya barta bai sani ba ko bataci komai ba.

Qaramin tsaki taja tana dauko wayarta ta soma danne danne,wani saqo data gani yadan ja hankalinta saita bude,nuradden ne ya tura mata shi,yana nuna yadda yayi rashi da kuma yi mata fatan alkhairi a aurenta,data duba date din sai taga tun ranar daurin aurenta ne,reply ta masa na godiya sannan ta fita ta laluba number anty zubaida tana son kiranta,duka yau babu wanda ya kirata kamar wadda tayi baqin jini ta raya haka a ranta.

Kafin takai ga kiran kiran mubina ya shigo,ta daga ta kara a kunneta,gaidata ta soma yi ta amsa tana tambayar umma
"Anty 'yan katsina zasu koma gobe da sassafe,zan rakosu zasu miki sallama"
"To shikenan,idan kun tashi tahowa mubina,ki biya ta wajen anty zubaida ki taho min da laptop dina dana bata ajiya,zan kirata na gaya mata"
"Tohm" ta amsa mata sannan ta sata ta kaiwa umma suka gaisa,tana ji tana cewa ga daada ta katse wayar tana sane,me daadan zata gaya mata kuma bayan tayi yadda takeso da rayuwarta me kuma yayi saura?,gwara a kawo mata laptop dinta don ko aiki zata koma abinta,bata ga kuma zaman da zatayi a gidan ba,aure ne dai sun daura bashikenan ba kuma?.

Daga bakin qofar falo taji knocking,ta tashi ta saka hijabinta ta bude,dattijon dake musu gadi ne,ta gaidasji cikin girmamawa sanda shima ke qoqarin gaidata
"Alhaji ne ya aiko dasu,amma yace yaron karya shigo masa gida yana waje,zan debosu yace a aje a qofar falo idan yazo zai shiga dasu"
"Toh baba,ba damuwa" ta fada tana kaucewa tabar masa qofar a bude,koda ta dawo don rufe qofar bayan ya gama saita tadda kayan abinci ne,babu nau'in abinda babu naci da sha,hatta dasu maggi da curry,ba zata iya kwashewa ba saboda haka ta maida qofar ta rufe ta koma dakinta.

Awa biyu sai gasu mubina sun iso,matan yayyen babanta biyu dana qannen babanta uku,sai su hasina mubina da khadija,sosai ta ware cikinsu aka shiga sabgogi,suna hira da matan kawunnan nata su hasina ana gyare gyaren indai takega ya kamata a gyara din,duk suka shigar da kayan abincin store suka jera,abinda ba zasu iya dauka ba kaman manyan buhunhunan shinkafa suka barshi a falon a gefe daya da zummar idan mai gidan ya dawo ya shiga dasu tunda ya hana wani ya shigo masa bare a shiga dashi,tunda suka zo hasina minti daya biyu sai tace amarsu ta ango tana mata dariyar shaqiyanci,tana sane da ita amma tayi banza da ita,bata tanka mata ba sai qarfe biyu na rana suna shirin yin sallar azahar bayan sun gama cin abincin rana
"Amarya amarya,aina tsammaci zanzo na tadda angon naki" harara ta balla mata
"Au da kika shiga dakina baki ganshi cikin handbag dina ba?" Sosai tasa su rafi'a cousin dinta da sukazo su dukka kwashewa da dariya,har ita hasinan da aka baiwa amsa
"Banson wulaqanci,duk take takenki ina sane dashi,idan kika cikani kuwa zaki gane shayi ruwa ne"
"Allah ya baki haquru,kawai na tsammaci sai munzo mun miki ruwan zafi ne"
"Yanzu ma bata baci ba"tana amsata ta miqe ta shige bandaki donta daura alwala,tana jiyo dariyarsu,ita abunma saiya bata dariya,hasina duk yadda zata qular dakai ta iya,ina ita ina wani anwar,abinda hasinan ke hasashe akai bata tsammanin yiwuwarsa har abada a tsakaninsu,don masoyi akewa wannan halaccin,ita kuwa ta jima da cire anwar daga layin masoyanta can wani zamani daya jima da shudewa.

Tana idar da sallah mubina data barsu a falo ita da matan kawuna nanta ta shigo tana gaya mata an kawo aike,cikin mamaki tace aike kuma?,ta amsa mata da eh,saita miqe kawai tabi bayanta.

Manya manyan baqaqen ledoji ne data duba ciki nama ne da kifi danye
"kai kitchen ki saka cikin freezer dake kusa da sink"ta fada tana juyawa sama abinta,qarfe uku hasina tace bari a dorawa ango,tasan tsokanarta take,don haka ko kallonta batayi ba,tana zaune suka shige kitchen din kuwa itadai tana cikin baqinta suna hirarsu.

Qarfe biyar suka kammala lafiyayyen abinci,hasina ta bude sabbin warmers din shahida ta zuba komai ta tsarashi saman table,sannan suka gyare kitchen da gidanma duka suka soma haramar tafiya.
Chapter 58 · 0% Book details