← Book details Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 49

Sashe 29

Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rumana
anwarsa wacce ya ke ji da ita, wacce yayi rainonta cikin kulawa da gata da so irin wanda bai ta
arewa ba, wacce bai ta
a barinta ta rasa komai ba amma ita ce yanzu aka mi
a, za ta rayu a wani wuri daban, tare da mutanen da bai san su ba.

Mutanen da zuciyarsa take gaya masa ba za su fahimce ta ba.

Ba za su kula da ita kamar yadda yake kula da ita ba.

Ta tashi a rayuwar jin dadi, cike da kulawa, inda kalma
aya kawai daga gareta take da muhimmanci, inda jira kawai ake ta fa
a ayi mata amma yanzu an tura ta zuwa rayuwar da ta bambanta da wadda ta sani.

Banbacin rayuwarta ta London da wacce za ta yi a nan a bayyane yake.

Ya bu
e idanu a hankali, ya kalli hanya da yadda jirgin yake ratsa gajimare, zuciyarsa tana hasko masa Rumana a wurin da ya bar ta durkushe tana kuka.
***********
angaren Rumana kuwa, da
yar ta iya mi
ewa daga inda take dur
ushe.

Idanunta sun kumbura, hawaye na ci gaba da zubowa akan fuskarta.

Ta fito da sauri, zuciyarta cike da buri guda
aya ta same shi kafin ya tafi.

Convoy
in motocinsu ya riga ya
ace, babu ko
urarsu da ta rage.

Wani irin kuka ne ya ku
uce mata, kuka mai cike kunci da ra
i.

Kafafunta sun kasa
aukarta, ta dur
ushe a
asa a tsakiyar harabar gidan, ta ri
e kai da hannu, ta yi tagumi, tana kallon
aramin gidan da take a cikinsa.
arami ne
warai idan aka kwatanta da nasu wanda ya linka wannan sau ashirin da
oriya.

"Ta yaya..." ta furta cikin kuka.

"Ta ya ya zan rayu a wannan akurkin gidan nasu?"
Ta girgiza kai da
arfi, hawaye na
ara kwaranya akan fuskarta, "A'a, ba zan iya ba, kawai ku mayar da ni gida wajen Umma da Yaya Junaid."
Amma babu wanda ya amsa mata.

Sai ita ka
ai a harabar gidan, zuciyarta cike da
in amincewa, tsoro da kuma rashin sanin makoma.

Ta da
e a dur
ushe a harabar gidan, Jidderh tazo kiranta taki zuwa, Islam tazo shima taki zuwa.

A daidai lokacin ne Imran ya dawo daga Morocco wanda kawo Rumana ne ya saka mutanen gidan suka shafa'a daga daukosa daga Airport, yana ta kallonta saidai baice komai ba, ya shige ciki.

Jim ka
an ya fito ya dubeta ya ce, "Ammi ta ce ki shigo ciki."
Kanta tsaye ta ce, "Ban shigowa, kuma a yau ba gobe ba sai kun mayar da ni gidan mu wajen Ummana da yaya Junaid nafi karfin in zauna a wannan akurkin kajin."
Bata
arasa maganar ba ta ji saukar mari akan fuskarta, marin da ya gigitata ta fasa ihu hannunta dafe da kuncinta, jikinta har rawa yake ta kira lambar yaya Junaid ta fashe mashi da kuka tana fa
in, "Na boni na lalace za su kasheni da mugunta."
Hankalinsa ya tashi yana tambayarta amma ta kasa magana sai dai kuka kawai, karshe ta tsinke wayar ta durkushe a wajen tana cigaba da kuka.

Hankali a tashe ya sauko parlour inda Umma take ta rafka uban tagumi damuwa kwance akan fuskarta, ka raini yaro tun yana jinjiri har ya girma sannan rana tsaka ya rabu da kai abu ne mai wahalar sha'ani musamman da take da kulafucin yara da kuma tabbaci da take da shi na gidan ba kamar wannan yake ba, tana jiyewa kanta, anya kuwa Rumana za ta iya jure rayuwa tare da wa
annan mutanen, koda yake koma miye bata da ta cewa, sune ahalinta sun fita iko a kanta.

Maganar Junaid ta katse mata tunani yana fa
in, "Umma akwai damuwa, yanzu Didi ta kirani tana ta kuka, tana cikin damuwa, a tsorace take, ba za ta iya rayuwa tare da su ba, muje mu tafo da ita."
Daga inda take zaune ta girgiza kai ta ce, "Junaid babu abun da zamu iya yi a kai, sun fimu iko a kanta, jininsu ce,
arsu ce, mu kuma bamu da wata dangantaka da ita sai ta zama da ta yi damu tun tana jinjira."
Junaid ya dafe kansa yana tunanin mafita, ba zai iya jure ganinta a damuwa ba gwara suje su tafo da ita kawai.

"Amma Umma, Rumana tafi sabawa da mu, yau ko tambayarta aka yi da wa take son ta yi rayuwa mu za ta za
a don haka mu makasu kotu kawai ay shekarunta sun kai sai a bata za
i ta za
a a tsakaninmu."
Umma ta girgiza kai ta ce, "Kayya, zalunci kenan, idan mukayi haka mu kanmu bamu yiwa kanmu adalci ba, na sace masu yarinya na kawota ta rayuwa damu, sunan abun da nayi a nan zalunci, sannan a yanzu kake maganar mu makasu kotu mu amsheta, bamu
auki darasi akan abun da ya faru ba kenan, ban zaci zakayi wannan maganar ba not after what happened."
Ya zauna fuskarsa dauke da damuwa ya ce, "Kuka ta ke yi sosai, kukanta yana sakani a cikin damuwa, kukanta yana damuna a zuciya, idan na tuna kukan da ta ke yi a lokacin da ta kirani sai inji na kuntata, ya kamata mu maido da ita ta rayu a cikinmu tunda ba zamu rasa mafita ba."
Umma ta yi jim tana nazari sannan ta ce, "Ta hanya
aya ce kawai Rumana za ta iya dawowa ta rayu tare damu sai dai bakin alkalami ya riga ya bushe, lokaci ya riga ya
ure domin mun makara, kawo maganar a yanzu babu abun da zai haifa face
ara rikita al'amurra ne."
Jin ta ambaci mafita bakinsa har rawa yake wajen jera mata tambayoyi a kan wacce mafita ce.

A shirye yake da aikata komai domin dawo da farin cikinsu a gidan, Rumana ita ce farin cikinsu a gidan, ita suke kallo suji sanyi a ransu, rabata da gidan daidai yake da fatali da farin ciki da walwala da yake wanzuwa a gidan.

"Umma wacce hanya ce wannan?

Wace mafita ce?

Please ki fa
a min inje in dawo mamu da ita."
Umma ta yi wani murmushi mai ciwo sannan ta ce, "Junaid wannan mafitar tana tare da kai sai dai kamar yadda na fa
a maka a
azu, lokaci ya riga da ya
ure."
Ya hade hannaye a waje guda alamar roko ya ce, "Please Umma ki fa
a min, a shirye nike in aikata."
Tausayinsa ya kamata, ita shaida ce a kan shakuwa da ke tsakaninsa da Rumana, ita kanta daurewa kawai ta ke yi, ita kenan da daman can tasan komai daren dadewa akwai ranar da maganar za ta fita ballantana kuma shi da abun ya rutsa da shi kwatsam babu zato babu tsammani.

Ta ce, "Zan fa
a maka amma sai idan na dawo daga Dubai tukunna."
Junaid ya ce, "Umma bayan bikin kenan, lokacin ya yi yawa please ki tausaya ki fa
a min a yanzu inje in tafo da ita, ba za ta iya rayuwa a gidan nan ba, kinga yadda gidan yake kamar akurkin ka ji, ina tantama idan suna da Ac, ba za ta iya rayuwa a gidan ba, ka da wani ciwo ya zo ya sameta."
Ganin ba zai rabu da ita da maganar ba ta murtu
e fuska ta ce, "Dole ta ha
ura ta rayu dasu sune dolenta, Junaid ka koyi ha
uri da dukkanin yadda rayuwa ta zo maka, ba komai ba ne mutum yake so yake samu, wata rana a kwana a gado wata rana a kwana a tur
aya haka rayuwa take, ita kuma kaddara tana zuwarma
an Adam ne ta inda bai ta
a tsammani ba."
Ya mi
e ya nufi hanyar fita ta tsayar da shi, "Ina za ka je?" Ta tambaya.

"Wajenta zan je idan ban ganta ba bazan iya rumtsawa ba."
Da mamaki take kallonsa jin abun da ya ce, ba mamakin zuwan ta ke yi ba, mamakinta shine ta ina zai je Katsina da tsohon daren nan.

"Ta ina za ka je domin kasan yadda rayuwa ta
aci da sace-sacen mutane ba zan barka ka
auki hanya a mota a wannan yanayin ba, na rasa
anwarka ba zan iya jure rasaka kaima ba."
Yadda ta yi magana da damuwa ya saka jikinsa ya yi sanyi, ya dawo ya zauna a kusa da mahaifiyar tasa ya rungumeta, kukan da take ta dauriya tana rikewa ya kufce mata, ta fashe da kuka.

Shima ji yake kamar ya yi kukan amma ya
aure ya share kwolla da ta zubo mashi ya ce, "Umma itama baki rasata ba, nan ne gidan zamanta kuma ina mai tabbatar maki da zan dawo maki da ita da hannuna."
Daga haka ya mike ya haura saman bene zuwa bedroom dinsa, kaya kala biyu ya saka a lugagge tare da abubuwan da zai bu
ata ya dauki kwamfutarsa da waya ya sauko kasa ya ce, "Umma na tafi, zan bi Private jet dina."
Ta gya
a kai ta ce, "To shikenan, ka gaida min da ita." Ya ce, "Ko ki shirya sai mu tafi tare." Ta girgiza kai ita kuwa idan akwai kunya ai bai kamata su ganta a gidan su ba.

"A'a sai ka dawo, Allah ya kiyaye hanya, Allah ya tsare." Ya amsa da, "Amin." Ya juya ya fita.

Karfe goma ya sauka a garin Katsina, rabon a yi ya sakashi fara zuwa gidan Aunty Zaynerb da nufin ya ajiye kayansa kafin ya wuce wajen Rumana.
Chapter 29 · 0% Book details