← Book details Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 49

Sashe 23

Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya girka mata abincin da ta fi so pounded yam da miya wato tuwon doya da miya ko ince sakwara da miya.

A parlour kuwa, tana zaune tana sauraron motsinsa daga kitchen.

Kowanne motsi da yake yi yana saka mata kwanciyar hankali.

Ta share hawayenta a hankali, zuciyarta na sau
a ka
an-ka
an.

Kasancewarta a tare da shi ya rage mata kaso mai yawa na damuwar dake ragargazarta a zuciya.

Sai da ya matsa mata sosai sannan ta
an ci abincin, ba don tana jin yunwa ba sai don kada ta
ata mashi rai.

Yana kallonta har ta gama, ya mi
e ya nuna mata wani
aki a gefen parlour ya ce, "Ki shiga ki yi wanka sai mu wuce Lagos."
ago kai ta kalleshi da mamaki, ta ce, "Lagos kuma?" Ya amsa a ta
aice, "Eh."
Ba ta
ara tambaya ba.

Ta jinjina kai kawai, ta nufi
akin.

Ta shiga bathroom ta yi wanka, amma zuciyarta ba ta da nutsuwa.

Tunani iri-iri ne yake yawo a ranta.

Me yasa Lagos?

Me yake shiryawa?

Shin zai kai ta wani wuri ne ko kuwa wani abu ne daban?

Ta sauya kayan da ya siya mata, tana sake-sake a ranta, zuciyarta cike da shakku.

Da ta fito taga baya parlour ta nufi
aya daga cikin
akunan.

A nan ta jiyo
arar ruwa daga bathroom, yana ciki yana wanka.

Idanunta suka sauka akan wayarsa da ke ajiye akan bedside table, ta
an yi jinkiri kafin daga bisani ta mi
a hannu ta
auka.

Ba don tayi mashi bincike ba sai dai tana son ta tabbatar da wani abu.

Mistenkly ta danna hannunta akan call log.

Nan take screen ya haska mata lambar Umma wanda ita ce lambar karshe da ya yi waya da ita a
asa kuma lambar Umar.

Zuciyarta ta buga da
arfi, wani sanyi ya ratsa jikinta.

"Kenan Yaya Junaid ya ha
a kai da Umma?" ta furta a ranta, idanunta suka cika da hawaye.

Ta saki wayar akan gado, lumfashinta ya fara rikicewa.

Abubuwan da take
arin dannewa sun dawo mata lokaci guda, tsoro, shakku, da kuma wani sabon rauni.

Ba ta sake tunani ba, ta juya da sauri ta fita daga
akin, zuciyarta na bugawa kamar zata faso kirjinta.

Lokacin da ta fito compound, mai gadi ya zagaya, wannan ne ya ba ta damar fita, ta bu
ofar get
in a hankali, ta le
a taga babu kowa sannan ta fita.

Ta yanki hanya ta cigaba da tafiya ba tareda tasan inda zata dosa ba, hawaye suna zuba a fuskarta ba tare da ta iya tsayar da su ba.

Tana tafiya tana kuka, zuciyarta cike da
acin rai da ciwo.

"Yaya Junaid ya daina sona..." ta furta cikin kuka.

"Yaya Junaid ya daina sona tunda har ya ha
a kai da Umma za su mayar da ni Katsina."
Kowanne tako da takeyi yana cike da ru
ani.

Ba ta san inda zata dosa ba, amma abu
aya da take da tabbaci a kansa shine ba zata koma ba.

Amma a zahiri ba ta san cewa abin da ta gani ba lallai ne ya zama gaskiyar da take tunani ba.

Amma a wannan lokacin, zuciyarta ta riga ta yanke hukunci, hukuncin da zai iya sauya komai.
*******
Junaid ya fito daga bathroom yana goge ruwa a jikinsa, ya samu shiru bata nan bayan kuma yaji shigowarta
akin.

Da farko ya
auka ta shiga wani
aki ne, sai ya fara kiran sunanta, "Rumana!!

Rumana!!!

Didi!!!

Ina kike?"
Amma shiru, yana daure da towel ya fito parlour yana kwala mata kira amma shiru, ya duba ya sake dubawa cikin gidan amma babu ita babu alamarta.

Da sauri ya koma dakin da ya fito ya zura jallabiya da sauri, ya nufi balcony yana dubawa amma bata nan.

Ya sauka compound da sauri ya duba babu ita babu alamarta.

A lokacin ne hankalinsa ya
ara tashi sosai.

Ya juya cikin gaggawa ya nufi mai gadi.

"Ka ga
anwata?" ya tambaya cikin sauri.

Mai gadin ya yi jim sannan ya ce, "A'a amma
azu na ga kamar an bu
ofa.

Na zo na tarar da get
in a bu
Junaid ya waro idanu waje, lumfashinsa ya tsaya na wucin gado, zuciyarsa na bugawa da sauri.

Ya koma ciki da sauri, hannunsa na rawa ya
auki wayarsa yana bu
ewa sai kawai ya ganshi a call log, idanunsa suka sauka akan lambar Umma.

Nan take ya dafe kai saying, "Shit!

Damn it!"
Ya kira lambarta switch off.

Yana fitowa parlour ya hango wayarta akan table, wani abu ya tsinke masa a ciki.

Ya dafe kai saying, "Shikenan ta fita da fushi ba tare da ta fahimci abun da ta gani ba."
Da sauri ya fita waje, ya shiga mota, ya kunna ta cikin tashin hankali.

Ya fice daga gidan da gudu, idanunsa na neman ko da inuwa ce da zata nuna masa inda ta dosa.

Yana jan motar a hankali yana dubawa amma babu ita babu dalilinta, zuciyarsa ta cika da damuwa.

Wayarsa na ta ringing ya duba yaga Umma ce, ya kasa
agawa.

Har dare ya yi sosai yana yawo cikin garin Abuja yana nemanta amma babu ita babu labarinta, babu alamar inda ta dosa.

Jikinsa ya yi sanyi, gajiya ta kama shi, amma zuciyarsa ta fi jikin rauni.

Yayi wujiga-wujiga da shi kamar wanda aka cire daga bakin kura.

Da ya tabbatar cewa lamarin ya zama gaskiya, ya
auki waya cikin sanyin jiki ya kira Umma.

"Rumana daga taga kiran da muka yi da ke, shikenan ta gudu.

Tun
azu nike nemanta ban sameta ba..."
Umma ta dafe kai tana fa
in, "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un...

Junaid ka kasheni..."
Shiru ya ratsa wayar tkafin kiran ya katse.

Daga baya, ya gano Umma tana gidansu da ke Abuja.

Ba tare da
ata lokaci ba, ya nufi can gabansa yana luguden faduwa yayinda yake tafiya zuwa hukunci.

Ya shiga falon kansa a
asa, cike da gajiya da nadama.

Umma ta kalleshi da mugun kallo, muryarta cike da fushi ta ce, "Dagowa zaka yi ka kalleni kuma sai ka nemo min yarinya tunda bani bace na ce ka
aukota ka gudu da ita ba, koda yake ba gudu bane, sata ce!."
Ta matso kusa da shi, ta nunashi ta ce, "Don haka ka nemo yarinya ko kuma in yi kararka akan ka sace min
iya."
Hawaye suka cika idanuwansa.

Ya dur
usa, murya tana rawa ya ce, "Umma... ki yi hakuri... tausayi ne ya sa ni..."
Ta katse shi da sauri, ba tare da jin hujjarsa ba, "Ko meye ne sai ka nemota."
Ya sunkuyar da kai sosai, hawaye na zuba a
asa.

Yana mai jin nauyin abin da ya faru YA FI KARFIN KANSA.

Cikin fushi da tashin hankali Umma take fa
in, "Duk wata damuwarka da kukanka ba zai saka in tausaya maka ba.

Ka je ka nemo min diyata, ko kuma yanzu in dam
aka a hannun hukuma.

Babu inda zan je, zan zauna nan ina jira, yadda ka tafi da ita, haka za ka je ka nemota ka dawo min da ita."
Hankalinsa ya tashi
warai.

Ya fita da sauri yana ta sintiri da kallo ko zai hango ta, amma babu ita, babu ko alamar inda ta nufa.

Yana fita, Umma ta
auki waya ta yi kira.

"Ku nemeta sosai, ka da ku bari ta tsallaka
asar nan," ta fa
a cikin muryar da ke cike da damuwa da tsoro.

Daga can
angaren aka amsa cikin girmamawa, "An gama, ranki ya da
e.

Za mu yi duk mai yiwuwa."
Saboda tashin hankali hannunta har rawa yake, ta ajiye wayar, zuciyarta cike da zafi da fargaba, ba ta san inda Rumana take ba, wannan tunanin ne yake
ara mata damuwa.

A gefe guda, Juanid yana ta yawo cikin garin cikin rudani, ya duba kasuwa, tituna, har ma da wuraren da bai taba zuwa ba amma babu ko alamarta.

Kowane minti da ke wucewa yana
ara masa firgici, zuciyarsa na bugawa da
arfi.
*****
Umma kuwa ba ta zauna lafiya ba.

Duk motsin da ta ji a kusa da gidan sai ta yi zaton labarin dawowar Rumana ne.

Amma shiru kakeji kamar an aiki loma zagayen makoshi.

Wannan shirun yana
ara mata damuwa fiye da yadda kalmomi za su iya bayani.

A karshe, ta sake
aga waya domin tabbatar da cewa an ci gaba da bincike.

Ta ce, "Ku
ara
ari."
Daga
aya
angaren aka tabbatar mata da za a ci ga ba da bincike da gaggawa.

Ta zauna a gefen gado, ta lumshe idanu na
an lokaci.

Amma ko ta lumshe, hoton Rumana bai gushe daga zuciyarta ba yana yawo kamar ba zai tsaya ba.

Duniya ta yi mata duhu a wannan lokaci, sai addu
a kawai take maimaitawa a zuciyarta.
*****
Junaid a wannan daren a mota ya kwana cike da tashin hankali da zullumi, idanuwansa a lumshe amma bacci ya
i zuwa.

Tashin hankali ya yi masa yawa, zuciyarsa na bugawa kamar za ta faso kirjinsa.

Duk lokacin da ya rufe ido, sai hotonta ya bayyanar masa, abun da ya
ara masa firgici.

Haka ya kwana a mota, cikin damuwa da gajiya, yana jin duniya ta yi masa kunci.

Babu ci, babu kwanciyar hankali, sai tunanin 'Ina Rumana take?'
Kwana biyar suka shu
e babu ita, babu ko sawunta.

Ya rame, fuskarsa ta fa
a, idanunsa sun nutse cikin damuwa.

A gefe guda, Umma ba ta sassauta masa ba.

Ta tsaya akan bakanta akan dole sai ya nemo mata yarinya ya maido mata ita Kaduna ko kuma ta ci mutuncinsa.
i take tana maimaita, "Tunda kai ka fita da ita, kaine zata nemo ta.

Ba zan yarda da wata magana ba sai ka dawo min da ita.

Zance
aya zan gane shine inga Rumana a gidan nan, inje in damkata ga ahalinta sannan in fa
a masu yadda aka yi aka kwana a ragaya."
Wannan magana tana masa nauyi fiye da komai.

Ya ji kamar an
aura masa dutse a kirji.

Ya fita hayyacinsa har a wasu lokuta yana magana shi ka
ai, yana bin hanyoyi ba tare da ya san inda zai nufa ba.

Duk inda ya je sai ya ga kamar tana nan, amma idan ya matsa kusa sai yaga babu komai.
Chapter 23 · 0% Book details