Sashe 54
Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Anty zubaida ita ke riqe da ita har mazauninta inda aka tanada saboda ita,bata barta ba sai data duqa ta mata gargadin karta sake ta bata musu taro ta hanyar yin wani abu na daban,hakanan cikin mayafinta da aka lullubeta har saman kanta ta dinga hadiyar wani abu mai tauri a maqogaronta,ta dinga kokawar maida kukanta,duk wanda yazo a haka zai mata liqi ya wuce taqi ta daga kaima bare ta tantance su waye a wajen,a haka har lokacin soma kamu yayi,tana jin sanda dangin mahaifiyarta dana mahaifinta suka iso inda take zaune,aka buqaci dangin ango su matso
"Ga turaren da za'a yiwa amarya kamu dashi inji angonta" taji wata murya wadda kamar ta santa tana fada,aka saki dariya gaba daya,wata mai azabar murya ta rangada guda wadda shahida taji kaman ana sakatar qwaqwalwarta,ta runtse idonta hawayen da take boyewa suka gaza riquwa,sai suka silalo suka zubo har saman tafin hannunta dake aje saman cinyarta,feshin farko na turaren da aka mata gabanta yayi mumunan faduwa,tabbas wannan qamshin anwar ne,turarensa ne,sake rintse idanunta tayi tanajin radadi a zuciyarta,waishin me yasa kowa ya kasa fahimtarta ne?,basa ganewa ne?,me yasa kullum kwanan duniya suke jawo abinda zai sake kusantata dashi ne?,a haka har aka qare fesheta akayi addu'a sannan akaci gaba da saka kidan qwarya,dangin ago suka buqaci yi mata liqi,haka anty zubaida tazo ta dagata zuwa amma ba tare data bude mata fuskarta ba suka shiga mata liqi,kowa sai daya tsaya ya kallesu ya qara.
Qarfe sha daya da rabi na daren ranar bayan taron kamu ya watse tana tsaye gaban window din dakinta dake bude iska na shigowa sosai mai sanyi na alamun dare ya soma nisa,iskar dake shigowa cakude take da turaren da aka yi mata barinsa daxu a jikinta wanda duk da wankan da tayi kusan aikin banza ne qamshin bai rabu da jikinta ba,kusan a yanzu ba wannan ne ya dameta ba,saqon anty zubaida data gaya mata kafin shigowarta dakin shine babban abinda ya hanata sukuni a yanzu,dinner da za'ayi gobe tsakanin ango da amarya da abokansu,ta yaya zata zauna bigire daya da anwar din a matsayin amarya da ango?,yadda anty zubaida ta tsume take ja mata kunne kan goben ta tabbatar kome tayi a laifi yake,ranta a bace yake sosai,ga mari ga tsinka jaka?,itakam me anwar zaice da ita?,ya jima da rusa dukka wani farinciki nata yanzu gashi ya sake dawowa yasa hannu ya takwabe wanda yayi saura,bata da wata mafita gashi ta gaji da tsaiwar,saboda haka ta saki labulen ta dawo cikin dakin wanda su uku ne duka duka a ciki don tace ba zata kwana da kowa ba,tsallakesu tayi wanda tuni sun fara barci ta shiga bandaki ta daura alwala sannan ta dawo ta kwanta tana fatan bacci ya dauketa.
🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
Duk yadda taso ta taushi kanta ta kuma qwararawa kanta gwiwa donta fita ga motoci hudu na anwar dake jiranta a qofar gidan hakan yaci tura,a dakin baqi na uncle hisham dake dab da qofar fita ta shiga ta zauna.
Ran hasina ya baci it hankalinta ya tashi na kada ta bada su,ga zunnurah tayi gaba tuni a motar mai gidanta da yace bai yarda tahau motar kowa ba bare ta mata magana ko shahidan zataji maganarta,irin kudaden da aka kashe mata kawai a ranar donta fito ba kadan bane,ta kuwa fita din tayi kyau,irin amaryar da duk wanda ya kalleta sau daya saiya maida kanshi ya mata duba na biyu,gashi dukka wanda ya dace hasinan ta yiwa magana kan yasa shahidan ta fito sunyi gaba,kusan su suka rage kawai,bata da wata dabara dole daga qarshe ta fita ta shaidawa muhsin da suke zaman jiran fitowarsu.
Kai ya jinjina kawai sannan ya juya ya nufi daya daga cikin motocin datafi kowacce kyau da girma,bude gidan baya yayi ya shiga inda anan anwar ke hakimce,cikin dan bacin rai yace
"Wai zaman me muke muhsin,haka kawai ka kawoni cikin mota ka aje bayan kasan inada abunyi da yawa"
"Kaga saurara....wayarka zaka dauka ka kira mana amarya ka lallabata ta taimaka ta fito" cikin rashin gane me yake nufi yace
"Kaman yaya?" Girarsa muhsin ya dage
"Eh to....qila sarautar tasu ce ta motsa,tana ciki taqi fitowa" dan jim yayi na wani lokaci sannan ya saki wani tsaki da qarfi
"Koma meye kaika jawa mutane wallahi" ya qarasa fada yana kokawar cire babbar rigar shaddar dake jikinsa wadda taci aiki tayi bala'in yi masa kyau,ko ba'a fada maka ba kana kallonshi kaga ango
"A'ah,meye na cire babbar riga kamar me shirin dambe?" Sai daya bude murfin motar ya saka qafarsa daya a waje sannan yace
"Damben zanyi" ya qarasa fita yana rufe murfin motar,yanajin muhsin din na cewa nifa kiranta nace kayi a waya ka fiddota fa ba wani abu ba,ko kallonshi baiyi ba ya wuce abinsa,dukka 'yammatan dake tsatstsaye suna jiran fitowat amarya donsu wuce dakin taron sai dayaja hankalinsu,kowacce idanunta bisa kanshi,b wadda bai burge ba cikinsu,a hankali yaci gaba da takunsa harya shiga gidan ya nufi dakin baqin kai tsaye ya tura qofar.
_ku ziyarci tashar SAUTIN HIKIMA dake youtube,don sauraron litattafanmu tsaffi da sababbi,dama wadanda zasu muku nan gaba wadanda babu su a duniyar watsapp,karku manta kuyi subscribe don sanin cewa mun dora sabon shirinmu_ *Alqawarin Allah*
3️⃣5️⃣
Tana kwance saman doguwar kujera ta juyawa qofar shigowa baya,hakan ya sanya sanda taji an bude qofar ta waiwayo ta saddaqar da cewa anty zubaida ce,saidai wanda ta gani din yana shigowa ya sanyata bude manyan idanunta da suka sake qawatuwa da kwallin da me makeup ta sanya musu tana dubanshi,fuskarta a yamutse alamun tambaya tacj gaba da kallonshi sanda shi kuma yake takowa cikin dakin,yayin da wani sashe na zuciyarta ya karkata wajen kallon adonshi cikin shaddar jikinsa mai azabar kyau da daukar ido,ta zauna masa das kai kace saboda shi kadai aka yita,shima ita yake kallo,duk yadda yaso kwabar kansa da hana kanshi yabata saida zuciyarsa ta zarme ta gano kyawun da tayi masa,tayi wani kyau na musamman,duk da ramar da tayi amma hakan bai hana kyawunta fitowa ba.
Nesa da ita kadan ya tsaya ya harde hannayensa yanaci gaba da kallonta,yace da ita sanda ta waiwaya tana niyyar sake juya baya ta koma kwanciyarta abinta
"Mudin kin tsammaci abokan wasanki ne?,ko ce miki akayi bamu da abunyi?,sauko maza ki wuce mu tafi tun ban aikata abinda nayi niyya ba" idan ta tanka to sauran kujerun dakin sun tanka,saima sake gyara kwanciyarta data yi kamar bada ita yake ba,hakan ya bashi haushi,shi zatama kunnen uwar shegu tana jinsa?,saboda haka bai sake ce mata komai ba ya taka har inda take kwancen a hankali ba tare data sani ba,ya isa bayanta ya ranqwafa gaba daya ya sanya hannunsa ya soma ciccibarta,cikin matuqar mamaki tayi yunqurin tashi gami da zillewa cikin zafin nama,ta zauna sosai fuskarta cike da bacin rai take dubanshi
"Me hakane?,karka kuma kuskuren tabani malam kaji na gaya maka"girar sama data qasa a hade ya maida mata amsa idanunshi cikin nata
"wannan sharadinki ne ba nawa ba,baki isa kuma ki kafamin shi ba,a banza ma wani ya taba bare ni?mema kike gudu ne?,meye abun killacewar?"ya qarashe furucin wannan karon yana tuna sanda nuradden ya kama hannunta a office yana niyyar sanya mata zobe,idanunta ta daga ta kalleshi cikin mamaki,kamar yaya wani ya tabata?,shi wai abu nawa ya gani?,abu nawa ya sani dangane da ita wanda ita bata da masaniya akan ya sani din?,ba abinda ya fado mata a rai sai sanda ta fada jikin mutumin da fiddausi ta kaita siyan kayan maye,anya bai wajen koya ganta ne yake mata gugar xana?,wani bacin rai ya sauko mata a take fiye da wanda take ciki,tsaki taja qasan ranta zuciyarta na mata suya,ta kwashe qafafunta da garin sauri ta saukesu qasa bata ma sani ba,yabi qafafun nata da suka sha lalle da kallo harta tanqwashe su tana niyyar sake kwanciya
"karki kuskura...wannan karon idan na iso inda kike banga abinda xai dakatar dani daga fitar dake ba da hannuna"baki ta tabe karon farko ta jefa masa harara,ji take kaman ta tashi tayita dukansa ko xataji sassaucin haushi da zafinsa da take ji,kansa ya nuna da yatsa
"Ni kike harara?"
"Saime don na harareka,kai waye?" Tayi furucin tana son ta tunzurashi ko hakan zaiyi sanadin da zaiyi zuciya ya fita ya qyaleta,don itakam ko daya bata da muradin zuwa ko ina,hannun nasa dake harde a qirji ya sauke yana sake takowa inda take idonsa akanta,kafin ya qaraso tayi zumbur ta miqe tsaye gami da kaucewa gefa
"Na gaya maka babu inda zani,ko ana dole ne?idan ka aureni dole baka isa kamin dolen zuwa wajen taro ba"
"Haka kika ce?"
"Eh" ta bashi amsa kai tsaye,wannan karon qwaqwalwarta bata gama bata shawarar abinda zatayi ba caraf taji ya sureta gaba daya ya fice da ita,sosai ta tsorata,kunyar jama'an da zasu tarar haushi da takaicinsa suka cikata
"Ka cikani malam,ka saukeni,wannan wanne irin wulaqanci ne haka?,baka ganin mutane?,a haka zaka fita dani har waje?" Bai saurareta ba harsai da sukaje daf da gate din sannan ya direta,hakanan ya babbake qofar ya tsareta da ido yana son yaga iya gudun ruwanta,daidai sanda wayar hannunta ta soma ruri,tana hadiye bacin ranta ta duba sunan mai kiran,anty zubaida ce ta daga ta kara a kunnenta
"Wai me kuka tsayane kuna ina har yanzu baqi sun gaji da jiranku?" Bata da wata dabara saita yanke wayar ta gyara tsaiwarta,takalman qafarta takeon gyarawa amma batason duqawa,ya tsareta da ido dole ta sunkuya a hankali da niyyar sake daure igiyoyin jiki,daidai nan shima ya duqa goshinsu ya gwaru,ta miqe tsaye da sauri dage da goshin nata tana jin zafin gwaren da sukayi,bai dago ya duqa,ya sanya hannunsa a nutse ya tattara igiyoyin ya soma daure mata su idanunsa kan farar qafarta data sha jan lalle har saman qafar,qoqarin qwace qafar ta shiga yi amma a banza sai daya gama sannan ya miqe,yaja da baya fuska a matuqar tsuke,sai data kalleshi sannan ta soma takawa ta fice daga gidan ya mara mata baya.