← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 73

Sashe 8

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsahon kwana uku irin hakan na faruwa tsakaninsu,ba wata magana data taba shiga tsakaninsu,duk sanda tayi yunqurin yin wata magana saita kasa sabida kwarjinin da yake mata,tana son tace ya daina rakota saboda ganin yadda idon sa'idinawan unguwa ya soma dawowa kansu saidai ta kasa furta masa hakan,cikin ranta takejin nishadi a duk sanda suke wannan tafiyar ta kurame tun daga masallaci zuwa qofar gidansu,ko sunanshi bata sani ba,sai taga meye nata na tambayar sunansa ma,aishi ya kamata ya soma tambayarta sunanta,wani sashe na zuciyarta ya qalubalanceta da a'ah ba haka ake ba,ke yakewa alkhairi,ko godiya baki taba yi masa ba kan rakokin da yake,ta jinjina kai tana tabbatarwa da kanta rashin kyautawarta,ta kuma quduri aniyar a gobe zata masa godiya ta kuma tambayi sunanshi,kai ta girgiza kuma tana sake sakin murmushi,batasan dalilin daya sanya take yawan tunashi ba,batasan me yasa takejin wani baqon yanayi game dashi ba tun ranar data soma dora idanunta a kanshi,bata da amsa,tilas ta aje tunaninta a gefe sanda ta jiyo muryar babanta sun soma rabon halin nasu shi da ummanta,saita miqe a hankali ta isa bakin windon dakinta,ta yaye dan labulen net din dake maqale jikin window din tana kallon yadda suke dagawa juna murya kamar zasu yagi juna,batasan lokacin da wani hawayen baqinciki ya sauko mata ba,baqinciki da b'acin rai ya bata dukkan wani farinciki data tsinci kanta a ciki,wannan wacce irin rayuwa ce?,ina zata je ta daina ganin wannan baqincikin da bacin ran?,tabbas da akwai inda zata ta qauracewa wannan masifar da tuni ta jima da tafiya,tana son mamarta,hakanan tana son bananta,duk cikinsu babu wanda take goyon baya a cikinsu,batasan me yasa suka zabi wannan rayuwar ba bayan ga zuria suna tarawa,hakanan kowa yayi musu shaidar kyakkyawar mu'amala a waje amma me yasa gidan aurensu ya gurbace haka kamar sansanin yaqi?,haka ta zauna cikin dakin ita d'aya tana rusar kuka harta gaji da jin sautukansu ta dannan kanta qarqashin filo tana ci gaba da zubda ruwan hawaye.

Kamar kowanne lokaci yauma ta shirya tsaf cikin atamfa riga da zani,sai hijabi mai hannu da yasha guga,kasancewar ummanta mai tsafta ce,hakan ya sanya dukka yaranta tun daga kan shahida zuwa faruqu zaka samesu fes dasu,hakanan ma gidanta da duk abinda ya shafi gidan,sosai higabi mai madauri purpule colour yayi mata kyau sosai,yau shigar ta musamman ce ita kanta tana jin hakan a jikinta,yau mai d'aukar matan bai qaraso ba tilas tadan zauna jiran zuwansa,tun tana jin ba komai harta soma qaguwa,haka kawai taji ra zaqu taje wajen,ta leqo agogo yafi sau nawa amma shuru yaron bai iso ba,saita kasa zama taci gaba da duba agogo har ummanta ta fuskanci haka,iya saninta shahida na zuwa kai sadakar abincin nan ne don kawai tana tsananin jin nauyin uncle isma'il,kusan kullum fuska a hade take tafiya a haka kuma take dawowa
"Ya akayi ne shahida?,ko tsoron makara islamiyya kike?" Cikin rashin jin dadin ranta ta kada kanta
"Toko yau zaki zauna kawai idan yazo saiya kai shi?"
"A'ah umma....zan kai bari dai yaxo din" ta fada da hanzari,don bata jin zata iya jurewa rashin zuwanta wajen
"To ai shikenan" umman tata ta fada tana kwashe shanyar kayan sawarsu da shahidan ta gama wankewa daxu,ciki harda ba mahaifinta don sam bata da quya ko gandar aiki.

Yana isowa ko zama bata barshi yayi ba ta sakashi ya dauka suka wuce,sai taga kaman bata sauri,kamar tabar wani yana jiranta,haka dinga ji har suka isa wajen.

Daga nashi bangare shima har ya soma tunanin me ya hanata zuwa har yanzu?,yana daga zaune cikin shagon bala yana duba agogon wayarshi,sama sama yake amsawa bala hirarsa,ya daga kai don sake kallon muhallin da take zama din sai yaga isowarta,wata ajiyar zuciya ya sauke ya zuba mata ido daga inda yake,kaman ance mata ta waiwayo sai suka hada ido,ta danso ta dirirce amma saita maze,ta samu waje ta zauna yayin da kowa ya soma fitowa da kwanonshi yana amsa.

Duk motsin da take sai taji kama idanunsa ne a kanta,eh ba kama bane kallon nata yake,a yau ya hana kansa kallonta,duk da ta kamashi yana kallon nata yafi sau shurin masaki amma ya gaza dainawa,haka suka dinga hada ido lokaci zuwa lokaci har abincin ya qare,hakanan yau take jin wani faduwar gaba,ta dinga hada kwanukanta da sauri tana son yau ta bace masa,saidai burinta bai cika ba,tana gama hadawar ya iso wajen,ya dauki botikin ya soma takawa,bata da abinyi illa binsa.

Suna isa inda suka saba ta zaci zaiyi yadda ya saba,amma ga sabanin tunaninta wannan karon sai yaja ya tsaya tsam yana riqe da botikin
"Baki da kirki" taji ya ambata,ba shiri ta dago suka hada ido,qwayar idonta cikin nasa,yayi.mata wani kallo fuskarsa dauke da murmushin da yasa gudun zuciyarta qaruwa,cikin hanzari ta sadda kanta jin yadda yake shirin karya lagonta cikin qaramin lokaci
"Nima na san haka ko baka fada ba....kayi haquri.....na gode da karamcin daka yimin harna tsahon kwana hudu,Allah ya saka maka da alkhairi"
"Amin...amma bawai kyauta nayimiki ba,nayi miki ne donki biyani" ya fada cikin salon tsokana,a nata bangaren ta zata da gaske yake,take mummunan tunani ya darsu a ranta game dashi,baya ta danja kadan sannan tace
"Ni bani da kudin biyanka,tun farko ma bansan biyanka kakeso nayiba da nace ka barshi" kai yake girgixawa dariya nason subuce masa,dariyar data qara masa kyau har tasa adam apple dinsa ya dinga motsawa
"Ba kudi nakeso ba 'yammata....zuciyarki kawai nakeso ki mallaka min" ya tsinci kansa da fada,don ya shagalta da kallonta har baisan maganar da yake qasan zuciyarshi ya bayyana ba,a bazata taji maganar,don bata taba tsayawa ga da ga wani namiji ya gaya mata hakan ba ita dashi baki da baki sai wannan karon,ganin ta riga dataji me yake fada ya sanyashi kada kanshi yana ci gaba da jifanta da murmushi
"Eh zuciyarki nakeso" cikin mintina qalilan kwanyarta ta hakaito mata abinda yake nufi,wata iriyar kunya da nauyi suka kamata,ta rasa tudun dafaww,saboda haka saita juya gudu gudu sauri sauri ta shige gida,yana tsaya mana amma ina ba zata iya ba,bata taba zaton a shekarunta sha biyar akwai saurayin da zai gaya mata wai yana sonta ba,kalmar tayi mata nauyi da yawa.

Murmushin jin dadi ya saki,ya zauna dakalin dake daura da gidansu,abinka da d'an makaranta ba'a rabashi da takarda,sai ya ciro qaramar jotter din dake aljihun wandonshi wanda ya gama duba wani karatu da ita yayi rubutu da basu wuce layi goma ba ya jefa cikin botikin,ya kira yaro ya bashi botikin shi kuma ya wuce.

*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

*Alqawarin Allah*
0️⃣7️⃣

Saida umma ta dinga qwala mata kira kan ta fito ta wanke kwanukan ta dauki abincinta taci kada lokacin islamiyya ya wuce sannan ta taso daga rub da cikin da tayi saman katifarta,ta harhada kwanukan ta kada ruwan kumfa ta soma sabesu,tanayi tana tunanin kalmar daya furta mata,ashe kalma ce mai nauyu da dadi haka,lokaci lokaci ta dinga sakin murmushi ita daya,harta zubawa botikin ruwa ta zubda ruwan sai taga takardar,ta tsame hannunta cikin kumfar ta dauki takardar sannan ta bude.

Soma fahimta da tayi takardar meye yasa tayi sauri ta shige dakinta,ta samu kebantaccen waje ta budeta inda zata sha iska ta bushe sosai sannan ta dawo taci gaba da wanke wankenta.

Kafin ta kammala shirin islamiyyarta saiga qawarta zunnurah ta iso cikin unifoarm din islamiyya
"Yauwa,dama banason cin abincin nan ni kadai,don Allah bari na dauko ki tayani" cewar shahida tana nufar kitchen ta fito da kwanon abincinta ta aje a qasa ta zauna dirshan
"Sauko malama muci"
"Ke nifa a qoshe nake wallahi ba abincin da zan iya ci"
"Ni zakima wulaqanci ko?,zaki sake cewa naci abinci a gidanku" tq fada tana saka hannu tayi bismillah ta soma ci zunnurah na mata dariya,wai ita zata cewa tana cin abincin gidansu,matar da nata abincin ma sai ya huce bata ci ba,hira suke jifa jifa shahida nacin abincin tana kuma duba lokaci kada a fito saga sallah a shiga aji basu tafi ba,saidai rabi da rabin hankalinta nakan takardarta dake shan iska
"Yauwa shahida....wai waye wanda yake rakoki ne kullum daga wajen sadaka" tsaida lomar da zata saka a bakinta tayi tana duban zunnuran
"Au har kin samu labari kema?" Harara ta watsa mata
"Uwar labari na samu,waye baya ganinku a tare wai kwana hudu kenan,tunda ansan baki kula kowa...."
"K'nnnn...nima ban sanshi ba wallahi zunnurah,acan nake ganinsa" dariya zunnurah ta saki
"Qawata nasan halinki sarai,duk yadda akai wannan din na dabanne tunda har kika kasa gwada masa halinki" murmushi ta saka,ita kanta tasan na daban dinne nasai zunnurah ta fada ba,tun kallon farko taji yakai mata ko ina,ganin farko taji wani qaqqarfan lamari dangane dashi,takan iya raba dare tana tunaninsa,kowanne second nata da tunaninsa take rayuwa
"Amma fa kinsan shaik hafiz zai shiga wani hali?" Dagowa tayi tana duban zunnurah kafin ta galla mata harara
"Kamar yaya?,sonshi nake?,ko ce miki yayi yana sona" nan ta zauna tsaf ta kwashe mata yadda dukkan dalibai suka lura da soyayyar da yake mata,baki ta tabe tana miqewa daga gaban kwanon,don ita dai tasan ko doguwar magana bata hadata dashi bare kuma wani abu daban can,fita tayi ta wanke hannunta ta dawo tana ware gogaggen hijabinta
"Qawata baki da mutunci fa,shaik ke kanki kinsan yammatan makaranta rububinsa suke,kuma kema kanki qaryarki kice baki san yana sonki ba,maimakon kiyi murna sainaga ke ko a jikinki labarin bai faranta miki ba ko d'aya"
"Don Allah zunnurah ki qyaleni da zancansa,sai....." Maganar tata ta katse jin sallamar fiddausi,yarinyar da tsakanin gidansu shahida da nasu gidan layi biyu ne,tun zuwanta islamiyyarsu shahida takeson qawance da ita,tun shahidan na janyewa harta saki jiki da ita,saboda ta lura yarinyar itama nada hankali,yawan shuru shuru da rashin son hayaniya.
Chapter 8 · 0% Book details