← Book details Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 73

Sashe 31

Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shagon akwai mutane saidai ba sosai ba,a falon ta tadda mai saloon din tsaye da wasu mata suna siyan ribboms,cikin fara'a da muntuntawa ta tarbi shahidan,saboda tasan duk sanda tazo din ba qaramin qaruwa takeyi da ita ba,suka gaisa sannan tace mata
"Kitso nakeso madam,amma manya nakeso yau ayimin ibra nakeso" cikin juyayyar hausarta tace
"Ohk madam babu damuwa..saidai akwai wasu da za'a wankewa kai,amma bari na soma sallamarka su sai su jira"
"A'ah madam,aisun rigani zuwa sallamesu tukunna"
"Ohk maa" ta fada tana juyawa ta duba wani waje da take aje magazines ta zubewa shahidan sannan ta sallami wadanda suke sayen ribbom ta koma ciki inda take wankin kan.

Daya daga cikin kujerun dake wajen shahida ta zauna,ta aje jakarta gefe daya sannan ta cire glass dinta da take amfani dashi lokaci zuwa lokaci saboda ado ta dorashi saman jakartata ta bude magazine din ta soma dubawa.

Hayaniya da hirar dake tasowa daga ciki ta cika mata kunne har tasa ta daina fahimtar abinda take dubawar,sai kawai ta rufe magazine din ta riqeta a hannu,hirar yammatan dake ciki na shiga cikin kunnenta
"Ya hadu iya haduwa,daa wlh ni bai dameni ba saboda a sannan baida wani abun burgewa,amma yanzu har wani kishi kishinta nakejin yana kamani wallahi,anya nan gaba kuwa ba za'ayi juyin mulki ba kuwa?" Dariya suka kece dashi
"Mima baki da kyau,daga daukanki sojan haya saiki fadi haka?"
"Ke qyale shegiya,shekara nawa ina mata bauta?,don tana biya na aiba halitta ta tayi ba" hirar sam bata wa shahida ma'ana ba,saboda haka ta zaro wayarta kawai tayi kiran ummanta,bayan sun gaisa tace
"Umma don Allah ki saka mubina ta soyamin wainar fulawa ina nan zuwa,na tsaya yin kitso ne,ta saka min albasa da yawa,ta manja nakeso"
"Toh shikenan,amma saita saukemin tuwona"
"Eh kafin sannan ma na qaraso"
"Allah ya kawoki lafiya"
"Ameen umma" bayan ta kashe kiran noradden ya shigo,ba yabo ba fallasa ta daga
"Yallabiya kin hanani sukuni sai naji muryarki" murmushi ne ya subuce mata ba tare data sani ba,ita mamaki ke kamata idan nura na nuna yadda yake tsananin qaunarta
"Dariya ma na baki?,don bakiga yadda na gaji tubus ba saboda tunaninki,shahida har yau kina daukan son da nake miki da sauqi"
"Ba haka bane,kawai dai haka kai ka fahimta"
"Koma yaya ne dai yanzu kin wuni lafiya?"
"Lafiya qalau,kaifa?" Sosai yaji dadin yadda ta tambayeshin,daga haka ya shiga janta da hira,ta biye mishi kodan ta ragewa kanta lokacin zaman jiran da takeyi.

Minti ashirin 'yammatan da akewa wankin kan daya ta soma daga labulen ta fito,tana sanye da riga dinkin straight gown wadda tafitar da duk wata sura tata,shahidan na shirin dauke kai dayar ta biyo bayanta,itama sak irin dinkin dayar ne a jikinta,har shahida ta dauke kai yadda taga ta zuba mata ido ya sanya itama ta maida idanunta kanta,da sauri taga ta juya ta koma ciki tana cewa
"Au...madam na manta qawata tace muyi jiranta a nan"
"Ohkey to babu damuwa" ta bata amsa sanda shahida tayi sallama da nooradden ta maida wayar jakarta sannan ta cire rolling din kanta,ta zare ribbom dinta ta soma taje kanta.

A gaggauce nafisa tayi parking na motarta a qofar shagon,cikin hanzari da sassarfa ta nufi qofar shiga wajen kai tsaye.

A sannan anyi rabin kitson da akewa shahida,labulen kawo sukaga an bankado hakan ya sanya shahida daga kanta ita da madam tawakkaltu dake mata kitson gaba daya,idanunta ne ya sauka cikin na shahida tana mata kallon fes,itama shahidan kallonta take,tasan fuskar,fuskace da ba zata taba manceta ba,fuska ce da anwar ya turo mata da hotunansu a tare yana bayyana mata ita a matsayin masoyiya a gareshi,ta yaya zata manta wannan fuskar,amma saita dauke idonta ta maida kanta qasa tana ci gaba da danne danne a wayarta,saidai wani abu yazo ya tsaya mata cak a qahon zuciyarta.

Madam tawakkaltu ce ta amsa mata tana ci gaba da yiwa shahida kitson,saidai idanunta na akanta tana neman jin abinda ya kawota wajen,don bata santa ba
"Amm,akwai friend dita mima da tazo wankin kai nan ko?" Nafisa tayi qarfin halin furtawa,ranta da zuciyarta gaba daya a jagule
"Eh sunaa ciki aeke sukee jira" ta amsa mata cikin gurbatacciyar hausa,kafin takai ga isa wajen mima ta fito da qawarta lima
"Gani...mu wuce ko?" Ta fada tana karantar fuskar nafisan,kaita jinjina yanayin fuskarta na sake sauyawa yana nuna rudani a ciki qarara,har sukaje bakin qofar da zasu fita tana duban shahida wadda bata ma san tanayi ba,saidai jikinta ya bata hakan
"Madam ko kinsansu ne?" Tawakkaltu ta tambayeta ganin yadda suke kallonta
"Ba wadda na sani a cikinsu" ta amsa mata a taqaice
"Allaho ya kyauta" ta fada tana mamakin irin kallon da sukewa shahidan su duka.

Duka sai komai ya tsayawa shahidan cak,ba bacin rai takeji ba amma ranta da jikinta sam babu dadi,wayar ta maida cikin jaka ta ciro carbinta ta maqala a yatsanta ta soma jan HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL,wansa babu jimawa taji komai na koma mata dai dai.

Dukan sitiyarin motar tayi da qarfin gaske har lima na zaro ido kada fa kan motar ya lalace
"Ba haka nakeso na ganta ba mima,ya akayi na ganta a cikin kyakkyawan yanayi?,so nake ta dilmiya ta lalace,so nake tayi nisa cikin shan kayan maye karta waiwayo komai nisan kiran da za'a mata,kudin dana biyaki bai kamata wasan ya tsaya iya nan ba,ya akayi haka?" Ran mima yadan sosu kadan sabida yadda nafisan koda yaushe taqamarta nakan kudin data bata,amma abinka da bariki saita danne
"Abinda ya bani mamaki ya girgizani kenan yasa har nayi kiranki" shuru ne ya ratsa motar abun na kaiwa nafisa ko ina,maganar mima ta katse mata zaren tunaninta
Ba wannan nakeson jiba,meye mafita?" Ajiyar zuciya mima ta sauke
"Toh....a yanzu dai babu batun saka wani kota bar wani ya shiga jikinta,na tabbatar ba zata sake barin haka ta faru ba a gareta...amma dai duk da haka,ba'a rasa nono a riga,ki fidda kudi,zansan aikin daya dace muyi a kanta,amma....kece zakiyi rabin aikin,ke kike tare da anwar kuma zakici gaba da kasancewa tare dashi,dole ki sake cusa masa tsana da qinta cikin zuciyarsa,kisan yadda zaki ki mamaye tunaninsa ki shiga lungu da saqo"
"Kudi ba damuwa bace,successful aiki shine damuwata"
"Karki samu damuwa,kinsan wace ni,nayi kin gani ai" locker motarta ta bude ta ciro kudi ta irga ta miqa mata,tasa hannu ta cafesu tana sakin murmushi
"Koma sit dina ki jamu,don bazan iya driving ba a yanzu"
"Ohkey" miman ta fadi,sukayi musanyan seat ta kunna motar ta figeta,wata ta sanya musu nafisa taja tsaki
"Ina cikin irin wannan mode din zaki kunnan waqa,kashe malama ki barni nayi tunani da kyau"
"Daqiqiya wanne tunani gareki?,bayan duk wani tunaninki nice nake miki" ta fada a zuciyarta tana cire waqar,yayin da a fili tace
"Am sorry,komai fa zai dai daita".

Qarfe shida ta shiga soron gidansu bakinta dauke da sallama,tsakar gidan nasu babu kowa sai mubina dake zaune saga qofar kitchen tana suyar wainar fulawarta,fes gidan yake kamar kullum,cikin gajiya
ta qarasa inda mubina ke zaune
"Sannu da zuwa yayaa"
"Yauwa mubi...ashe kin soma?" Tayi maganar sanda take duqawa ta bude flask din dake gaban mubina ta gutsiro wainar takai bakinta
"Da tunima na gama ai,maqociyarmu ce ta shigo umma tace a zuba mata shine nake tara miki wata yanzu"
"Ummmm....amma fa tayi dadi sosai" ta nemi waje kusa da mubinan tana zama ta janyo yaji ta soma gutsira tana dangwala,mubina na bata labarin bikin wata cousin dinsu dake matsowa,shirin da akeyi anko da dai sauransu
"Kowa shiri yake yaya sosai,kinsan wanda zata aura din yana da kudi ba laifi" murmushi kawai shahida ta fitar,wato duk wadda akace yau zata auri me danshi murna ake mata
"Allah yasa abokin zama ne,ya sanya alkhairi"
"Ameen yaya,naga umma ma tasa an kawo mana ankon,amma bandake" harararta tayi
"Ce miki akayi ni cima zaune ce da za'a min anko?" Dariya mubina ta qyaqyace da ita
"Waya isa yace miki cima zaune,hajiya accountat da kanta"sai data ci ta qoshi sosai sannan ta isa bakin famfo ta wanke hannunta ta daura alwala ta wuce falon umma.

Da sallama ta shiga,su biyu ne zaune suna hira,ita da wata baquwar fuska da batasan wace ba,saidai kallo daya ta yiwa matar taji gabanta yayi mummunar faduwa,itama matar idanunta kan shahida,murmushi kan fuskarta tana amsa sallamar tata,dauke idanunta tayi ta samu gefen kujera ta zauna
"Sai yanzu kika shigo?"
"Haba tun daxu umma,na tsaya naci waina ne"
"Ashe takice amma umma ta bamu muka cinyeta" cewar matar cikin fara'a,sai shahida ta juya ta dubeta itama fuskarta ba yabo ba fallasa tace
"Ina yini?"
"Lafiya qalau,mun yini lpy shahida ko?" Ta amsa gaisuwar gami da jeho mata tambaya daga qarshe,kai ta gyada tana mamakin yadda akayi matar ta san sunanta,bayan umma bata furta sunan a gabanta ba
"Tunda nake zuwa ban taba ganinki ba sai yau,Allah dai yayi yau zanga yaya shahida" ta kuma fada tana murmushi,itama murmushin shahidan ta maidata mata,ganin kaman bata saki jiki ba ya sanya umma cewa
"Maqociyarmu ce nan gaba kadan gidanta yake,tayi wajen wata shida da tarewa sai yanzu Allah yayi ta leqo mana,gidan nan da faruq yake gaya miki ana sadaka duk juma'a?" Sai a sannan ta fahimci gidan da take nufi,kai ta gyada tana sake fadada fara'arta,don mubina tasha bata labarin kirkin matar,daki ta wuce daga haka tana jiyo hirarsu da umma.

Har ta gama zamanta ta soma shirin tafiya matar tana nan,a nan taci abincin dare tare dasu umman,mamaki take sosai shahida,a ina suka santa ne?,wace ita?.
Chapter 31 · 0% Book details