← Book details Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 49

Sashe 9

Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ajiyeshi ta dauki hoton da mutanen gidan baki
aya suke a ciki, matar da mijin ne, sai mai kama da ita sai kuma wannan
aramar yarinyar da kuma wanda ya zo da ita, ta tsura masu idanu tana nazari, dukkanin yaran fuskar mahaifin suka biyo, suna kama da shi sak kamar kobo da kobo, ta ajiye hoton tana mai ta
e baki tana mamakin yadda mutum zai iya kwana a wannan
aramin dakin, katon bedroom ne amma ya fi mata kama da akurkin kaji idan aka ha
a da dakinta da kuma gidan da ta fito, ta bude closet tana bin kayan da ke ciki da kallo, rabin kayan hijabs ne sai dogayen riguna, atamfa, shadda, leshe, babu mayafi ko daya, ta ta
e baki duk da tana kama da wacce take da dakin amma rayuwarsu ta bambamta.

"She have weird taste," ta furta tana
arewa kayan kallo.
*****
Da misalin karfe bakwai na safe, Abbi, Ammi, Imran da Islam sun yi jigum-jigum a parlour, da
yar suka samu suka rufeta bayan da suka kai mata abincin safe ta yi masu haukan da ya fi wanda ta yi masu jiya.

Wannan saurayin da ya hadu da Rumana ne ya shigo falon da sallama a kan bakinsa.

Islam ta ruga da gudu ta yi hugging kafafunsa tana fa
in, "Uncle Al'ameen, Jidderh bata gane mu ba, tana ta cewa ba sunanta Jidderh ba, wai sunanta Rumana."
Al'ameen ya dubesu ya ce, "Mi take nufi da Jidderh bata ganeku ba, bata cikin hayyacinta ne ko kuma bugar mata kai sukayi ta rasa tunaninta na baya!?"
Imran ya ware hannuwa ya ce, "Bamu sani ba, but she's acting weird, sai tana abu kamar ba ita ba, tana cewa ita ba Jidderh bace, that sunanta Rumana kuma kalamanta sunyi tsauri kamar wacce ba'a yi wankin bakin jarinta ba."
Islam ta ware idanu ta ce, "Yaa Imran miye wankin bakin jarinta?"
Ya ware hannuwa ya ce, "Nima ban sani ba."
"Tana ina!?" Al'ameen ya tambaya.

Imran ya nuna mashi matakalar bene ya ce, "Tana dakinta."
Al'ameen ya ce, "Okay bari in yi mata magana." Ammi ta ce, "Amma ka kula ka da garin yi mata magana ta ji maka ciwo." Ya jinjina kai ya ce, "Babu damuwa."
Ya nufi matakalar bene, ya zare makulli da ke akan kofar ya shiga, Rumana ta mi
e ba tare da ta kalli wanda ya shigo ba ta ce, "Tun muna shaida juna ku mayar da ni inda kuka daukoni, na fa
a maku ni ba Jidderh bace, sunana Rumana." Maganar ta tsaya cak a sanadin tozali da ta yi da wanda ya shigo dakin ta nunashi da hannu ta ce, "Kai!."
Al'ameen ya tsara tsayuwa ya ce, "Ni ne da kaina
ar gadara, abu ya yi kyau, na ce yanzu ina katon da kika ce ya daukeni a kafa
a ya jefar a kwatamin kwata."
Ta ware idanu ta ce, "Ohhh dama kaine ka saka suka satoni?" Ya girgiza kai ya ce, "A'a ko
aya bani bane na saka suka daukoki ba, saidai wacce kike kama da ita mamarta cousin dita ce, a ranar da na ganki kin yi min kama da ita ne shiyasa na yi maki magana amma sai kika za
i kiyi min rashin kunya.

Yanzu wa gari ya waya?"
She was like, "Kana hauka ne?" Ya maida kofa ya rufe ya ce, "Kuma fa da gaskiyarki ina ganin kamar na ci kai," ya yi wani shegen murmushi ya ce, "Ya ake ciki
an mata?

Idan kin bani izini ina so in tsaraki kamar yadda saurayi yake idan ya ga budurwa yana so."
Rumana ta ware idanu, ta rasa bakin magana, ji take kamar ta rufeshi da duka, ji take kamar ta cigaba da kwallo da shi a wajen.

Ta ta
e baki ta ce, "Koma miye mun hadu da kai tun kafin
iyarsu ta
ace, Jidderh take ko wa, koma miye sunanta ban damu ba, ka je ka fa
a masu komai su kyaleni in tafi."
Duk da ya fahimci inda maganarta ta dosa amma saboda ya kular da ita sai ya ce, "Ban gane ba."
Ganin yana nema ya
ata mata lokaci ta fasa ihu ta ce, "Suna zaton ni ce diyarsu Jidderh kuma ni da kai mun san ni ba Jidderh ba ce don haka ka je ka fa
a masu gaskiya tun kafin laifin saceni ya rataya a kanku."
Dariya ta bashi sai da ya dara sannan ya ce, "Na san ke ba Jidderh ba ce sai dai su basu sani ba, tambayar ita ce shin waye zai fa
a masu su yarda, ke ko kuma ni."
Ta buga tsaki ta ce, "Malam kana ta
a min lokaci ka je ka fa
a masu tun kafin na fusata raina ya
aci."
Al'ameen ya jinjinawa tsaurin idanunta, ya goya hannuwa a kirji ya ce, "Huh...

Umarni kike bani?" Ta ce, "Eh umarni nike maka kuma dole kayi, ni Didi walki ce daidai kugun uban kowa." Ya ce, "To shikenan," ya zauna a kan kujera ya daura kafa
aya a kan
aya yana mai murtuke fuska ya ce, "Ki yi min dole."
Ta dafe kai ji take kamar ta fasa ihu, kamar za ta yi kuka ta ce, "Yaa Junaid da Umma suna cikin tashin hankalin
atana, ka je ka sanar dasu ni ba Jidderh bace, ko sun barni in koma wajen dangina."
Ya gyara zama ya ce, "Saboda mi zan yi haka bayan rashin kunya da ki ka yi min a waccen ranar da kuma tsaurin idanu da kika nuna min a yau.

Tambaya nike, saboda mi zan yi haka."
Kanta tsaye ta ce, "Saboda shine gaskiya shiyasa za ka je ka fa
a masu." Ji ta yi ya ce, "Idan na ki fa?" Da mamaki ta ce, "Ban gane ba?"
Al'ameen ya ce, "Ranar da muka hadu kika min rashin kunya sannan yau kuma kina ba ni umarni, kina da abun mamaki
an mata.

Idan kina son in fa
a masu gaskiya to ki rokeni, ki durkusa a kan gwuwowinki ki bani hakuri a kan rashin kunya da kika yi min, a lokacin ne zan yi tunani in gani idan zan iya fa
a masu gaskiyar."
Rumana ta saka dariya tana ta
a hannuwa ta ce, "Ni Rumana
iyar Alhaji Abdurrahman Jikar Imran
anwar Junaid ni ce zan durkusa in roketa, ashe kuwa za'a shekara a shekare ana abu
aya."
Ya ware idanu ya ce, "Kenan kin gwammace in barsu su yi ta daukarki a matsayin Jidderh."
Ta ta
e baki, ji take kamar ta rufeshi da duka, sai dai ba za ta yi wannan kuskuren ba domin babu mai tare mata a kusa, ta murtuke fuska ta ce, "Idan ka gadama ka fa
a masu gaskiya, idan ka gadama kada ka fa
a masu, a je a dawo dolensu su barni in tafi tunda ni ba Jidderh bace.

Now, ka bani aron wayarka inyi kira."
Mamaki da dariya take bashi, ta gama gadara ta dawo tana cewa ya ara mata wayarsa, ya murmusa ya ce, "Yanzu kuma wayata kike son in ara maki, ina ce wayata ce torh ban badawa Jidderh." Ya
arasa maganar da kiranta da Jidderh domin ya kular da ita.

Ta fasa ihu ta ce, "Ni ba Jidderh ba ce, sunana Rumana." Ya ce, "Eh na sani Rumana aww Jidderh." Ya fice yana mata dariya, ji take kamar ta bi shi ta yi ball da shi a wajen
. (Wannan shiga hanci da kudundune haka
kuce wa Al'ameen ya fita hancin Rumana tun kafin ta saka a watsashi a kwatami
Ta ta
are ta fasa ihu tana mai jin takaicin yadda yake mata magana cike da gadara da gatsali, sai dai meyy, tana
aga idanu ta ga kofa a bu
e, ba ta yi wata-wata ba ta mi
e ta fice da sauri ta bi ta kofar baya ta bayyana a bayan gidan, a gefe ta hango kofa ta yi sa'a kuba ce kawai aka saka, ta bu
e ta fice ta yanki hanya tana
arin tuna sunan unguwar da gidan Aunty Zaynerb ya ke.

Al'ameen yana sauka
asa ya ce, "Wannan yarinyar ba Jidderh ba ce ba, sunanta Rumana."
Baki
ayansu suka zuba mashi idanu cike da tu'ajjibin abun da ya fa
a, sudai idanunsu Jidderh suka gani amma yake ce masu ba ita bace, to idan ba ita bace, to wacece, kuma mi yasa suke matu
ar kamanni, sannan ina Jidderh take.

Da mamaki wanda yake ha
e da rudani Ammi ta ce, "Ban gane ba, Mi kake son sanar da mu?" Al'ameen ya zauna sannan ya ce, "Gaskiya take fa
a maku sunanta Rumana, tana kamanni da Jidderh ne amma ba Jidderh ba ce ba," ya juya ga Imran, ya ce, "Imran ka tuna kwanakin baya lokacin da na kiraka ina tambayarka Jidderh har na ce maka ka je ka tabbata idan tana gida."
Imran ya gya
a kai ya ce, "Eh na tuna lokacin." Al'ameen ya lumfasa sannan ya ce, "To lokacin da wannan yarinyar na hadu na yi mata magana ina tunanin Jidderh ce ina mamakin shigar da ta yi."
Imran ya ce, "Then wacece ita?

Ina Jidderh take?

Mi yasa take kamanni da Jidderh?

Mi yasa suke kama kamar kobo da kobo da har mu da muke rayuwa da Jidderh muka
asa tantance ba ita ba ce?" Tambaya ce wacce basu da amsarta sai dai su tambayi ita Rumana.

Baki dayansu suka dugunzuma zuwa sama, sai dai wayam suka tarar da dakin, babu Rumana babu alamarta, ta yi
atan dabo, sun duba baki
aya gidan amma basu ganta ba, ganin kofar baya a bu
e ya tabbatar masu da a nan ta fita.

Al'ameen, Abbi da Imran suka bi sawu amma ko mai kamanni da ita basu gani ba.

A bangaren Rumana kuwa tana fita bakin titi ta debi hanya ta cigaba da tafiya a lokaci guda tana son tuna sunan unguwarsu Aunty Zaynerb amma ta gagara tunawa, sai da ta yi tafiya mai tazara har kafafunta suka fara ciwo sannan ta yi nasarar tunawa.
Chapter 9 · 0% Book details