← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 73

Sashe 61

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana dab da fita ta tsinceshi a gabanta,suna hada ido ta kauda kai saboda yadda qwayar idanunshi ta sauya launi
"Bazan taba lamunta ki fita wani waje mahada jama'a maza da mata ba da sunan aiki,ki gogayya da maza kiyi magana dasu,ki fita da safe ki dawo da yammaci,idan na barki kika koma lallai na tabbata wawa,kuma abinda nayi baiyi riba ba,kina nufin komawa office din danaga wani ya kama yatsarki zai saka miki zobe?,Karki soma gigin aikata kuskure irin wannan,idan ba haka ba zaki gane baki da wayau,idan kuma baki yarda ba bismillah" daga haka ya kauce daga hanya ya bata waje yana komawa mazauninsa,da gudu gudu ta fice daga falon ta soma sauka qasa,tayi nasarar riqe kukanta batayi agabansa ba sai data danga da dakin gadonta,wani irin tuquqi takeji cikin qirjinta da zuciyarta,sam bazata yarda ba,ba zata lamunci ya sake cin galaba a kanta ba bayan wadda yaci,idan yayi haka aiya tauyeta da yawa,tayita zama kenan cikin wannan gidan da zaman cikinsa harya soma gundirarta,zaman da bai mata ma'ana ba sam?,gobe kam saidai ayi duk wadda za'ayi,idan yaso yace ta wuce gidansu.

Iska yake furzarwa daga bakinsa mai dumi bayan fitarta yana murza tafin hannunshi kan hannun kujerar da yake kai,yanajin bacin rai nason taso masa yana danneshi,ta yaya zai barta ta koma aiki?,aikin da tun ranar daya ganta cikinsa bai sake samun nutsuwa ba sai daya tabbatar ta daina zuwa ta sanadin aurenshi,randa yaga nuradden din cikin office dinta da qyar ya samu ya saisaita kansa,ji ya dinga yi kaman hawan jininsa zai tashi,sannu sannu ya dinga ambaton sunan Allah har ya samu zafin da yakeji ya sauka,yunwar da yakeji ta dawo masa sabuwa fil,bashi da mafita illa slipper dinshi daya zira ya sauka zuwa qasan.

Karon farko da zauna kan dining din,ya jawo warmers din ya soma budewa daya bayan daya,take qamshi ya cika wajen wanda ya qara qaimin yunwar tasa,tun kafin ya soma ci a ido abincin yayi masa,sanda ya soma ci kuwa saiya samu kansa da lumshe idanunsa,dadin girkinta ya ninka fiye da wanda ya sani a baya,a nutse yaci abincin,ya kuma yi qoshin daya manta rabonshi da yayi irinsa,baibat abincinba sai daya diba wani yayi guzuri ya haura sama dashi.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Bayan ta idar da sallar asuba bata koma ba ta soma gyara dakinta,sannan ta fito falo,ga zatonta zata dauki fulasan abincin kamar yadda ta saba kowanne lokaci amma saita tarar anci fiye da rabin abincin,harara kwanukan abincin tayi kaman su suka mata laifi
"Dan rainin hankali,nina kwana ina baqinciki,shi kuma ashe zuwa yayi ya cika cikinsa,bacin raina dadi ma kenan yake masa,bai taba cin abincina ba sai yau daya fuskanci a bacin rai nake kenan,aikuwa bazan yadda ba nima" da wannan tunanin ta gama komai na gidan,ta kuma shirya abincin safe ta jera yadda ta saba sannan ta shiga wanka.

Tara saura ta gama komai,ta shirya tsaf cikin laffaya data nade jikinta fes da ita,qafarta sanye take da takalmi me tsinin dunduniya,ba qaramin kyau tayi ba,kana kallonta kasan sabuwar amarya ce.

Tana tsaue bakin dining tana break don ko zama batasonyi bare ta makara taji takun takalmi da alama ana saukowa ne daga sama,tasan shine don haka taqi daga kanta bare ta dubeshi,daga saman step din ya tsaya yana dubanta cikin mamaki,tana nufin fita kenan zatayi da gaske?,a ina shahida ta sauyo hali ta koyi musu da kafiya?,bari ya zuba ido yaga iya gudun ruwanta,dole ya nuna mata shine mijin itace matar,zata ga qarfin qwanji yau kuwa idan batayi wasa ba.

Bai qara taku daya ba yana tsaye yana kallonta harta gama,ta ciro paper daga jakarta tayi rubutu ta ninke ta aje anan sannan ta tattara jakarta ta zuge ta riqe a hannunta ta soma takawa don ficewa. *Alqawarin Allah*
39

"Karki kuskura ki fita" ya fada yana daga tsayen yana dubanta,kamarma bada ita yake ba haka taci gaba da takawa.

A nutse ya gama saukowa sannan ya saka hanzari irin na ingarman namiji,kafin kace meye wannan ya cimmata,yasa hannu ya maida murfin qofat falon ya rufe idanunshi cikin nata ya bata umarni kai tsaye
"Wuce ki koma ciki" dubansa tayi itama
"Kaman yaya?,bayan na gaya maka tun jiya aiko?"
"Ki koma ciki kawai nace" saita dubeshi na tsahon minti daya,ta karanci da gaske yake,ita kuma na zata yarda yaga lagonta ba bare yaci gaba da sanyata yin abinda batayi niyya ba kuma bata shirya ba,saita sake dora hannunta kan handle din qofar da niyyar budewa,caraf ya riqe hannun nata,tana shirin masa tsiwar ya saketa bata ankara ba taji an sureta gaba daya daga ita hat jakar hannun tata,ya juya ya soma taka matakalar da zata sadashi da sama,sosai ta soma qoqarin zillewa ranta na quna na yadda ya maidata kaman wata karmami,ya dagata ba komai bane a wajensa kamar ba mutum ba?,sai kace wata 'yar baby
"Meye haka ne?,ka saukeni don Allah bana son irin haka,ka saukeni,ka saukeni bana so" abinda ta dinga fada kenan tana qoqarin qwacewa daga daga hannunsa,baiko bi ta kanta ba hakanan bai fasa hawa saman ba har sai daya dangane da bedroom dinsa sannan ya cillata saman lallausan gadonshi yana maida numfashi,fuskarshi a daure,ranshi a matuqar bace wanda ko ba'a gaya maka ba zaka fuskanci haka ta idanunsa da suka soma sauya kala,nunata yayi da yatsa cikin bambami dake nuna ranshi ya baci
"Na fuskanci cewa sassauci na yana neman kawo raini a tsakaninmu,barinki kiyi yadda kikeso yasa kikejin kece mijin nine matar ko?,to daga yau komai zai sauya,zaki gane wane shugaba tsakanin ni da ke" daga haka ya maida muqullin dakin ya rufesu shida ita gaba daya,cikin hanzari take saukowa daga saman gadon nashi tana cewa
"Ka budemin qofa,ya zaka rufeni anan,wai me yasa ka fiya son kanka ne da yawa?,me yasa kake zalunt...." Maganar tata ce ta katse sakamakon yadda ta sauko qafafunta qasa da hanzari da cogenta,sai akayi rashin sa'a qafar tata ta turgude da tsinin takalminta,maimakon ta qarasa maganar da take saita buge da sakin qara,ta koma tayi zaman dole bakin gadon tana duba qafarta.

Towel din dayake daukowa ya rataya a wuyanshi sannan ya waiwayo yaga me ya sakata yin qarar,idanunsa ya sauka a qafarta da take dafe da ita,a hankali ya qarasa ya duqa gabanta,ya saka hannu zai taba qafar ta janyeta baya da sauri tana ci gaba da dafe wajen,ya gane me take nufi,tana nufin batason ya taba nata qafa kenan,saboda haka ya qyaleta ya juya abinshi yayi shigewarsa wankansa.

Azabar data dinga ji cikin qafar ya tabbatar mata mawuyacine idan ba targade tayi ba,batasan ya zatayi da qafar taya ba,hakanan ita daua cikin dakin ta dinga dafe qafar tana jin zugi na ratsata.

Sai daya kwashe awa guda cur sannan ya fito,a shiryensa kaman ba shine ya shiga wanka da towel da jallabiya ba,ya isa gaban mudubi ya dauki turarukansa ya fesa,ta cikin madubin yaje dan kallonta yadda ta soma hada gumi,tuni harta cire yafen lafayar jikinta,idanunsa ya sauka kan lallausar t.shirt din dake jikinta fara sol mai dogon hannu da rufaffen wuya,wadda ta lafe sosai a jikinta ta fidda shape din albarkatun qirjinta,saiya dauke idanunsa daga kanta da sauri,ya gama fesa turarensa ya taje kansa sannan ya juya ya sake takawa inda take ya tsugunna gabanta karo na biyu,zata sake janye qafar yayi caraf ya riqeta sosai,ta saki ihun azaba sanda ya gama zare takalmin ya soma mammatsata,take ya gane targade ne,ya kuma gamo wajen,sai daya faki numfashinta ya kama wajen sosai wanda babu shiri ta qwalla wata irin qara tana qoqarin tureshi,saidai ko gezau baiyi na yaci gaba da gyara wajen,tun tana masa masifa tana jin girman kan ta roqeshi ya qyaleta harta soma roqon nashi tana hadashi da Allah,ta hada gumi jagaf kafin ya gama,yana sakinta ta saki ajiyar zuciya,sai kuka ya qwace mata,dama zuciyar na akusa,gani take kaman yana sane ya taba ciwon da yawa yayine kawai saboda mugunta.

Baiko dubeta ya juya ya isa bakin qofa yabude zai fice,taso yunqurawa ta miqe ta bishi a baya da hanzari ko xata samu nasarar ficewa amma ina babu damar ta taka qafar,tana kallo yaja qofar,saidai wannan karon bai rufeta ba,abinda ya sanyata sakin ajiyar zuciya kenan,ta maida kanta jikin filo ta jinginar tana lumshe jiqaqqun idanunta da duka jiqe da ruwan hawaye.

Tun tana sauke ajiyar zuciya tana shaqar qamshinsa daya kama dakin har bacci ya soma fisgarta,ta dinga dagewa don bata son yin bacci saman gadonshi amma ina yafi qarfinta.

Qarfe biyu na rana ya sake dawowa saman,duka yau ba inda ya fita,duk da yaso yayi fitarsa ya qyaleta amma saiya kasa,sanin cewa mawuyacine ta iya tabuka komai saboda targaden data ji din ba kadan bane.

A hankali ya turo qofar dakin,yayi tsammanin samunta zaune,sabanin hakan saiya sameta a kwance a rigingine tana bacci sosai,ya qarasa a hankali ya tsaya kanta hannunsa rungume a qirji ya zuba mata ido,irin kallon daya jima baiyi mata irinsa ba,abubuwa biyu na kokawa cikin zuciyarsa,ya samu ya kauda su,ya isa gefan kanta yadan bubbuga filon da take kai a hankali,bude idanunta tayi sannu sannu,saita tuna inda take,saboda haka ya ware idanun nata da sauri gami da miqewa zaune sosai tana masa wani kallo da yafi kama da harara
"Ki tashi ki sallah" ya fada yana aje mata takeaway,sannan ya goya hannunsa a baya ya tsaya yana kallon yadda take kokawar miqewa cikin dabara,da alama tana shan zafi amma taqi nemon taimakonsa,data gaji da kanta ta koma ta zauna tana lumshe ido saboda zafin da wajen yake mata,gami da sauke numfashi
"Ki tashi na taimaka miki badon halinki ba"
"Banaso" ta fada da hanzari,sai ya daga kafadunsa alamun bai damu ba ya soma takawa zai fice,ta kalli agogo ta tabbatar idan ya fita da matsala,lokaci zai iya qwace mata,ita kuma idan tace zata tashi da kanta zata sha wahala,saboda haka kaman wadda aka yiwa dole tace
"Dawo ka tayani,amma karka soma tabamin jiki don zaka rakani alwala"
"Riqe jikinki na riqe taimakona" ya bata amsa sanda ya tura qofar kamar xai fita,tana kallo ya sake ficewa,sai wani abu ya tokare mata maqoshi,ita zaiwa wulaqanci?.

Sau uku tana gwada takawar amma zafi da tsoro ya hanata,dole ta koma ya zauna tana kallo lokacin sallah na sake wuceta,baqinciki kamar tayi yaya.
Chapter 61 · 0% Book details