Sashe 40
Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Falon inna ya wuce kai tsaye bayan ya isa gidan,ya tadda kawu dahiru da kawu modu suna rumfar innar suna hira da alama anan sukari karin safe tare,cikin girmamawa ya gaida inna sannan ya gaidasu yana zama daura da ita,ita ta yunqura da kanta ta hada masa lafiyayyen kunun tsamiya da sukayi da wainar gero,cikin marmari yake ci suna ci gaba da hira dasu kawu dahirun,yana kammalawa kawu shehu ya iso,basu wani jima ba suka miqe gaba daya zuwa gidan daada,shi yaja motar,kawu shehu da yake shine babbansu yana gaba,kawu dahiru da kawu modu kuma suna baya.
Sanda suka isa gidan sha daya na safe har ta dan gota,hakan yasa suka tadda kawun nan shahida sun riga da sun iso,sulaiman shi ya musu jagora kamar ko yaushe zuwa cikin gidan
"A'ah....shehu,kardai kacemin yaron dake neman shahida dan wajenka ne?" Kawu ummaru wanda yake yaya ne ga mahaifin shahida ya fada yana dariya sanda sukayi musabaha da kawu shehu
"Yaro na ne,dan wajen qanina ne mai rasuwa"
"
"Kai ma sha Allah,amma naji dadin abun nan qwarai,to ai abunma duk na gida ne,ita kanta daadan ma bata sani ba,inaga basai anje anata kaiwa da kawowa ba,ayi komai kawai a gama lokaci guda"
"Kana ganin babu wata damuwa ko matsala?"
"Haba shehu,kaine fa,babu wata damuwa wallahi,dama meye burinmu banda muga yaranmu sunata aurensu".
A ranar gaba daya kawu ummaru suka amshi kudin auren shahida harda sadaki,aka kuma tsaida lokacin biki ko ince daurin aure a wajen maza watanni uku masu zuww,wanda yayi dai dai da watannin da aka tsaida a farko na daurin aurenshi da nafisa.
Yana tsaye jikin motarshi qafafunshi amatuqar sanyaye,irin wannan lokaci ya jima yana mafarkin zuwanshi shekara shida baya,ya qiyasta yanayin farinciki da zai samu kansa a duk sanda Allah ya tabbatar masa a wancan lokaci har baisan sau naya ya qiyasta din ba,sai gashi abun yazo a bahagon yanayi,yanayin daya kasa tantance wani iri ne,farinciki ne ko baqinciki?,kansa ya daga a hankali sanda ya soma jiyo muryoyin su kawu dahiru da alama suna sallama ne dasu kawu ummaru.
Ranar kasa shiga yayi wajen daada duk da yaso suyi sallama,haka ya sake dibansu kawu shehu ya sauke kowanne a gidansa sannan suka wuce wajen inna shida kawu modu.
Murmushi ne kawai ke fita a fuskar daada sanda 'ya'yan nata ke gaya mata yadda komai ya kasance
"haba,ba banza ba nutsuwar yaron ta yimin,naji ya shiga raina sosai,ashe jinin gidan malam usman ne(sunyi zama na maqotaka ne tun iyayensu da kakanni,zaman da sukaji dadinsa,kunsan mutanen daa akwai riqo da zumunci da kuma girmama alaqa da dangantaka komai qanqantarta),na godewa Allah,Allah yasa albarka ya kuma tabbatar da alkhairi"
"Amin daada" dukkansu suka amsa suna jin dadin hadin
"Yanzu daada za'a sanar dasu kenan?"kai ta girgiza
"qwarai kuwa,ka shaida ma ita uwartata,sannan kuma ka kira can gidan hishamun a shaida musu,duk da cewa shi ya sani amma sai a gaya masa an karba harda kudin auren da sadaki,gobe idan ka dawo kai ummaru ka kiramin rahamar ka hadani da ita"
"To shikenan daada" ya fada yana lalubar wayarshi dake aljihun rigarsa.
*_GUDUN QADDARA guzurin taddata....._*
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke wadda ta fito tun daga zuciyarta,ta sauke idanunta kan tafin hannunta tana bitar maganganun nuradden daya gama furta mata ayanzu,dauta dauko na anty zubaida data gama gaya mata jiya,kusan maganganun nasu sunyi kamanceceniya da juna,a yanzu bata da wata mafita bata da wani uzuri kaman yadda anty zubaida tace mata,imma dai ta baiwa nuradden dama wa imma ta sallameshi hakanan ya daina wahala,ko ga ummanta madai wannan karon ta matsa qwarai kan ya kamata ta tsaida manemi tayi aure,tunda dai abinda ya farun da ita bawai qarshen rayuwarta ya kawo ba,saima sabon babin rayuwa daya sake bude mata,idan ta sallami nuradden bata jin akwai wani qwaya daya cikin samari dama masu auren dake kara kaina akanta da zata iya kwatanta rayuwarta ta wanzu tare da tashi
"Na amince nuradden....Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi" hannayensa gaba daya ya hada ya rungume a qirjinsa yana lumshe idanunsa,wani farinciki da baisan a wanne mizani zai dorashi ba ya shiga dawainiya dashi,sai kawai ya zame saman gwiwoyinsa a gabanta
"Shahida,ki fadamin me kikeso na baki ladan wannan kyakkyawan albishir din naki?" Kai ta kada kawai qwalla na taruwa a idanunta,murmushi mai cakude da alamun son yin kuka na kubcewa saman fuskarta
"Babu abinda zaka bani face nace kayi qoqari karka sa na sake yin nadama da dana sani a rayuwata karo na biyu"
"Koda baki roqi haka ba wannan duty na ne" da ido kawai ta dinga bishi yadda ya rasa inda zai tsoma ranshi ya dinga bata mamaki,harta daina mamaki ma abun ya soma bata dariya,sai daya tabbatar ta dan saki ranta sannan yace
"Yanzu yaushe za'a kai maganata katsina?,shine abu daya da zai sake sawa in samu nutsuwa a raina,in kuma tabbatar na yiwa duk wani dake da buri ko hanqoran mallakarki na masa fintikau din da dole ya haqura" murmushi ya qwace mata,tasan cewa burinsu daada kenan,tana da tabbacin indai nuradden ya isa katsina to magana ta qare,don ba wani lokaci zasu ja ba ba tare da sun bashi ita ba
"Karka damu duka abun bana sauri bane,next month za'a dauki azumi,sai kayi haquri mu barwa salla" fuska yadan bata
"Gaskiya yayimin nisa,saidai idan har kin yarda ne ni zan kaiki,qafarki qafata"hannu ta daga tana murmushi
"Shikenan naji,sai kuma me?"
"Aikin gama min komai nikam,yau nafi kowanne namiji dake fadin duniyar nan sa'a" yayi furucin a sanda yake kallon sararin samaniya cikin madaukakin farinciki.
Qarfe tara ta shiga gida don bata wuce hakan a waje,duk da dama ba fita take wajen kowa ba,kusan nuradden din ne kawaima yaci qwallo da har take fita ta saurareshi,ga mamakinta saita tadda anty zubaida zaune saman kujerar falon hannunta daya tallafe da kanta,gwiwar hannunta saman hannun kujera,ba kowa falon sai ita kadai,kallon wani series da suke haskowa a mbc take,sallamar shahidan ya sakata dagowa da sauri tana dubanta
"Anty,yau yana sameki a nan?" Qoqarin daidaita kanta tayi
"To ya zanyi,uncle dinki yace lallai lallai naga shigowarki na tura masa ke" murmushi tayi tana zama hannun daya kujerar dake daura da anty xubaidan
"Hala anty kinkai masa qarata ne kan nuradden?,to kisha kuruminki,na riga na baiwa nuradden dama,zuwa nan da qaramar sallah xai isa gasu daada in sha Allahu" ta qarashe tana duban anty zubaida,don tasan ta gama mata abinda ranta keso kenan,sai taga ta murmusa kadan
"Ya za'ayi nakai qararki?,koda nakai dinma ai Allah abinda ya hukunta dole shi zai faru ko?,yanzu dai kije yana falonshi yana jiranki" sai data miqe sannan tace
"Anty muje tare mana don Allah"
"Ba ruwan zubaida" ta fada da hanzari,dariya ta baiwa shahidan yadda tayi maganar kamar wata baquwar uncle hisham din,saita juya ta wuce tana cewa
"Ai shikenan anty".
"barka da dare uncle"shahida ta furta sanda ta nutsu a gaban uncle hisham,ya sauke takardar da yake dubawa ya kalleta
"barka kadai shahida,sai yaushene zakuyi hutun naku kamfanin?"
"Eh to uncle gaskiya ina zaton sai sai dab da sallah,saboda wannan season ne na yawaita da kuma cunkoson custumers" kai ya jinjina sannan ya danyi shuru kamar mai nazari kafin daga bisani yace
"Daada ce keda buqatar kije,to ban sani ba ko xaki samu ko weekend ne kije kiji kiran nata na meye?"
"Shikenan uncle babu damuwa,yau alhamis ranar juma'a tunda da wuri muke barin kamfani saina shirya naje,idan yaso ran lahadi da yamma saina dawo"
"Hakan yayi,shikenan dama kiran"
"To uncle saida safe" ta fada tana miqewa
"Allah ya bamu alkhairi".
A inda tabar anty xubaida nan ta taras da ita,saita daga kai tana kallon shahidan,ganin babu sauyin fuska tattare da ita ya tabbatar mata uncle din bai gaya mata komai ba,zai turata ne kaman yadda dada ta buqata,sallama anty zubaidan tayi mata ta wuce wajen uncle din,tabar shahidan na sake sabon xaman ganin maimaicin wani shiri,tana mitar baccin wuri da yau su faruqu sukayi suka barta ita daya,don bata jin dadin zaman falon ita kadai.
A nutse yake murza motarsa tamkar wanda baison barin titin har zuwa sanda ya isa unguwarsu anty usaina,cikin nutsuwa ya faka motar sannan ya kasheta ya fito,cikin wani irin karsashi yake takawa zuwa cikin gidan,haka kawai yake jinsa kaman mai yawo cikin farin gajimare wanda shi kansa baisan dalilin haka ba,yana shirin saka qafarsa kan step qwaya daya da zai sadashi da falon gidan ya jiyo muryar sa'ida na kiranshi,a nutse ya waiwaya,sai ya tsaya hannayensa zube a aljihun wandonsa yana dakon qarasowarta.
Aladabce ta rusuna tana gaidashi ya amsa yana dubanta
"Daga ina kike?" Sai data dan waiwaya sannan ta dawo da dubanta wajensa
"Uncle....gidansu anty shahida,ummi ta aikeni na amso mata saqo?,kasan me uncle?" Kai ya girgiza yana dubanta
"Na ganta mafa tazo wajen mamansu,uncle kaganta kuwa kaman ba ita ba...."takun data jiyo ya sanyata tsuke bakinta,cikin minti daya anty usaina ta bayyana,akwai 'yar tazara tsakaninsu kadan,ya juya ya dubi sa'idan
"Wuce kafin tazo ta fara miki jajayen idanuwa" maganar ta baiwa sa'ida dariya har sai data qyalqyale da dariya sannan ta soma takawa don wucewa ciki
"Wato kin dawo shine kika samu waje kika tsaya kina masa wannan dan banzan surutun naki ko?"kai ta gyada
" a'ah ummi,nima fa yanzu na shigo"harararta tayi cikin ranta tana qissima lallai ya zama dole ta kwabi sa'ida,donta fuskanci kanta yana rawa tanason ta lalata mata plan
"Wuce,saura kuma naga qafarki a wajen" da hanzari sa'idan ta wuce,anty usaina ta bita da kallo harsai data shige sannan ta dauke idanunta,dai dai sanda anwar yake tsaye daga inda yake,a nutse yana karantar duk wani motsi na anty usaina,murmushi ya kubce masa,ya gama ganeta tsaf,ya gama karantar tsoronta,ya kuma gane me take boye masa,saidai baisan nata shirin ba,koma meye nata shirin shi zai mata ba zatan da bata tsammata ba,idonta ta sauke a kanshi,tana tsaye har ya isketa
"Yaushe kai kuma ka dawo?,daga wuni daya sai kwana har biyu?"
"Tun jiya na dawo,wasu sabgogi ne suka riqeni,duk yadda naso in shigo baiyiwu ba" bata ce komai ba ta bude qofar falon ta shiga yabi bayanta.