← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 73

Sashe 34

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin harabar gidan yake zaune cikin motarsa,murfin motar side din da yake a bude yake,hakanan ya ziro qafarsa daya waje,iska mai dadi dake kadawa tana shigowa har inda yake,iskar na masa dadi qwarai,,dalilin kenan daya sanya idanunsa lumshewa yana shaqarta har tsakiyar kanshi,knocking glass din motar yaji anyi,ya ware idanunsa a hankali suka sauka kan fuskar nafisa dake tsaye cikin kwalliya tana dubanshi daga sama har qasa,duk da fuskarta qawace take da kwalliya amma annurin cikinta kadan ne,shigarsa take kallo,yayi kyau cikin qananun kaya baqaqe qafarshi saye cikin wani booth mai bala'in kyau,quruciyarshi da kyanshi muraran suka bayyana,sai taji sonshi na sake shigarta,baqinciki da bacin ran daga bikinsu ya sake mamayeta har hakan ya bayyana kan fuskarta
"Whats wrong with you" ya tambayeta idanunsa qyar a kanta,saitayi narai narai da idanu,qwayar idonta cike da qwalla,,da alama gab take da sakin kuka,shuru tayi ba tare data amsa ba,fitowa yayi gaba daya daga motar ya rufe sannan ya jingina da ita hannayensa shima harde a qirji
"Me ya sameki kuma?"
"Au..baka ma sani ba zaka cemin?" Hannayensa ya watsa yana harde qafafunsa sannan ya soka hannayensa a aljihun wandonsa
"Eh to,xai iya yiwuwa ni abinda nake tunanin shi zai saki kuka ke a wajenki bashi bane"
"Me yasa anwar me yasa har qarin watanni uku bayan wata gudan dake gabanmu" girarshi biyun ya dage yana murmushi
"Au,kice ke kukan aure kike,to saurin na meye?,wata hudu kawai saiya zama damuwa?" Langabe kai tayi tana dubanshi
"Ni sai ya zama damuwa mana a wajena idan har wajenka bai zama damuwa ba,dama ni na damu dakai ai na sani" murmushi ya kuma saki,yadan tafa hannunshi kadan
"Abinda ya faru ya riga ya faru,sai a jira zuwan lokaci"
"Ai shikenan,yana iya"agogo ya kalla sannan yace
"Zan wuce" idanu ta zaro
"Duka duka yaushe kazo?,haba ya anwar mana don Allah,hajiyama fa tace ka shigo kaci abinci"
"Sauri nake nafisa,amma idan na samu chance anjima zan dawo,idan ban dawo ba kuma sai gobe" ya qarashe maganar yana bude motar,sai daya shiga sannan ta mayar masa da murfin ta rufe ta daga masa hannu
"Allah ya kiyaye" shima hannu yadan daga mata,har zai tada motar tayi hanzarin tsaidashi
"Sorry...don Allah ka yimin alfarma mana"
"Allah yasa batafi qarfina ba" murmushi tayi
"Bata fiba,saidai idan ba za'a min ba" dan qaramin murmushi yayi
"Fadi muji"sai data danyi shuru na sakanni sannan tace
"Kamfani triple R Gem nakeso ka rakani don Allah" shuru yayi yana dubanta
"Me zakiyi a can" hannu ta yarfar
"Kai ya anwar,da banso gaya maka ba Allah,amma..."
"A'ah,riqe cikinki" yayi maganar sanda ya tada motar,da sauri ta zaburo
"Bafa wani abu bane,wasu sarqoqi nakeson saya a can" kallonta kawai yake,burin nafisa yayi girma da yawa,duk sarqoqin garin nan amma sai taje har triple R ta saya?,iya saninshi wajene dake da babu abun qaramin kudi a can,dutse ne masu daraja da tsada suke sarrfasu,wanda ba kowa ke iya siyan abun kwalliya ba acan,bayason ya fiya gwasaleta har taji kaman ya tozartata,sai ya gyada kai
"Alright..amma gaskiya bani da lokaci cikin satin nan gaba daya,saidai ko zuwa next week"
"Well,yayi indai zaka rakani din" da haka sukayi sallama ya fice daga gidan yabarta tsaye awajen sonshi na shawagi da ita,sai kuma ta tuna yau akwai partyn da zata saboda haka da sauri ta juya zuwa cikin gida.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Qarfe biyar ta fito daga kamfanin kaman yadda qa'idar lokacin tashinsu yake,saidai gaba daya hankalinta ba'a kwance yake ba saboda baqin hadarin daya hado yake kwance a sama yana shirin zub da ruwa.

Kusan mutum uku ne sukayi mata tayin sauketa a gida amma ta doje don kare mutunci da qimarta,ciki harda alhajin dake nacinta wanda ta lallaba ta fito abinta ta baroshi a office din rayyan mai kamfanin gaba daya suna lissafin wasu sarqoqi da sukayi masa,haka ta fito cikin ranta tana addu'a Allah yasa ta isa gida lafiya qalau.

Titin babu wadatar motoci sai jifa jifa,ko dama can titin bashi da wadatar wucewar ababen hawa musamman ma na haya,yawanci saina gida,hakan ya sanya ta ku

sa kashe minti goma tsaye ba tare da taga gilmawar wani abun hawa na haya ba,cikin abinda bai gaza minti biyar ba hadarin ya taso sosai,iska ta shiga kadawa ko ina sama ta sake duhu,fargabarta ta dadu,ta runtse ido tana jin saukar ruwan saman bisa fuskarta,Allah dai yayi saiya daketa.

A hankali yake tuqin saboda yanayin ruwan dake sauka din,uwa uba yanajin kaman yayita shawagi saman titi ba tare daya koma gida ba,yakan kasance cikin kewa da kadaici duk sanda ruwan sama irin haka ke zuba yana cikin gidan shi daya,yakan tuna masa wata hira da suka tabayi da uta,duk da yadda yakeson bunne komai nata amma duk lokacin da ake ruwan sama kaman haka sai hirar ta fado masa
"Nafison damina akan kowanne yanayi,tana saka nishadi cikin zuciya,komai yana wankewa yayi fes,tsirrai zaka ga sunyi kyau ya anwar sunyi kore shar,kosu kasan suna farinciki da zuwanta,qamshin qasa iska mai dadin da babu kamarta" tayi maganar ne idanunta na alumshe,saita budesu tar cikin nashi a lokacin da ya zuba mata ido yana tayata murmushin da takeyi na tuna yanayin da tayi
"Kasan me yaya anwar?" Ta tambayeshi wanda bata kai ga fadin abinda takeson fada din ba kiran nafisa a sannan ya katsesu,dai dai sanda shima nashi tunanin ya katse yana hango tsaiwar wata matashiya cikin ruwan saman da har hazo hazo yake,tsurawa wajen ido yayi yana ci gaba da tuqin a mugun slow kai kace motar na dab da mutuwa ne,baikai ga qarasawa ba wata farar mota ta yanko daga layin da yake kusa da ita,dab da ita ta tsaya na cikin motar ya fito riqe da lema ya iso gabanta ya matsar da lemar zuwa kanta da alamu magana yake mata,idanu ya runtse yana tsaida motar duk da a tsakiyar titi yake,idanunsa qur akansu,alokaci shahida ta sake ja baya
"Ka wuce kawai,bani da damuwa nasan ko ban samu mota yanzu ba ruwan daya tsagaita zan samu"
"Haba yallabiya,ke kuwa yau dai kawai,uzuri ne fa,kiga yadda ruwa ke dukanki ke daya atsaye anan,uwa uba tsaiwarki a titi irin wannan lokacin hatsarine ga rayuwarki"kai ta girgixa
"ba komai Allah zai kareni"
"Duk da haka amma kiyi...." Ta gaji dajin kalaman bakinsa,saboda haka kaman adan hasale tace
"Don qaunarka da mahaliccinka kayi tafiyarka" ya fuskanci kaman tanason hasala ne don haka yace
"Allah ya baki haquri,naji zan tafi,amma kema don qaunarki da mahaliccinki ki karbi wannan lemar" batason dogon zance saboda haka tasa hannu ta amsa,ya koma ya shiga motar ya tasheta ya wuce,ajiyar zuciya ya saki ganin tafiyarsa,duk da haka saiya kasa tafiya yaci gaba da tsaiwa kaman me gadinta.

Ganin ruwan yadan fara sauqi saita soma takawa don canza wani titin ko zata dace,shima saiya tashi motar yaci gaba da binta sannu sannu,yana kallon yadda take digar ruwa har cikin zuciyarsa,saidai bazai iya daukarta amotarsa ba,yanajin wani abu cikin zuciyarsa,kallonta na tuna masa da ganinta da yayi,fitowarta daga motar wani,wanda ba qaramin suya yake masa a qirjinsa ba.

*ga mai buqatar littafina da zan fara bayan gama alqawarin Allah,zaije youtube yayi searching SAUTIN HIKIMA,daga qasa zaiga an rubuta SUBSCRIBE da jan rubutu,ya danna sau daya zai koma black,yayi screen shoot ya tiro zuwa wannan number,za'ayi adding dinsa agroup din in sha Allah*
07038670166 *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don girman Allah karki sharing,idan kina da buqata ki tuntubi wadan nan numbers din*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

*Alqawarin Allah*
2️⃣3️⃣

Gab da zata tsallaka daya titin mai adaidaita ya taho,ta tsaidashi da sauri,babu kowa a ciki ta gaya masa inda zata ya dauketa suka wuce,sai da yaga tashinsu sannan ya saki ajiyar zuciya
"Wai anwar meye damuwarka ne haka?" Wani sashe na zuciyarsa ya jeho masa tambaya,sai a sannan ya dinga tuno abinda ke faruwa,sam duka baisan yana abinda yayin ba,kamar wani umarni yaji ana bashi,kai ya girgiza yana jin haushin kansa,yana ganin ya tsaya ne kawai ya bata lokacinsa,motar ya bawa wuta sosai cikin gudu ya figeta ya harba titi.

Su duka suna zaune a falon suna kallo,da sallama ta shiga,dukkansu sannu da zuwa suke mata,anty zubaida na cewa
"Wai wai,sannu rahamatullah" murmushi tayi tana zuge lemar hannunta,huda ta tashi da hanzari zata tarbeta ta dakatar da ita
"Tsaya huda karki jiqe,don ni da kika ganni yau jalaf nake a kaina ruwan yau ya qare" tayi maganar sanda take aje jakarta
"Ahto...haka kawai za'a baki mota kika qi,da kinga yanzu ba ruwanki da ruwa ko rana"
"Wallahi anty to ya za'ayi....faruqu don Allah zazzagemin jakarnan ka duban wayata ka shanyan abinda kaga ya jiqe" da sauri huda ta amshe cikin shagwaba
"Anty gani sai kice ya faruq kuma?"hararta faruq yayi
"To kishiyata" Dariya shahida tayi
"Auto auta yi haquri,gyaramin bari naje na sauya kayan jikina sanyi sanyi nakeji"
"Idan kin saukoma ga dinkunanki nan an kawo" waiwayowa tayi
"Yauwa,yaushe ya kawo?,jiya fa mukayi waya dashi yace bai gama ba"
"Dazu ya kawo"
"Ya kyauta,don kayan matar data bani aron style nakeson maida mata,kar taga rashin hankalina...bari naje na dawo saina gani"
"Uhmmm" anty zubaida ta fada.

Sai data soma kunna qwan dakin data kashe dazun da zata fita aiki,haske ya gauraye ko ina,ko.ina tsaf yana fitar da qamshi kaman yadda ta saba masa,ta kalli agogo,shida harda rabi na yamma,an kusa kiran magariba kenan,kayan jikinta ta fitar ta shiga bandaki ta hada ruwa mai dumi sosai tayi wanka hade da alwala sannan ta dawo daki ta shirya cikin wasu kaya masu dan kauri,sai datayi sallar magariba sannan ta sake fitowa.

Yanzun ma a zaune ta samesu,saidai da alama faruqu da haidar sunje masallaci sun dawo,anty zubaidan ma wannan karon da hijabi jikinta,huda dake duqe gaban socket ta dago tana cewa
"Yauwa anty,yaa nuradden ne ya kiraki"
"Uhmmm" ta amsa tana dubanta,saita ciro wayar ta kawo mata ta karba tana dubawa,Allah ya taimaketa ba abinda tayi ruwa bai tabata
"Na gode hudallahi" shahida na murmushi ta fada.

Saida sukaci abinci sannan ta duba dinkunan,sunyi masifar kyau ko ba'a fada ba tasan zasu zauna mata a jiki,saita yanke kawai ta barsu saida bikin da zasuyi,ta ninke kayan ta kwashesu ta haura sama dasu,don yau da wuri takeson kwanciya har yanzu kuma yayyafi ake,saboda gobe sammakon fita zatayi akwai ayyuka da yawa.
Chapter 34 · 0% Book details