← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 73

Sashe 35

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana shirin jan abun rufa kiran nura ya shigo wayarta,ido ta lumshe sannan ta waresu,ba yadda ta iya haka ta daga
"Ranki ya dade....yau an manta dani kwata kwata ko?,koda yake dama idan ban nemeki ba saidai na shekara ina jajenki"
"Ba haka bane...ayyuka ne yau sai hamdala"
"Ina fatan dai basu gajiyarmin dake ba?"ajiyar zuciya ta sauke
"Gajiya kam akwaita,don yanzu ma shirin kwanciya bacci nake"
"Da wuri haka?,da qorafi nakira nayi,amma tunda haka ne kiyu baccinki dakyau,ki gayan yaushe zanzo mu hadu?" Kanta ta juya daya sashen,ta danyi nazari kadan
"Kasan yanayin aikin nawa,wunin office ne,idan na dawo kuma na gaji bacci kawai nake buqata" tsaf ya gama ramfota,haduwar tasu ne bataso,ita kuma takurawa da zancan aure da yake a 'yan kwanakin da yadda yake marairaice mata ya sanya bata fiya son haduwar tasu dashi ba,sakata yake kawai a corner
"Duka ba damuwa bace,ni idan anmin izini saina riskeki har office din lokacin break mu tattauna abinda zamu tattauna din,karki damu bazan jima ba zan tafi,daga nan har zuwa next week ina jiranki" numfashi ta sauke,ya gama kamata kenan iya wuya,amma itama bari ta qure haqurinsa
"Saidai nan da sati daya rana ita yau"
"Allah ya kaimu" ya amsa hakan bisa ga mamakinta,da haka sukayi sallama ta kwanta tunani fal ranta,tana mamakin yadda nuradden yake iya shanye duk wani hali nata,bata taba kamashi da rashin yi mata uzuri ko hanzari ba,tanajin nuran na hawa wani mataki fiye da wanda yake kai a baya,ya kamata ta sake bashi wata damar ko yaya take,da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita.

*BAYAN SATI DAYA*

Turare ta dauka ta fesa abu na qarshe cikin shirin fitarta office,ta kalli kanta sosai ta tabbatar komai yayi mata,shiga mai kyau da tsari,riga da skert na swiss atampha wanda suka mata cas da mayafi yalwatacce wanda ta dorashi saman daurin dankwalinta data dan turoshi gaban goshi,hannunta agogo ne kaman yadda tafi son sakashi fiye da awarwaro,wuyanta sarqa ce da dan kunnayensu masu azabar kyau qirar kamfaninsu,wanda gwaji ne akayisu aka bawa masu manyan matsayi a kamfanin,takalmanta ta jawo rufaffe na mata wanda ya dace da shigarta,tana zuge jakarta da zata fita da ita taji shigowar saqo a wayarta,saita dakata da abinda take ga zatonta mudassir ne daya daga cikin abokan aikinta wanda yace zai tura mata wasu bayanai kan lissafin da suke tayi na wasu siyayya da wani kamfani yayi na sarqoqi,ga sabanin tunaninta saita tarad da nuradden ne

_Da fatan wannan kyakkyawar halittar ta tashi lafiya cikin amincin ubangiji,yau sati guda cif cif,Allah yasa banyi azarbabi da yawa ba_

Kyawawan idanunta masu kyau da haske ta juya gabanta yadan fadi,sam ta manta da zancansu wanda yace ya bata sati guda,saita sauke numfashi data tuna cewa bai taba zuwa kamfanin nasu ba,asalima bata taba gaya masa inda yake ba,hakan na nuna baisan office dinta ba,bazai kuma iya zuwa ba har sai ta bashi adress,tuna hakan ya mata dadi,don idan yazo din bata jin zaya samu amsar da yake da muradi,saboda haka ya kashe wayarta ta jefa a jaka tana murmushin nasara,ta duqa ta qarasa saka takalminta ta dago tana rataya jakarta huda ta shigo cikin shirin makaranta itama,gaida shahidan tayi ta gaya mata sun fito
"Muje hudallah...wannan makaranta anaji da ita" dariya ta saki
"Sosaima anty,kinga randa me makarantarmu yazo,ya bamu labarin wahalar da yayi saboda karatu,yace mu dake muyi karatu sosai muma donmu zama irinshi" yatsine fuska shahida tayi saboda yadda zancan ya tuna mata da ranar
"Allah ya kiyaye" shahidan tayi subul da bakan fada wanda yasa buda ta juyi da sauri
"Allah ya kiyaye kuma anty?,yana da kirki fa,sannan yana da karatu,ya iya turanci da larabci,gashi kyakkyawa,shiyyasa ranar banji dadi ba da kika koma gida baki ganshi ba.....kinsan me?,uncle fa muke ce masa,yace duka mu yayanmu ne..."
"Hudaa....a'ah" shahida ta fada tana kallonta,itama sai ta saka ido kawai tana kallon shahidan
"Oya muje karki sa muyi late dukanmu" dariya ta saki tana tafiya sauri sauri
"Mu yanzu ai ba'a dukan late comers,uncle ya hana" goshinta ta dafe da tafin hannunta,wato dai hudan ba zata daina mata zancan mutumin nan ba.

Tana mamakin yadda suke ganin kirkinsa haka da yawa,basu san cewa macijin sari ka noqe bane shi?.

Agurguje kuma a tsaye ta hada tea dan kadan ta kurba,duk yadda anty zubaida tayi kan ta tsaya tayi break sosai cewa tayi sauri take yau suna da aiki da yawa,haka ta fice bayan ta musu sallama,aka dauki huda itama ta shiga tata adaidaitan suka wuce.

A cikin company ya ajeta kaman yadda suka saba ya juya ya fice ita kuma ta shige zuwa cikin ainihin kamfanin,a sashen kula da baqi na musamman zata wuce cikin hanzari tajuyi muryar mudassir
"Kin kusa makara fa" waiwayowa tayi fuskarta babu yabo ba fallasa ta dubeshi
"Wallahi,amma na gode Allah da ban makara ba,ina fatan komai ya zama ready" kafadarshi ya daga yana dubanta,yana da muradin shahidan sosai tana burgeshi,komai nata abun sha'awa ne amma kame kai da jan ajinta yasa ta masa wani irin kwarjini daya sanyashi ya kasa kwatanta mata bare ya furta
"Eh tuni ma" ya qarashe maganar yana miqa mata daya daga cikin file biyun dake hannunshi,hannu ta saka tana buda shafukan farko tana dubawa sama sama,daga kai tayi sai suka hada ido yana kallonta,hakan ya sanyata dan tsare gida
"Ka sameni a office dina muyi acan inaga zaifi" ta juya abinta ta isa bakin elevator da xata kaita zuwa bakin ofishinta.

Da sallama ta shiga duk da cewa ya sani babu kowa ciki,a nutse ta qarewa office din kallo,ko ina tsaf yake yana fidda sassanyar qamshin da ita ta yiwa kanta zabin kalar freshner din da takeso wadda ta banbanta data kowa,wadda ke mata shara din ta qwarai sosai,sannan kuma tasan aikinta,hakan yasa takejin dadin aikin da take mata,tasan ra'ayinta da tsarinta,jakar hannunta da file din ta dora saman teburinta sannan ta taka a hankali ta isa bakin windows din office din ta bude kowanne,iska mai dadi da sanyaya rai ta soma kunno kai,irin iskar damina mai taushi da sanyi,tana son irin wannan iskar,sabida banu iska mai dadinta,fresh ce daga indallahi,sai data tabbatar ta gauraye office din sannan ta rufe windows din,ta sauke labulayen ta kunna AC,hakan ya qarawa office din wani dadi da yanayi na musamman.

Tana zama mudassir ya shigo,yaja kujera ya zauna yana qarewa office din kallo sanda take kiciniyar futo da system dinta wadda a office din ta kwana bata je da ita gida ba jiya
"Kai masha Allah,duka kamfanin nan ba office din dake burgeni nakejin dadin shigoshi irin wannan,komai neat masha Allah" ya qarashe maganar yana sauke idonshi a kanta,dan qaramin murmushi ta saki sannan ta soma dai daita cumputer din gabanta,ba tare data sake bashi wata qofar sako wani zancan ba ta soma gabatar masa da abinda ya zaunar dasu.

Tun tara da rabi suke abu daya har qarfe daya da rabi na rana kafin su kammala,ta gaji matuqa tayi tubus,ga 'yar banzan yunwa dake damunta,kujerarta taja baya bayan ta rufe system din tana hamma idanunta lumshewa wanda sam bata kula da yadda mudassir ya zuba mata ido yana kallonta ba cikin burgewa,tunda suka zauna qamshinta ke burgeshi
"Yadai madam?" Ya tambayeta har yanxu idanunshi na kanta,sai a sannan ta juyo ta dubeshi,fuskarta adan hade kaman yadda ta saba idan ta fuskanci kana da shiga sharo ba shanu
"Da akayi me?,ai mun gama ko?,sauran aikin ya rage naka da nawa,kowa yaje ya tsara abinsa cikin system dinsa,duk randa zamu gabatarwa da boss kowa yasan me zai fada" kai ya rausayar
"Ba haka nake nufi ba,naga kaman bakijin dadi ne" miqewa tayi tsaye tana gyara yafen mayafinta,bandaki takeson shiga sabida fitsari ya matseta gashi yaqi fita ya bata waje
"No,ba komai gajiya ce kawai.." Ta tura kujera baya sosai yadda zata samu damar fita daga tsakanin kujerar da teburin.

Gab da zata shige bandakin aka nemi izinin shigowa office din ta bayar,masinjarta ce cikin girmamawa tace
"Kinyi baqo ne anty(haka take kiranta saboda yadda take ganin qimar shahidan" cikin mamaki tace
"Baqo kuma?,custumer ne?", ta tambaya duk da tasan bashi bane,don yawanci ba'a ganinta ita idan ba wata matsala bace akan pyment da custumer zaiyi,koda kuma zai ganta ma za'a rakoshi ta qarqashin wani office dake kula da shige da fice da kuma siyayyar kaya a kamfanin
" a'ah,yace yana son ganinki ne personal"tayi tsammanin cikin mutanen dake takura mata ne,abun saiya qona mata rai,batason abinda zai shafi mutuncinta a wajen aikinta,sabida haka taja tsaki
"Jeki ce masa lokacin aiki ne yanzu,ya nemeni ta waya ko waye idan na tashi daga nan"
"Toh" ta fadi tana juya ta fice daga office din,tsaki taja ta dawo don daukar ruwa ta soma sha tukunna
"Sai haqurifa,kinsan kowanne mutum da yadda Allah yake masa baiwar jama'a" waiwayowa tayi ta kalleshi,shaf ta mance dashi cikin office din,saita dauke kai tana sake hade girarta ba tare datace masa komai ba,batason a dinga zama mata cikin office tafison kuna gama aiki ka kama gabanka,wayarta dakw cikin jakar hannunta wadda ke saman teburinta tayi qara,a nutse ta qarasa ta zugeta ta cirota,sai taga number nuradden,fuska tadan yamutsa saboda yadda taji gabanta yadan fadi,ta daga ta kara a kunnenta
"Allah ya baki haquri gimbiya nine fa,ko nima ba za'a samu damar ganina ba bayan alqawari aka yimin?" Mamaki ya cikata,ta yaya akayi yasan kamfanin da take aikin,banda abinki wannan wajen kina tunanin zai xama boyayye ne?,shahararren waje irin wannan? Wata zuciyar tace da ita,murmushi ta qaqaro
"Ayyah bansan kai bane,minti daya ina xuwa" kiran nashi ta katse ta soma neman wata number cikin ranta fana dana sani da Allah wadai da kunna wayarta data yi,data sani tun daxun ta barta a kashe kawai,wani sashe ta kira na kamfanin ta bada umarnin a rakoshi,daga haka ta kashe wayar,duka sai jikinta yayi sanyi taju qafafunta kamar an bubbuge mata su,sai ta zauna saman kujerun cushion dake gefe daya na office din.
Chapter 35 · 0% Book details