← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 73

Sashe 55

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dukkansu xaman kurame sukayi shida ita cikin motar,kowa ya kama owners corner ya hade fuska kaman zasu masgi juna,ta cikin glasa muhsin ya qare musu kallo,dariya ta cikashi,ya girgiza kai kawai,shikam wannan abun yafi masa kama da fadan masoya,sai shine daya gaji da shurun ya soma sako musu hira don gudun xaman shuru,ba wani hadin kai ya samu daga wajensu ba na tayashi hirar ba,har gwara ma anwar akan shahidan ta takejin wani abu ya tokare mata wuya,tunda suka shiga motar sai kace bai santa ba,kai bakace shine a daxun ke shirin mata daukan amarya ba.

Sanda duka isa muhsin shiya fara ficewa a motar,tana shirin budewa itama ta fita anwar ya danna lock,waiwayowa tayi ta dubeshi,batason wata magana ko gajerace bare mai tsaho saboda haka ta kalleshi kawai daidai sanda shima ya kalleta
"Saurin me kikeyi?,kina gudun jerawa ne dani,saidai ni na fiki gudun na jera dake don kar a dauka nida ke Ali yaga Ali ne"
"Ai baka cika wanda yake gudun jerawa da 'yar maye ba tunda zaka iya aurenta" ta maida masa amsa idanunta akanshi,saiya dauke kanshi yana cire belt din jikinsa,hakanan ya samu kansa dajin zafin kalmar 'yar maye data fada din.

Sanda suke shiga wajen babu wanda basu burge ba,duk wanda ya dora idonshi akansu saiya shagala da kallonsu,perfect martch da yawa suke fada,yayin da duka jama'ar dake wajen suka miqe don nuna girmamawa a garesu,da yawa wadanda sukasan tsohuwar alaqar dake tsakaninsu kuwa irinsu anty usaina zunnurah da maqota fuskokinsu sunqi gushewa da murmushi
"Lallai *ALQAWARIN ALLAH BAYA TASHI* ba wanda ya isa ya canza alqawarin Allah" zunnurah take fada a bayyane tana kallon maigidanta sanda shahida da anwar suka zauna a muhallin da aka tanadar musu,tana tuna tsahon zamanin da suka dauka basu tare,tana tuna yadda kowanne yaqi dan uwansa yake nesanta kanshi dashi,dai gashi cikin qanqanin lokaci ubangiji ya nuna buwayarsa,ya sake dawo dasu cikin rayuwar juna duk da yadda kowannensu ke tsaye kai da fata akan qudurinsa amma Allah yayi nasa hukuncin.

Sanda aka fara gabatar da komai akayi kiran dangin ango anty usaina ta fito sai abun ya baiwa shahida mamaki,ruwan kudin data musu yasa ta sanya ayar tambaya a kanta,wace anty usaina?ta tambayi kanta lokacin data tsaya gefan anwar suna magana qasa qasa yadda shahidan bataji,gabanta ya fadi cikin ranta tana addu'ar Allah yasa ba abinda take zato bane.

Saidai kuma addu'ar tata batayi tsaho na aka ware fili na musamman saboda babbar yayar ango aka bata dama,cikin qananun hawaye da suka kasa riquwa a idanunta ta miqe ta isa inda anwar da shahida ke zaune,tasa hannunta ta tashesu tsaye gami da dan matso dasu gaban step din da suke kai kadan yadda kowa zai iya ganinsu,ta karbi abun magana tayi taku biyu gaba kadan dasu sannan ta tsaya
"Yanzu da zan tambaya cewa suwa kuke gani a tsaye a nan wasunku zasuce amarya da ango,wasu zasuce masoya,eh....masoya ne saidai ba ordinary masoya da kowa ya sani ba,masoya ne da kalar soyayyarsu ta bambanta data kowa,masoyan da Allah zai cika alqawarinsa a kansu koda ba wanda yaso hakan,nasan zaku yarda dani idan kukaga wannan" saita juya ta kalli masu gabatarwa,cikin sakannin da basu wuce goma ba majigin dake kafe a bango daban dake hall din ya soma haske wanda hakan yaja hankalin kowa,ciki harda anwar da shahida,cikin qanqanin lokaci hotuna suka soma bayyana kansu daya bayan daya,hotunan anwar da shahida shekara biyar zuwa shida baya,mamaki ya kama anwar ni na a ina anty usaina ta samo wadan nan hotunan?,hotuna ne da sukan dauka lokaci zuwa lokaci shida shahidan idan yaje zance sanda ya siyi waya torching ya siya mata itama,tana ainihin shahidarta yana ainihin anwar dinsa,nan fa murmushi ya cika fuskokin al'umma kowa nabin hotunan daya bayan daya da kallo,abokan tsokana suka samu nayi,yayye da iyaye suka dinga dariyar hotunan,wasu da hijabai a jikinta,wasu ta sunne kai,shi kuwa yana dan tsirit dinsa babu wata cika ko kumari tattare dashi,a hankali hotunan suka dinga shiga zukatansu suna tuna musu wani lokaci can baya,lokutan da sukafi kowanne dadi cikin rayuwarsu,hoto na qarshe ya soki zuciyarsa shida ita,dukkansu basu manta ba,wannan shine hoto kusan na qarshe da suka dauka tsakaninsu dab da mai afkuwa zata afku,idanunta ta runtse hawaye nason saukowa tana hanashi,turota da anwar yayi daga gidansa shine abinda yazo mata a rai,daidai sanda shima ya dauke kanshi daga kallon hotunan,suna qarewa gurin ya rude da hayaniya da kuma tafu gami da sowa,saida mc ya daidaita komai sannan anty usaina taci gaba da magana
"Zuwa yanzu nasan kowa ya gasgata maganata ko?"
"Eh..." Duka hall din ya amsa,kaita jinjina sannan ta sake komawa gabansu tana dubansu har yanzu abun magana na hannunta
"Inason ku sake tabbatarmana da cewa zaku kula dakanku,zaku kula da amanar juna,ga shaidu nan suna kallo" ta qarashe maganar tana fidda murmushi gami da fatan hakan ya kawo sauyi tsakaninsu komi qanqantarsa,anwar ta fara miqawa abun maganar tana tsareshi da ido,dole ya amsa yakai bakinsa,sassanyar muryarshi mai cike da mazantaka ta cika hall din wanda hakan ya taso da tsohon mikin dake danqare zuciyar nafisa dake maqale ita da mima a wani sashe na hall din,ji tayi kaman zuciyarta zatayi bindiga,sonshi da qaunarshi ya sake narkewa cikin zuciyarta,taji inama tun farko batayi sakin bakin cewa ta fasa aurenshi ba?
"In sha Allah zan kula da ita,zan sauke duk wani haqqi nata dake wuyana..."
"Kayi mana qwange....zaka bata soyayya da kulawa?" Anty usaina ta tari numfashinsa ta fada cikin sauri ta sigar tambata,kasancewar ba abun magana a hannunta yasa wadanda ke zaune gaba gaba abokanshi su kadai sukaji me tace sai kuwa su,idanu ya fiddo yana kallon antyn ya tabbatar qure takeson yi masa,cikin qasa qasa da murya yadda su kadai zasuji yace
"Idan naga ta cancanta ba" yana miqawa antyn abun maganar,duka takai masa wanda ta manta ma a inda suka saboda jin haushi ya goce yana dariya,abun ya baiwa mutanen dake wajen sha'awa suka saka dariya gami da sanya musu tafi,harara ta jefa masa sannan ta juya ta miqawa shahida abun maganar
"Uhmm...uwar gidan anwar,ina naki alqawarin" murmushi ta qaqalo sannan ta jefawa anwar harara wanda har cikin zuciyarta ita tayi hakan,yayin da sauran mutane suka tsammaci soyayya ce
"Alqawarin daya dauka baiyimin ba anty,ba abinda ya iya,baisan haqqin soyayya ba baisan mutuncin masoyi ba,baisan komai ba a soyayya bai iyata ba" tsit kowa yayi yana saurarenta cikin mamaki,gaban anty usaina ya shiga faduwa,hasina da zunnurah dake zaune cikin mutane ji sukayi kaman su rugo da gudu su qwace abun maganar daga hannunta,yayin da nafisa ta tsaya cak farinciki na ratsata,me zai farune?,ba hadin kai tsakaninsu kenan ko jituwa
"Haka kikeso anty na fada irin kalaman da wata amarya da aka yiwa auren dole ta fada?,idan ban yabi masoyi kamarshi ba me zance?,bashi da buqatar yabo ko daukan alwashi a kansa,shi yasan komai,duk alqawarin da zan dauka anan na fallasa sirrin soyayyarmu ne,alqawarin daya dauka duka namu ne mu biyu basai nayi maimaici ba,ni dashi duka abu daya ne" ta qarashe fada tana murmushi saman fuskarta can qasan ranta kuma tana jin ciwon lafazinta,sowa da ihu wajen ya kaure dashi,ba wanda ya fuskanci me take nufi daga anty usaina saishi uban gayyar,sai zunnurah da hasina,kowa ya zaci cewa abinda ta fada din zallar soyayya ce da qauna,miqawa antyn abun maganar tayi,tana juyowa suka hada idanu dashi saita dauke idonta gefe guda.

Sosai dinner din ta qayatar ta sanya farinciki cikin zukatan al'umma da dama,takuma burgesu,komai ya gudana yadda anty zubaida tayi fata shahidan bata bada matsala ba,tayi qoqarin kula da duk wani motsi nata da action nata. *Alqawarin Allah*
3️⃣6️⃣

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Daurin auren da za'ayi sha daya na safe amma tun takwas na safe gidan ya soma cika da 'yan uwa,a sannan tana kwance daga saman gadonta tana kallon yammatan nata hada hadarsu abinsu suna breakfast,ko sha'awar abincinma batayi bare takai gaci,babu yadda hasina batayi da ita ba amma ko kallonta batayi ba bare ta tashi,sai juyi take daga nan zuwa can,ji take kaman zazzabi zai kamata,har goma saura tana kwance tana kallon masu wanka nayi masu kwalliya nayi.

A sannan ne anty zubaida ta shigo tana dubanta
"Wankanne yau baki da niyyaryi ko kuwa?" Bata amsa mata ba illa miqewa da tayi ta zauna sosai saman gadon tanajin jikinta a matuqar mace,haka zuciyarta a cunkushe,kanta a qasa anty zubaida ta aje ledar hannunta
"Ki tashi kiyi wanka ki shirya,mai kwalliya zata shigo tayi miki"
"Anty.." Ta kira sunan anty zubaidan zuciya a karye,juyowa tayi tana kallonta
"Don Allah ki qyale mai kwalliyar nan yau,don Allah" dan shuru tayi sannan tace
"Shikenan zata koma,hasina ta shafa miki ko powder ne" daga haka ta fice daga dakin.

Dariya hasina tayi sosai tana qarasowa inda shahida ke zaune tana tare qwallar idonta,idan da hali yau batason ko sau daya tayi kuka
"Hajiya shahida,nikam na rasa me kike nufi,don Allah yammata ba kukan dadi wannan matar take ba?" Ta tambayi sauran yammatan dake dakin tana watsa hannaye,dariya aka sanya sannan ta dora
"Allah ya baki miji irin wannan da yaji komai da komai amma ki tsaya kina wani nuna qiyayyar banza,ke idanunsa kawai aka kallah Allah ansan dan soyayya ne na qarshe,baku lura da yanayin kallonsa bane?" Ta sake jefawa 'yammatan dakin tambaya
"Ashe bani kadai na gani ba,nida daada ta fadamin tun farko aini zan sako kai akwai amanta da batunki" daya daga cikin cousin sis din shahida ta fada,muryarta kamar ta mutumin daya tashi yanzu a bacci tace
"Yanzu ma lokaci bai qureba,da zasu taimakeni da sun maida daurin auren kanki,don Allah ki shaida musu" daya daga cikinsu ta saki dariyahatda qyaqyacewa
"Kuna ganin idonta kunsan qarya take,wannan aka qwace miki shi idan baki kuka ba yanzu gaba sai hawan jini ya kamaki" dukka suka sheqe da dariya,abun ya bata haushi ganin wai basu yarda da ita ba
"Nikeson anwar?,amma kun yaudari kanku" daga haka ta zira takalmanta ta shige bandakin ganin suna sake turata.

Kafin sha daya na rana layin ya dinke tsaf da jama'a,hayaniya ta kowanne sashi,yayin da fargaba da faduwar gaban shahida suka dadu duk sanda wani minti ko sakan ya shude,idanuwanta kan agogo,duk surutan da ake cikin dakin bata jinsu bare ta fahimci me suke fada.
Chapter 55 · 0% Book details