← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 73

Sashe 70

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Komawa tayi da baya kitchen din ta shirya komai ta dauko kan tray sannan ta sake fitowa
"A'ina za'a aje maka?" Nuni yayi kata da gabanshi,ta qaraso nan ta aje ta shirya komai ta dauko sauran na wajen dining shima ta shirya masa,tayi sarving dinsa sannan ta yunqura zata miqe saiya dakatar da ita yace ta zauna,ba musu ta koma ta zauna din,saidai duka bata jinta dai dai,baiyi magana ba harya qare cin abincin sannan ya soma da cewa
"Da can kafin aurenki ina tare da wata yarinya nafisa wadda har an saka mana rana lokacin biki ya rage saura sati uku,to wasu abubuwa suka biyo baya wanda ya zama silar fasa auren namu a wancan lokacin,a yanzu maganar ta dawo wanda ina tunanin duka ba za'a wuce sati uku ba nan gaba" bata taba tunanin zataji irin abinda taji a zuciyarta ba'a yanzu,tunda ya ambaci sunan zuciyarta da idanunta suka haska mata ita,saita dinga binsa da kallo kawai sanda yake bayanansa,gaba daya saita daina fahimtarsa,duka bayanan da yake kawai tana ganin yana yine saboda radin kanshi,yarinyar daya aiko mata da hotunanta sanda take tsaka da radadin rashin mahaifinta?,yarinyar daya turo mata da fuskarta sanda take tsaka da jimami da alhinin rabuwa dashi?,yarinyar daya kawo mata hotonta ta gani cewa ya samu wadda ta fita?,ya sauya wata a madadinta,a yanzu ita zai aura ya kawo gidan?,shine yake wani rufa rufa dason yiwa zancan kwaskwarima?,tana ganin abu mafi sauqi kawai ya fito ya gaya mata zai cika muradi da burinsa ne,yanzune manufar da yasa ya aureta zai bayyan muraran baro baro,me yayi saura?,me xata xauna taji daga bakinsa,ai komai ya qare hakanan komai ya fito fili,sai kawai ta miqe sanda yake tsaka da bayanin nashi,binta yayi da kallo ganin ta soma tafiya zuwa hanyar dakinta ba tare data ko waiwayeshi ba,kiran sunanta ya soma yi abinda ya jima rabonshi dayin hakan,saidai ko daya bata saurareshi ba bare taji me yake fada,da hanzari ya miqe ya bi baya,taji takun tafiyarsa,saboda haka tana shiga dakin ta saka key,ta samu gefan gadonta ta xauna ba tare datasan me zata tuna ba,wani kuka ne mai sautu ya qwace mata wanda ta kasa tsaidashi,hannunsa saman kanshi yana yamutsawa jin sautin kukanta dake ratso har inda yake tsaye
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya furta yana kallon qofar dakin da yayi juyin duniya ta bude taqi,bai taba xato ko tunanin xata damu ba ko sau daya,me yasa ta damu?,me yasa ranta yw baci?,bayan ta gaya mishi cewa bata qaunarshi ko kadan?.

"Me yasa kike kuka shahida?,kukan me kike?,kins kukane saboda mutumin da kika dainaso xai qara aure?,ko kina kuka ne saboda mutumin daya daina sonki xai auro wadda yakeso?,muradin zuciyarsa?,haske rayuwarshi?,meye abun damuwa a ciki shahida?,har yanzu anwar na cikin zuciyarki ko kuwa?" Tambayoyin da zuciyarta ta dinga mata kenan wanda yasa ta soma tuhumar kanta da kanta.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Duban nafisan mima takeyi sosai da wani irin banzan kallo,cikin ranta ji take kaman ta tashi ta shaqe nafisan,cikin ranta tana ala wadai da sakacin da tayi har ta bari tunanin nafisa yakai gata nemi anwar karo na biyu,tabbas da tasan da irin wannan ranar da tunu ta saka almakashi ta datse alaqar da tayi saura tsakanin anwar din da nafisan,koda yake a yanzu ma bata baci ba,saidai kuma ba haka taso ba,dole ya saka taka tsantsan da nutsuwa dinta wargaza tsakaninsu,don a yanzu bata da burin daya wuce ta ganta itama gidan anwar din a matsayin matarsa,sake duban nafisan tayi a karo na biyu yadda taketa faman fara'a,bakinta kamar zai hade da kunnenta,irin kallon da miman ke mata yasanya jikinta yadan soma sanyi
"Ko bayi dai dai bane hajjaju?,bafa zan iya haqura da anwar ba matuqar ina raye shima yana raye" baki miman ta tabe tana ci gaba da dubanta
"Dama aida kin jira ni nidin xan miki wannan aikin,abinda yasa kika ji shuru ba'a kai gabar bane,naso mu gasashine harsai ya kawo kanshi da kanshi ta yadda koda kin shiga saikinfi daraja da qima a idanunsa,amma a yanzun yadda kikayi wallahi qimarki ta zube qasa warwas,kuma haki da wata fuffuka da xakiyi idan kin shiga gidan,hasalima ba baiyi matsuwar shigowarki gidan ba kinga baki da abun cewa sawa ko hanawa koda kin shiga gidan" sai jikinta ya danyi sanyi,taji maganar mima tabbas tana kan hanya,shigen maganar da mummynta ta gaya mata kenan,ita kuwa a rayuwa yanzu burinta na gaba shine ta shiga gidan anwar ta zama ita ke fada aji,ita zata sa ayi ta hana kuma a hanu,wanda daga qarshe take fatan shahidan ta fita tabar mata gidan gaba daya taci gaba dayin yadda takeso.
"Gaskiyar magana mima banason nayi rayuwar da bani zance ayi ba cikin wannan gida,saboda har yau ina tsoro kuma ina shakkar soyayyar dake tsakanin anwar da wannan mayyar yarinyar" abun nema ya samu wajen mima,hanyar da zata wargaza rayuwar auren nafisan cikin sauqi,duk da haka saita sake tsuke fuska ta kuma gum da bakinta harsai da nafisan ta sake magantuwa cikin mitar tayi mata shuru,fuska ta yatsina
"In sake shiga sabgarki ki watsamin qasa a ido?,ina qoqarin fiddo miki da daraja da martabarki amma ke baki gani,gwara kawao na qyaleki kici gaba da samawa kanki mafita" harara ta watsawa miman
"Banason wulaqanci wallahi mima,haba don Allah,sau daya dai don nayi amfani da shawarar kaina saiya zama matsala?" Sai data gama shan qamshinta sannan tace
"Shikenan,zaki samu yadda kikeso,zaki mulka anwar ki kuma juyashi shida waccar yadda kikeso matuqar zaki jure ki kuma bi doka da qa'ida,zan dawo next week randa kikacemin zaki fara rabon IV zakiji sauran qarin bayani" kamar ta goya mima haka nafisa taji,kudade masu yawa ta baiwa miman sannan ta rakata.

Dariya mima ta saki bayan ta gama irga kudaden,mota takeson sauyawa,kuma ba shakka lokacin da zata sauya motar da takeso din yayi,a jikin nafisan zata hada kudinta tsaf,daga qarshe kuma ta tashi a tutar babu,ba anwar din ba kuma kudinta,daga haka ta tada motarta taci gaba da tafiya tanabin waqar dake tashi cikin motar cikin nishadi gami da tsara yadda zata mallaki anwar ita kadai bayan ta fitar da shahida da nafisan ma daga gidan dukkansu.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Kaman a mafarki take jiyo sallamar anty xubaida cikin falon nasu,da sauri ta sauko daga gadon wanda ta maidashi wajen rayuwarta,idan kaga ta fito tota tabbatar anwar ya fita baya gidan sannan zata fito tayi aikace aikacenta a gaggauce ta koma,sam bata qaunar haduwa dashi ko daya,Suna shirin yiwa kansu mazauni ta fito fuskarta a washe
"Anty yau a gida na?,ashe xakixo?"
"Kamawa ai take,gashi ta kama shahida naxo" cikin walwala da farinciki ta tarbesu.

,sun jima sosai ranar,sunata hira dasu huda,duk sai yaji kewar gida ta sake kamata,kaman ta koma gidan haka takeji.

Saida suka dan kebe sannan anty zubaidan ta gaya mata abinda ya kawota,zancan auren anwar,kebe fuska shahidan tayi cikin nuna halin ko in kula,saidai can qasan ranta wani abu ke tsinkulinta,maganganu sosai anty zubaidan tayi mata,gami da jan hankalinta,suna gama cin abincin rana tace zasu koma,kaman shahidan tayi kuka amma hakan ta haqura,taso sosai antyn tabar mata hudan amma qememe taqi,haka suka tattara tanaji tana gani suka tafi.

Zuwan antyn yasa tadan sake ranta,ta koma sabgoginta kamar baya,saidai ta sake janye sosai daga anwar din,sati biyu da faruwar hakan anwar ya shigoda set din manyan akwatina guda hudu,da farko tayi burus amma daga bisani tayi tunani kada ya tsammaci kishinsa take saita karba ta masa godiya,yayin daya bita da kallon mamaki,da gaske bata jin kishinsa? Hakan na nufin bata sonshi?.

Cikin kwanakin ka'in da na'in ya maida hankalinsa ga koyon abinda yasa gaba daga raha computer instute,ya ware lokaci har gida yake iskeshi malamin,baisan me yasa abun ya tsaya masa a rai ba,bai san me yasa ya maida hankali fiye da yadda ya xata ba,wanda yake da tabbacin cewa cikin wata uku ya cimma abinda yakeso ya cimma din,ta bangare guda guda kuwa yayi qoqarin kawo sauyi ko yaya yake tsakaninsa da shahidan,don ko kusa baida burin nafisa taxo ta fuskanci komai dangane da zamansu,duk da qoqarin nasa sau da yawa yakan cimma tasgaro,saboda rashin samun cikakken hadin kai daga shahidan.

Ta bangaren amarya nafisa kuwa shirye shirye sun kankama ka'in da na'in,dukkan wani abu da aka sani na bidi'ar biki ba wanda bata tsara xatayi ba,harda ma wanda ba' saba gani ba,ko sauraren abinda anwar din zai bayar batayi,sha'aninta kawai take.

Qarfe shida saura malamin da suke karatu tare ya tafi,yarage saura shi kadai a dakin,ya shiga cumputer din sosai yayi shige da fice wanda ya tabbatar masa lallai ya soma nisa,hakanan yana cimma abinda ya nufa din,saiya kasheta yana sakin murmushi wanda yayi dai dai da shigowar kira a wayarshi,duban wayar yayi sai yaga nafisa ce,ya manta shaf cikin satin zasuxo jeran kaya,bai daga ba harta katse,saiya janyo wayar yana laluba inda ya aje numberta,cikin sauyin da aka fara samu wanda ada bashi da ita.

Har tayi ringing sau biyu tana katsewa ba amsa,sai ana ukun sannan ta daga,shuru tayi tana sauraren muryarsa wadda ko mutuwa tayi ta dawo ba zata kasa gane muryar waye ba
"Bakisan ina cikin gidan bane?" Ya tambayeta ganin tsahon zamansu baiji motsinta ko gilmawarta ba,shuru babu amsa saboda haka ya kautar da wancan zancan
"Ki sameni a dakin karatuna....am yana nan daga baya kaman zaki shiga qofar kitchen ta baya" ya sake mata bayani don ya sani bata sani ba,tunda bata taba zuwa ba.

Wayar ta sauke tana jin wani haushinsa na kamata,tome zaiyi mata,kiran me kuma yake mata?.

Har sai daya zaci ba zata zo ba yaci gaba da aikinsa sannan yaji an murda murfin qofar,ya daga kai yana kallon bakin qofar,itace cikin jar doguwar riga wadda ta yane kanta da qaramin mayafinta,idonsa ya dauke wani abu na tsirga masa,ba kwalliya a fuskarta amma tayi masifar amsarta rigar wanda ya kasa kubuta daga qyasata da zuciyarsa tayi.
Chapter 70 · 0% Book details