← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 73

Sashe 33

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Hannu nuradden ya saka cikin aljihun wandonshi ya ciro wani dan qaramin akwati,ya budeshi yana murmushi ya ciro qayataccen zobe a ciki ya miqawa shahida yana murmushin,kallonsa tayi sannan ta kalli zoben
"Da zaki miqo min hannunki na saka miki sai nafison haka,ki saka da hannunki shahida....amma shahida,don Allah zaki aureni?" Maganar ta shiga kunnenta a bazata,daga idanunta tayi ta kalleshi
"Me ya kawo wannan maganar nuradden?"
"Ban cancanci nayi wannan maganar bane shahida?,kina tunanin akwai wani namiji da zai kalleki yaji ba burinsa bane ya mallakeki?,ko tsahon zamanmu tare bai kamata ace na nemi mu zama miji da mata ba?" Bayyananniyar ajiyar zuciya ya saki,gaba daya ya rusa mata lissafi da plan dinta
"Hakane....amma kayi haquri zamuyi wannan maganar daga baya,kaga yanzu dare yayi naga kiran anty xubaida ma"
"Shikenan" ya fada yana maida zoben akwakunsa sannan ya miqa mata,ta saka hannu ta amsa ya zagaya seat dinsa ya shiga ya tayar da motar.

Kashi anwar ya jingina da kujerar da yake kai idanunsa kan motar tasu har suka fice daga wajen,hakanan yaji ya kasa zama shima ya tada motar tasa ya figeta yabi bayansu da hanzari,ba jimawa ya cimmasu,haka ya dinga bin bayan motar har zuwa cikin unguwarsu qofar gidan,gotasu yayi yayi parking din motarsa daga gaban tasu ya kasheta yana kallon abinda ke faruwa,motar ta bude ta fice ta tura gate din gidan ta shige sannan nura ya tashi motarsa ya fice daga layin.

Ya kusa a qalla minti goma a tsaye a wajen
"Wanne abu kake ne haka anwar,kana cikin hayyacinka kuwa?" Yaji maganar daga sama,wani sashe na zuciyarsa na tuhumarsa
"Ya Allah" ya fada shima cikin jin haushin kansa,gami da tuhumar kansa na me ya kaishi aikata haka,saiya kunna motar yana duban agogon dake gaban motar,qarfe tara harda minti goma sha shida,yana jin da qyar idan zai iya zuwa gidana anty usaina yanzu duk da tana can tana jiranshi,kawai saiya wuce gidanshi,zuciyarsa na masa wani irin zafi haka kawai.

Baiyi nisa a tafiyar ba wayarshi ta dauki qara,ya kalli wayar da ido kawai,sa'ida ce ke kiranshi,saiya danna sannan ya maidata handsfree yace
"Ya akayi sa'in(shi yakan kirata dashi wani lokaci)"
"Uncle,zaka zo ne?"
"Me ya faru?"
"Uncle wani abu na gani,wata na gani tazo wajen ummi uncle kasan dawa take kama?" Kai ya kada
"A'ah,dawa take miki kama?"
"Uncle kaman anty shahida nidai haka na gani,amma wannan ta dan fita girma ta kuma dan fita kyau" gabanshi ne yafadi baisan sanda yace
"Yaushe?" Ba
"Dazu dazu suka shigo gida tare da ummi" dan shuru yayi na dan wani lokaci sannan ya sauke boyayyar ajiyar zuciya
"Shikenan...yau bazan samu shigowa ba,amma ki bari gobe idan nazo sai muyi maganar"
"Toh uncle,ka siyomin turaren?"
"Zan kawo miki karki damu,ki gaida ummin naki kice mata wani dan uzuri ya riqeni"
"Toh uncle" daga haka dukkansu suka kashe kiran,tunani ya shiga sosai,sai salon tuqin nasa ya koma slow kaman bazashi gida ba,tunaninta ne ya dawo masa sosai tun farko alaqarsu irin wanda bai taba tsintar kansa a ciki ba.

Sai daya kashe wasu mintoci kafin ya isa gida,a gajiye ya isa falonshi ya fada saman kujera yana lumshe idanunshi kafin ya budesu,yanason manta komai amma abubuwan nata zarya bisa qwaqwalwarsa,sai kawai ya miqe zuwa bedroom dinshi,ya cire kayanshi ya daura towel ya shige toilet ya sakarwa kansa ruwan sanyi sosai.

Ya jima zaune gefan gadonshi yana neman bacci ya sureshi amma abun yaci tura,saiya miqe zuwa wani safe na musamman dake dakin,ya saka lambobin sirri ya budeshi,envalope din daya tsani gani yau da kanshi ya daukota,ya bude abubuwan dake ciki gaba daya,hotunan ciki suka bayyana,take kanshi ya soma daukan zafi,idanunsa suka kada jazur dasu,saiya kasa ci gaba da kalla ya soma tattaresu yana tuhumar shahida cikin ranshi
"Me yasa shahida me yasa?,me yasa za k

iyi haka,me yasa kika tarwatsani,me yasa kika tarwatsa duk wani buri da fata na?" Ya qarashe maganar yana cilla envalope din cikin abun ya maida ya rufe,saiya fada saman gadonshi yana maida numfashi gami da ambatar
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil"

*WASHEGARI*

Qarfe goma da minti arba'in ya isa gidan cikin dinkin shadda wadda tayi masifar masa kyau da fito da kyawunshi.

Dukkansu suna falo suna karyawa
"Uncle sannu da zuwa,ina kwana" suka dinga fada daya bayan daya,fuska a sake yake amsa musu yana tambayar lafiyar kowa suna amsa mishi
"Ina ummin taku?"
"Tana sama tana wanka" sa'ida ta bashi amsa bakinta fal da zance,turarenta ya ciro ya miqa mata tasa hannu biyu ta amsa cikin Murna
"Uncle na gode,na gode"
"Yauwa" ya amsa yana duban tashar da suke kallo,hijra tv waqoqi suke sanyowa na mawaqa daban,sa'ida ce ta tashi daga cin abincin da take ta dawo kan kujerar da anwar yake kai
"Uncle" ta fada qasa qasa,waiwayo yayi yana kallonta
"Uhmmm"
"Maganarmu ta jiya...." Shuru tayi ta ganin saukowar anty usaina,suna hada ido tahau rarraba idanu,miqewa tayi tsaye kafin ta iso,ta jefa mata harara
"Ku kwashe farantan nan kukai kitchen,munaya ki hadasu ki wanke,ke kuma uwar zance ki bita ki daura abincin rana,kafin ki gama laqaqin naki kin gama" duka suka miqe falon ya zama daga ita saishi,ta zauna tana dubanshi
"Jiya sai kuma na jika shuru,sa'ida tace ba zaka samu shigowa ba" yana shafa kanshi yace
"Wallahi,jiyan na taho wani uzuri ya tsaidani"
"To Allah ya rufa asiri" a mutunce ya gaisheta ta amsa masa cikin kulawa sannan daga bisani tace
"Ko a hado maka abincin kari?"
"Eh to...amma bada wani yawa ba" dauke idanunta tayi daga kanshi ta mayar qofar kitchen din ta kira sa'ida tace ta hado mishi.

Yana karyawan suna taba hiran,a hankali shurunsa yafi maganarsa yawa,hankalinsa ya karkata kan hijra tv da suka sako waqar jarumar mata,saita dinga taba ranshi kadan kadan,tana tuna mishi wani lokaci can baya,a nutse ya dauki remote din dake aje kusa dashi ya sauya tasha,dai dai sanda anty usaina tace
"Anwar....ya kamata fa ace ka soma shiri,biki saura sati hudu amma banga alamun hakan tattare dakai ba"sai daya hadiye abincin bakinsa sannan yace
"to me zanyi anty bayan wanda nayi"
"Kamar ya me zakayi?,haka zaka aurar musu diya babu maganar lefe babu komai?" Aje cokalin hannunsa yayu sannan yace
"Nifa anty,da zaki yadda da maganata ayi haquri a qara min wasu watanni"
"Saboda baka da gidan sakata ko baka da kudin yi mata lefan?,ko sadaki ne baka dashi?" Murmushi ne ya subuce masa ba tare daya shirya ba
"Au dariya ma nake baka ko anwar?"kai ya girgixa dariyar na kubce masa
"ni na isa antyna,kawai dai....naga kina yin nafisa ne da yawa" zamanta ta gyara sosai,alamun maganar da zata masa nada muhimmanci
"Ba haka bane anwar,ka fahimceni,mutanen nan suna da kawaici da dauke kai,basu da son zuciya ko tilasta mutum,da wasu ne su yadda suke ganin sun isa dakai dinnan kawai zasu baka umarnin ka auri diyarsu ne,su saka kuma ranar biki da komai baka data cewa,uwa uba ina gudun halayyarku ta maza kafa kazo ka murje ido kace ka fasa ka barmu da kunya" murmushi yayi yana kallon qasa,shikam dama bayajin zai dauki irin wadan nan abubuwan,dalili kenan da tun farko ya zabi yaci gashin kansa,bai qasan wani bare ya tilastashi koya tauyeshi,rama halacci dai wannan yasan abune mai kyau,kuma shine hujja daya,dalili daya da zai sakashi ya haqura ya auri nafisa
"Anty kiyimin kyakkyawan zato,ba abinda zai faru da yardar Allah indai daga bangarena ne,abinda kawai yasa na buqaci qarin shine,akwai wata 'yar tafiya da zanyi ta wata uku,kinga zaifi kyau naje na dawo,hankalina ya hadu waje guda,duk abinda za'ayin ma sai ayin,zan baki kudin da zai isa a hada lefan kafin wucewata da sauran abubuwan da aka sabayi na al'ada" ajiyar zuciya ta saki
"Shikenan,yanzu ya za'ayi ka shaida musu?"
"Wannan duk ba damuwa bace,zan samu alhj da kaina,baida matsala,yasan da tafiyar tawa dama"
"Shikenan,Allah yayi mana jagora ya bada sa'a"
"Amin anty" daga haka suka shiga hirar data shafesu,sai wajejen shabiyu na rana ya baro gidan shima ganin haduwar hadarine,baya

n ya tambayesu ya tabbatar basu da wata damuwa.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
Chapter 33 · 0% Book details