← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 73

Sashe 11

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau bayan ya rakata sunyi sallama ta amshi botikinta ta juya zata shiga gida taga baquwar mota qofar gidan nasu,tana kallon motar ta tabbatar da cewa sunyi baqi ne,kuma bata raba d'ayan biyu uncle hisham ne,wanda shine ya baiwa ummanta kwangilar dafa abincin sadaka da kullum take kaiwa bakin masallaci a rabar,da farincikinta ta qarasa cikin gidan,don kuwa jininsu ya hadu qwarai da matarshi aunty zubaida,a tsakar gida ta taddasu,fuskarta washe da fara'a ta aje botikin nata ta qaraso saman tabarmar da suke zaune anty zubaida na cewa
"Oyoyo 'yammata....sannu da qoqari" tana dariya dariya ta gaidasu,cikin kulawa suka amsa ta juya tana tambayar yaron anty zubaida na faro farouq yashe sukazo?,
"Sannu da qoqari khadijatu....lallai na yarda ba qaramin qoqari da amana gareki ba.....gaskiya ali Allah yayi maka baiwa da yarinyar qwarai" cewar uncle hisham,kanta na duqetana murmushi
"Alhamdulillahi kam,Allah ya azurtamu da diyar qwarai,mu kanmu muna alfahari da hakan" umma ma kai take jinjinawa,don ita kanta zata iya cewa cikin yaranta shahidan ta dabance,wani irin hankali da nutsuwa gareta,biyayya da kyautata iyaye tana sahun gaba,hakanan take qaunarsu,dalili kenan dako yaushe itama take ta qoqarin daina biyewa mahaifinta suna raba gari shahidan na kallo,sunfi kowa sanin cewa abun ba qaramin ciwo yake mata ba a rayuwa
"Nawa ake bina ne kudin kai sadaka khadija?" Uncel hisham ya tambaya yana fiddo kudi daga aljihunsa,dariya ita abun ma ya bata,wanne irin binsa kudi?,mutum mai tsananin kirki da kyautatawa a garesu?,ko iya kai abincin ma da take ita ta sani Allah ne kadai yasan ladan da take samu
"Ba kudin da nake binka uncle....nima ai ina samun ladar kaiwa" kai ya gyada
"Na sani,wannan amma dole na baki haqqinki ne"
"Banda abin shahida aiko kayan kwalliya kya saya ki dinga gogawa idan surukin namu zaizo ko?" Kunya ta kamata ta dan duqar da kanta qasa tana murmushi,mubina uwar surutu kuwa tayi caraf
"Kullum sai yazo kuwa mamansu faruqu,yana da kirki kullum saiya kawo mana tsaraba,ko ya bamu goma goma yace mu siya" kunya tasa shahida kasa zama saita miqe zata gudu,yayin sa antu xubaida ta soma tsokanarta
"Ah lallai,zanso naga wannan surukin namu,na tabbatar shima yana da kyau da nutsuwa kamar diyarmu..."
"Rabu dasu shahida....dawo ki xauna muyi lissafi" uncle husham ya tare mata,haka ta dawo tana sunkui da kai ta zauna
"Mu lissafa kwana nawa akayi ana kaiwa?"
"Allah uncle ka barshi kawai"
"Naqi din" ya fada yana soma irga kudin
"Ki fada kona baki yadda naga dama"dariya ta danyi tana basar da maganar,kudi mai yawa ya irgo yace
"toh gashi"
"Uncle ka bawa umma ta ajemin"
"A'ah a'ah,ba ruwan umma,wahalarkice karbi kiyi duk yadda kikeso dashi...iyakata in baki shawarar me zakiyi dashi" cewar umman tana miqews don zuwa kitchen ta hadowa su anty zubaida abinci,hannu biyu ta saka ta amsa tana masa godiya,a nan ta barsu anty zubaida harta gama shirin islamiyya suna zaune suna hirarsu,tayi musu sallama ta wuce.

************************

"Malam balarabe ina kayan anwar?" Shahida ta tambayi balarabe mai kanti lokacin da anwar din ke can yana hada kwanukanta don lokacin komawarta gida yayi
"Gashinan ina aunawa...bari na hada miki harda kwakin"murmushi tayi sanda take amsar ledar kwakin daga hannunsa
"Anwar...anwar kaina dabanne,ko me zakayi da garin kwaki kuma?"
"Na'am?....ai aikin muhammadu kenan,ba yadda banyi dashi ya dinga sauyawa da wani abun ba,ya amshi bashi duk sanda Allah ya hore masa ya biyani amma sam sam ya qiya...gaskiyarki kuwa shi na dabanne,rayuwarsa ma haka,ni tsorona ma kar yayi masa illa yawan cinsa da yake,bashi da abinda ya wuce gari" sam batasan zancan zucin da take ya fito fili ba saida taji sharhin malam balarabe fadi ba'a tambayeka ba,saidai maganar tashi ta taba ta,ko a fuska bata taba ganin wani abu makamancin haka daga wajen anwar ba,hasalima bai taba karbar abincin da take kawowa wajen ba ko sau daya kuwa,a gabansa take rabarwa har ya qare iyakarsa ya dauka mata kayanta suje gida ya aje mata ya wuce,a sanyaye take bin ledar garin da kallo,tausayin anwar din ya kamata,ta yaya mutum zai rayu da cin gari kullum?,tsananin maraicin ne yasa haka?,amma indai da gaske ne sun zama abu daya mai yasa bai taba gaya mata ba?,ta yaya tana cin shinkafa kullum anwar yaci gari?,sosai taji haushin boye matan da yayi,wasu qwalla suka cika mata idanu,saita dauki ledar kawai ta juya ta fice daga kantin ba tare data ce komai ba.

Sanda ta isa wajen har ya gama hada komai tsaf yana dube duben nemanta,fuskarshi yadan tsuke kadan
"Ina kuma kika shiga?,banason ki dinga darawa ko ina daga nan fa,kinsan halin mutane da shegen kallo da sa ido"
"Ba wani waje naje ba,na karbo maka saqonka ne daga wajen malam balarabe"
"Balarabe kuma?"ya tambayeta yana nazartar fuskarta,fes ya fuskanci yanayinta ya sauya,ganin bata ce komai ba yasa shi daukan botikin ya soma yin gaba,ga tunaninshi zata biyoshi amma saiyaga bayansa take bi kamar yadda suka fara can watannin baya da suka shude sanda suke baqin juna.

Cikin jinin jikinsa yaji sauyin yanayin shahidan bai masa ba,ko shakka babu akwai abinda ya faru shigarta shagon zuwa fitowarta,zuciyarsa yaji ta tsinke sanda ta qyasa masa wani tunani game da malam balarabe,baisan sanda yaja birki ba,ya waiwayo a sukwane,wanda saura qiris suyi karo da juna,baya ta danja kadan tana duban qwayar idanunshi da suka sauya launi,saiya sake matsowa gab da ita,kanta ta girgiza qirjinta na bugawa gana duban hagu da damarta,layin tsit yake babu kowa,yana daya daga ciki layukan da yake da qarancin zirga zirgar jama'a
" me malam balarabe yayi miki?"ya tambayeta da wata iriyar rikitacciyar murya,tuni qwallar data cike da idanunta ta soma silalowa,rikicewa yayi jikinsa ya soma rawa,kafin ya sake furta komai ta bude ledar hannunta garin ciki ya bayyana,kallan garin yayi sannan ya kalleta,tashin hankalin daya sauko masa yaji ya soma yayewa,hankalinsa ya soma kwanciya ganin ba abinda zuciyarsa ta raya masa bane,ya saki wata wawuyar ajiyar zuciya wadda ta sanya duk wani qarfi na jikinsa raguwa,har sai daya jingina da bishiyar da suke tsaye qasanta yana sauke wata qatuwar ajiyar zuciya
"Me yasa zakamin haka?,wannan abincine yanzu?" Sai yanzu ya sake fahimtar dalilin sauyawarta,kuka take sosai,saiya amshe ledar ya dora saman botikin daya aje gefansa
"Wannan bai isa ya zama dalilin da zai saka min ke fidda wannan tsadaddun hawayen ba,wanda duk duniya babu kudin da zasu iya sayen darajarsu a wajena.....ungo nan share hawayenki" ya fada yana bata qaramin handkherchief dinsa wanda baya rabo dashi saboda share zufa da yake gwanin zufa ne,hannu ta saka tana goge fuskarta,tsahon minti biyar ya bata don ta nutsu sannan ya bata damar magana
"Ohk...yanzu fadi duk abinda yake damuwarki"
"Kafi kowa sanin ba haka mukayi alqawarin gina tarayyarmu ba,munyi alqawarin xamu ji dadi da wuya a tare,kukanka nawa ne,kukana naka ne,haka nan dariyarmu,don me zaka boyen wannan?" Murmushi mai kyau da qayatarwa ya subuce masa,kullum kwanan duniya yana jin ana qara masa sonta ne,duk sujjadar da zaiyi saiya roqi Allah yasa shahida mallakinsa ce daga duniya har lahira
"A ganina wannan ba wani abu bane Allah ya taimakeki,na jima ina cinsa har kawo yau gashi ina raye ban mutu ba..." Saita mele baki cikin muryar kuka tace
"Zancan mutuwa ma kake?....." Kasa qarasawa tayi ta sake sakin masa wani kukan,kanshi ya dafe sosai,ya tsani kukanta,idan yana ganin hawayenta ji yake kaman wani babban tashin hankali ya sameshi
"Ya salam shahidaaah....,Allah ya baki haquri,kin manta cewa mu mutu ka raba ne?" Da tausasan kalamanshi dake sawa rayuwarta nutsuwa yayi amfani ya lallasheta sannan suka ci gaba da tafiya,bayan ta sa yayi mata alqawari bazai sake shan gari ba saidai da marmari.

Sanda suka isa tsaidashi tayi ta shiga gida cikin sauri,bata zarce ko ina ba sai kitchen dinsu,tasan ba'a rasa abincin a gidan nasu,koda bamai yawa bane amma za'a dafa,foodflask dinta ta dauka ta cika masa shi da taliya da wake sannan ta fita.

Yana tsaye harde da hannayensa a qirji,idan ka dubeshi da kyau ya zaka fahimci ya fada zurfin tunani ne,ledar hannunta ta miqa masa baqa wadda babu ta yadda za'ayi ya iya gane meye a ciki,saida dubeta ta masa alama da kai akan ya karba sannan yasa hannu ya amsa
"Ka tafi dashi"
"Meye wannan din?"
"Guba na baka kaci nima naci saimu mutu tare" dariya ta bashi sosai har sai daya dara,itama sai data fada din maganar ta bata dariya
"Kinsan kuwa zai zame min abun alfahari...kuma babban labarin da zai karade duniya...masoyiya ta baiwa masoyinta guba donsu mutu tare" murmushin daya qarawa fuskarta daraja da kyau ta saki
"Zan iya cin guba don tunkudeka daga cinta" girarsa daya ya dage sannan ya sassauta murya
"Idan babu ke ai babu ni shahida....kina tunanin idan kika mutu kika barni zan iya qara kwana daya a duniya" wani far tayi da ido wanda ya sanyashi yin baya da sauri
"Inni sa'im...naga alama so kike ki....." Da hanzarinta ta juya masa baya cikin shagwaba tana dan buga qafa alamun batason ya qarasa maganar da yake
"Shikenan.....sai anjima,na gode" ya fada yana takawa don barin wajen,tana wajen tsaye harya bacewa ganinta,saita lumshe ido ta saki hannayenta tana sakin siririn murmushi,tsakanin ita da anwar batasan waye yafi wani son dan uwanshi ba,wannan amsar kuwa tasan cewa Allah ne kadai masaninta.

Cikin kudinta ta cire dubu uku ta siya qaramar waya sabuwa irinta anwar,ummanta bata hanata ba bare abbanta,sunsan cewa waya ba damun shahidan tayi ba,yanzun ma sun tabbatar saboda anwar ta siya,wanda dukkansu zuwa wannan lokacin anwar ya zama kamar d'a a wajensu,mutum ne da Allah yayi masa baiwar saurin shiha zukatan al'umma,hakan kuwa baya rasa nasaba da hankali nutsuwa uwa uba tarbiyya da yake da ita,ko cikin unguwarsu dattawan nan son anwar suke,kusan kowa zakaga yana janshi a jiki,shi kuwa ya daukesu dukkansu tamkar mahaifansa,dalili kenan daya sanya wasu daga cikin matasan unguwar kejin haushinsa suka kuma qwafa masa,hakanan suka daura dambar sake danqwafar dashi,hakanne yasa duk sanda ya samu wani abu sakakke sai an haura gidan an sace,kama daga sutura zuwa takalma ko d'an kudi,ya rasa su waye?,baisan kuma meya tsare musu ba,shi da bashi da komai?,bai baiwa kowa ajiya ba amma ya tsone musu ido.

*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899
Chapter 11 · 0% Book details