← Book details Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 49

Sashe 33

Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya jinjina kai ya ce, "Hakane."
Ta kalli Rumana da ke makale da shi sai kuma ta murtu
e fuska ta ce, "Me nace maki a kan yawo da mayafi?

Tunda kikazo gidan nan kinga Jidderh ta fita ba tare da dogon hijabi ba."
Rumana ta turo baki ba tare da ta ce komai ba, Junaid ya ce, "A gafarcemu zamu kiyaye." Ammi ta jinjina kai ta ce, "Idan wadanda na bata ne bata so kaje da ita kasuwa ka dinka mata kuma kaja mata kunnuwa, ta shiga taitayinta da ni domin
aramin aikina ne in kiraka daga Kaduna kazo ka hukunta min ita."
Ya waro idanu yana fa
in, "Na'am." Rumana ko motsawa ba ta yi ba domin maganar ta yi mata kama da almara, tunda take bai ta
a dukanta ba ballantana wata wacce ba Umma ta ce za ta saka ya doke ta.

Junaid ya yi tsuru-tsuru da idanu, dukkanin ranar da aka sakashi hukunta Rumana ai an bashi babban aiki, abun da kamar wuya wai guguwa da auren nesa.

Ammi ta ce, "Naji baka amsa ba ko a matsayina na uwa ban isa in saka ka hukunta
anwarka ba, ko kuma ka fi gane in saka kaninka Imran ya yi mata hukuncin."
Da sauri ya
ago idanunsa a waje ya ce, "A'a zan yi mata hukuncin da kaina." Ammi ta ce, "To madallah."
Ta yi mashi hakane sanin ba zai iya hukuncin ba, kenan idan ba ya son ya yi mata gardama dolensa ya takawa Rumana burki akan wasu abubuwan da ta ke yi.

Ta mi
e ta wuce sama tana fa
in, "Ka tsaya muci abincin dare." Ta haura bene.

Rumana ta turo baki ta ce, "Kenan ka yarda zaka hukuntani." Ya kama kumatunta yana ja yana mata dariya ya ce, "Ba zan dokeki ba sai dai inyi fa
a da wanda yake shirin saka hannuwansa a kanki."
Rumana da samun waje ta ce, "So nike ka ajiye takalma waccen Imran din yana tsallakewa kayi mashi dukan tsiya ka rama min dukan da yayi min, matar gidan tana da kirki ba za ta yi magana ba." (Ohh Rumana ashe kin san Ammi tana da kirki).

Dariya ya yi jin wautarta bai bata amsa ba sai cewa ya yi, "Tunda tana da kirki ki rin
a girmamata ko kuma idan na koma Kaduna ba zan dawo ba, tunda tana da kirki kema ki rin
a yi masu kirki."
Ta ta
e baki ta ce, "Tab!

Naji
azu ka yarda zakaci abincin da suka yi, to ina gaya maka da safe na ji matar gidan tana cewa tuwo miyar kuka za'ayi."
Idan ta ce matar gidan tana nufin Ammi, tun a nan ya fara gyaran gudun saka kanshi a tsulla-tsulla, gudun Ammi ta sakashi hukuncin da zai yi mashi wahalar aiwatarwa kuma kunyar da ke tsakaninsa da ita bai isa ya yi gardama ba.

Ya ce, "Ba matar gidan zaki ce ba, Ammi zaki ce, mahaifiyarki ce nima mahaifiya take a wajena."
Ta turo baki tana fa
in, "Kai haba, a'a gaskiya, Ammi kuma sai dai ince mata Mama, gwaggo ko Inna haka naji irinsu
an gidan akurki suna kiran uwayensu."
an bata fuska ya ce, "Ke wai mi yasa baki jin magana." Ta
ata fuska tana kukan shawaga
a, kukan da babu hawaye.

A take ya murtu
e fuska ganin wankin hula yana neman ya kaishi tsakiyar dare, ya shareta yana danna wayarsa, itama ta yi fushi taki kulashi, saida taga da gaske yake sannan ta fara rarrashi ya yi kamar bai san tana yi ba, ta kama gemunsa tana ja tana dariya tana fa
in, "Kamoshi-Kamoshi."
A haka Ammi suka sauko suka samesu, ji ya yi kunya ta kamashi ya kama hannunta yana fa
in, "Ya isa haka."
Ammi ta nuna masu hanyar dinning table ta ce, "Muje." Rumana ta ce, "To Yadikko." Junaid ya girgiza kai kawai wato Ammi din ne ba za ta kira shine ta buge da cewa yadikko shima wannan babu damuwa tunda ta daina cewa matar gidan, atleast idan ta ce Yadikko ba za a kirashi a ce ya yi hukunci ba.

Ya kama hannunta suka wuce teburin abinci, tuwo ne da miyar kuka da tasha naman rago ga man shanu da ya jin daddawa, tun kafin ya fara aikawa cikinsa yawunsa ya fara tsinkewa, loma
aya ya yi ya lumshe idanu yana jinjina kai
in abincin yana kai mashi har tsakiyar kai, ya ce, "Waye ya girka?" Jidderh ta ce, "Nice na girka." Ya murmusa yana mamaki ya ce, "Godiya dubu, Allah ya
ara zakin hannu."
Rumana ji ta yi kamar ta fasa ihu jin yana yabon wannan abun da yake nema ya sakata amai, ta ture farantin gabanta tana turo baki ta ce, "Ban cin wannan abun."
Imran ya daka mata tsawa sai da ta tsorata ta ri
e hannun Junaid gam, Junaid ya rumtse idanu ya ce, "Imran ka daina mata tsawa, kana tsoratata, bata saba da hayaniya ba, ko a gida bata cin tuwo."
Imran ya ce, "Shine kuma sai ta yi wa mutane magana da gadara, waye sa'anta a nan."
A take Ammi ta tsawatar, "Kai Imran ban san rashin kunya, yayan naka kake fa
awa magana, ina ce a gabansa ta yi maganar kuma shine sama da kai, sai ka barshi ya yi hukunci ba wai ka hayayyako ba, kada in kuma ji, kada in kuma gani, daga yau idan yana nan sukayi laifi a gabansa ban so ka ce uffan shine zai yi hukuncin ai babban wa uba."
Daga haka bata ce uffan ba, Junaid ya yi tsuru-tsuru ta
aure shi da jijiyoyin jikinsa, ya fi karfin mintina biyu bai motsa ba, Rumana za ta yi magana ya kama hannunta yana mata magana a hankali tun kafin ta
allo mashi
allin da zai sakashi a tsulla-tsulla wai dungurin uwar miji da muciya.

Ya juya inda Jidderh take ya ce, "Jidderh a taimaka a girka mata wani abun mana." Kafin Jidderh ta yi magana Ammi ta rigata da fa
in, "Taje da kanta ta girka." Junaid ya waro idanu yana fadin, "Ai bata iya girka komai ba." Ammi ta ce, "Wannan yarinyar da yau zan iya yi mata aure ta zauna gidan miji ita ce kake fa
a min ba ta iya girki ba, to kafin ka tafi ka nema mata makarantar koyon girki ko kuma ta koya a wajen
ar uwarta."
Rumana ta kwashe da dariya, wai ita ce za ta koyi girki, miye amfanin amfanin
an aikin da za'a daukar mata a gida, shi kanshi tasan kunyar Ammi ce ta saka ya amsa da to.

Ta juya inda Jidderh take ta ce, "Jeka ki girka mata farar shinkafa sai taci da miya." Jidderh ta mi
e ta wuce kicin, Junaid ya bada himma yana kwasar lagwadar girki, ya manta a inda yake, da tsokana ya yanko loma ya nufi bakinta ta kawar da kai tana turo baki ya saki dariya.

Bayan sun gama kowa ya wuce parlour ya rage Junaid da Rumana ne kawai a zaune a teburin abinci, Jidderh ta gama ta kawo Rumana bata ce uffan ba ta dauki cokali tana tsakurar abincin kamar wacce take cin magani.

Sai Junaid ne ya yi godiya, "Mun gode sister, Allah ya biya." Jidderh ta amsa da, "Amin."
Ta koma kitchen domin wanke abubuwan da suka
ata, Ammi ta
aga murya tana fa
in, "Idan ta gama ta taya Jidderh wanke-wanke." Junaid ya ce, "Ammi shima bata iya ba."
Ammi ta jinjina kai ta ce, "Wannan kuma laifinka ne sai kayi a maimakonta."
Ya ce, "To," ya kama hannun Rumana suka wuce kitchen, tana cin abinci yayinda shi kuma yake taya Jidderh da daurayewa kayan idan ta wanke.

Jidderh ta ce, "A'a ka barshi." Ya waro idanu ya ce, "A'a barni inyi tunda Ammi ce ta saka." Bayan sun gama ya fito da shirin wucewa Ammi ta hana, ya ce, "Ba gidana zan koma ba, gidan kanwar babana zan je in kwana." Sai a lokacin Abbi ya saka baki ya ce, "Da nan da can duk
aya ne ka kwana a dakin Imran."
Babu damar ya yi musu da su, ya kama hannun Rumana da ke biye da shi kamar bindi suka koma
aya bangaren suna kallo a wayarsa.

Sai da ya lalla
ata ta yi bacci dakinta sannan ya wuce dakin Imran da nufin ya kwanta, ko mintina ukku cikakku baiyi ba ta biyo bayansa, Imran ya murtu
e fuska ya ce, "Ke koma inda kika fito bacci zan yi."
Ta turo baki tana fa
in, "Ban fita." Maganar Ammi a kan idan Junaid yana waje kada ya
ara hukunci ne ya hanashi marinta amma ya shaka ba ka
an ba.

Yana jiran ya ji Junaid ya yi hukunci amma sai ya ji lukus kamar an watsa fulawa a kwararo, ya
an dubeshi ya ce, "Kamar rashin kunya ta yi min yanzu amma ba ka ce komai ba." A takaice Junaid ya ce, "Ka yi ha
uri yarinta ne."
Rumana da samun waje ta ce, "Wai kai nan fanfo kake so kayi mashi ya dokeni, to ba zai dokeni ba sai dai in saka ya yi kasa-kasa da kai ya rama min marin da ka yi min.

Kuma gobe zan saka ya ajiye takalma kana tsallakewa ya
agaka ya nana da
asa."
Imran bai san lokacin da ya durfafi inda take ba zuciyarsa tana tafarfasa ya
aga hannu ya wanketa da mari, bai sauke hannunsa ba Junaid ya wanka mashi mari (lukutar tsiya).

Sai da Junaid ya yi marin sannan nadama ta kamashi, a fusace Imran ya fita zuwa dakin Ammi.

Junaid ya yi tsuru-tsuru da idanu yana ji kamar ya yi tsuntsuwa ya bar gidan, sai zufa yake kamar tsohon munafuki.
Chapter 33 · 0% Book details