← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 73

Sashe 5

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai daya shafe awanni biyu sannan ya iya fitowa bayan ya rufe motar,ya dinga takawa ahankali zuwa babban ginin kamfanin daya mamaye iya kallon mai kallo,sauran mutane dake dakon jiranshi suka yo masa caa,yayi qoqarin ganin ya dawo da mode dinsa duk da yadda yake jin kwanyarsa a birkice.
Tsaki taja bayan ta kammala karanta saqon,kafin daga bisani ta cilla wayar gefanta,dawowarta kenan daga makaranta a matuqar gajiya ta zauna a falon,bata ma kai ga qarasawa dakinta ba saboda gajiya,gaba d'aya ta gundura da wannan d'an banzan shirye shirye da hukumar makarantarsu keyi na zuwa shugabanta,wanda ita a ganinta ko president ne zai kawo musu ziyara iyaka kenan,ta k'agu yazo ya tafi a wuce wajen,saiga saqon nuraddeen kuma wanda ta tsani gani kamar yadda ta tsani mutuwarta,batasan sai yaushe zai gaji da halin shakulaton b'angaron da take yi dashi yayi zuciya ya barta ta rayu ita d'aya ba kamar yadda ta sama ranta.

Sun riga sunyi waya da anty zubaida tasan ta fita yau bata nan,don haka girkin gidan na yau na wuyanta,ga huda da suka dawo tare tasan yunwa takeji,don ma ta siya mata cake da lemo a makaranta kafin su iso gida.

D'aki ta shiga ta tube ta fada wanka,bayan ta fito ta sanya huda itama ta shiga tayi don yau babu islamiyya,a gurguje ta shirya tayi sallar azahar sannan ta shiga kitchen.

Indomie ta soma dora musu sannan ta dora girki a dayan wajen
"Anty kin gama?" Huda data shigo yanzu ta fada tana qarasowa inda shahida ke zaune sosai qasan kitchen din tana gyara kayan miya,don ta duba nasu markadadden da suke ajewa ya qare
"Sauran kadan hudallah....dadina dake bakya juriyar yunwa"
"Anty yunwa bata da hankali,haka d'an almajiri fa yake cewa" murmushi shahida tayi wanda ya qara kyawun fuskarta,hakanan ya bayyana wushiryarta,kafin tace wani abu hudan ta sake cewa
"Anty...dama d'an wake kika yi mana,inason d'an wake" a hankali ta juya ta dubi yarinyar saboda tuna mata wani abu da tayi,yana matuqar son d'an wake a rayuwarshi,a duk sanda taga abincin ko taji an ambaceshi saita tuna dashi.*ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH)KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don samun shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi*

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

*AA*
0️⃣4️⃣

Kasa cewa komai tayi,maganar hudan ta cillata tunanin wata duniya can baya,wanda duk yadda takai ga hana kanta batasan sanda ta fada ba.

Sai data sallami huda sannan taci gaba da sabgar girkinta,batasan me yasa ba sam batajin yunwa,ko zancan da huda tayi ne ya cushe mata cikinta gaba daya ya sanya har walwalarta ta ragu.

Tana tsaka da kwashe abincin cikin coolers huda ta shigo da sauri hannunta dauke da wayar shahida tana fadin
"Anty ana kiranki,zata katse" ta fada tana miqa mata,bata amsa ba ta kalli screen din wayar dake hannun huda,nuraddeen ne,saita dauke kai taci gaba da juye abincin tana cewa
"Ajiyeta kawai huda,aiki nake" juyawa yarinyar tayi ta fice da wayar zuwa falo da gudu don kada cartoon din da take kallo ya wuceta.

Tana cikin kintsa wajen sallamar anty zubaida ta karade falon sannan ta taddata cikin kitchen din
"Sannu da dawowa maman huda"
"Yauwa sannunki shahida,kin ganni sai yanzu ko?,wallahi layi yau na samu....me aka dafa mana ne yau da yunwa na dawo" nuni shahida tayi mata da food flask din dake jere a wajen,ta qarasa tana budawa
"Hmmmmm,kice yau na musamman ne abincin,bari wannan sai nayi wanka zan zauna sosai tukunna na kwashi dabge" qaramin murmushi shahida tayi mai fitar da d'an sauti tana duban anty zubaidan,har takai bakin qofa ta dawo
"Au....ni kuwa kinsan nuradden na qofar gida zaune cikin mota yana jiranki?" Asanyaye ta daga kai ta dubi anty zubaidan,sai ta sadda kanta tana goge plates din data wanke zata jerasu a muhallinsu,hakan da tayi shi ya tabbatarwa anty zubaida ya kira bata daga ba kenan
"Shahida.....wannan wacce irin rayuwa ce kika daukarma ranki?,mai sonka fa ya wuce ka wulqantashi,laifin wani dama yana shafar wani?" Shuru ta sake zabar tayi,saboda tana ganin sun gaza fahimtarta ne gaba daya,ta yiwa soyayya hidima,ta yiwa soyayya halacci,ta yiwa soyayya dukkan wata kara da alkunya,qarshe data tashi ita mai ta bata?,data tashi da wanne sakamako tazo mata?,sunfi kowa sani saboda haka sunfi kowa amsar dukka tambayoyinta,ko daya bata tsinci komai cikin soyayya ba face tsantsar butulci mummunan sakamako da kuma mummunar makoma,shin ta yiwa kanta a dalci kenan idan ta sake cusa kanta a wannan bigiren?
"Nidai ya roqeni alfarma,saboda haka idan na isa dake ki leqa ko gaisawa ne kuyi" zancan anty zubaida ya katse tunaninta,daga haka bata sake cewa komai ba ta ida ficewa daga kitchen din,tana jinta sanda ta kira huda suka haye sama tare,tasan kuma tayi hakanne don sanin halinta,ba qaramin aikinta bane ta fita ta baro masa huda ta cikashi da surutu wanda idan ya gaji da zama yake sallamar huda shima ya wuce nashi guri.

Anty zubaidan tafi qarfin komai a wajenta,don haka ta dauraye hannayenta ta wuce dakinta,ta zari hijabi ta saka ta sanya slipper dinta ta wuce qofar gidan.

Kamar kowanne lokaci yana zaune cikin motar,bayanshi jingine da seat din kujerar dayake kai,da alama ya jima zaune a wajen,duk da haka ganin fitowarta bai hanashi miqewa ba yana sakar mata murmushi harta qaraso
"Barka na tunda na samu kin fito" ya fada tamkar wanda baiyi zaman jiranta ba
"Inda kayi aiki da shawarata tun a karon farko da duk bamu kawo wannan matsayin da muke kai yanzu ba" ta fada kanta tsaye tana dubanshi,kafin daga bisani ta janye idanunta,har ga Allah wulaqanta dan adam ba dabi'arta bace,zatafi kowa farinciki idan har noraddeen ya janye daga qudurinsa daga kanta,ga sabanin tunaninta sai taga ya saki murmushi
"Bani da damuwa shahida,nasan cewa mahaqurci mawadaci,zan iya jure koma meye indai a kanki ne shahida" idanunta ta lumshe tana jin kamar jiri zaya kada ta,a rayuwa yanzu babu abinda ke damunta sama da matsalar nuradden,ya soma shiga jiki da zuciyar makusantanta,bata da buqatar a yanzu dukkan abinda zai kuma d'aga ma rayuwarta hankali.
"Koma meye tabbas mai wucewa ne watan wata rana" furucin nuradden ya sake ratsa dodon kunnenta,a sanda take kiciniyar dai daita kanta
"Don Allah.....shahida inason ki bani dama,ki saurareni koda wayata ce kadai ki dinga dagawa,bazan takuraki kan koda yaushe saikin fito na ganki ba,amma ki daga wayata,hakan kadai ya isarmin....don Allah" ya fada yana hade hannayensa waje d'aya alamar roqo
"Naji ya isa,ka sameni ta wayar" ta fada tana juyawa don ta shige gida kamar wadda take kan qaya ko wuta
"Tsaya mana shahida....." Yayi hanzarin fada,tsayawa tayi cak kamar yadda ya umarta,saidai bata waiwayo ba a haka ya cimmata,gabanta yasha,yana murmushi ya miqa mata wata leda
"Ga wannan,ki karba don Allah....." Batason doguwar magana saboda haka ta saka hannu ta amsa kawai ta shigeshi,kallo ya bita dashi yana jin dad'i cikin ranshi,yau an samu wani ci gaba da har shahida karo na farko ta amshi abun hannunsa,tabbas watarana yana saka ran komai zai wuce,bai taba tsammatar tsintar kanshi cikin soyayya makamanciyar wannan ba,saidai shahida ta cancanci komai,tana da nutsuwa tana da hankali uwa uba kyau,shahidan tayi masa,tako ina ta amsa sunan irin macen da yakeso,yake da burin mallaka,macen da cikin dubu sai an duba.

Tana shiga a nan falo ta ajewa huda ledar,tace ta dauka ta bata,tana jin huda na tsallen murna da kacaniyar bude ledar tawuce dakinta ta hau sabgar gabanta,duk don ta yakice komai,wanka ta soma yi,sannan ta jawo plate din abincin data shigo dashi daxu sanda zata fita wajen nuraddeen din ta soma tsakurar abincin ciki,ci take kawai,amma ko za'a rutsata da bindiga batasan wanne taste ke ga abincin ba,tana cusa wa ne kawai maganin yunwa,duk sanda taji irin wannan yanayin tattare da ita tasan cewa can cikin zuciyarta ba lafiya qalau take ba,ta hanata kanta dukkan wani tunani,ta bude jakar makarantarta ta dauko exams din dalibanta ta shiga marking tana shigarwa cikin paper din dake dauke da sunayensu.

Tana tsaka da haka wayarta dake aje can gefe ta soma haske,don dama abadan wayarta a silent take,batason wani qwaqwwaran motsi da xai dameta,daga kai ta dubeta,kamar ba zata daga ba saita miqe tsam tace ta duba,anty amina sunan dake yawo saman screen din kenan,dan qaramin murmushi ta saki wanda bai bayyana ba koda saman fuskarta ba bare mutum ya gane,saida ta bari wayar ta katse da kanta sannan tabi kiran
"Ranki ya dade yallabiya,don naga alama kin xama hukuma saida lallashi,kinbar rayuwar kowa bare ki nemeshi ko?" Wani murmushin ta kuma saki wanda yafi ja daxu armashi fa bayyana,sai data koma ta zauna inda ta tashi sannan tace
"Ni na isa,ta yaya zan manta da anty amina ta?" Ta fada tana tura hular kanta zuwa baya,hakan saiya qara fidda kyanta,sakamakon gashinta mai santsi daya bayyana
"Gashi kuwa?,kin d'aura aniyar mantawa dani din?,anya duniya da amana kuwa shahida?" Duk sai komai ya tsaye mata cak,duk da cewa gaskiya anty aminan ta fada,abinda bata sani ba tana gujewa kiranta ko haduwa da itane,saboda tana daga cikin abubuwan dake tuna mata baya,wanda take ra yaqi shafe komai shekara da shekaru
"Yanzu dai ayimin afuww,inayini anty amina mun yini lpy?"ta fadi tana kada biron dake hannunta hagu da dama
"Lpy alhmdlh....ya gida?"
"Lpy qalau muke,ina yarana?"
"Yaranki duka sunyi fushi" murmushi ta sake saki
"Suyimin afuwa,ina nan zuwa,zuwan ba zata"
"Haka dai,kullum maganar kenan,fafur kin qimu kin gujemu,na rasa ma LAIFIN NA WAYE?" jin anty aminar nason fadawa wani bigiren na daban ya sanyata soko wata hirar don kauda waccar maganar
"Zan baku mamaki anty amina,kedai ki sharen hanya"
"Yo sharar hanya kuma ta nawa,na share na share har na gaji,kedai sai an ganki kawai" sai ta miqawa yaran nata wayar suka shiga gaisawa d'ai d'ai da d'ai,su dinma bikonta sukeyi duk tace musu tana nan zuwa susha kuruminsu,daga bisani suka miqawa mamarsu wayar suka dan sake tattaunawa sannan sukayi sallama da juna.

Tana shirin aje wayar wani kiran ya sake shigowa,anty zubaida ce take kiranta
"Ki sameni a falo" ta fada kawai ta yanke kiran,saita sauke wayar daga kunnenta tana miqewa tsaye ta gyara daurin zaninta,tana zura hijabinta wayar ta sake haske,nuradden ne ke kira saita dauke kai ta qarasa saita hijabin nata ta fice a falon.
Chapter 5 · 0% Book details