← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 73

Sashe 29

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai data raba dare tana gayawa kanta ya kamata ta motsa gaba,ta watsar da komai,ta ciyar da rayuwarta gaba,ya kamata ta shafe komai kaman yadda take gayawa kanta a 'yan kwanakin nan,idan bata manta ba,idan kuma zata iya tunawa,anwar din data gani dazu da anwar din data gani satin daya gabata ba shine anwar din data sani shekaru goma baya ba,lallai ba shakka bashi bane,ya kamata aga wata shahidan ta daban ba wannan ba
"Yes!" Ta fada tana baiwa kanta qwarin gwiwa da tabbacin zata sauya komai.

Washe gari da qwarin gwiwarta ta fito,hakanan tayi yaqin maida murmushi da fara'arta gaba daya,koda bata samu duka ba taji a jikinta ta maida kaso hamsin cikin dari,wanka ta soma yi sa'annan ta fito ta shirya cikin kwalliya madaidaiciya a riga da skert na atamfa don kusan tafi son atamfa saboda tana son kaya cottoon kasancewarta mutum da batason zafi,feshe jikinta tayi da turarenta na din din din,ta tsaya gaban mudubi tana kalli kanta,ita kanta tasan tayi kyau,kwalliyar data jima bata bari ta rabi koda fuskarta ba,murmushi ta sakarwa kanta da kanta tana sake baiwa kanta qwarin gwiwa,sai taji gaba daya hankalinta ya karkata ga aikin da abbun yace zai sama mata,batason ci gaba da zama haka
"I need to make my self busy,so i can forget dat am deeply hurt and broke" ta qarshe maganar tana juyawa cikin hanzari ta dauki wayarta ta fice daga dakin.

A tunanin anty zubaida zata ganta sukuku ko cikin damuwa saboda maganar jiya amma sai taga sabanin hakan,itama hakan yayi mata dadi sosai,ranar alhamis ce babu islamiyya,haka ta sake sosai cikinsu huda sukayita buga games bayan sun gama karatu,ta kira mutanen data jima bata kirasu ba,ta kira zunnurarta sun jima suna hira,har ita kanta ta dinga tambayarta yau da alama ranar ta musamman ce.

Koda noradden yazo shima yazo yau a sa'a,ta tanqwara zuciyarta ta fita ta saurareshi ba tare da wani dogon turanci ba,ba laifi kuma ta dan jima wajensa,don ta dauki mintuna aqalla ashirin abinda bai taba faruwa ba a tarihin zamantakewarsu,ita kanta yau taji zuciyarta sakayau kaman ta rage mata nauyi daga cikin nauye nauyen dake takure da ita. *zafafa biyar na kudine,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karkiyi sharing,idan kina buqatar siya ki tuntubi wannan number*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

*ga mai buqatar littafina da zanyi bayan kammala alqawarin Allah,yaje youtube yayi searching SAUTIN HIKIMA,zaiga SUBSCRIBE da jan rubutu ya dannan zai koma black,yayi screenshoot ya turo zuwa ga number da zatazo a qasa,zan sakashi group din da yardar Allah SUBSCRIBW KYAUTA NE BA'A DAUKAN KO SISI*

07038670166

*Alqawarin Allah*
2️⃣0️⃣

Zaune yake shi daya cikin dan qaramkn garden din dake bangare raban na gidan nashi,wanda yasa aka masa shi sannan aka qawata masa,yakan yawaita zama lokaci zuwa lokaci musamman a sanda yake buqatar kebewa ko yin wani gagarumin aiki da bai buqatar surutu ko takura,snye yake da t.shirt mai gajeran hannu gami da trouser light and dark brown,tray ne dan qarami aje a ganshi da butar shayi hadi da qananun kofuna guda biyu akai,daya kofin yana hannunsa,idanunsa zube kan laptop din dake kunne gabanshi tana aiki yana kallon wani aiki daya soma tsarawa,inda yake fidda duk wajajen dake da kura kurai,yayi. Da wani sashen kuma ranshi ke a bace saboda sanarwar da nafisa ta fitar a fashion tv,baisan ya akayi ba sai saqonnin taya murna ya tashi dashi fal email dinshi,watsapp dinshi da twitter,angage din ma da ba'akai ga tabbatar dashi ba.

Qarar bude gate din gidan da mai gadi yayi ya shiga kunnuwansa,sai yayi tsai yana sauraro,iyakar saninsa yasan dai ya gaya masa kar yabar kowa ya shigo masa gida idan ba muhsin ba,saboda yana son ya hada hankulanshi waje daya,zuciya da qwaqwalwarsa ta samu cikakken hutu.

Ba'a wuce minti biyar cikakke da budewar ba ya juyo taku,kamn ya juya saiya basar yaci gaba da abinda yake,don qamshin turarenta daya rigashi isowa ya gaya mishi ko wacece.

Ta dauki minti biyar tana tsaye a bayanshi,hannayenta harde a qirji tana qare masa kalla,ba shakka ta jarabtu da son anwar irin soyayyar da bata tsammaceta ba,har kwanan gobe kuma bata ji a jikinta zahiri da badini ta samu irin soyayyar da take kwadayi daga gareshi,haka ta gaji ta saki hannayenta tana fidda ajiyar zuciya ta taka har inda yake,gabanshi ta zagayo ta tsaya tana dubanshi,fuskarta a narke haka ta karyar da wuyanta,sai daya mula don kanshi sannan ya dago ya mata kallo daya,haka kawai yakeji wasu abubuwa marasa dadi akanta,har yanzu baisan a wanne aji zai sanya nafisan ba,ta kuma qi ta gane taqi ta fuskanceshi
"Baki iya sallama ba?" Sai tadan sassauta kwabw fuskar da tayi,tana son ta koyi sallama duk sanda ta iskoshi kaman yadda ta fahimci tsarinsa ne amma takan yawaita mantawa,kuma mima ta gaya mata dole ta siffantu da duk wani yanayi da tasan yana so yana kuma cikin tsarinsa
"To salamu alaikum" amsa mata yayi duk da har yanzu bai daga kai ya sake dubanta ba
"Ba zakace na xauna ba?" Ta fada cikin shagwaba,ture kofin dake gabansa yayi
"Sai nace ma?,ai ga kujera nan kina gani ko?" Kai ta gyada a hankali taja kujarar dake fuskantarsa ta zauna.

Hannayenta ta hade waje guda,ta sake sassauta murya
"Dear...don Allah me nayi maka?,me yasa kakeson sanya zuciyata cikin rudani,kasan ya nake ji duk sanda na kiraka baka daga ba,ko na turo maka saqo baka karanta ko ka turamin reply ba?" Idanunshi ya daga ya dubeta sai ya sake kautar dasu yaci gaba da abinda yake,tunu qwalla ta cika mata idanu,ta tsani wannan miskilancin nashi ya motsa,wahala takesha,tana ji a ranta duk sanda ya soma shariya irin hakan kaman dai ya tuna tsinanniyar yarinyar da yanzu tsanarta ta ninku a zuciyarta wato shahida,data sani baya ga rabasun da tayi ta nakastata yadda ko da wasa ma bazai sake kawota cikin zuciyarsa ba,amma data taba masa zancan ya tunata ne ranar taqa zallar bacin rai,ya gaya mata karta sake mishi wannan zancan don ba huruminta bane,sannan kuma karta sake masa maganar wata shahida,abinda ma yasaka ranta ya danyi sanyi kenan,ta cika da fatan Allah yasa tabar ranshi kenan har abada.

"Meye laifina dear..." Ta fada cikin son fashewa da kuka,saiya tattara dukkan abinda yake gefe guda ya rufe system din sannan ya daga kai yana dubanta duba na kai tsaye,yana fata Allah ya yaye mata wannan son da take masa,sam ko kadan shi hakan baya masa dadi
"Ni na aikeki kona bada daman ki bada sanarwar engage dinmu rana ita yau?" Kai ta girgiza tana dubanshi hawaye na sake cika idanunta
"Wannan wacce irin banzar dabi'a ce,mu yahudawa ne nafisa?" Nan ma kai ta gyada saidai cikin ranta tana jin dadi da sauqin radadin da take ji,ta zaci wani babban laifi ne ta aikata,koya ganta ne ranan nan da saddam randa sukaje dinner din abokinsu,wanda basu dawo ba sai sha biyu da rabi na dare,ita a ganinta wannan sam ba laifi ne ba,hasalima saika isa ka qasaita ka amsa sunanka wani sannan za'a ga wani abu daya shafi event dinku a gidan talabijin din
"Kayi haquri,kuskure ne,bani na biya bama siyama ce tace lallai a saka"
"Siyama....ita tace rana ita yau din kiyi wani bikin engage namu kenan?,ohk tunda haka ne rana ita yau din ita saita tabbatar da abun kota tursasani" ya qarashe fada yana janyo wayarshi dake gefe,da sauri ta riqe hannun nashi don tafison a kawo qarshen komai,bata jurewa fushinsa,jinsa take har zuciyarta,kallonta da yayi ya sanyata saurin janye hannun nata,yasha mata kashedin tabashi ba sau daya ba ba sau biyu ba
"Don Allah dear don Allah,wallahi na fasa ba za'a yi ba" yana da tausayin mace hakanan mutum ne shi da tun asali yake tausaya raunin 'ya mace ko wacece
"Kome mutum xaiyi ya kamata ya dinga duba da abinda bai sabawa addini da al'adarsa ba,sannan ka dinga dogon nazari da tsinkaye a duk lamarinka kafin aiwatar dashi"
"Kayi haquri"
"Ya wuce" ya fada a taqaice
"Yanzu daga ina kike?" Kame kame ta soma yi,don tun dazun suka fito gantali ita dasu mima,yanzu haka suna cikin mota su suka rakota bashi haquri,ko hajiya bilkisu ma batasan tazo ba,ganin ta rasa qwaqwqwaran abun fada guda daya ya dakatar da ita
"Is ok...yanzu ki wuce gida"
"To yaushe xakazo?,kwana biyu ma gaba daya ka daina zuwa ko cin abinci,mama nata complain" ta fada cikin shagwaba
"Zanzo da zarar na samu dama"
"Can i call you anjima?" Ta sake tambaya,idanunsa ya lumshe kana ya bude,don maganar ta soma isarsa
"Allah ya kaimu anjima" miqewa tayi ta masa sallama cikin salon nuna qauna sannan ta juya ta fice daga gidan,ajiyar zuciya ya sauke sanda yaji fitarta,saiya hada kayanshi gaba daya don zaman gun har ya fita akanshi kuma.

Bacci ya samu yadanyi,qarfe hudu ya tashi,yayi alwala ya fice masallaci,daya dawo ya shiga wanka ya shirya tsaf cikin dogayen kaya wanda bai fiya sakasu ba,ya dauki wayoyinshi da maqullin motarsa ya fice,ya yiwa mai gadin sallama ya wuce.

Tafiyar mintuna qalilan ta sadashi da gidan anty usaina,suka gaisa sosai da mai gadin qofar da yake shiga,saidai qofar ana gyaranta ne saboda gate din yana masa tauri bai buduwa da sauri,tilas yayi rivers ba don son ranshi ba ya zagaya ta daya layin.

Idanunshi fes yana iya hangen qofar gidan daga qofar gidan anty usainar,a hankali ya dauke kanshi yana fidda zazzafar iska daga bakinsa,horn daya yayi aka bude masa don tuni ya zagayo mai gadin,ya saka motar tashi yayi parking sannan ya kasheta ya fito.

Anty usainan ya tadda da yaran ta zaune cikin valcony din dake gefan matattakala hudun da zata sadaka da babban falon gidan,assigment sukeyi,dukansu suka hada baki suna masa sannu da zuwa cikin girmamawa ya amsa,har ta miqe zasu shiga ciki taga yana zare sau cikinsa
"Barni daga nan anty na zauna cikinsu nima,sati biyu kenan bamu hadu ba" da d'aya da d'aya ya dinga bibiyar karatunsu,yammata masu kimanin shekara sha hudu sha biyar da sha shida,sai namiji mai shekara sha uku,yaji dadin yadda yadda ya samu karatun nasu na tafiya daidai,wansa daga qarshe ya sallamesu da kyautar dari biyar biyar suka shige cikin gida suna murna,wajen ya rage daga shi sai anty usainar.
Chapter 29 · 0% Book details