← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 73

Sashe 56

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sha daya da minti goma sha biyar qanwar ummanta ita da wasu yan uwan babanta su uku suma shigo dakin suna sakin guda wadda ta firgita shahida gamida saka zuciyarta gudu da matsanancin sauri,inda take zaune suka qaraso hannun daya daga cikinsu na dauke da turare ta dunfarota tana cewa
" *Alqawarin Allah* ya tabbata,yau Allah yayi,shahida ta zama matar anwar"wadda ke tsaye a bakin qofa qanwar abbanta tace
"Allah ya jiqan habibu,Allah baiyi zaiga aurenki ba shahida,duk qaunar da yake miki Allah bai nufa ba,Allah ya jiqanka habibu yakai haske kabarinka" kalaman da suka sake tunzura zuciyar shahida kenan sanda suke fesheta da turaren,ta saki kuka sosai mai sauti wanda ya tunawa da abbanta yasa taji auren ya sake fice mata daga kai,karo na biyu tun bayan lokacin da al'amarin ya faru da taji ba zata iya yafewa fiddausi ba wadda ita ta zama sila kuma jagorar afkuwar komai a rayuwarta,me ta yiwa fiddausi haka dataso tarwatsa mata rayuwa?.

Daada ce ta shigo dakin jin hayaniya da gudar dake tashi a cikin dakin,yawan kukan da taga shahidan nayi yasa daadan ta fitar da kowa daga dakin taja mata qofar,tayi hakanne donta bata damar yin kuka sosai ko zataji sanyi a ranta.

Daidai lokacin da nafisa ke kaikawo kaman wadda ta hadiyi kunawa tana zufa,bata tabajin cewa tayi kuskure ba sai yanzu da labarin tabbatuwar auren shahida da anwar ya ratsa kunnenta
"Anya banyi ganganci ba kuwa mima?"
"Gaganci kuma na nawa?" Ta fadi a zuciyarta,amma a fili saits iso inda take ta dafa kafadarta
"Babu wani ganganci da kikayi,badai gani na iso ba?zaki shiga gidan anwar a sanda ya dace dake,ki sawq ranki kamar kin sameshi kin gama" sanyi ya ratsa ranta ta saki ajiyar zuciya
"Please mima,duk wani shiri da zakiyi karkiyi na dogon lokaci,kiyishi a gajeran zango,don zuciysta ba zata iya jurar tunawa da zan dinga cewa anwar nacan ya kebe da wata macen ba bayan ni"
"Baki da damuwa fa hajiyata,kisa ido kisha kallo" mima tayi lafazin tana daukan jaka da dan yalolon mayafinta ta fice daga falon.

*5:00 pm*

Qarfe biyar na yammaci cikin dakin nata da aka gama kwashe komai nata take zaune saman kujerar madubi,da kanta a yanzu take shiryawa don tasan me afkuwar ta riga data afku,komai ya qare mata,babu sauran wani abu da zai tasiri koya hanata shiga gidan anwar,ta gama yankewa kanta gwara ta sassautawa zuciyarta,ta yadda da hakan ta kuma sallama,taci alwashin samawa kanta walwala da nutsuwa,saidai hawayen da har yanzu ta kasa cin galaba akanshi gaba daya duk da ya ragu,amma lokaci lokaci yakan sako kai tasa hannu ta daukeshi.

Tsaf ta gama shirin nata hasina da anty xubaida na gyara mata wasu abubuwan har komai ya kammala,lallai amarya amarya ce,gaba daya kaman sauya shahidan akayi da wata sabuwar halittar,tayi wani kyau na musamman gami da kwarjini,anty usaina ta zauna daga bakin gado tana dubanta
"Za'a soma kaiki wajen umma,daganan kuma akaiki gidan yayarshi,za'a barki a nan shi zaizo ya daukeki ku wuce,munyi magana da ita ta gayan dalilanta nayin hakan kuma na gamsu,shahida,zamana dake zamane mai dadi wansa nake alfahari dashi,kuma dukkan abinda ya kamata na gaya kiki koki sani kin riga dakin sani na kuma sake miki tishinsa,abu na qarshe kawai da zan rufe dashi shine ince miki,shi aure bautar ubangiji ne,hakan ya sanya dadinsa bai rufewa mace ido ta manta da mahaliccinta,haka dacinsa ma bai sanya mace ta manta da cewa bautar Allah take,Allah yasa kin shiga a sa'a,ya sauya zukatanku da manufofinku cikin qanqanin lokaci,ina maraba da tambaya daga gareki duk sanda wani abu ya shige miki duhu,amma ki sani,dole ki zama jaruma,dole ki koyi hadiye wasu abubuwan ba tare da kowa ya sani kokin gayawa kowa ba,ciki badon tuwo kawai aka yishi ba,Allah ya sadamu da dukkan alkhairinsa" daga haka anty zubaida ta miqe don batason tayi qwalla ko daya don karta sake karyawa shahida gwiwa tunda ta fuskanci kamar ta aro dakiya da juriya,daidai sannan huda ta shigo da sauri,ta isa gaban shahida ta rungumeta,zata fara kuka anty zubaida ta zare mata ido gamida korata don karta karyawa shahidan gwiwa,a haka aka fita da ita zuwa gidansu.

Can dinma gidan cike yake da jama'a 'yan yinin biki,uwar dakan ummanta aka ajeta,'yan uwa suka dinga shigowa aka dinga gaisawa ana yi mata Allah ya sanya alkhairi,tayi qoqarin tarbar kowa cikin mutuntawa,tunda kusan dangin ummanta ne duka,ba wani bare ko baquwar fuska.

Sai gab da magariba sannan umma ta zauna da ita ita da sauran yayyenta,fadane dai irin wanda uwaye kewa diyarsu,daga bisani kuma umma ta taba nata,ta nemi yafiyarta cikin kuka tana tunawa da abbanta
"Bakiyimin komai ba shahida,saidaima ni nace ki yafe mana nida mahaifinku" kukan da bataso ba a yanzu shi take haiqan,kaman ba zata fita daga gidan ba haka ta tako suna riqe da ita aka fito da ita,saitaji wani qauna da kewar mahaifiyarta na ratsata,taji kaman karta tafi,taji kaman taci gaba da zama dasu,a yanzu bata buqatar anwar sam,bata da buqatarsa cikin rayuwarta.

Tun daga harabar gidan anty usainan zaka gane wata walima ake ta daban saboda yadda harabar ta qawatu,uwa uba ankon da yake jikin duk wanda ke farfajiyar dama cikin gidan cikin wata atamfa mai azabar kyau da tsari.

Sabon shagali na walimar da dangin ango suka hada aka bude,nan aka zaunar da shahida suka dinga mata barin liqi tako ina,ba'a tashi ba saida akayi sallar magariba,anty usaina bata bari an shiga da ita cikin gidan ba,can wani babban falo dake da daki da bandaki aka kaita,babu kowa wurin da niyyar ko zatayi sallah,aka aje mata abinci aka barta ita daya donta sake,tuni 'yan uwanta suka koma gida ba wanda ya zauna,fashin sallah take hakanan abinci bata sha'awarsa,kuma batajin zai iya wucewa ta maqoshinta,saboda haka ta zauna kawai idanunta kan tv din dake aiki ita daya,volume dinta can qasa don ba'ajin ma me ake cewa,sam ba tv dince a gabanta ba,sabuwar rayuwar da zata fuskanta itace a gabanta,abu na gaba tsakanin kunyar anty usaina,ta yaya zata kalleta?,idan ta tuna kalaman data gaya mata na batason dan uwanta sai taji duk nauyi ya sauko mata,batasan itace wannan yayar tashi qwaya daya da bashi da kamarta ba,da duk yadda take qin abun ba zata yarda bakinta ya fada ba,addu'a take cikin ranta Allah yasa kada ta shigo.

Bakwai da rabi zuwa takwas na dare taji hayaniyar gidan ta ragu sosai,da alama masu tafiya sun tafi kenan,masu shigewa cikin gida sun shige,turo qofar da akayi shi yaja hankalinta,ta dan dage mayafinta kadan tana kallon mai shigowar,sa'ida ce saidai ita batasanta ba,fuskarwa a washe ta qaraso falon tana takowa a hankali tana waigawa,da alama ba'asan tayo.nan ba,dab da shahida ta zauna tana kallonta
"Anty,saike kadai?,nayi nayi da ummi tabarni nazo tace a'ah zamu takura miki kina hutawa ne,da qyar na samu na sallabo" murmushi shahida tadan saki tana duban sa'ida
"Ina yini anty,ya gajiyar biki"
"Lafiya lau,me sunanki"
"Sa'ida,'yar anty usaina ce ni,kuma qawar uncle anwar" girarta shahida ta dage duka biyun tana dubanta alamun tambaya,dorawa tayi
"Wallahi kun dace sosai anty keda uncle,uncle ya samu mata me kyau" tana murmushi sosai ta fada tana kuma sake kallon fuskar shahidan data ji tana burgeta,murmushi shahidan ta kuma saki
"Ko?" Tace cikin sigar tambaya,kaita kada
"Qwarai kuwa,amma anty,don Allah ki kularmin da uncle dina,wallahi inason uncle anwar,yana da kirki sosai,yana sonmu shima,yana kula damu sosai da sosai,don Allah anty" saita tsaya tana sake dubanta kafin ta kuma sakin murmushi,ta dora hannunta saman hannun sa'ida
"Uncle din naki nima zai iya kula dani ne sa'ida?" Dariya ta saki
"Tabdi,sosai kuwa anty,kinsan uncle anwar kuwa?,ai matarshi ta caba" saitayi qasa da murya
"Na zaci fa zai iya aurena harna cewa ummi ina sonshi,ranar saida na daku sosai,ashe babana ne" dariya ta kubcewa shahida da sa'idan duka,da sauran dariya a fuskar shahidan tace
"Babanki ne sa'ida,amma kita addu'a Allah ya baki wanda ya fishi nagartar halaye"
"Akwai wanda yafi uncle dina kuwa?" Ta fada cikin tantama da tunani,kaita jinjina
"Qwarai kuwa,duk wanda kika gani kome kika gani a duniya akwai wanda ya fishi akwai wanda baikaishi ba akwai dai dai dashi"
"Tohm shikenan......" Bata qarasa maganar ba suka jiyo taku ana nufowa wajen,saita fiddo idanu
"Na shiga uku anty,Allah yasa ba ummi bace" riqe hannunta tayi
"Karki damu,zance nina kiraki ki tayani hira" shuru sukayi suna jiran ganin wanda zai shigo din.
Chapter 56 · 0% Book details