← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 73

Sashe 49

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***** ******* *********

"Ina kwana anty" shahida ta fada sanda take sanya kanta cikin kitchen tana daura agogon hannunta,anty zubaida ta amsa hankalinta na wajen siyayyar da akayi mata tana dubawa,sai data gama daura agogon sannan ta daga kai,turus tayi yadda taga kitchen din ga kacame da kayyaki
"Anty,wadan nan kayan kuma fa?" Ajiye dan qaramin botikin butter din data duba tayi
"Kayan aikin abincin masu kawo lefe ne" wani mummunar faduwar gaba taji ta ziyarceta,duk wani dan kuzari data samu ta sauko dashi yau ya soma yin nashi waje,saita dan dafe kujerar dake kusa da ita
"Lefe kuma?" Kai anty zubaida ta kada tana karantarta
"Eh,jiya da dare daada ta gayamin" sai kawai ta kada kai tana qoqarin hadiye wani abu,ba tare data ce komai ba ta juya ta fice a kitchen din,ko abincin break dake saman tebur bata saurara ba ta fice daga gidan,ta samu mai adaidatanta na jiranta ta shiga ta zauna yaja suka bar gidan.

Ko data isa office rufe kanta kawai tayi ba tare data bar kowa ya shigo ba,ta rasa shin kuka zatayi ko kuwa,idan tayi kuka babu mai sauraren kukanta,idan bore zata ci gaba dayi wanda zatayiwa borenma bata ganshi ba,wannan wanne irin cin zaline anwar ya shiryawa rayuwarta?,me yasa zai bibiyi rayuwarta da irin wannan sakamakon na daban,tunda bai ra'ayinta ya barta tayi rayuwarta cikin salama,irin rayuwar da zata samu nutsuwa mana,saiya shigo don ya rusata?,ya rusa dukkan walwala da farincikin data jima tana tattalinsu da rainonsu?.

Kusan haka ta wuni cikin kamfanin babu cikakkiyar madafa ko mafita,don haka suna tashi ta yanke shawarar zuwa gida,donkarta koma ma ta tadda su anty zubaida na aikin kayan masu kawo lefe,lefen da takeji kamar ta cinnawa mai lefen da lefan kanshi wuta.*AA*
3️⃣2️⃣

Sallama tayi a tsakar gidansu,khadija dake qofar kitchen tana tankadewa umma dake cikin kitchen garin tuwo ta amsa,a matuqar kasalance kamar wadda tayi aikin shekara ta tsaya da qofar kitchen din tana gaida umman,ta waiwayo ta dubeta sannan ta amsa tana karantar yanayinta,khadija na gaidata ta amsa mata tana shigewa falonsu,jakarta ta aje waje daya sannan ta cire mayafinta ta dora akai,ta samu daya daga cikin kujerun falon ta kwanta tana sauke numfashi a hsnkali,saita tashi ta sake qaro gudun fankar dake sama tana juyawa ta sake dawowa ta kwanta a riginginen dai,haka kawai zuciyarta tayi wani rauni,hawaye ya soma bin kumatunta yana zirarowa gefan fuskarta,ta dinga shareshi akai akai,duk sanda ta tuna anwar zata aura sai taji zuciyarta ta quntata,a ganinta bata dace dashi ba,bata cancanci mutum kamarsa ba,tunda a baya ya iya guje mata a gaba babu abinda zai hanashi aikata hakan,bugu da qarima gaba daya auren manufa zaiyi da ita,yayi ne don kawai ya rusa walwalarta ya rabata da nuradden.

Umman ta dan jima tana kallonta ba tare data sani ba kafin tatako zuwa cikin falon,ta samu kujera daya ta zauna sai a sannan shahidan ta ganta,miqewa tayi daga kwanciyar kuka na balle mata sosai,baki ta sake umman tana dubanta sannan tace
"Saikace qanqanuwar yarinya zaki tasani gaba kina kuka?,meye hakan?" Zamowa tayi daga saman kujerar da take kai tayin kneeldown a gaban umman ta kama hannayenta
"Don girman Allah umma ki dakatar dasu,ke daya ce burina na qarshe,wallahi umma bana sonshi shima baya sona,ku aura min koma waye umma amma banda anwar?" Idanu ta saka tana kallonta,a iya saninta abinda ya faru tsakaninta da anwar ma laifi nata ne,iya abinda ta saninma baiyi zafin da zata rikice hakan ba harta rasa sukuni da walwala ba,Yayin da khadija wadda shigowarta kenan ta tsinci xancan ta dafe baki gami da zare ido cikin mamaki,har batasan sanda tayi subutar bakin cewa
"Yaaya?,ya anwar ne fa?" Daga kai umma tayi tayi mata nuni data fice,haka ta fita cikin dimbin mamaki,ta zaci antyn tata zatayi farinciki da dawowar anwar rayuwarsu fiye da yadda su sukayi,amma ga sabanin hankalinta sai taga ba haka bane sam.

A nutse umma ta zuba mata idanu,cikin sanyin murya wanda ke nuna har jikinta ma a sanyaye yake tace
"Ashe so kike ki tona mana asiri shahida bayan lullubin sutura da Allah yayi mana?" Ta qarasa maganar wani abu na taba zuciyarta wanda ya bayyana har a muryarta
"Shahida ashe baki qaunata?,ashe ba rufin asiri Allah yayi miki ba damu kanmu daya dawo miki da anwar?,meye a zuciyarki shahida?,bakison farincikina ashe da walwalata?"kai shahida ke girgizawa kuka na qwace mata
"ba haka bane umma,umma bana sonshi kiyi haquri umma,wallahi banajin sonshi kwata kwata"
"Shahida indai nice na haifeki ina....."
"A'ah,karki qarasa don Allah umma" sukaji wata murya da sako kanta kenan dakin ta tsinci zancan shahida na qarshe da lafazin umman ta fada,dukkansu suka juya suna kallonta,anty usaina ce,ta qarso inda suke zaune,wajen shahida ta nufa kai tsaye ta kama hannayenta sannan ta zauna gab da ita,hankalin umma yadan tashi kadan don ba zataso shahida tacigaba da magana kan anwar ba,don tana da tabbacin batasan wace ita a wajenshi ba
"Idan kika fadi haka kamar kin mata qarfa qarfa ne ai" tana kallon umman tayi maganar,wani sanyi shahida taji cikin ranta,tana fatan Allah yasa zuwan matar ya zame mata haske
"Idan kuma tana da hujjarta fa wadda tafi taku qarfi?,ki barta aji hujjarta da dalilanta tukunna".

Miqewa umma tayi
" bata da wata hujja ko dalili usaina"
"A'ah bari naji ta bakinta tukunna"
"Koda kinji ta bakinta na riga na yanke matuqar nina haifeta ina bata umarnin auren anwar" daga haka umma ta fice daga dakin tana mamakin wauta da sakarcin da shahidan takeson tafkawa,kamar batasan meya wakana cikin rayuwarta a baya ba,bata taba tsammanin ma anwar zai sake waiwayar shahida yace zai aureta ba sabida abunda idanunshi suka gane masa a zahiri ba labarj,dama tazo mata tanason tayi wasa da ita?,koda taqi anwar din batajin zata samu kamar anwar din,mutumin da tun wancan lokacin ya samu karbuwa cikin kaf danginta na uwa da uba,badon komai ba sai kyawun halayyarsa da kyawawan dabi'un da Allah ya huwace masa.

Maido dubanta kan shahida tayi bayan ficewar umma,suka hada idanu,hakanan shahidan taji gabanta ya fadi,ta dauke nata idanun tana matsar qwalla,cikin taushin murya ba tare data saki hannunta ba tace
"Shahida....inason naji meye matsalarki dashi wannan din da umma tace saikin aura,indai naji dalilanki masu qarfi ne nayi alqawarin tsaya miki harsai an warware komai" shuru na 'yan sakanni ya ratsa tsakaninsu,batajin zata iya furtawa wani komai,yin hakan kamar ta dabawa cikinta wuqane,tana ji ceqa wani sirri ne agareta ga duk wanda baisan meye faru ba,a hankali ta motsa labbanta sannan tace
"Kawai bana sonshi,shima kuma baya sona,hasalima mun rabu dashi a qalla shekara shida kenan,ba wanda keda muradin wani" shuru anty usaina tayi tana nazarin kalamanta,ba shakka akwai wani abu,amma dukkansu amsa kusan guda ce,jiya jiya ta titsiye anwar din kan meye sanadin rabuwarsu da shahida amma ya kasa bata amsa daya qwaqwqwara,kowannensu bayason fallasa asirin dan uwanshi,hakan na nufin akwai ragowar wani abu da yayi saura game da zukatansu qarqashin zukatansu kenan koda su basusan da hakan ba?
"Amma shahida....ya akayi kikasan baya sonki?,kuma dama an taba rabuwa hakanan babu wani dalili?"tambayar taso kaita maqura saboda rashin amsa
"Miji da mata ma kan iya rabuwa haka kawai ya saketa badon ta masa komai ba,saidon qarewar wa'adin zamansu da Allah ya qaddara musu" saitayi shuru tana hadiyar zuciya tana neman amsa ta biyu da zata bata wadda zata gamsar da ita,da qyar ta iya hada abun fadi bayan anty usainan tace
"Uhmmm,ya akayi kikasan baya sonki?"
"Duk wani abu na nuna kulawa ko xiyara da zai nuna saurayi yana son budurwa babu shi tattare dashi,sau daya ya taba zuwa wajena,shima bamuyi ganawar dadi dashi ba,ta yaya zance yana sona?" Ta qarasa maganar badon abinda ta fada ya dameta koya dadata da qasa ba,a'ah,ta fada ne kawai donta riqeshi hujjar da anty usaina zata taimaka mata ta rana wannan auren da take kallonsa a matsayin qarfen qafa mai wuyar kwantuwa a gareta.

Lallai ya zama dole ta shiga alaqar shahida da anwar,tana fata nan gaba dukkansu suyi dariya,tana fatan ko meye silar shiga tsakaninsu nan gaba ya zama tarihi,rayuwarsu ta koma kamar yadda take a baya
"Naji dadi da kika kasance yarinya mai biyayya wa iyayenta,ina mai miki kyakkyawan fatan ba zaki toxarta ba in sha Allahu,biyayyarki zata kai miki da ixinin ubangiji" da wannan kalaman sukayi sallama,ta fice daga gidan bayan ta samu umma ta roqeta kan karta gaya mata dangantakarta da anwar,donta tabbatar hakan zai baiwa shahidan kunya.

Tun a kan hanya ta soma gwada number anwar din,saidai bata sami wayarshi ba akashe take,da alama yana muhimmin wani abune,dole ta katse kiran ta isa gida,saidai lokaci lokaci tana gwada number tashi ko xata dace ta shiga.

Tana idar da sallar magariba ta soma shirin barin gidan,umma ta dubeta
"Amma da kin dan jinkirta tafiyar tukunna,saboda garin a dinke yake da hadari ga iska ta soma kadawa"
"Idan ya sauko bansan ranar da zai dauke ba,anty zubaida kuma zataji shurun yayi yawa,don ban gaya mata ma ina nan ba"
"Shikenan,Allah yayi miki albarka,yasa albarka a rayuwarku"
"Ameen" ta amsa tana maida qwallar dakeson fitowa,haka ta baro gidan tana tafiya kamar wadda batason taka qasa,wanda bai sani ba sai ya zaci salo ne ko tana sane,amma ba komai bane sai tsabar damuwa dake cinta a rai,tana jin yadda hadarin ya taso sosai sanda takai tsakiyar layin nasu,iska ta dinga kadawa tana ratsa jikinta,saidai sam bata damu ba,bata damu da ruwan ya sauko ya daketa ba,hakanan bata damu data koma gida donta samu mafaka ba.
Chapter 49 · 0% Book details