← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 73

Sashe 45

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sanda ta kammala saman abun sallar ta zauna tana jan hasbunallahu wani'imal wakil,saboda faduwar da gabanta yaketa yi wanda batasan dalili ba.

👑 https://youtu.be/H7M7h6l6wNM

*xafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don girman Allah karki sharing,ga mai buqatar siya zai tuntubi wadan nan numbers din*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

*Alqawarin Allah*
3️⃣0️⃣

"Kana nufin kaine mutumin daya kawo sadakina da mudin airena ba tare da sani ko yardata ba?" Ta furta wani bala'i na cinta,maimakon ya bata amsa da baki saiya daga mata dukka girarsa biyun yana dubanta kai tsaye ya kafeta da idanunshi,wani tashin hankali taji ya rufto mata irin wanda bata taba jin irinsa ba tunda maganar aurenta ta bullo,tashin hankali da ba'a saka masa rana,ko zata yarda da kowa ba zata yarda da anwar ba,ko zata amince da auren kowa ba zata taba amincewa da auren anwar ba koda su biyu kadai suka rage a duniyar,murmushin takaici ta saki wanda qasan zuciyarta ji take kaman zata fashe
"Kaima kasan ka dauko abinda bazai taba yiwuwa ba har abada,tamkar wanda ya mutu ya dawo ne,kai bakaji kunya ba anwar?,kana tunanin akwai abinda yayi saura?,kana tsammani akwai wani sauran abinda ya rage tsakanina dakai?,to bari kaji na gaya maka,ba zaka taba samun yardata ba,ba zaka sake samun soyayyata ba,har abada aure tsakanina dakai,har abada...." Qawataccen murmushi ya saki,da alamun kwanciyar hankali kwance kan fuskarshi,sai daya sauke qafarsa ya sauya jinginar da daya sannan ya rungume hannunsa daya dayan kuma yana shafar sajensa idanunshi a kanta,fara'ar fuskarshi ta bace bata
"Hajiya shahida....dukka tunaninki bai baki dai dai ba,baije inda ya kamata yaje ba" sauke qafarsa yayi ya soma takowa inda take tsaye,sai daya rage tazarar dake tsakaninsu sosai sannan ya tsaya ya soke hannayensa cikin aljihun rigarsa
"Kina tunani ko tsammanin soyayya ce tasa na nemi aurenki?,ko kina tunanin neman yardarki nake kafin na aureki?"sai ya sake takowa gab da ita kamar zai hadeta da jikinsa,ya nunata da yatsa
"Zan aureki don na nunawa wancan wawan cewa nidin na girmi qaramin dalili babban dalili ne ni,sannan nayi isar da zan yanke guntuwar soyayyar da yake taqama da ita,soyayyar da bai iyata ba,bai gama saninta bama bare ya iya,baisan kanta ba baisan mece ita ba!" Ya qarasa fada yana dan daga muryarsa gami da nuna qofa da yatsa kai kace nuradden ne ke tsaye a wajen,saiya sauke hannun nashi yana maidashi aljihunsa kana yaja baya kadan har yanzu bai dauke idonsa daga kanta ba
"Yana tunanin ya sanki?,yana tunanin yafi kowa saninki koya riga kowa saninki?,ya gayamin magana yayi tunanin yaci bulus?,inaso yaji ciwo ya kuma ci gaba da jin ciwo a ransa duk sa'a daya da zata wuce da tunanin wani mai suna anwar ya haramta masa auren wadda yake iqirarin yanaso,wadda yake iqirarin ba wanda ya isa ya shiga tsakaninsu" yana kaiwa nan ya juya mata baya,yana jin kamar ana yankar zuciyarsa
"Baki cancanci na qyaleki kici gashin kanki ba,baki cancanci na barki kiyi zabin da kikaga dama ba,bayan kin cutar da zuciyar da bata cancanci sakamakon da kika bata ba,kin bata rayuwar da alokacin ya kamata ki tattaleta kodon iyaye da qannenki,kin bada jikinki ga wani har yayi ajiya a wajen daba muhallin......" Saiya kasa qarasawa saboda wani dunqulallen abu daya tokare masa maqoshi,ya dinga jin wani turari tun daga zuciyarsa zuwa fuskarsa,bakinsa yaji ya dauki zafi ya fitar da iska zazzafa,yana jin wani irin ciwo da qunci duk lokacin daya tuna da lokacin da kuma abinda ya faru,hotunan dake wajensa da ganin da yayi kaya ido da ido sun kasa gogewa daga qwaqwalwa da zuciyarsa,yana jin wani irin ciwo mara misaltuwa,tabbas da yana da iko daya dawo da lokacin ya goge duk wani abu daya faru ko xai samawa zuciyarsa salama.

Tuni hawaye ya soma wanke mata fuska tana tuna lokacin da abinda ya faru alokacin daya bayan daya,sai a sannan ta dinga tuna kaman ta ganshi,kaman a gabanshi aka sauketa,hakan na nufin ya ganta cikin maye?,ya ganta a lokacin da jini kebin qafafunta?,yaga sanda aka cillo mata pant dinta da kwalabenta?,amma me yasa ya zama mai qaramin tsinkaye?,mai yasa ya zama mai gajeran nazari?,me yasa ya yanke mata wannan danyen hukunci farat daya,haka soyayya take?,haka masoyi yakewa masoyinsa?,sai taji ya sake sireta,daya zama mai dogon nazari da dukka abubuwan da suka faru yanzu basu faru ba
Ranta ya ninka bacin da yayi,hankalinta taji ya tashi,da qyar ta bude baki cikin muryar kuka tace
"Mugu azzalumi,ba ruwanka da kowa sai kanka,ba ruwanka da damuwar wani sai taka,ka tanadi mugun nufi akaina kan abinda baka da cikakkiyar hujja a kai...."
"Wacce huja nake nema baya ga wanda na samu....!" Ya juyo a fusace ya fada idanunshi da suka kada zuwa jaa suna kanta
"Ba hujjar kake nema ba,kanayin komaine don ka wulaqantani dama,ka shirya komai ne donka tozartani,to Allah ya fika,ba zaka taba samun nasara a kaina ba,nuradden kuma idan Allah yaga dama kai baka isa ka rabani dashi ba"itama ta fada cikin tunzura fushi da bacin rai
"kome zaki fada dai dai ne,duk yadda kika fassara lamarin a ranki ko a bakinki kisa a ranki haka ne,any ways ma ni nasan na taimaki rayuwarki ne,ko kina tunanin wancan wawan idan yaji wace ke a baya zaici gaba da haukan da yake a kanki?,kinga 'yammata....koki sawa ranki sauqi ko kar kisa duk uwar ubansu daya" kai take gyadawa bacin rai na cinta,idanunta fes cikin nashi,ji take kaman ta shaqe anwar din,a yanzu babu halittar data ji ta tsana sama dashi
"Zan saka salamar duk da bakayimin fatanta ko burin samunta,amma ka sani....tsugune bata qare ba,don babu abinda zanyi da masoyi irinka nawar!,ka shirya tarbar duk wani abu da zai tunkaroka!" Tayi lafazin da alama wani abu ya motsa ranta qwarai,duk da murta na a raunane amma amma fuskarta da qwayar idanunta na bayyana jarumtarta,wani malalacin murmushi ya saki ya sake matsowa inda take,wannan karon har qamshin turarensan nan data sanshi dashi yana busowa zuwa hancinta,ya kafeta da idanunsa,muryarsa can qasa kamar mai shirin furta kalaman soyayya a gareta yace
"A shirye nake,kece zan gayawa ki shirya zama dani idanma ba'a shirye kike ba,yaushe kikeso wasan ya fara?" Ya fadi cikin halin ko in kula,ganin kallon da yake mata bacin rai ya sanya ta fashewa da kuka sosai ta zube saman kujerar tana rufe fuskarta da tafin hannunta,saiya tabe baki yana isa inda hularsa take yasa hannu ya dauka yana cewa
"Ashe raguwa ce ta gaske,tun yanzu?,wasan namu kuwa zaiyi iri qarkon da nakeso?" Ya dora hularshi saman kansa sanda ya qarashe maganar,saiya sanya hannunsa cikin aljihunsa ya ciro kudade sabbabi masu dan yawa ya aje hannun kujerar da take kai yana cewa
"Ga kudin zance nan,kuma bance a sayi abunda za'a bugu da kudina na,idan aka siya Allah ya isa na" sosai maganar ta doketa,tana niyyar daga kai ta dubeshi ta fuskanci ya juya zai fita ne,har yakai bakin qofa sai yasake cewa
"Ammmm..." Yana dawowa da baya,kanta yazo ya tsaya hannunsa daya a aljihun wandonsa dayan kuma yana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa
"Karki manta da sadakina akanki,shaidu kawai za'a tara a daura,ban lamince ki kula kowanne dan iska ba,ciki harda wannan looser din,idan kuma kikayi hakan shima Allah ya isa ban yafe ba" saiya sassauta murya ya sauko da kansa qasa qasa gab da ita
"Ina fata har yanzu wasu daga halayen anwar basu bace miki ba daga kanki,mutum ne mai kishi,ina da kishi kan mace koba wadda ban biya sadakinta ba bare wadda na cire halalina sa nasha wahalar nema zafi da sanyi nabiya" a fusace ta bude fuskarta saboda yadda maganganunshi suka isheta,saita ganshi dab da fuskarta,cikin bacin rai da muryar kuka take cewa
"Sadakinka din banza da wofi,idan kana son nunan kudinka wata tsiya ce kaje ka karbi sadakinka idan har ka isa cikakken namiji" tsaf ya karanci bacin ran dake kwance muraran saman fuskarta,saidai yadda yake jin quna yana tunanin bata jin haka,duk sanda zai kalli fuskarta yana tuna sanda aka sauketa ne a gabanshi,cikin maye,cikin jini,pant dinta a gabanshi aka cilloshi,wani ya riqe zuwa jikinsa gaban idanunsa,saiya runtse idanunsa kana ya bata baya ya soma takawa
"Idan kin isa ke kije ki karbo kin kiga idan ban amsa ba,dama taimako nayi kuma na fuskanci ke bakiga hakan ba" daga haka ya qarasa ficewa daga dakin,sake rushewa da kuka tayi,ta tsani kalmar taimakon nan,wannan wanne irin cutace?,ita zai taimaka.

Cikin gida ya qarasa,daada na rumfarta a zaune ita da hasina,saiya cire takalmansa ya zauna saman tabarmar dake shimfide qasan inuwar bishiyar dake tsakar gidan,daadan tayi tayi dashi ya shigo amma yace wucewa zaiyi,dole ta fito ta zauna daga gefan tabarmar itama
"Zan wuce daada,ina tunanin rana ita yau za'a kawo lefe,to bansan inda za'a kai ba,can wajen umma,ko nan garin ko kuma gidan uncle hisham?"
"Babu damuwa akai can hidan hashimun tunda acan za'a yi duka bikin,muma can zamu tattara ai mu tafi"
"To daada,Allah ya saka da alkhairi ya qara girma" ya furta yana dan sadda kanshi qasa alamun girmamawa
"Ina kuma ta shiga?" Daada ta tambaya,ya fuskanci shahida take magana,saiya saki murmushin daya qwata fuskarshi duk da baikai masa qasan ranshi ba
"Tana daki tana kukan bata sona can na barota" kama baki daada tayi tana salati harta baiwa anwar dariya,harya miqe ya aje mata kudi ma sam bata kula ba tana ta jajjabi tare da sillewa shahidan hasina na dariya,sai daya sanya takalmansa sannan ya kalli hasina
"Taimaka kije ki fito da ita daga dakin karta rube" dariya hasina ta saki sosai,abun saiya qayatar da ita,ya yiwa daada sallama suka fice zuwa soron gidan shida hasina.
Chapter 45 · 0% Book details