← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 73

Sashe 63

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A nutse ya gama saukowa sannan ya saka hanzari irin na ingarman namiji,kafin kace meye wannan ya cimmata,yasa hannu ya maida murfin qofat falon ya rufe idanunshi cikin nata ya bata umarni kai tsaye
"Wuce ki koma ciki" dubansa tayi itama
"Kaman yaya?,bayan na gaya maka tun jiya aiko?"
"Ki koma ciki kawai nace" saita dubeshi na tsahon minti daya,ta karanci da gaske yake,ita kuma na zata yarda yaga lagonta ba bare yaci gaba da sanyata yin abinda batayi niyya ba kuma bata shirya ba,saita sake dora hannunta kan handle din qofar da niyyar budewa,caraf ya riqe hannun nata,tana shirin masa tsiwar ya saketa bata ankara ba taji an sureta gaba daya daga ita hat jakar hannun tata,ya juya ya soma taka matakalar da zata sadashi da sama,sosai ta soma qoqarin zillewa ranta na quna na yadda ya maidata kaman wata karmami,ya dagata ba komai bane a wajensa kamar ba mutum ba?,sai kace wata 'yar baby
"Meye haka ne?,ka saukeni don Allah bana son irin haka,ka saukeni,ka saukeni bana so" abinda ta dinga fada kenan tana qoqarin qwacewa daga daga hannunsa,baiko bi ta kanta ba hakanan bai fasa hawa saman ba har sai daya dangane da bedroom dinsa sannan ya cillata saman lallausan gadonshi yana maida numfashi,fuskarshi a daure,ranshi a matuqar bace wanda ko ba'a gaya maka ba zaka fuskanci haka ta idanunsa da suka soma sauya kala,nunata yayi da yatsa cikin bambami dake nuna ranshi ya baci
"Na fuskanci cewa sassauci na yana neman kawo raini a tsakaninmu,barinki kiyi yadda kikeso yasa kikejin kece mijin nine matar ko?,to daga yau komai zai sauya,zaki gane wane shugaba tsakanin ni da ke" daga haka ya maida muqullin dakin ya rufesu shida ita gaba daya,cikin hanzari take saukowa daga saman gadon nashi tana cewa
"Ka budemin qofa,ya zaka rufeni anan,wai me yasa ka fiya son kanka ne da yawa?,me yasa kake zalunt...." Maganar tata ce ta katse sakamakon yadda ta sauko qafafunta qasa da hanzari da cogenta,sai akayi rashin sa'a qafar tata ta turgude da tsinin takalminta,maimakon ta qarasa maganar da take saita buge da sakin qara,ta koma tayi zaman dole bakin gadon tana duba qafarta.

Towel din dayake daukowa ya rataya a wuyanshi sannan ya waiwayo yaga me ya sakata yin qarar,idanunsa ya sauka a qafarta da take dafe da ita,a hankali ya qarasa ya duqa gabanta,ya saka hannu zai taba qafar ta janyeta baya da sauri tana ci gaba da dafe wajen,ya gane me take nufi,tana nufin batason ya taba nata qafa kenan,saboda haka ya qyaleta ya juya abinshi yayi shigewarsa wankansa.

Azabar data dinga ji cikin qafar ya tabbatar mata mawuyacine idan ba targade tayi ba,batasan ya zatayi da qafar taya ba,hakanan ita daua cikin dakin ta dinga dafe qafar tana jin zugi na ratsata.

Sai daya kwashe awa guda cur sannan ya fito,a shiryensa kaman ba shine ya shiga wanka da towel da jallabiya ba,ya isa gaban mudubi ya dauki turarukansa ya fesa,ta cikin madubin yaje dan kallonta yadda ta soma hada gumi,tuni harta cire yafen lafayar jikinta,idanunsa ya sauka kan lallausar t.shirt din dake jikinta fara sol mai dogon hannu da rufaffen wuya,wadda ta lafe sosai a jikinta ta fidda shape din albarkatun qirjinta,saiya dauke idanunsa daga kanta da sauri,ya gama fesa turarensa ya taje kansa sannan ya juya ya sake takawa inda take ya tsugunna gabanta karo na biyu,zata sake janye qafar yayi caraf ya riqeta sosai,ta saki ihun azaba sanda ya gama zare takalmin ya soma mammatsata,take ya gane targade ne,ya kuma gamo wajen,sai daya faki numfashinta ya kama wajen sosai wanda babu shiri ta qwalla wata irin qara tana qoqarin tureshi,saidai ko gezau baiyi na yaci gaba da gyara wajen,tun tana masa masifa tana jin girman kan ta roqeshi ya qyaleta harta soma roqon nashi tana hadashi da Allah,ta hada gumi jagaf kafin ya gama,yana sakinta ta saki ajiyar zuciya,sai kuka ya qwace mata,dama zuciyar na akusa,gani take kaman yana sane ya taba ciwon da yawa yayine kawai saboda mugunta.

Baiko dubeta ya juya ya isa bakin qofa yabude zai fice,taso yunqurawa ta miqe ta bishi a baya da hanzari ko xata samu nasarar ficewa amma ina babu damar ta taka qafar,tana kallo yaja qofar,saidai wannan karon bai rufeta ba,abinda ya sanyata sakin ajiyar zuciya kenan,ta maida kanta jikin filo ta jinginar tana lumshe jiqaqqun idanunta da duka jiqe da ruwan hawaye.

Tun tana sauke ajiyar zuciya tana shaqar qamshinsa daya kama dakin har bacci ya soma fisgarta,ta dinga dagewa don bata son yin bacci saman gadonshi amma ina yafi qarfinta.

Qarfe biyu na rana ya sake dawowa saman,duka yau ba inda ya fita,duk da yaso yayi fitarsa ya qyaleta amma saiya kasa,sanin cewa mawuyacine ta iya tabuka komai saboda targaden data ji din ba kadan bane.

A hankali ya turo qofar dakin,yayi tsammanin samunta zaune,sabanin hakan saiya sameta a kwance a rigingine tana bacci sosai,ya qarasa a hankali ya tsaya kanta hannunsa rungume a qirji ya zuba mata ido,irin kallon daya jima baiyi mata irinsa ba,abubuwa biyu na kokawa cikin zuciyarsa,ya samu ya kauda su,ya isa gefan kanta yadan bubbuga filon da take kai a hankali,bude idanunta tayi sannu sannu,saita tuna inda take,saboda haka ya ware idanun nata da sauri gami da miqewa zaune sosai tana masa wani kallo da yafi kama da harara
"Ki tashi ki sallah" ya fada yana aje mata takeaway,sannan ya goya hannunsa a baya ya tsaya yana kallon yadda take kokawar miqewa cikin dabara,da alama tana shan zafi amma taqi nemon taimakonsa,data gaji da kanta ta koma ta zauna tana lumshe ido saboda zafin da wajen yake mata,gami da sauke numfashi
"Ki tashi na taimaka miki badon halinki ba"
"Banaso" ta fada da hanzari,sai ya daga kafadunsa alamun bai damu ba ya soma takawa zai fice,ta kalli agogo ta tabbatar idan ya fita da matsala,lokaci zai iya qwace mata,ita kuma idan tace zata tashi da kanta zata sha wahala,saboda haka kaman wadda aka yiwa dole tace
"Dawo ka tayani,amma karka soma tabamin jiki don zaka rakani alwala"
"Riqe jikinki na riqe taimakona" ya bata amsa sanda ya tura qofar kamar xai fita,tana kallo ya sake ficewa,sai wani abu ya tokare mata maqoshi,ita zaiwa wulaqanci?.

Sau uku tana gwada takawar amma zafi da tsoro ya hanata,dole ta koma ya zauna tana kallo lokacin sallah na sake wuceta,baqinciki kamar tayi yaya.

Turo qofar da aka sakeyi yasata daga kanta,shine dai ya sake dawowa dauke da wata roba dake fidda tururin ruwan zafi,hannunsa dayan riqe da towel,gabanta ya iso saitin qafar ya aje robar sannan ya jawo wani qaramin qawataccen stool dan gajere ya dora robar akai,bai kalleta ba ya kama qafar ya dora saman robar,zafi yasa ta saki 'yar qaramar qara zata riqe hannunsa sai kuma tayi saurin janyewa,tana ji ya dinga tsoma towel din yana matsewa gami da danna mata wurin,tun tana jin ciwo harya soma sake mata,radadin ya ragu,tunda ya soma aikin bai daga kai ya dubeta ba,lokaci lokaci idanunta kan fada kansa ba tare data shirya ba,amma ko sau daya taci sa'a basu hada ido ba,tsahon mintuna sannan ya miqe ya dauki towel da robar ya fice dasu.

Sake gwada miqewar tayi wannan karon saita dan taku,a daddafe ta samu ta tura qofar da zata sadaka da falonshi don dakinta takeson tafiya,sam bata qaunar zaman dakin nasa,a bakin qofar falon wadda zata sadaka da matattakalar benan suka kusa karo yana dawowa tana shirin sauka,fuskarnan a tsuke kaman baisan meye dariya ba yace
"Ina zaki haka?"
"Inda nafi wayo" ta amsashi tana duban ta inda zata rabashi ta wuce
"Koma ba inda zaki,kin dawo nan kenan harsai kin gane kece matar nice mijin,don na fuskanci baki banbance tazarar dake tsakaninmu ba" wani kallonsa tayi
"Ba inda zan koma,dakina xan koma" girarshi ya dage
"Ashe?,tunda kin yarda dakinki ne can ashe nine mai gidan ko?"
"Oho?" Tace tana juya masa baya gami da turo baki,anwar din yakai mata ko ina,ya soma quret,ta fuskanci duk abinda zaiyi ya qureta ya iya,saita soma qoqarin rabeshi,qyaleta yayi harsai data raba tsakiyarsa sannan ya cukukikuyeta gaba daya cikin qirjinsa ya mata wani kyakkyawan ruqo,karon farko shida ita a rayuwarsu,ihu ta saki kaman wadda taga abun tsoro tana qoqarin qwacewa,daukarta yayi cak kamar yadda ya saba mata,abinda tafi tsana kenan,saboda idan yayi hakan gani take kaman ya raina mata wayo,bai sauketa ko ina ba bandaki,ya ajeta saman toilet sit,ta bude baki zatayi magana yasa yatsa ya dalle mata bakin gami da cewa
"Shshshs,karki sake ki mana surutu a bandaki" yana maganar yana zaro ido kaman wanda yakewa qaramin yaro,bacin rai ya hanata magana,saita qyaleshi tana kallonsa ya daura mata alwalar,zai sake sungumota ya fito da ita ta zille,ta tashi tana dingisawa ta fito,fafur taqi zama a bedroom dinsa sai a falo,a nan tayi sallarta.
Chapter 63 · 0% Book details