← Book details Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 49

Sashe 25

Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hotunanta kuma suka zame masa abun dubawa domin tunawa da abun da ya rasa da kuma abun da yake ci gaba da nema ba tare da sanin inda zai fara ba.
*******
*SOMEWHERE IN ABUJA*
Rumana tana zaune a dakin tayi tagumi ranta a dagule, Sultana ta kawo mata abinci.

Bayan ta ajiye mata farantin, ta ce, "
awata, yaushe za ki wuce London?"
Runana ta kalleta ta gyara zamanta sannan ta amsa a hankali ta ce, "Sai nan da sati guda."
Da jin haka, Sultana ta jinjina kai, zuwa yanzu ta fara shakku musamman yadda Rumana take sauya magana kullum.

Ta juya ta fice daga
akin cike da tunani da shakku.

Kai tsaye ta wuce dakin mahaifiyarsu wacce suke kira da Nene, ta zauna kusa da ita, ta ce, "Nene lamarin
awar nan tawa yana bani mamaki sosai, ina tsoron ka da mu saka kanmu a abun da daga baya za a zo ana wallahi summa tallahi damu.

Yarinyar nan
ar masu ku
i ce sosai, kuma ba
awata ba ce, ko a makaranta ba magana muke yi sosai da ita ba, sai dai gaisuwa daga nesa, gashi sai sauya magana takeyi, yau take kaza, gobe kuma ta ce wani abun daban."
Ta mi
e tsaye tana kallon Nene, ta ce, "Bari in kira
awarta Jasmine, in sanar da ita halin da ake ciki.

Wata
ila ita ta fi fahimtar abun da ke faruwa."
Ta fice ta koma dakinta, ta zauna akan gado, ta
auki wayarta tana jujjuyawa a hannu kamar mai neman tabbaci.

Tana ji a ranta akwai wani abu da Rumana ba ta bayyana mata ba dangane da wannan zuwan duk da cewa ba ta da hujja kai tsaye.

Nan take ta kira Jasmine.

Bayan ringing, Jasmine ta
aga ta ce, "Hello Sultana?"
Sultana ta gyara zama, ta rage murya kamar tana tsoron a ji ta tace, "Jasmine, kina jina?"
Daga
aya bangaren Jasmine ta ce, "Eh ina sauraron ki, lafiya?"
Sultana ta ce, "
awarki ce muka ha
u a nan Abuja ta ce za ta wuce London nan da sati guda amma har satin ya wuce babu magana kullum sai sauya zance ta ke yi."
Jasmine ta yi dariya ta ce, "Sai kuma aka yi mey Sultana?

Ke dai bakya son mutane ne kawai."
Sultana ta ce da sauri, "Ba haka bane.

Ki ji ni da kyau.

Ta sauya magana sau da yawa, yau sai ta ce this nan da gobe sai ta ce that."
Jasmine ta yi jim kafin daga bisani ta ce, "Anya ba kina overthinking bane ba?"
Sultana ta amsa da sauri, "A
a Jasmine.

Na san abun da gani, tabbas akwai abun da take
oyewa."
Sultana ta cigaba da magana cikin damuwa, "Damuwa ce bana so, bana son daga baya muce da ace mun sani."
Jasmine ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Nasreem ba ta da damuwa fa, ki kwantar da hankalinki."
Sultana ta katseta da sauri, "A'a Jasmine, ba Nasreem nike magana ba.

Rumana nike nufi."
Jasmine ta zaro idanu ta ce, "What?!

Dama duk neman da ake yi mata tana nan?

To ya aka yi har ta san gidanku?"
Sultana ta ce, "Wallahi haduwa muka yi na ganta tana tafiya a hanya."
Da sauri Jasmine ta ce, "To ki saurare ni da kyau.

Rumana family issue suka samu ta baro gida, for all those days nemanta ake yi sosai, zan fa
awa Ummarta cewa tana nan gidanku amma ki kwantar da hankalinki, kada ki nuna mata komai ko ki bari ta fahimci wani abu."
an dakata kafin ta
ara fa
in, "Yanzu zan kira gidansu a zo a
auke ta amma ki yi taka tsantsan, ka da ta gane wani abu yana faruwa."
Sultana ta yi shiru, sannan ta amsa a hankali, "Toh..."
Ta kashe wayar cike da tambayoyi da ru
ani.

A hankali ta koma
akin Mom, ta zauna tana fuskantarta ta ce, "Mom, ashe Rumana baro gida tayi ana ta nemanta, yanzu Jasmine ta ke fa
a min ta ce zata kira gidansu su zo su
auke ta."
Mom ta ce, "Dama na yi zargin haka, Allah ya kawo su lafiya."
Sultana ta amsa da, "Amin."
A bangaren Jasmine tana gama waya da Sultana, ta yi gaggawar kiran Umma ta bayyana mata dukkanin abun da Sultana ta gaya mata na cewa Rumana tana can, ta kuma fa
a mata adireshin gidansu Sultana.

Umma ta ce, "Alhamdulillah, mun gode, yayanta yana Abujar bara in kirashi sai ya sameni a Airport mu wuce gidan."
Ta kira Junaid.

Junaid yana zaune a balcony na gidansa dake Abuja ya samu kiran Umma, yayi zuru yana kallon wayar yana mamakin dalilin kiran tunda a kwanakin nan ko ya kira bata
agawa.

Yana
agawa, ta fara magana cikin gaggawa, "An samu Rumana a Abuja, tana gidan wata
awar
awarta don haka ina nan zuwa Abuja, ka sameni a Airport sai mu wuce gidan da take."
Junaid ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Alhamdulillah, Allah shine abun godiya."
Umma ta kashe wayar ta mi
e ta shirya da sauri, zuciyarta cike da gaurayayyen jin dadi da kuma damuwa, dadin samun labarin Rumana, da kuma damuwar yadda yarinyar za ta tsinci kanta a rayuwa inda bata saba ba.

Flight dinsu Umma yana landing ta samu convoy na motocin da za su je tare da Junaid suna jiranta.

"Barka da zuwa," Junaid ya fa
Ta yi murmushi ta ce, "Yauwa, Allah yayi albarka." Rabon da tayi mashi magana ko murmushi har ya manta, ya share hawayen da suka zubo mashi ya ce, "Amin."
Motoci suka ratsa hanya cikin sauri suka nufi gidansu Sultana kamar yadda Jasmine ta fa
awa Umma adireshin.

A lokacin da suka isa gidan, Rumana tana jin
arar motoci sun tunkaro harabar gidan, gabanta ya yanke ya fa
i, ba ta tsaya tunani ba ta fice ta nufi backdoor domin neman hanyar tserewa.

Amma kafin ta kai, ta tarar da security a hanya.

Nan take suka dakatar da ita, babu wata hanya da ta rage mata face ta juya ta koma ciki a cikin ru
ani.

Mom ta ganta tana dawowa ta nuna mata hanya ta ce, "Mu je parlour, Ummarki da yayanki sun zo."
Rumana ta tsaya tana kallon Mom cike da tsoro, hawaye suna neman zubo mata ta ce, "Zasu mayar da ni Katsina ne."
Nene ta daka mata tsawa ta ce, "Na ce mu je!."
Rumana ta yi shiru tana raba idanu ta bi bayan Mom har zuwa parlour.

Tana shiga falon, Umma ta mi
e tsaye, takaici, sau
in lumfashi da farin ciki duk sun gauraye a fuskarta.

Ta ce, "To mu zamu tafi.

Mun gode sosai."
Mom ta ce, "Babu komai.

Allah ya
ara tsarewa."
Rumana tana tsaye gefe, zuciyarta cike da ru
ani domin ta tabbatar daga nan sai Katsina. ta
arasa inda Junaid yake da gudu tana hawaye, ta rungume shi sosai, tana roko tana magiya da rawar murya, "Please ka da ka bari a mayar da ni wajensu."
Junaid ya ja da baya da sauri, ya cire hannunta daga jikinsa, fuskarsa cike da takaici ya ce, "Ka da ki
ara min magana, kin yi min abun da ban ta
a zato daga gareki ba.

Ba zan
ara yarda dake ba."
Wadannan kalaman nasa sun sakata a ru
ani.

Kafin ta ce wani abu, ya juya ya fice daga falon.

Nan take ta dur
ushe ta fashe da kuka mai tsuma rai, kuka mai cike da sheshsheka da kiran sunansa, amma ko juyowa bai yi ba.

Umma ta daka mata tsawa, "Zaki tashi mu wuce ko kuma sai na laka
a maki
an banzan duka tukunna."
Rumana tana kuka ta mi
e suka fita.

Sukayi boarding flight zuwa Katsina ta Dikko Dakin Kara Kunya Gareku Ba Dai Tsoro Ba.

Ko a cikin jirgin Rumana ba ta daina kuka ba.

Hawayenta sun gagara tsayawa, zuciyarta cike da tsoro, nadama da rashin tabbas.

Lumfashinta yana fitowa da wahala, amma babu wanda ya yi mata magana a tsakanin Umma da Junaid.

Umma ko murmushi taki tayi yayinda Junaid yake danna waya ya basar kamar bai san da wanzuwarta a jirgin ba.

Babu wanda yayi magana throughout the journey har suka sauka a Birnin Dikko, convoy na motocin alfarma suka
aukesu zuwa gidan Ammi.

Rumana tana rakube a mota tayi tagumi, idanunta sunyi ja, zuciyarta ta cika da fargabar abun da zai biyo baya na barinta da za su yi a nan.

Ammi ta tarbesu da fara'arta aka saukesu a babban parlour yayinda matakan tsaronsu suke a compound.

Junaid ya zauna yana mai gaishe da Ammi, "Ammi ina wuni?" Ammi ta amsa da, "Lafiya lau
ana, kunzo lafiya?" Ya ce, "Lafiya lau." Ta ce, "Allah yayi albarka." Ya amsa da, "Amin."
A sanyaye Rumana ta shiga falon ta rakube a kasan carpet hawaye suna ci ga ba da zuba daga idanunta.

Jidderh ta zuba mata ido tana kallonta da mamaki.

Tana tuna yadda watanni biyu da suke wuce ta shigo gidan da izza da gadara amma gashi yanzu tana zaune a
asa cikin kuka, tana kallon kowa da idanu cike da tsoro tana neman hanyar tsira.

Jidderh ta yi shiru tana bin ta da kallo daga sama har
asa.

A ranta ta ce, "Duniya abin tsoro."
Shiru ya ratsa falon, babu sautin da yake tashi sai sautin sheshshekar kukan da Rumana take yi.

Umma ta ja dogon lumfashi, ta gyara zamanta zuciyarta cike da nauyin shekaru da abubuwan da suka faru.

Ta dubi mutanen falon, kowa shiru, suna jiran abun da za ta ce.

Ta fara magana cikin sanyi murya, "Ga Rumana, Allah ya bayyanata..."
Ta dakata tana tattaro
arfin zuciya sannan ta ci ga ba, "Don haka a yanzu zan fa
a muku abun da ya faru, zan baku labarin tarihin rayuwata domin ku fahimci lamarin sosai ku kuma gane dalilin da ya sa na tsinci kaina a cikin wannan hali."
Rumana ta
ago kai a hankali, hawaye sun wanke fuskarta tana kallon Umma tamkar wacce take neman amsa tun kafin a fara.

Tana kallonta tana girgiza kai alamar kada tayi mata haka.

Umma ta sauke ajiyar zuciya sannan ta cigaba da magana, "Abun da zan fa
a maku ba yau ne ya fara ba, akwai tarihi mai tsawo a bayansa.
Chapter 25 · 0% Book details