← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 73

Sashe 26

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ganin lokaci yana ja anwar yaqi soma maganar aurensu babban burin daya rage mata a duniya yasa ta soma masa shagube,qwarai ya fahimta saidai har yanzu baiji nutsuwar zama da nafisa a matsayin matar aurensa ba,duk da ya sani tunda ya furta dole ya cika amma har yanzu zuciyarsa taqi karban hakan,abinda yaketa yaqi akai kenan,ita kuma tasan cewa iyayenta ba zasu taba yi masa batun ba,mutum daya ce nan duniya zata ce yayi ya zame masa dole yayi anty husaina,dalili kenan da yasa ta wanki qafa bisa shawarar mima taje mata da batun,wanda a yanzu haka akan qadamin da suke kai kenan yanzu haka(idan baku manta ba a baya kunji inda anty usainan ke masa maganar kar suji kunya kan nafisan).

Ta bangaren shahida ma kwanaki watanni zuwa shekaru sun soma tafiya,tuni ta kammala degree dinta wanda ta samu gamasu da qananun shekarun da kowa ya kalleta sai yayi mamaki,hakanan ta dora da masters shima Allah ya taimaketa ta kammalashi cike da nasara mai tarin yawa,a sanda sakamakonta ya fito uncle hisham yaso ta amshi tayin lacturing da jami'o'i suka yi mata tace sam bata ra'ayi,ya tura takardunta kamfanoni da dama ta samu aiki daga wajensu nanma tace ba zatayi ba ciki harda kamfaninsu,ba yadda ya iya hakanan ya qyaleta.

Sanda tazo masa da zancan koyarwa a *NOOR INTERNATIONAL* sai daya cire gilashinsa ya kalleta don ya tabbatar da wasa take koda gaske,hakanan taji kawai bata da burin daya wuce itama yaran talaka su amfana da karatu ilimi da baiwar da Allah ya bata,ba haka yaso ba sam,saboda tayi karatu kai kyai wanda ya dace ta tsaya ta moreshi tayi amfani dashi ta hanyar yin aiki a gurbi da kuma bigiren daya dace,hanatayi kai tsaye yace maida kai baya ne,ta nace ta dage wansa ya sanyashi dole ya amince,amma bisa wasu sharudan.

Duk sanda suka mata wani abu da bai gamsheshi ba to ba shakka ta gama koyarwa a makatantar,kai tsaye ta amince don bata ga ma abinda zai gamota dasu ba bare wani abun ya faru,kan wannan sharadin ta soma koyarwa cikin makarantar,ta kuma samu karbuwa daga wajen dalibai har malamai,zama cikin makarantar kuma yayi mata,hakanan yana mata dadi qwarai.

Wannan shine labarin taurarinmu guda biyu da abinda ya zama sanadiyyar rabuwarsu ba tare dakowannensu yasan cewa MAQARQASHIYA CE ba.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Zaman bitar rayuwarsu ita da anwar din data tsaya yi daren jiya ba qaramin taba zuciya ruhi da kuma gangar jikinta yayi ba,tayi kuka irin wanda ta jima ta jefashi kwandon shara tare da yiwa kanta alqawarin ta daina har abada,dalilin daya sanyata makara kenan bata kwanta da wuri ba,hakan ya sanyata bata tashi farkawa ba sai qarfe bakwai na safe,ko sallar asuba ta qwace mata kenan,cikin hanzari ta sauko daga saman gadonta duk da yadda jikinta yake a matuqar mace,hakanan ya mata nauyi tun daga gangar jikinta zuwa kanta.

Tana idar da sallar da ake binta tana cikin yin azkar dinta na safiya huda tayi knocking ta turo qofar,ta shirya tsaf cikin wankakku kuma gogaggun unifoarm dinta,kai kace yau ne zata soma zuwa makarantar,fuskarta qunshe fal da walwala da farinciki,saidai tana ganin alamun shahidan bata shirya ba ta turo baki kaman zatayi kuka
"Anty...bakishirya ba,yaune fa?" Murmushi ta saki tana qarashe salatin annbi guda goma da takeyi ta shafa sannan tace
"Banajin dadine yau huda"
"Amman zaki ko?" Ta tambayeta da sauri cikin fargabar kada tace ba zata samu zuwan ba
"Zanje huda...amma inajin zamu makara da yawa fa" qafa ta soma bubbugawa shahidan ta gane me take nufi
"Kinga...ki shirya a soma kaiki,idan yaso in ya dawo daga kaiki ni saiya kaini,saimu hadu a hall din hakan yayi?" Kaita kada tana murmushi
"Bari naje naci abinci to" ta fadi tana juyawa a guje ta fita a dakin,sai data bacewa ganinta sannan ta dauke kanta tana sauke nannauyar ajiyar zuciya,tanajin inama ace itace hudan,quruciya abu ne mai dadi,baka da matsala baka da damuwa,dukka ka tsere musu.

A nutse ta cire kayanta ta shige bandaki ta tara ruwan dumi ta soma wanka,saboda yanayin jikin nata da batajin dadinsa yasa komai nata ma cikin nawaa take yinsa,hakan ya sanya ta kashe kusan awa guda a wanka da shiryawa.

Ta jima gaban mudubi tana kallon fuskarta kaman yadda ta saba koda yaushe,dukda idanunta sun dan sauya saboda kukan da tayi daren jiya amma sai taga fuskarta tayi wasai,farar affaya mai taushi data nade jikinta ta amsheta qwarai,akwai adon golden jikinta,hakanan taji kaman ta cireta,me yasa ma tayi shigar ne?,batason dukkan wani abu da zai mata kyau a yanzu har yaja hankalin wani zuwa gareta,ta saka hannu ta soma cire lullubin laffayar dake kanta anty zubaida ta turo qofar ta shigo,wanda hakan ya tarwatsa abinda tayi niya
"Me kike haka?,yau lafiyanku kuwa shahida?"koda ta boyewa antyn yadda take qare mata kallo tasan saita fahimceta,jin tayi shuru saita girgiza kai tana tabe baki
" damuwa dai damuwa dai?,ina zakikai damuwa shahida?,wannan kuma da kike niyyar cireta fa?,don ta miki kyau?"dole yadda anty zubaidan tayi maganar ya baka daroya,saita murmusa tana maida lullubin gami da zarar jakarta
"Ina kwana anty?"
"Lafiya lau ni zan fita inason idan ya saukeni saiya wuce dake makarantar basai ya sake dawowa ya dauki wani ba"
"Tohm anty" tare suka fito daga dakin shahida ta wuce saman dining ta soma tsakurar abinci,anty zubaida kuma ta koma dakinta don dauko mayafi da jakarta.

Sam abincin ji take bazai ciwu ba,don haka ta hada tea kawai tasha anty zubaidan na fitowa suke fice tare.

Sun dan sake bata lokaci a hanya saboda cunkoson ababen hawa da suja tarar a hanya wanda shahidan ta rasa na meye,titi ne da yake da wuya ka samu cunkuso akanshi,ita kanta data dubi agogonta sai da taga makarar tayi yawa,da qyar suka samu hanya suka wuce,ta sauke ajiyar zuciya sanda suka isa bakin katafaren ginin makarantar noor international academy
"Yau ina tunanin zamu iya kaiwa biyu,saboda yaune hutu,idan mun tashi zan maka waya in sanar maka"
"To babu matsala" ya fada yana tashin adaidaitan,tana tsaye kaman wadda aka dasa har adaidaitan data sauketan tabar gurin,sannan ta soma takawa a hankali kaman mai sanda zuwa cikin makarantar,haka kawai taji zuciyarta tayi mata nauyi,qafafunta kuwa kaman an sare su,bugun zuciyarta na daduwa duk sanda ta qara wani taku guda da zai kusantar da ita da cikin makarantar.

Harabar makarantar fetal,sai ababen hawan wasu daga cikin malamai da kuma wasu baqin motoci guda uku da take kyautata zaton na baqonsu ne,shuru makarantar take,hakan ke nuna mata cewa duk an tafi zuwa hall din da za'a gudanar da taron da kuma hutun dalibai,ta dan tsaya tana shawarar ta soma kaiwa huda maganinta tasha kota bari sai sun hadu a dakin taron?
"Malama shahida ya akayi haka?" Taji muryar kausar wadda ta fito daga can wani sashe wanda zai sadaka da dakin taron,murmushin yaqe shahida tabi kausar dashi saboda yadda takejin jikinta ba qwari haka kawai
"An sallami kowanne aji saura naki,yau tsarin na daban ne,inviglating ya yiwa kowanne aji saiya gama dubaka sannan sai ku wuce kai da dalibanka dakin taron" murya qasa qasa tace
"Yana naki ajin yanzu ku kawai ake jira a soma,kiyi sauri ki riskeshi donma yana da kirki,nima amakare na iso amma ina bashi uzuri ya karba" kai kawai shahida ta kada mata sannan ta soma takawa zuwa sashen azuzuwa.

Bayanshi take iya hangowa saboda qofa da ya baiwa baya,tsaye yake gaban blackboard sanye da suits ash da suka zauna das a jikinsa,fuskanshi na kallon 'yan ajin da alama wani abu yake saurara daga garesu.

Sautin fitar murmushinsa shi ya soma dukan kunnenta,bisa alama wani cikin daliban ya fadi abinda ya bashi dariya
"To shikenan...next question....who is the best teacher in dis school?"
"Anty rahama...aunty rahama!" Suka hada baki dukkansu suna fada,abinda ya sake sashi dariya qwarai,irin dariyar daya jima baiyi irinta ba,baisan wanne irinso yaran kewa malamar tasu ba,komai anty rahama anty rahama,wai wace anty rahama nan
"Auntyyy" wasu daga cikin yaran da suka hango tsaiwarta bakin ajin suka fada cikin shauqi da nuna qauna tamkar sunji tambayar da yakewa kanshi,duban yaran yayi sannan a hankali ya waiwaya yana son yaga wace.

Shahida....shahida ce dai tsaye cikin shigar kamala ta lafaya,jakarta rataye a kafadarta idanunta saye da farin gilashin daya zamto yana taimaka mata wajen gani,sakamakon matsalar idanu da taso gamuwa dashi tun shekarun baya saboda yawaita kukan da take,wani irin abu yaji yana zagayawa saman kanshi,tsigar jikinsa gaba daya ta zuba,zuciyarsa ta kasu kashi biyu,kowanne sashe na zuciyar tasa da abinda take ayyanawa.
Chapter 26 · 0% Book details