← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 73

Sashe 28

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai daya tabbatar da fitar likitan sannan ya miqe riqe da takardar maganin ya qaraso inda anwar din ke zaune,idanu ya zuba masa yana kallonsa wanda hakan ya sanya anwar kau da kai
"Tsahon shekaru kana fama da wannan damuwar,kaqi gayawa kowa dalilinta,kaqi gayawa kowa dalilin faruwarta,duk dai amma bazai wuce akan shahida ba,anya kuwa anwar anya?,me yasa kake shirye shiryen halaka kanka ne babu gaira babu dalili?" Zumbur ya miqe ya soma takawa don barin gurin
"Kar sake cewa dominta ne,na riga dana shafe babinta kamar yadda na shafe babin komai daya faru dani a baya" qara sauri yayi ya wuce zuwa bedroom dinsa yanason baiwa kansa qwarin gwiwa don baison ma anty husaina taji cewa baida lafiya,yanzu dukkan tsofaffin matsaloli zasu taso,magana wata nabin wata har sai yaji kaman kanshi zai tarwatse.

Kwananta goma sha hudu tana qoqarin saisaita kanta da maida kanta cikin yanayin daya dace,yaqi tayi ba dan qarami ba a kwanakin da kanta,ta rame qwarai saboda jinya tasha sosai,bata fita ko ina,hakanan hatta da wayarta ma a kashe take,daga daki sai daki,sam anty zubaida batasan meye ya faru ba,saidai dukkaninsu tattalinta suke har ta soma jin dadin jikinta.

Ranar wata karaba qarfe hudu na yammaci ta fito daga dakinta,gidan yayi mata shuru haka yayi mata fadi,haka take ji duk sanda su huda suka wuce islamiyya saisu barta daga ita sai anty zubaida kawai,hakan ya sanyata tunanin samo islamiyya itama da zata dinga zuwa daukan karatu,don sanda ta fada din anty zubaida dariya ta dinga mata
"Ohni zubaida,shahida bansan inda zakikai wannan son karatun naki ba" murmushi kawai tayi
"Anty karatu fa baya yawa,indai ba mutuwa kayi ba ilimi bai yanke maka ba,ba zaka rasa cin karo da wani abun da baka sanshi ba"
"Gaskiya ne" ta fada cikin nuna gamsuwa.

Sanye take da atampha riga da zani wrapper,sai qaramin mayafi data yane kanta dashi,ta sake haske haka ta fada,a hankali take takawa har zuwa cikin ainihin falon,babu kowa kaman yadda ta zata,sabida haka ta juya ta nufi kitchen don tasan a wannan lokacin anty zubaida tana can.

Da sallama a bakinta ta shiga da dashasshiyar muryarta irin ta marasa lpy,anty zubaida ta juyo tana amsawa fuskarta qunshe da murmushi
"Patient an taso kenan"
"Wallahi anty...na gaji da kwanciyar nan" ta furta tana jan kujera ta zauna akai
"Ai gwara ki tattaka ko zakiji dadin jikinki" sama sama suke hira ita da anty zubaidan,inda tana daga zaune ta amshi wasu ayyukan tana tayata,a haka su faruq suka dawo daga islamiyya suka tarar dasu,zama sukai cikin kitchen din suma,saidai basu bar bakin anty zubaida ya huta ba,wannan ya buda wancan wannan ya buda wannan wai duka yunwa sukeji,sudai tunda anty shahida ta soma lalura kawai gidan sai a slow,waiwayowa anty zubaidan tayi
"Kinga shahida...don Allah debe qannenkin nan ku bani waje na yafe taya aikin wallahi" dariya shahidan ta bushe da ita sannan ta miqe tana duban su huda
"Oya....lets go" ta furta tana kada hannunta,ba musu suka bita a baya suka fice zuwa falon.

Haidar ne ya soma canza tasha zuwa mbc bollywood faruq yace sam shi mbc action xai kalla,huda kuma ta tubure ita mbc three takeso
"Dalla malama matsa kona kwada miki mari" faruq ya fada yana duban huda gami da zare mata ido
"A'ah wallahi,dalili dame?,bani remote din gaba dayanku na raba gardama
"please anty" faruq ya fada cikin langwabe kai yana miqa mata remote din,ta gane me yake nufi,saita basar tana cewa
"Babu wanda za'a kamo zabinsa,zabina kowa zai kalla" gwalo kowa kema dan uwanshi,tana murmushi ta kamo TVC news kwana biyu tayi missing labarai bata samun kalla,tana jin haidar na gulmarta
"Miss news" ta waiwaya ta kalleshi
"Zamu hadu anjima" da sauri ya dawo ya fasa hawa saman da yake qoqarin yi
"Sorry my aunty kar aji kanmu,niba dake nake ba,Allah kwana biyu dama da baki da lafiyar nan duk sanda ustaz zai karbi hadda fecewa nake kar 'yammatan ajinmu su min dariya...ki taimakeni"
"Saika biya cin hanci"
"Na yarda" ya fadi yana dariya,idnunta a kansu sanda suke wucewa dakunansu don sauya unifoarm dinsu,saida suka bace mata sannan ta janye idanun nata tana sauke ajiyar zuciya,duk sai taji kaman ita kadai keda matsala,takura da quncin zuciya,tana son ta rabu dasu amma ta rasa me yasa qoqarinta ya gaza?.

Ganin cewa suma ba labaran suke ba saita sauya tasha zuwa FASHION TV,sabuwar tasha ce amma tana tashe kuma ta samu karbuwa wajen al'umma sosai,sukan nuna abubuwa kala daban daban,kama daga sutturu na zamani,bukukuwa,birthday,engagment da sauransu,wani lokaci tana son kallon tashar saboda takan debe mata kewa,wasu abubuwan da suke nunawa na burgeta.

Yauma ta tadda suna hira da wata mai gyaran jiki shuwaarab cikin harshen turanci,shirin ya qayatar da ita sosai,ta bada dukkan hankalinta akai,sai suka yanke suka tafi talla,tallan farko da suka sako na engagment din wasu igbo ne,tsaki taja tana gyara zamanta saboda sam bata ji dadin tafiyarsu hutun ba,cikin ranta tana ganin rashin aikinyi ne kawai da zaka tsaya batawa kanka lokaci saboda an maka egage da wani,wai itama soyayyar nan gaba daya meye zaqi ko ribarta?,ta sake jan tsaki sanda aka nunosu suna bayyana yadda suke son juna da farincikinsu da kuma saqon godiya ga duk wadanda suka halacci bikin engage din nasu,remote ta dauka da niyyar sauya channel idan sun gama ta dawo,talla na gaba da suka fara haskowa sai yaja hankalinta matuqa fiye da komai,engage ne na wasu couple da za'ayi musulmai masu cikakken sunan hausawa,hoton farko na amaryar ne tayi kyau cikin shiga ta alfarma,wanda kallon farko idan kayi mata zaka tabbatar ta samu gata,hoto na biyu shi ya sanyata jin wani abu ya tsirga mata,a hankali kanta ya sara,hoton anwar ne a matsayin shine angon da za'a gudanar da bikin engage din nasu kwanaki goma masu zuwa,sosai ya fito tarwai,ya cika screen din tvn tamkar yana tsaye ne a gabanta,sanye da wasu shegun suit,daga sama har qasa shigarsa abar birgewa ce iya kallon mai kallo,miqewa tayi tsaye ba tare data shiryawa hakan ba,wani abu mai nauyi na danne zuciyarta kamar ana shirin riqe numfashinta ne,remote din taji ya mata kadan ta kauda fuskarsa daga screen din tvn,saboda haka bata tsaya ba har sai data dangane da socket din dake jone da kayan kallon ta kasheshi gaba daya,sannan ta juya da sauri don barin falon zuciyarta na wani irin gudu tamkar wadda taga wani abun tsoro.

Sallamar uncle hisham ita ta tsaidata cak,tasan dole ya ganta bai kyautu kuma ta wuce ba tare data yi masa barka da zuwa ba,daidaita yanayinta taketa qoqarin yi,kafin afkuwar haka anty zubaida ta fito daga kitchen din,da sauri ta juya don batason taga fuskarta,ta gwammace ta fuskanci uncle hisham a haka akan anty zubaida,yanzu zata saka ayar tambaya kan sauyawar yanayinta lokaci guda bayan ba haka ta baro kitchen ba.

"Sannu da zuwa abbu" ta fada a sanyaye idanunta na kallon qasa saboda tana ji a jikinta kamar qwayar idanun nata ba dai dai suke ba
"Yauwa rahamatullah(ya kirata da ainihin sunanta),ya jikin naki"
"Da sauqi abbu" ta amsa masa da sauri saboda wani abu dayake qoqarin shaqe mata wuya
"Ma sha Allah" juyawa tayi da zummar barin falon yace
"Shahida" sake juyowa tayi
"Na'am abbu"
"Anjima inason ganinki"
"Toh" ta fada tana sake juyawa zuwa dakinta.

Takai ta kawo tayi hakan yafi sau babu adadi,hawaye keson fita daga idanunta amma ta hana kanta hakan,tanason lalubowa kanta dalilin da zai sanyata kuka
"Enought is enought shahida,kinyi kuka a rayuwarki da yawa...ya isa haka,ya kamata ki kawo qarshen komai,ya kamata komai ya qare" take fadawa kanta da kanta bayan ta tsaya gaban mudubin tana duban qwayar idanunta da kanta gaba daya saika zaci zararriya ce,kallon kanta da kanta take tana bawa kanta qwarin gwiwa,saidai ina hawaye ba'a masa shamaki,saida daya ya ziraro mata wanda ya baiwa dukka sauran damar samun hanya,ta fashe da kuka sosai cikin sassarfa ta isa saman gadonta tayi rub da ciki tana cusa kanta qasan filo tana kokawar hana kanta ci gaba da kukan.

Kaman ba zata falon ba amma dole ta qarfafa jikinta ko don saboda abbu da yace yanason ganinta,ta gyra fuskarta gaban mudubi ta zizara kwalli bayan ta shafa powder,batason kowa ya fuskanci tayi kuka,a kasalance take kawowa har ta iso cikin falon,wanda a al'adar abbun dama bayan cin abincin dare yana zama ne cikin yaran nashi su taba hira kafin ya tattara ya wuce dakinshi.

"Rahama,meye ya faru ranar hutun noor international?" Tambayar da abbun ya jefo mata kenan bayan ta gama dubawa su farouq haddarsu da wajibul manzil da aka basu kan tajwidi,a hankali ta dago idanunta ta dubi abbun,daita sunkui da kanta qasa,tana tuna duk wani cin fuska da anwar yayi mata,tanq tuna kalamanshi akanta daya bayan daya,wani daci na tasowa daga qirjinta zuwa harshenta,saidai ta dake zuciyarta,batason ko daya ta sake zubda qwalla a rayuwarta saboda anwar
"Uhmmm..." Abbu ya sake bata dama ganin tayi shuru
"Abbu sun koreni ne"
"Kora kaman yaya?,me kika musu?,wannan wanne irin cin fuska ne?" Anty zubaida ta fada a hasale,yayin da abbu yayi shuru har sai da anty xubaida takai aya
"Dazu gamayyar malaman makarantarku sun sameni har wajen aikina,sun bani haquri kan abinda ya faru,na gaya musu banda masaniyar abinda yafarun,sun bayyanamin cewa mai makarantar ne gaba daya ya sallameki,dukkansu basu da masaniyar ainihn dalilin daya sanya ya koreki ba,duk da kina daya daga cikin haziqan malaman da suke alfahari dasu,idan don kamarace bake daya kika makara a ranar ba,amma suna so na baki haquri in sha Allahu zasu magana dashi master din,kuma sunsan yana da sauqi zai fahimta,to,duka dai sun gama bayanansu,na kuma ari bakinki naci musu albasa cewa kema ba zaki koma ba,idan baki manta ba dama kan yarjejeniya na barki koyarwa a makarantar,yanzu kuma abinda muka gina yarjejeniyar akai ya afku,saboda haka yanxu kinga nayi winning,dole ki karbi duk aikin dana samo miki kenan" ya qarshe yana murmushi,don bashi da ra'ayin tursasa dan adam ne,amma dama tun asali ta yaya shahida me matakin karatun irin wannan zata tsaya koyarwa a primary?,wanne irin maida kai baya ne
"In sha Allahu abbu,nima bani da sha'awar komawar har abada"
"Shikenam faduwa tazo daidai da zama,Allah yasa hakan shine yafi alkhairi"
"Amin abbu na gode" ta furta idanunta har yanzu na kallon qasa,nan ta yimusu saida safe da zummar zata sha magani ta kwanta.
Chapter 28 · 0% Book details