Sashe 60
Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Yana kwashe fasassun gilasan yana tuna abinda ya farun,yakai tatsunsa saman lips dinsa ya shafa,yadan cije lebansa na qasa kadan,tabbas yaji zaqi a bakinta,saidai yasan ba kayan maye bane,don tunda ya bada sadakinta ya zuba ido akanta sosai amma bai taba ganin wani abu da zai sashi ya zargeta ba,ko da shahida nakan halayenta nada da idanunsa suka gani,koda bazai dore a zaman aure da ita ba zaiyi qoqarin ganin ya maidata saitinta kodon soyayya da amanna da mahaifinta ya bashi a baya,duk da hakama baiga wani mummmunan abuba game da ita har yau daga sanda ya soma sanya idanu a duk motsinta.
_gashinan yau na muku,amma har gobe sai jibi idan Allah ya kaimu_🙏🏽🙏🏽 *Alqawarin Allah*
3️⃣8️⃣
Kafin ta sauka qasa ta dan jima a tsaye saman step na kusa da qarshe tana dai daita yanayinta sannan ta sauka a hankali.
Ana qwala kiran sallahn ya sauko cikin jallabiya mai gajeran hannu fara sol da ita,bisa dukkan alamu sabuwa ce,jikinsa na tashin qamshin turare mai sanyi kaman wanda yayi wanka dashi,zuciyarta taso yadan fisgeta ta kalleshi amma tayi ta maza ta dake kaman bata ganshi ba har ya fice masallacin.
Ba'a jima can da idarwa ba ya dawo,ya zauna saman kujerar falon suna dan taba hira da anty amina kafin su kammala kintsawa,da suka tashi tafiya saita rasa me zata basu,qarshe data shiga dakinta wajen akwatunan lefanta ta isa ,karo na farko data budesu ta kuma kalla abinda ke ciki,guda biyu ne masu dauke kayan sawa taf daqyar aka rufesu don ba abinda aka taba a ciki,ta dinga daga kayan daya bayan daya tana kalla,kan wata shadda lace ta tsaya,ta kalleta sosai,tun daga colour har design din choice dinta ne,tasan duk duniya kuma babu wanda yasan hakan sai anwar,hakan ya saka ta sanya hannu ta cirota,ta kalleta sosai,iya kyau ta mata kyau qwarai,kuma kana ganinta kasan babbar ce,saidai ba zata iya sanyata a jikinta ba,tasan anwar ne ya zabeta,ta yanke ta baiwa anty amina ita,sauran manyan su uku ta zaba musu atamfofi,yan yaran da yan matasan kuma ta diba musu kayan kwalliya,ta zaba kayan gararta da yawa ta hada musu.
Anwar yana tsaye ta miqawa kowa,ta miqo ledar anty amina yafi kusa da inda take tsaye,saboda haka ya zira hannu ya karba ya buda yana gani sannan ya rufe,daga kai yayi tasan ita zai kalla saboda haka ta dauke kai,ilai kuwa itadin ya kalla,haka kawai yaji kyautar ta masa ciwo,bawai saboda kudin abarba,a'ah,yafi qarfin kudinta hakanan anty amina a wajenta tafi qarfi wannan,yasan cewa da biyu tayi kyautar itama ta san da hakan,abinda ya bata ranshi kenan.
Har bakin mota tayi musu rakiya,anwar yace a matse sukazo hala,su ragu wasu su shiga motarsa ya kaisu,ta musu sallama ta koma cikin gida,harsun gama shiga yace yana zuwa,ya buda murfin motar ya koma cikin gidan.
Tana tsaka da tattare wajen taji shigowarsa,ta daga kai ta dubeshi saita basar taci gaba da abinda take kaman bataga shigowarsa ba,bayanta kadan ya tsaya,kaman bazaiyi magana ba sannan daga bisani yace
"Duk yadda kikeji a zuciyarki game dani kusan nima haka yake koma fiye,amma,karki sake gangancin da kikayi yau,duk kayan dana siya nasan wa na siyawa shi,idan da buqatar bada kyautar irinsu a siyo daga waje ba daga cikin akwati ba" idanunta ta watsa masa sannan tace
"Ina ruwan wani?,ina cewa kayana ne ko?"
"Alright,hakane fa,amma keda kayan qasan wa kuke?"
"Oho" tace tana ci gaba da aikinta,shuru yayi yana kallonta,saiya jinjina kai sannan yace
"Zaki gane kurenki" ya juya ya fice saboda tunawa da yayi yabar mutane a mota,tsaki taja taci gaba da aikinta tana cewa
"Na dade ban gane kuren nawa ba"
A gurguje ta gama duk abinda zatayi ta dauki duk abinda take buqata ta shige dakinta,wanka ta soma yi sannan taci abinci,ta jawo wayarta ta fara amfani da ita,kama daga kiran waya,da duba saqonnin wayarta ta watsapp,bataji shigowarsa ba sai wajen qarfe goma na dare,dai dai sannan ta miqe ta kashe qwanta ta koma gado tayi addu'ar bacci tayi kwanciyarta.
Shika koda ya shigo dakinsa ya wuce abinsa,baibi kota kan abincin dake kan tebur ba.
🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
Washegari ma ta samu baqi ba laifi duk da basu kai na jiya ba,abinda ya debe mata kewa kenan har wata washegarin,saidai randa ta cika kwana na hudu dif kakeji,duk sai taji gidan babu dadi,haka ta wuni ita kadai,daga kwanciya sai kallo sai latse latsen waya,har zuwa dare data kammala abinda take tayi shigewarta daki.
Tunda ta gama yin baqi bai kuma sakata a idanunsa ba,kafin magariba ta gama komai tayi shigewarta daki,bata fitowa sai washegari shima idan ya fita a gidan,zatayi abincin safe haka na dare ta aje masa,saidai shima bai bata taba abincin ba,yadda ta jera haka zata kwashe abinta,kusan hakan na faruwa ne saboda ya koma aikinsa gadan gadan,bai samun damar dawowa gidan dawuri,hakanan da wuri yake fita.
Sati biyu cur aka suka kwashe a haka,idan ya dawo bai ganinta,hakanan idan zai fita ma haka.
Zaman taji ya isheta,kadaicin ya mata yawa,tayi kallo har ta gaji,tayi chart ya isheta,saita yanke shawarar ta sameshi tayi masa magana kan komawarta office don tana da buqatar hakan.
Sai data idar da sallar magariba yau sannan ta shiga tayi wanka,ta shirya cikin wani cotton material baqi da aka yiwa adon purple wanda yadan ciza,ta gyara gyara gashinta sannan ta feshe jikinta da turaruka yadda ta saba,duk da ko batasaka turaren ba qamshi kayan suke bayarwa na turaren wutar da take turare kayan nata dashi,nan bakin window din dakinta dake fuskantar harabar gidan ta tsaya,ta yaye labulen tana kallon harabar gidan kawai,duk da babu kowa sai mai gadi dake zaune can bakin qofar gidan,amma ko ina gauraye yake da haske tarwai kaman rana,haka gidan yake da wuta 24hrs.
Ta jima tsaye tana saqo tana warwara,har ta soma gajiya da tsaiwar ta saki labulen da niyyar komawa ta zauna taji horn,saita tsaya tana ci gaba da kallon qofa sanda baaba ya tura gate din anwar ya sako motarsa cikin gidan,tabi motar da kallo har zuwa harabar da yake ajesu,tana kallo baban ya qarasa bakin motar bayan ya maida qofar ya rufe,ya tsaya daga bakin window din da alama magana suke sannan ya juya ya tafi.
Tayi zaton bazai fito daga motar ba jin shuru na wasu mintuna,kana daga bisani taga ya bude murfin motar ya fito,sanye da mens blazzer ruwan blueblack da baqin takalmi sau ciki,yanayin takunsa kawai zai gaya maka a gajiye yake,idanunta akanshi har ya bacewa ganinta sannan ta saki labulen tana sauke ajiyar zuciya,hannunta saman kanta tana son tuna wani abu tana tursasa zuciyarta kan kada ta tuna mata.
A qalla sai data bada minti talatin kyawawa sannan ta yafa mayafinta ta fito,sam bata ko sha'awar hawa samansa amma dole ce xata kaita,taso ace yana zama a falo ta cimmasa a can.
Yauma da zata gota table din sai data kalla,komai yana nan akai kamar yadda ta dora,saita tabe baki tayi gaba cikin zuciyarta tana cewa
"Kai ka jiyo,nidai na sauke haqqina ko".
Yana zaune saman kujera one sitter,sanye da boxer da short sleeve shirt farare qal,fitowarsa kenan daga wanka,yayi relaxing bayansa a makarin kujerar,idanunsa na lumshe ya hada yatsun hannanunshi cikin na juna,haka kawai yakejin gidan ya masa shuru tamkar shi kadaine a cikin gidan,yunwa da gajiya suna damunsa,yana buqatar abubuwa da yawa amma ya rasa wanne zai fara tunawa cikin zuciyarsa,cikin haka yaji kaman an buda qofar falonsa,da mamaki ya ware idanunshi da suka dan kada saboda yadda ya jima da rufesu yana kallon qofar,qwarai yayi mamakin ganinta,amma ya shanye mamakin yana ci gaba da dubanta sanda take takowa ciki,bazaiyi qarya ba ta masa kyai cikin yadin jikinta,saiyaji wani bangare daya cunkushe a zuciyarsa yana budewa,tunanin da yakeson yi ya soma dawowa,kwanaki yau kusan goma sha uku kenan bai sanyata a idanunsa ba,ko motsinta bazai iya fadin yaushe rabon daya ji ba,tana sake matsowa qamshin jikinta na shiga ta qofofin hancinsa,qamshin daya sanyashi lumshe idanunsa ya sake budesu a kanta sanda ta samu hannun daya daga cikin kujerun dake can nesa dashi ta dosana ta zauna kan wuta,shuru ya ratsa dakin bayan sallamar data yi na wasu daqiqu sannan tace
"Inason magana dakai" idanunshi ya daga ya kalleta na wasu sakanni kafin ya janye duban nashi daga kanta ya maida idanun nasa ya rufe kaman yadda suke dazu,don shine mafita kawai a wajensa
"Uhmmm" yace da ita a taqaice
"Inason na koma aiki idan Allah ya kaimu ranar monday" da sauri ya bude idanun nasa ya zubesu fes a kanta,saitaji ya mata kwarjini saboda haka ta janye idanunta daga kanshi
"Labari kike bani ko umarni?" Ya tambayeta kai tsaye,yanayin tambayar daya mata yasa dole ta kuma kallonshi,tadan sake tsuke fuska
"Shaida maka nake"sai ya maida idanun nashi ya rufe sannan yace
"Tunda ba umarni bane ba zaki koma ba,kin gama aiki a triple r gem,bama nan ba kawai,kin gama kowanne aiki ako ina idan ba cikin gidan nan ba" haushi takaici da baqinciki suka cikata,me yake nufi kenan?,yana nufin ya rabata da aikinta,cikin hasala tace
"Me kakeso kace?,bayan duka qarfa qarfan daka yimin bai isheka ba har saika qara da wannan?,toni ban yarda ba in gaya maka gaskiya,ai bamuyi haka dakai ba" miqewa tayi tsaye ta soma tafiya
"Dama na gaya maka ne donkar kazo ka tarar bana nan kace ban shaida maka ba".