Sashe 1
Alkawarin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
🪐 *ALK'AWARIN ALLAH* 🪐
_HUGUMA_
0️⃣1️⃣
"Allah ya taimakeki" lafazin da ya shiga kunnenta kenan,lafazin da a bakin mutum daya take jinsa,furucin da ko mutuwa tayi ta dawo bata jin zata kasa tantance daga bakin wanda yake fitowa dare da rana,a hankali ta waiwaya fuskarta qunshe da murmushi,yana tsaye daga bayanta kamar koda yaushe,wannan annurin data saba gani kan fuskarshi kowanne lokaci na nan shimfide saman fuskarsa,kwarjini cikar zati da haiba cakude saman kyakkyawar fuskarsa,batasan me ya shigeta ba,sai taji bacin rai ya sauko mata a take,b'acin ran daya sanyata ta dinga ja da baya,ja da bayan daya zama silar data soma ganinshi dishi dishi,yana tsaye hannayenshi goye a k'irjinsa,dubanta yake ba tare daya tsaidata ko yace mata komai ba,saidai annurin fuskarshi ya ragu cikin kaso d'ari zuwa kaso ashirin cikin d'ari.
A firgice ta farka,sa'annan tayi zumbur ta miqe tayi zaman dirshan saman gadon nata,dukka hannayenta ta sanya ta dafe kanta dasu bayan ta dora gwiwar hannunta saman cinyoyinta,gashinta mai tsaho da sulbi ya sako ya rufe fuska da hannayen nata gaba daya,inda zaka ga fuskarta a sannan zazzafan hawaye ne ke layi saman kuncinta,inda ace tana da iko data hana kanta mafarkinsa,da ta isa data hanashi bayyana a duniyar mafarkinta,sam ko kusa ko alama bata da buqatarsa a duniyar mafarkinta kamar yadda bata da buqatarsa a zahiri
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" idan ka kasa kunnenka da kyau zakaji tana fada cikin muryar kuka.
Ta jima cikin wannan yanayin kafin ta iya lallashin zuciyarta,kanta ta dago sannan ta sanya hannayenta guda biyu ta tattare gashinta baya ta daureshi,kyakkyawa kuma sassanyar fuskarta datayi jajur ta kuma tasa saboda kukan data yi ta fito fes duk da qarancin haske da d'akin keda shi,a hankali ta zuro qafafunta qasa sannan ta yunqura ta miqe,kai tsaye ta nufi wata qofa dake kallon gadonta ta murda ta shige.
Mintuna biyar kyawawa tayi ta fito daure da alwala,ta bude ma'ajiyar kayanta ta fidda after dress da hijabi ta sanya,sannan ta nufi wani kebantaccen waje dake daura da gadonta tahau saman abun sallar dake shimfide a wajen ta kabbara sallah.
Ita kanta batasan adadin lokutan data kashe zaune saman abun sallar ba,don sam bata marmarin sake komawa barcin da tayi mafarkinsa a ciki,saidai shi bacci ba wanda yafi qarfinsa,saboda haka sanda yazo yayi awan gaba da ita bata shiryawa hakan ba,sai jingina da tayi da jikin gadon,carbin hannunta kuma ya silale ya fadi nan saman dardumar.
******* **** ********
Qarfe takwas na safiya ta kammala shirinta tsaf,tsaye tayi kawai tayi gaban mudubin tana qarewa kanta kallo,tayi kyau iya kyau,irin kyan nan mai sanyi,saidai wasu abubuwa da suka soma mata yawo akai take suka d'auke duk wata sauran walwala da taketa yunqurin d'orawa fuskarta,qarar kira daya shigo wayarta yaso janye hankalinta,saita zubawa wayar dake gefan mudubin ido tana kallonta ba tare data tabata ba gudun zuciyarta na qaruwa,bata kuma da niyyar hakan ma gaba daya,har ta qaraci b'urarinta ta katse,tamkar mai jira kiran ya katse din kuwa tayi gaggawar surar wayar ta kasheta gaba daya sannan ta jawo locker din madubin ta jefata ta maidata ta rufe.
Cikin kasala kamar wadda tayi wani babban aiki ta koma da baya ta zauna gefan gadonta tana ci gaba da kallon fuskarta cikin mudubi,ko kad'an bata qaunar ta raba wani abu ajikinta da zai sata tayi kyau,don dai kawai bata k'aunar bata ran anty zubaida ne,amma da bata ga dalili ko alfanun kasancewarta a haka ba.
"Auntyyyyy...." Muryar huda ce ta ratsa kunnenta,firgigit tayi tana dubanta kafin ta samu qaqaro murmushi wa fuskarta
"Anty ina kwana"
"Lafiya huda ta,kin shirya kenan?" Ta furta tana janyo yarinyar kusa da ita tana gyara mata daurin jelar rigar makarantar dake jikinta
"Ummi tace ki fito karmu makara"
"Muje na gama ai,fitowa kawai xanyi" ta fada tana miqewa,ta qarasa ma'ajiyar jakankunanta ta ciro daya daga ciki da zata dace da shigarta,sannan ta dauko wata daban ta zuge,ta fiddo da tarkacen ciki ta maida wadda zata fitan da ita sannan ta kama hannun huda suka fice.
A kitchen suka tadda anty zubaida tsaye tana shirya lunch box din huda,sanye take da rigar bacci da qaramin hijabi,kallo daya anty zubaidan tayi mata ta karanci yanayin data shiga,don haka bayan sun gama gaisawa ta shigar da qorafinta
"Yauma kinyi halin ne?" Murmushi kawai tayi wanda ya fito da ciwo tun daga zuciyarta zuwa labbanta,maimakon ta amsata saita shigo da wata maganar
"Yanzu anty dan Allah ta yaya zanci gaba da kwanciya kina tashi kina girki bayan kula da uncle aby da kike?"
"In kinason komawa kitchen sai kiyo qoqarin maida mode dinki yadda yake....." Cikin seriouse ness ta waiwayo tana dubanta
"Cikin shekaru biyu mun soma yin nasara shahida....saidai bansan meke neman tarwatsa nasarar da muka samu muka yi ta tsahon shekara biyun ba" ta fada cikin nuna damuwa,shuru shahida tayi tana k'okarin kokawa da damuwar data taso mata,tun lokacin data san cewa suna rayuwa ne ashe cikin gari d'aya da anwar bata sake samun peace of mind ba,murmushin yaqe kawai ta jefi anty zubaida dashi,don bata son dukkan abinda zai sake jagula nutsuwar da take ta yunqurin samarwa kanta,shuru ne ya ratsa tsakani,ganin bata da niyyar magana anty zubaidan ta saki hannayenta tana dauko lunch boxs din huda ta miqa mata gami da cewa
"Shikenan,ku wuce ku karya karku makara,amma dai.....kota halin qaqa karki bari abinda ya riga ya gabata a rayuwarki ya bata future dinki,koda anwar ko babu ki baiwa kanki qwarin gwiwar xaki rayu,rayuwa mai inganci...."
"Zan rayu babu shi ne anty rayuwa mai inganci,babu batunshi ma cikin babin rayuwata" ta fada wani radadi na tasowa tun daga cikin zuciyarta har saman fuskarta,murmushin da ita kadai tasan ma'anarsa anty zubaida ta sako,shahida mutum ce me confidence,tana da qwarin gwiwa saidai har zuwa yau kaman hakan yaqi tasiri ga wannan lamarin,duk da koda yaushe tana yunquri da fadi tashin baiwa kanta wannan qwarin gwiwar,da idanu ta bisu har suka fice daga kitchen din ita da huda sannan ta saki ajiyar zuciya tana yiwa deejan addu'a a fili da zuciyarta.
Suna gama karyawar abby ya fito,sanye yake da jallabiyya,mutum d'an kimanin shekara arba'in da takwas,mai cikar kamala da fara'a,cikin girmamawa shahida ta gaidashi,ya amsa fuskarsa qunshe da fara'a yana fadin
"Teacher uban karatu....baku wuce ba kenan?,hala yau keda dalibar taki tare zakusha bulalar latti" murmushi ta fidda,tana mamakin abbyn sau da dama,wuta ne shi a wasu lokutan,amma wani lokacin yafi xuma dad'i
"Yanzun nan zamu wuce abby" ta fadi tana sab'a jakarta
"Gwara kam,don qila hadi(mai adaidaitan dake kaisu makaranta)yana waje yana jiranku na sanshi da himma" dai dai sanda anty zubaida ta fito daga kitchen din sukayi mata sallama suka wuce.
A bakin k'aton gate din *NOOR INTERNATIONAL ACADEMY* ya saukesu
"Daganan zan kai adaidaitan wajen gyara....amma zanyi qoqari in sha Allahu na dawo na d'aukeku"
"Karka damu,yauma muna shirye shiryen wasu abubuwa da za'a gudanar a makarantar,ina zaton ma zamu d'ara lokacin tashi,zamu bi ta haya mu koma"
"To na gode,amma du da haka idan na gama akan lokaci zanzo" bata sake ce masa komai ba ta kama hannun huda suka ratsa gate din makarantar zuwa ciki.
Dukansu ita da hudan sashen 'yan nursery da primary suka nufa,saboda a nan ne deejan ta zabama kanta ta koyar,duk da tarin ilimi da Allah ya bata,wanda tana da cikakkiyar damar da zatayi lacturing amma bisa wani dalili nata ta zabi koyarwa a qaramin mataki na 'yan nursery da primary,tun daga bakin section din yara ke gaidata cikin nuna qauna da soyayya,yayin da ita kuma take amsa musu cikin fara'a da jansu a jiki,sai da zata shiga staffroom sannan suka rabu da yaran,suka wuce azuzuwansu ita kuma ta shiga ofishin malamai.
Office ne madaidaici mai girma da tsari,duk da girman office din su uku ne kacal a ciki,makaranta ce da kallon farko.idan kayi mata zakayi tsammanin private ce irin mai tsadar nan,saidai sam ba haka abun yake ba,makaranta ce da wani shahararren d'an kasuwa ya ginata saidai akwai sa'ido da kulawar gwamanti akanta,duk da cewa shike dauke da duk wani nauyi na makarantar,kama daga school unifoarm,littafan karatu,abincin da yaran zasuci na break da dai sauran dukkan wasu lalurori,aqidarshi ce haka,yakan gina makarantar a duk inda yaga hakan ya dace,ya kuma hada hannu da gwamnatin garin donta tayashi lura da makarantar,bawai lura na su bada wani abu ba,a'ah,tsarin gudanarwa tsaro da sauran abubuwan da ya kamata,kusan kowacce qasa dake africa ya gina makarantu d'aya,saidai a inda makarantun suka fi yawa a nigeria ne yankin arewa,duk dalibin dake karatu cikinta yana farinciki haka iyayensa farinciki da kasancewar dansu a cikinta,saboda ta tsaru da tsari mai kyau,hakanan tana da dukkan wani qualities da akeson makaranta dashi.
Hidaya kawai ta samu cikin office din tana hada littafan dalibai da tayi marking,da alama tana da ajine qarfe takwas,murmushi suka yiwa junansu
"Kinso makara yau malama shahida"
"Yau da gobe hidaya...." Ta fada tana zaman kan kujerar teburinta.
"Sai Allah..." Hidayan ta qarasa mata kana ta gyara yafen mayafinta
"Mun tashi lpy...."cewar hidaya
"alhmdlh....mun godewa Allah"
"Ma sha Allah....zan wuce aji don Allah idan kausar ta iso kice mata ga kayan nan ta duba"
"Babu damuwa" cewar shahida,tana kallon hidaya ta bude office din ta fice sannan ta maida qofar ta rufe musu,saita maida kanta a hankali ta kwantar saman teburin dake gabanta,idanunta a lumshe,batason tuna komai,batason tunanin komai,tanason ta saita kanta kafin lokacin shigarta aji yayi,don nan da minti goma sha biyar periode dinta zai shiga.
***********************