Sashe 17
Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwatsam dare guda mahaifinta ya jijjigo maganar qarin aure suna tsaka da rayuwarsu cikin rufin asirin Allah,wanda hakan ya sanya mahaifiyarta tayi tsalle ta dire tace batasan wannan zance ba,dalilin daya janyo tashin tashina da fadan da bata taba gani ya wanzu tsakaninsu ba,hakan ya sanya walwalarta da duk wani kuzari nata ya ragu,anwar ne mutum na farko dayafu kusanci da ita a sannan shiya soma gane tana cikin damuww,amma baisan dalili ba,taqi kuma sanar masa,ta yaya zata gaya masa wannan murdaddeb zance?,tun baya baisan halin da gidan nasu ke ciki ba saboda kare martaba da qimar iyayenta,duk sanda ta fuskanci akwai rashin jituwa tsakanin iyayen nata bata taba yin zance a gidansu,a gidan anty amina take zancanta,toko yanzu ma da lamarin gidan nasu ya lalace can take tafiya ya sameta anan,don ba zataso wataran wani mummunan abun ya faru a gabansa ba duk da yana musu kallon iyayensa amma asirin ciki sai hanji.
*MAFARI*
Cikin tashin hankalin da bata taba tsintar kanta a ciki ba ta fito daga gidan nasu tana hawaye,yau a gidansu a gaban idanunta ake doki in doka tsakanin ummanta da abbanta?,wanne irin iyaye gareta?,ya ilahi ji take kaman zuciyarta zata fashe,ji takae bugawa zuciyarta zatayi,ita kadai tasan yadda takeji tana jin kaman zuciyarta ta kumbura ne ta cika qirjinta,zataso ace zunnurah na nan saidai ina,gidan anty amina takeson zuwa amma babu ko nutsuwar daukan kudin mota a wajenta,ba tare da tuna nisa da tazarar dake tsakaninsu ba ta hau tafiya cikin fitar hayyaci da tashin hanakali bacin rai da baqinciki.
Dawowarta kenan daga inda taje ta sauka a abun hawa,tana yunqurjn shigowa layin nasu ta hangi kaman shahidan,tayi mamaki don shahidan bata taba zuwa gidansu ba,hakanan bata yowa layinsu don asalan ita bamai yawo bace,sauri ta qara donta cimmata,sai taga itace dince kuwa,amma a binda ya bata mamaki hawayen data gani shabe shabe a i fuskarta,hannu tasa ta kamota tana cewa
"Shahida,meye haka kuka kike fa akan hanya" sai a sannan ta kula da fiddausin,sake fashewa da kukan tayi,ita koma waye ta gani zata iya fada masa abinda ke damunta ko zataji sassauci a zuciyarta,abun ya mata yawa,wannan damuwar bata shekara daya bace ko biyu,ganin haka sai fiddausin ta janye shahidan zuwa gidansu,ta tura gate din gidan suka shige sannan suka nufi dakinta ta qofar baya,sau tari takan iya shigowa ba tare da an sani ba saboda gidan nada girma babu laifi.
Kuka take sosai tana cewa
"Na gaji fiddausi....na gaji da wannan bacin ran,ina zanje naji dadi,me zanyi na samu sassauci?" Murmushi fiddausin ta saki,duk da shahidan bata gaya mata damuwarta ba amma tana ganin sara ne yazo kan gaba
"Ina da maganin damuwa shahida,maganin da zai dauke duk wata damuwa da kike ciki komai qarfi da girmanta,zaki jiki fresh kaman yau aka haifeki,nauyi da zuciyarki keji ya sauka kaman bai taba faruwa ba" idanunta dake jiqe da hawaye ta daga tana kallon fiddausi
"Don girman Allah ki bani kona daina jin suyar da qirjina yakemin"
"Kwantar da hankalinki basai kin hadani da girman Allah ba" ta fada tana zuge jakar data shigo da ita,kwalabe ta fito dasu ta hada abubuwan ciki ta gauraya sannan ta miqawa shahida
"Daga kanki ki shanye nina daga wajen likita nake shi ya rubutamin shi yace maganin damuwa ne" ba tare da kowanne tunani yazo kanta ba,ba tare da tayi lissafin komai ba,ba tare da ta jinkirta ba ta daga kai ta shanye duka din kamar yadda fiddausin tace mata,cikin wasu qananun mintina ta soma jin dummm,ta soma ji kamar ana sauyata daga tata duniyar zuwa wata daban,ta soma daina gane komai,take a nan ta zube saman gadon fiddausin,lokaci qanqani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita,dariya fiddausin ta saki tana rufe kwalabenta tare da maidasu haka tana cewa
"WASA FARIN GIRKI YARINYA".
*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videoshttps://youtu.be/T9a10h1Apqs
👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽
*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani DON GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina da buqata ki tuntubi wadan nan numbers din*
07067124863
*ko kuma*
09032345899
*Alqawarin Allah*
1️⃣2️⃣
A hankali ta farka tana mutstsuka idanunta da taji sun mata nauyi,sam ta mance inda take saida tayi dan tunani sannan ta tuna,da hanzari ta tashi ta zauna ganin gari yayi duhu sabanin sanda suka shigo gidan akwai hasken rana,agogon bango ta kalla sai taga qarfe takwas,hakan yana nuna kenan ta rasa sallar la'asar magariba dama isha'i.
Da hanzari tayi nufin tashi saidai gaba daya jikinta a mace yake babu qwari,daidai lokacin da fiddausi ta shigo dakin dauke da plate din abinci,cikin murmushi take duban shahida
"Sannu kin tashi?,ya kike jin kanki yanzu fresh ko?" Eh to,lokacin da tayi baccin ta mance komai,saidai yanzu bayan ta farka komai ya sake dawo mata,saidai baccin da tayi din ya rage mata bacin rai kadan,amma duka ba wannan ba,sallolin data rasa lokacin da take bacci su sukafi damunta,saboda haka tace
"Banyi sallah uku ba fiddausi,nunan bandaki na daura alwala"ta fada tana jin babu dadi har cikin ranta,wannan wanne irin bacci ne?,bata taba irinsa ba,hakanan koda bata da lafiya bata taba hada salloli ba.
Qofa ta nuna mata wadda take cikin dakin gadon nata,nan shahida ta shiga ta daura alwala,ta fito sannu sannu saboda yadda takejin jikinta sam.babu qwari,gagara yin sallar tayi a tsaye saboda yadda takejin qafafunta kamar lagwani tilas ta zauna ta yita a zaune.
Tana gamawa ta miqe don hankalinta yayi gida kuma,don bata taba tsayawa a waje har wannan lokacin ba bata koma gidan ba
"Ki tsaya kici abinci saiki sake samun qarfin jikinki"
"A'ah fiddausi gwara na wuce gidan,ba wanda yasan inda naje"
"Shikenan....bari na baki wannan duk sanda kike cikin bacin rai kina sha zaki baccinki ki manta da kowa" sam a cikin ranta batajin zata sake sha,saboda bata taba bacci irin haka ba,bugu da qari ita babu wani raguwar bacin rai data ji,don kada ta gwasaleta kawai ta amsa
"Maganin damuwa ne,zaki samu relief,kin ganni nan,ko bacci ne yaqi daukata saboda wani bacin rai dana sha zanyi baccina hankali kwance" kai kawa i ta gyada,fiddausi ta rakota har qofar gida ta wuce ita kuma ta koma cikin saurin don ta labartawa mima komai da yadda abubuwa suka gudaba,sannan ra fara da turo mata kudin data alqawarta mata,don syrup dinta dama ya qare tana buqatar siyan wasu ta aje.
Tsakar gidan nasu babu wadatar hasje sosai kasancewar babu wutar nepa,bata nemi kowa ba don bacin rai ke sake taso mata na yadda tabar gidan nasu dazu,uwa uba kuma wani sabon baccin take ji,gqba daya jikibta jibsa take kaman an tsoma lagwani a ruwa.
Kan katifarra ta fada rub da ciki tana lumshe idanu tanajin yadda gabobinta sukayi rauni,idanun nata na arufe taji wayarta na ruri,sam baki daya ta mance da ita,ta miqe cikin kasala ta daukota daga saman akwatin kayanta,anwar ne yake kira,take ta dannan ta kara a kunneta
"Ina kika shiga haka shahida?,nazo gida ana nemanki sama da qasa ba'a ganki ba?,na kira wayarki ya kusa sau hamsin ba'a daga ba" sai data lumshe ido sannan tace
"Babu inda naje fa,ina gidansu fiddausi,wayar kuma na manta ta ne cikin akwatin kayana,koka kira babu lallai aji sautinta" ajiyar zuciya ya sauke yana jin tashun hankalin da yaji dazu na sauka
"Karki sake irin wannan fitar,hankalin umma ya tashi sosai"
"In sha Allahu" ta fada amma cikin zuciyarta tana fadin koma meye sune suka ja
"Ya naji muryarki haka?,lafiya kike?" Saidata gyara kwanciyarta saboda baccin dake fisgarta tace
"Lafiya qalau....kawai...bacci ne yakeson saceni"
"Bacci yau kuma?" Ya tambaya cikin mamaki,sabida yasan a qalla suna kaiwa sha daya suna waya,a hakama shike datsewa yace tayi bacci,sam bata iya baccin wuri ba
"Wallahi" ta fada a gajarce,saiya raya a ransa jiki da jinine kawai don haka yace
"Alright,asuba ta gari to,tunda yau anmin ruwa gani da jin muryarki" murmushi ta saki a kasalance tace masa na gode ta datse wayar ta cillar gefe tana maida kanta saman filo hadi da sake lumshe idanunta.
Mubina ce ta dago labulen dakin ta shigo
"Yaya kizo inji umma...ashe kin dawo tun dazu ake nemanki" juyar da kanta tayi daya side din cikin muryar jin bacci tace
"Saida safe...kice mata nayi bacci" yau ba 'yan maganar bane akan mubinan don haka ta fita ta shaidawa umman tasu saqon shahida,sai gata ra taso da kanta
"Ke shahida....ina kika je tun dazu?"
"Gidansu fiddausi" ta bata amsa ba tare data juyo fuskarta inda umman tata ke tsaye ba
"Tashi ki dauko abincinki a kitchen kici"
"Ba qoshi" ta sake fada cikin muryar bacci,sam umman tata bata lura da sauyin dake tattare da ita ba,ga tunaninta fushi tayi kaman yadda ra saba a duk sanda wani abu ya gilma tsakaninta da mahaifinta,saboda haka ta tabe baki
"Indai ba zaki sawa ranki haquru da kauda da kai ba zakita ganin bacin rai,kije ki hadu da hawan jini a banza,babanku baida haquri kuma baida adalci,ni kuwa bazan tsaya ya tauyen haqqina ba atoh" tana gama fada ta juya ta fice,sama sama take jin abinda umman ke cewa,ga mamakin kanta da kanta,maimakon ta sake jin haushi yadda ta saba sai taji sam maganganun basu d'a d'ata da qasa ba,baccinta ya fiye mata komai,idanu ta sake rintsewa ba jimawa kuwa wani nannuyan bacci ya kwasheta.
Kwana biyu tsakani suka ci gaba daga inda suka tsaya,a lokacin tana daki zaune tana turawa anwar tex,tun tana daure zuciyarta harta kasa,ta toshe kunneta duk a banza,takai ta kawo cikin dakin ita kadai saita fita,haquri ta soma basu tana kuka kowa idanunshi ya rufe ba wanda ya saurareta bare yayi shuru ya ragawa dan uwanshi,dare yaui ba damar ta fice daga gidan ta huta,sai kawai maganin da fiddausi ta bata ya fado mata ta juya da sauri ta koma dakin ta rufo qofar don sautin tartsatsin fadan ya ragu,ta duba saman madubinta yana aje ta dauka ta bide ta shanye gaba daya,ta koma gefan gadon ta zauna tana kuja gamida addu'ar Allah yasa yayi mata aiki,Allah yasa baccin yazo da wuri ya dauketa kota huta dajin meke faruwa cikin gidan.