← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 73

Sashe 39

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu yasa ya amshi kwanon sanda take shirin xama ya ajeshi gabanta,saida ta zauna sosai sannan ya soma gaidata
"Mun sameku lafiya?"
"Lafiya qalau alhmdlh....yaro kaike hidima damu haka tsahon shekaru uku amma baka taba tsayawa na ganka ba ko wani cikin 'ya'yana ya ganka ba bare yayi maka godiya" murmushi yayi har fararen haqoransa suka bayyana idanunsa a qasa,sai taga ya sake koma mata anwar din sak,anwar din da har kwanan gobe takeson tasan ina yake?,meya rabashi da jikartata,amma har yau idan zata tambayi shahidan sau dari bazata tada kai ta bata amsa ba,harsai ta gaji tayi shuru
"Amma saurayi....sai naga kamar anwaru ko?,anwarun shahida" daga kai yayi yana duban dadan tare da jinjina ma qoqarinta data iya ganeshi
"Shine daada" gaba daya fuskarta ta washe da fara'a sosai,wani irin farinciki ya mamayeta,tunda taga anwar din a wancan shekarun Allah yasa mata qaunarsa,ya shiga ranta sosai,dai daikun ranaku ne da zasu zo su shude bata tuna dashi ba
"Ma sha Allah,Allah abin godiya,kana nan dama anwaru?,har kana iya zuwa guna ka aikomin da saqo amma ka kasa shigowa na ganka mu gaisa ko sau daya ne?,haba anwar,me muka yi maka haka?" Murmushin dai ya sakeyi
"Kawai haka Allah ya tsara mana daada,shi ya raba ganawarmu sai yanzu daya qaddara haduwar tamu"
"Wannan haka yake" ta fada tana jinjina kai cike da gamsuwa,har yanzu bakinta ya kasa rufuwa
"Ashe daada baki manta dani ba?" Baki ta kama tana cewa
"Ta yaya zan manta dakai anwar,bani bama hatta da qannen mahaifin shahida sun kasa mantawa dakai,kaiba irin mutumin da za'a manta dashi bane anwaru,gashi shekara kusan uku kanamin alkhairi ba tare daka bari nasan cewa kai bane....kai sule,zo nan zoka amsowa anwaru damammiyar fura da nono" tafada tana qoqarin kunce daurin habar zaninta dake daure da kudi,da sauri anwar ya dakatar da ita
"A'ah daada,don Allah karki wahalar da kanki" dakatawa tayi da abinda take
"Karka tsaidani anwaru,nasan yana daya daga cikin abinda kafison sha rahama ta gayamin tun lokacin ban manta ba,wannan shine kadai abinda nakejin zan iya maka" saiya qyaleta ta kunce kudin ta baiwa sulaiman ya amsa ya fice.

"Wanne laifi muka yi maka haka anwaru daka gujemu haka?,ka bace mana bat,ina tsaka da murnar jikata ta samu nagartaccen miji,tunda har naji isma'ila Allah ya jiqan rai na yawaita maganarka na tabbatar da nagartarka,dana ganka kuma saina sake tabbatarwa lallai nagartaccen ne kai,ita kuma waccar almurar koxan kwana kwana tambayarta ba zata cemin kanzil ba" gyara zamanshi yayi sannan a nutse yace
"Dukkan abinda ya faru a rayuwar bayi ba shakka muqaddari ne daga Allah,kisa a ranki hukuncin ubangiji ne bacewata daga rayuwarku..."
"Gaskiya ne" ta amsashi tana gyada kai,sadda kanshi qasa yayi sosai
"Zuwa nayi ki bani aurenta daada" kyakkyawan murmushi ya subuce kan fuskar dattijuwar,cikin ranta tana godewa Allah tare da hamdala,tayi tsammanin shahidanta ta rasa nagartaccen anwar din nan,sai gashi ya dawo a sanda basu zata ba
"Wannan ai tsohon zance ne anwar,shahida ai taka ce" wani abu ya tsaya masa a wuya,zayafi kowa farincikin jin hakan da ace a baya ne sanda shahidan take shahidan anwar ba yanzu data zama ta kowa ba
"Na sani daada,amma wannan karon nazo ne a bani auren shahida da gaske ba kamar a bayan ba"
"Indai wannan kake da buqata kana iya komawa da aurenta,bamu da haufi kanka anwaru,koda mahaifin shahida na raye nasan haka zai fadi" hakanan yaji wani sasauci a ranshi da zuciyarsa,wanda ya danganta hakan da nasarar da zai samu ce ta nunawa shahida da saurayinta cewa shiba sa'ansu bane takowanne fanni
"Amma duk da haka,ka jira zuwa gobe zan kira kawunnanta na tabbatar musu da aurenka da shahida"
"Na gode qwarai da gaske daada da wannan karamci,amma inason kimin wata alfarma guda daya"
"Ba zata gagara ba insha Allahu anwaru"sassauta muryarsa yayi
"mun samu sabani da shahida wanda shi ya zama silar rabuwarmu na wadan nan shekaru,na dawowa shahida saidai yadda ta dauki zafi fiye dani ta tabbatarmin ba zata taba karbata a matsayin miji ba..." Yadan dakata a ranshi yana istigfari kan qaryarda yayi
"Inason don Allah dada a boyewa shahida gaskiyar wanda ke neman aurenta,inason na gaya mata da kaina mu sasanta kuma kanmu ba tare da kowa ya shigo ciki ba" qanqan da ido daada tayi cikin masifa tace
"Wato ja'ira tasan komai shi yasa ko zaka kwana tambayarta saita dinke bakinta ko?,yoni aida ka barni da ita don dakalin qofar gidansu mu gauraya da ita,ja'ira tana tafe kaman daben masallaci kai kace ba ita bace..." Duk yadda yake jin ransa saida fadan dadan ya bashi dariya,ya danne yana cewa
"Ki haquri daada karki tasarmin ballina"qwafa taja
"Don dai kace haka ne amma da goben zan gaya mata da kaina,idan yaso ta iskoni katsina ta hukunta ni" daada na tsaka da fadan dake baiwa anwar dariya yake kuma sakashi nishadi sabida nasarar daya samu sulaimanu ya dawo da damammiyar fura mai sanyi data sha suger,sosai anwar ya sake ya dinga sha suna hira da dadan tana bashi labarai wanda anan yaji labarin rasuwar abban shahidan,sosai jikinsa yayi sanyi qwarai,ya dinga jin babu dadi har cikin ransa,ya dinga tuno abubuwa da dama tsakaninsa dashi,yana qaunarshi sosai hakanan yana ganin girmansa,kaman dan cikinsa ya daukeshi ba suruki ba,yayiwa daada ta'aziyya sosai.

Bata barshi ya tafi ba saida tayi masa irin danwaken da yakeso,wanda ta taba yi masa zuwansa ziyara wajenta na farko,baici da yawa can ba saboda tuna wani lokaci da yayi a baya,hakan yasa yaji cikinsa ya cushe,sai bayan la'asar sannan yayi mata sallama ya wuce.

Daga nan gidan wani abokinsa ya wuce,bashi ya baro wajensa ba shima sai gab da magariba,koda ga koma unguwar kakannin nasa yana aje motarsa ya wuce sallah masallaci,acan suka gamu da kawu modu suka rankayo gida bayan an idar.

Inna na zaune cikin rumfarta iskar fankar solar da anwar ya hada duka gidan na kaiwa da kawowa a falon,bata qure fankar can ba hakanan batayi qasa da yawa ba,hakan ya sanya iskar ke kadawa dai dai
"Ina ka tsaya haka daga cewa yanzu zaka ka dawo?" Sosai yakejin gajiya da kasala yadan motsa fuska
"Wallahi inna..nima ban zaci zan dade haka ba" dauke kai tayi ta kalli jijarta bushira dake xaune tana kallo falon inna tace ta miqawa anwar tuwon darenshi da mamarsu ta aje masa,cikin sabbin fulasai kaman da plates masu kyau harda ruwan sha a jug kaman yadda suka saba masa duk sanda yazo.

Qasa ya sauko ya soma zubawa da kanshi duk da cewa ba wata yunwa yakeji sosai ba,amma saboda innar kar tava dazu baici ba yanzun ma haka taji ba dadi
"Naje gidan daada ne,kakar shah....." Saiya kasa qarasa fadin sunan
"Rahama" ya qarashe fada da ainihin sunanta,wanda baya jin tsahon zamanin da yayi da saninta ya taba ambatar ainihin sunanta
"Wacece haka?"
"Yarinyar da zan aura..na taba baki labarinta shekara shida baya,wadda ta kasa zuwa gaidaku?" Murmushi inna ta saki
"Shahida wai?,yarinyar da usaina ke bamu labari wadda ta damu kan rabuwarku?" Kai ya gyada yana ci gaba da ci tuwon
"Ma sha Allah,amma saidai wani hanzari ba gudu ba,ina maganar yarinyar can nafisa 'yar wajen alhajin nan?,ina cewa duka duka watanni aurenku ya rage?,don dama zuwan naka nake jira naji ainihin sati nawa ya rage"
"Maganar nafisa tana nan,kuma watanni uku suka rage"
"Anya anwar?,kana nufin auren mata biyu lokaci guda?" Inna ta fada tana kallonshi,kai ua gyada
"In sha Allah inna,tunda Allah ya hore saidai a tayamu addu'a" shuru ta danyi kadan kafin daga bisani tace
"Shikenan...Allah yayi jagora,ubangiji ya kore abinqi"
"Ameen"sai daya hadiye lomar bakinsa sannan ya sake cewa
"Na shaidama kakartata gobe su kawu zasu je su tambayamin izini a wajensu,to gashi ban samu na sanarwa kawun ba,kuma a goben nakeson na koma saboda na baro ayyuka,ban tsammaci ma yau din zan kwana ba"
"Aiba wata matsala bace,ai ado kawai za'a yiwa waya(qaninta kenan)a sanarwa,shehu da dahiru suna kan hanya yanzu muka gama waya,sunje duba ta'annabi,idan suka shigo sai kuyi maganar".

Bashi yabar gidan ba sai qarfe goma na dare,sai daya tabbatar komai ya kammala ya kuma tsaru sannan ya nufi masauki,yana fitowa daga wanka yana shirin kwanciya wayar nafisa ta shigo,ya gaji tubus duk da yaga tarin miscal dinta niyyarsa saida safe zaya kirata saboda bacci yake da buqatar yi,dole ya daga bayan ya kwanta sosai saman gadonshi
"dear,ina ka tafi ne?,muhsin yace min baka gari"
"Katsina"
"Me kuma kajeyi can dear?"
"Kin manta ina da dangi ne a can?,naje gaida su inna,sannan kuma na gabatar da wani dan aiki"
"Au haka ne,me yasa baka hadani da ita ba na gaidata?"
"Idan kin matsu kina iya karbar lambarta tunda tana da waya,da can baki gaidata ba saida nazo zakice na baki?" A shagwabe tace
"Am so sorry dear,ka turomin number din nata saina kirata"
"Saidai gobe idan Allah ya kaimu,yanzun kam na gaji bacci nakeson nayi" da haka ya samu ya sallameta ya aje wayar tunani nakai kawo cikin ranshi,kenan yanzu idan lamarin ya tabbata mata biyu zai aure kenan?,juya lamarin yayi cikin zuciyarsa,koda wasa bai taba kawowa kanshi xai auri mata biyu ba,sai kuma tunaninsa ya juya kan shahida da nuradden,zayaso yaga fuskar kowannensu a sanda labari ya isa kunnensa,murmushin mugunta ya saki yana mirginawa hannun damanshi ya soma karanto addu'ar bacci bayan ya kunna suratul baqara cikin wayarshi ya rage mata sauti sosai.

*ga mai buqatar littafin da zan soma bayan kammala rubutun alqawarin Allah,zaije youtube yayi searching SAUTIN HIKIMA,akwai jan rubutu na SUBSCRIBE daga qasa,zaka dannan sau daya zai koma baqi,sai kiyi screenshoot ki turawa wannan number da zataso daga qasa,za'a sakaki a group din littafin da yardar Allah*

07038670166 *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gansu don GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina da buqata ki tuntubi wannan numbers din*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

*Alqawarin Allah*
2️⃣6️⃣

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Washegari qarfe tara na safiya ya gama shirinsa tsaf cikin yadinsa na maza mai kyau da tsada,yayi masifar kyau yadda hularshi ta zauna kanshi sosai kawai ya isa ya gaya maka ya hada jini da kanawa,hakanan yake jinsa wani sawai kuma fayau dashi,ya qarasa reception yayi maida musu key din dakinsu ya sallamesu ya wuce zuwa gidan inna.
Chapter 39 · 0% Book details