Sashe 32
Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A falo tana rataye da jakarta ta dubi mubina
"Cikin kayan da antyn katsina ta kawo miki daukomin na zabi style zankai dinki,yi sauri ki daukomin,sa'id yayi anguwa mai nisa yace ya barshi basai ya dawo dakata ba tunda kusa da anguwarsu yake,motar haya zanbi kar dare ya sake yimin"
"Wallahi duka na sakasu yaaya suna wajen wanki" goshinta ta dafe tana jan dan tsaki cikin rashin jin dadi
"Halinku daya ai indai mubina ce,kowanne kaya da an saka an cire duk kyanshi sai ruwa,saiki haqura ai har sai ta karbo itama da dan banzan sanabe,ki kama kayanki ki wanke amma saikin kai wankau" murmushi matar tayi har fararen haqoranta suka bayyana kan idanun shahida,gabanta ya sake faduwa,matar tana mata kama da wata,kaman ta taba ganin fuskar
"Kinga qanwata zo muje ki zabi style wanda kikeso kinji"tayi maganar sanda ta miqe tsaye ta dauki hijabinta dake aje gefe tana sakawa,kallonta shahida tayi,sai taji tana jin nauyinta sosai,banda haka ce mata zatayi a'ah ta barshi,amma saita kasa fada,don ita gaba daya ta jima rabonta da sake amincewa da wani a rayuwarta,duk wata baquwar fuska da zatayi kutsewa rayuwarta kaffa kaffa take da ita.
"umma...ina kuka samota newai?,ni gaskiya ba wani gidanta da zan bita" shahida ta fada dai dai saitin kunnen umman cikin nuna rashin yarda
"Babu komai matar sananniya ce,hakanan mun dan jima tare,kije kawai" hakanan jiki ba qwari ta fito ta sameta bakin famfo tana daura alwala,ta kammala ta yiwa umma sallama suka fice.
Ko a tafiyarma bata yarda sun hada kafada ba,tana gaba ne tana binta a baya,duk da haka takan juyi jefi jefi ta sako ma shahidan hira,nata eh ko a'ah ne har suka qaraso gate din gidan,tsaiwa shahidan tayi tana kallon gidan,kaman taso ta taba ganin anwar tsaye bakin gate din sau daya,saidai bata tabbatar dashi dinne ko bashi bane,kawai dai tun daga ranar ta tsani kallon qofar gidan ma
"Muje ciki mana shahida saiki zaba a nutse" murmushin yaqe ta saki
"Nan ma ya isa,idan da yara saiki turo su miqo min na wuce,yau nayi dare sosai a waje takwas ta kusa"
"Yanzu zaki wuce ai,ki shigo ko kuma nace mubina ta fiki kirki dason mutane" murmushi tayi saita bi bayanta kawai.
Sosai falon ya burge shahida,komai a kammale a tsaftace yana fitar da qamshi
"Zauna gu waje nan shahida" tana nuna mata kujera da hannu,a darare ta zauna din tana bin falon da kallo mai gwanin sha'awa da burgewa,sanda yake fidda hijabinta wata 'yar budurwa ta sauko daga sama ta matakalar benan dake falon
"Sannu da zuwa ummi kin dade yau" ta fada tana duban maman tata
"Wallahi sa'ida...yauwa shiga dakina ki bude wardrobe dina,inda na aje dinkunan da aka kawomin din nan shekaran jiya ki cirosu gaba daya"
"Toh" ta amsa tana shirin juyawa idanunta ya sauka kan shahida,saita sake juyowa da sauri ta kalleta ta kalli ummin nata,sai kuma ta juya ta sake hayewa saman.
"Ina zuwa shahida kinji" ta fadi tana nufar wata qofa dake nuna alamun kitchen ne,wayarta dake jaka ta dauki kuka alamun kira ke shigowa,ta cirota tana dubawa,noradden ne,saita latsa tana karawa a kunnenta
"Ranki ya dade,ya akayi sa'idu yabarmin ke a waje da daren nan?,naje gida baki nan,na kirashi yace wajen umma yabarki,kuma kince basai ya dawo ba"
"Eh uzuri nayi masa ne" ajiyar zuciya ya aje
"Ni gaki kin fiddoni,kema kinsan ba yadda za'ayi na iya kwanciya kina waje,fito gani a qofar gida"
"Na fito daga gidan ai"
"Ina kika je?"
"Ina maqota" sai tayi mishi kwatancen gidan yace gashinan,babu jimawa ta fito dauke da wani dan qaramin faranti da aka dora ruwa da lemo,gefe daya dambun nama da meatpie ta aje gabanta
"Ga ruwa kisha" murmushin yaqe ta danyi don har yanzu a darare take,hakanan taji ta kasa sakewa
"Na qoshi wlh anty"
"Da alama dai da gasken shahida baki da kirki" dariya maganar ta bata,saita kuma sakin murmushi sosai
"Ba haka bane anty,kina gani kusan ma tare mukaci abincin"
"Eh...amma ko albarka kyasa" bata sake cewa komai ba ta gutsuri meatpie din kadan,dai dai sanda ta qwalawa yarinyar kira
"Sa'ida me kike ne?,kiyi sauri sauri fa take gida zata wuce"
"Gani nan ummi" tana maganar ne sanda take sakkowa daga saman cikin sassarfa rungume da kayan a qirjinta,a gaban ummin ta zubesu
"Riga daya ce ban gani ba ashe ta shiga cikin wasu kayan
"ok...gasu ki xaba wadanda zasu miki" a nutse take daga dinkunan,duka sun mata hakanan sunyi bala'in kyau,tana son yace xata dauka duka tanajin nauyinta,saita zabi uku daga ciki
"Wadan nan ma sunyi,na gode" tura mata sauran tayi
"Jeki dasu gaba daya,mai yiwuwa telan yaga wanda zaifi miki kyau akan wanda ke kika zaba" haka ta tattara duka kayan ta zuba mata a wata 'yar jaka mai kyau,ta mata sallama ta fito.
Yana tsaye jikin motarsa wayarsa na hannunshi yana danne danne,ganin fitowarta ya sanyashi maida wayar aljihu,ya tarbeta cikin fara'a ya amshi ledar hannun nata sannan ya bude mata gaban mota,dubanshi tayi sosai
"Kaima kariga da kasan qa'idata ko,mu taka zuwa titi ka tsaremin napep" kai ya langwabar mata yana dubanta
"Kar muyi haka dake don Allah,yau dai daya kiyimin wannan alfarmar na kaiki,tunda muke dake shahida ko kara babu baki taba shiga motata kosau daya ba,koda batan hanya" maganar tashi ta bata dariya amma ta maze,ita bata da ra'ayin hakan kwata kwata,ganin yadda yaketa roqarta gashi dare nayi yasa tayi bismillah gami da addu'a ta shiga ya zagaya ya rufe ya tada motar.
Farinciki yau fal zuciyar nuran,haka ya dinga sako mata hira,suna tsaka da tafiya taga ya dauke hanya,idanu a waje zuciyarta na gudu ta kalleshi
"Ina zaka dani malam" dariya yayi
"Karki damu shahida,duk sanda kike tare dani cikin aminci kike,wani waje kawai zamu shiga,ki rakani zanwa mama siyayya"shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya,duk da haka hankalinta bai kwanta ba har sai data ga sunyi parking qofar wajen ta bude murfin motar suka shiga.
A tsaye yake wajen biyan kudi da yake dab da qofar shiga da fita,yana saka pin dinshi jikin p.o.s machine da ma'aikin wajen ya turo gabanshi,yana gama sawa ya tura musu donsu ciri kudinsu wanda hakan yayi dai dai da ganin gilmawar wata da zuciyarsa hakanan ta afu da sanin wacece,suna miqa masa resit ya karba ya soma takawa don ficewa daga wajen,saiya tuna ya yiwa sa'ida alqawarin turare,tace tana son irin turarenshi randa yaje gidan,yace mata ba lallai a sameshi qasar nan ba,amma zai siya mata copy dinshi,yana da wuya yayi alqawari ya saba banda haka da bazai sake komawa ba,a gajiye ya sake juyawa zuwa ciki ya soma laluben sashen turaruka.
Tunda ya shiga side din daga nesa yake hangowa kamar shahidan,tana tafe yana biye da ita a bayanta kaman wani bodyguard,taku kadan zai qara ya hade tazarar dake tsakaninsu,tana zaban abu tana zubawa a cart din da nuradden ke turawa,ya bata dama ne ta zabarwa maman komai,da fari taso zuqewa yace indai tayi hakan bata dauki maman mamarta ba,dole tayi yadda yakeso.
Sanda ta waiwayo don dawowa daya side din fuskarta ta bayyana fes cikin idanunshi,tana murmushi ne gami da hararar nuradden daya tsokaneta da
"Iyee,ashe madam din tawa an iya siyayya,irin wannan siyayya me aji haka?,gaskiya idan mukayi aure ke xaki dinga min shopping" dauke kanshi yaso yayi tare da aiwatar da abinda ke gabanshi amma sai ya gaza hakan kamar wanda aka haneshi,haka kawai yaji idanunsa na masa yaji yaji,wani abu mai zafi ya sauka a qirjinsa,suna dab da cimmasa ya juya ya soma takawa don barin shagon gaba daya.
Kallon bayanshi kawai ya haifar mata da mummunar faduwar gaba,duk da batasan waye ba bata ga fuskarshi ba,haka kawai ta dinga kallon bayanshi har ya bacewa ganinta nuradden nacan yana zaben zobe,yanayin tafiyarshi da bayanshi kaman anwar
"And so what koda ya kasance anwar dinne?" Zuciyarta ta gaya mata wanda hakan ya sanyata tabe baki da daga kafada.
Tun kafin ya qarasa ya bude motar,yana zuwa ya shiga ya maida murfin ya rufe,saiya samu kansa da kasa tafiya,ya sauke glass din side dinsa gaba daya qasa abinda ba dabi'arsa bace,numfashi yake fitarwa dai dai idanunsa kan qofar fitowa daga wajen,shi kansa baisan zaman me yayi ba me yake jira oho duka bai sani ba,saiya duba agogon hannunshi,tara saura,tara saura fa na dare?,sake maida idanunsa yayi qofar shagon dai ya kafeshi da ido.
Minti goma ya sake duba agogo,tara na dare saura kadan,har yanzu dai shuru?,ya tambayi kansa
"Lafiyanka kuwa anwar?,wai shin ma me kake jira ne?" Ya tambayi kansa da kansa,tuna hakan da yayi yasa ya dage gilasan motar da gaggawa ya zura key zai tasheta,dai dai sanda ya sake duban qofar kanti,sai gasu sun fito fuskokinsu cike da murmushi,yana riqe da ledojin siyayyar,yayin da ita kuma take riqe da iya tata jakar.
*Ga mai buqatar littafin da zan fara bayan kammala alqawarin Allah,ya shiga youtube yayi searching SAUTIN HIKIMA zaiga an rubuta (subscribe) dajan rubutu,ya danna sau daya zai koma black,yayi screenshoot ya turo zuwa wannan number zanyi adding dinsa a grpup din in sha Allahu 07038670166*
https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos alliya:
*Alqawarin Allah*
2️⃣2️⃣
Fasa kunna motar yayi ya tsaya cak yana dubansu ta cikin gilashin har suka isa bakin motar nuradden din,shi ya bude mata qofar motar ta shiga sannan ya sanya ledar daya a baya,saiya dora dayar saman cinyarta,runtse ido anwar yayi ganin haka yana jin wani abu ya dunqule masa a wuya.