← Book details Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 49

Sashe 27

Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta kan ce, "Zaman auren ne bata so shiyasa take nema ta kasheshi ta dawo ta yi zaman zawarci abun uwarta take kitsa mata kenan, Suleiman mutum ne mai fara'a da son mutane." Gaskiya ne abun da ta fa
a Suleiman mutum ne mai fara'a da son mutane, sai dai tana
oye
aya gaskiyar saboda Suleiman mutum ne mai kyauta yana mata hidima.

Daga karshe ta yi nasara, Baffa ya koro Amina tare da ja mata kunne da gargadi, "Amina idan har kika kashe aurenki sai dai ki nemi wani gidan amma ba gidana ba, sai dai ki sauya wasu iyayen domin yafeki zan yi wa duniya koda dangina kika nufa ba zan yafe maki ba."
Wannan furucin ya tada hankalin Nene matu
a, tana son ta yi gyara a kan kuskuren da yake tattare da furucinsa sai dai idan ta yi magana za ta kwabe komai ne musamman da ya kasance a kullum maganar Baabaa Hadiza shine Nene ce take zuga Amina ta kashe aurenta saboda suna ganin ita ce ta kawo mijin.

Nene ta zaunar da Amina ta yi mata nasiha sosai, "Amina dukkanin abun da zai yi maki kiyi hakuri, ki
ara hakuri, ki ci ga ba da hakuri, wata sai labari, a kwana a tashi wata rana gaskiya za ta yi halinta, shi ramin
arya kurarre ne."
Tun daga wannan lokacin komai Suleiman zai yi wa Amina ba ta fa
i sai dai ta bar abun a ranta, tana lura da ya sha abar za ta janye jikinta ta gudu
aki ta kulle sai dai idan tsautsayi ya rutsata, a lokacin ne za ta sha duka, daga baya ya zo yana nadama da kansa yake gasa mata jiki yana kuka yana bata hakuri, yana kuka, "Amina ki yi hakuri kada ki gujeni nima ba laifina ba ne ba, janyo mashi aka yi, SUNE SUKA JANYO MIN."
Sai dai ba a dadewa za su koma gidan jiya, ya kumbura mata jiki, ya kumbura mata fuska, ya
arya mata hannu, ya
arya
aya hannun kuma Baabaa Hadiza tana da labari amma ta kawar da kai saboda hidima da yake mata, dukkanin abun da yake bata ganin laifinsa, kishiyoyinta da mutanen gari suna yawan nusar da ita gaskiya amma sai ta bisu da fitina, "Mutum ba ya da gadonka amma saboda fitina sai ya dauki gadon maganarka ya daura a saman kanshi, ina ce diyar yayana ne don haka dukkanin abun da zan yi kada wata mata ta
ara saka min baki, ehe."
Kishiyarta Marka ta ce, "Mun san diyar yayanki ce shiyasa muke nusar da ke gaskiya, gaskiya
aya ne mahaifinta ya yarda da ke amma sai kika za
i kici amana a kan kudade da Suleiman yake baki."
Baabaa Hadiza ta taso mata da bala'i, "Sai kuma aka ce abun ya shafeki naga baki da alaka da ita."
Marka ta shiga matu
ar al'ajabi na furucin Baabaa Hadiza mutum ana fa
a mashi gaskiya yana gocewa saboda kudi sun rufe mashi idanu, "Gaskiya ne ba zan gaji da fa
a maki ba," ta fa
a a takaice.
*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*
*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*
Taku Har Kullum Aysher Angel (Matar Aliyu)
*ZANE A KAN RUWA*
_(Mai Wahalar Gane Kamanni)_
*NA*
*AYSHER ANGEL*
Page 9
Free Page
*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*
*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*
Baabaa Hadiza ta ta
e baki tana tsikara kallabi akan goshi tana sakace kazar da ta gama ci wadda Suleiman ya kawo mata ta ce, "A'a cewa za ki yi gulma ne bazan gaji da yi ba, magulmaciyar banza, magulmaciyar wofi, aikin banza aikin wofi."
Marka tana jinta amma sai ta za
i ta rabu da ita tunda ta lura da ita gaskiyar ce bata so ba, idan ta biye mata sai abun ya koma tujara.

Ana cikin haka ne ya doketa tana da
aramin ciki cikin ya zube, ya ha
a baki da Baabaa Hadiza suka yi
arya akan sanadin zubewar cikin, tasha wahala ba ka
an ba, sai da ta yanke tsammani da rayuwa.

Shekara
aya a tsakani ta
ara samun wani cikin, har ciki ya girma ta santalo diyarta mace mai kama da shi sak kamar kobo da kobo, yarinya ta ci suna Maryam amma bata san dalilinsa na hana kiran sunan ba saidai suka sakaya suna kiranta da Meemah.

Meemah ta tashi cikin so da kulawa na iyayenta, Suleiman bai daina halin ba, a wasu lokuttan a gaban Meemah yake dukanta, jinjina yarinyar idan taji hayaniya sai ta yi ta kuka, yana yawan tafiya ya yi sati
aya sati biyu amma Amina ba ta damu ba, ba ta kawo komai a ranta ba kasancewar tun da ta aureshi yake tafiye-tafiyen.

Tana son haihuwar
iya mace wannan ya saka ta dauki son duniya ta
aurawa Meemah ta yi mata wanka ta yi mata kwalliya, kaya kala da kala take siya mata, ta gyara mata sumar kanta wacce take da baki da yalwa irin na buzaye.

Zuciya tana son mai kyautata mata idan Amina ta ce ba ta son Suleiman ta yi
arya, tana sonshi, shaye-shayen da ya ke yi ne damuwarta da shi.

Mutum ne mai saukin kai, yana da dadin zama, ba ya da hayaniya sai dai idan yasha abar, shekarata uku tare da shi, a cikin hakane kaddara ta zo mata na mutuwar aure a lokacin ko zama Meemah bata fara ba, mutuwar auren ya juyar da rayuwar Amina daga sama zuwa kasa,
asa zuwa sama.

A lokacin da ta kammala
aramar makarantar sekondire har sakomakonsu ya fito, kwanansa ukku ba ya gari, tana zaune a tsakar gida ya shigo.

Kallo
aya ta yi mashi ta san akwai damuwa wannan ya saka ta kama kanta a tunaninta watakila ya sha abar ne, duk da ba ta ta
a ganinsa a wannan yanayin ba, yana shiga daki ta mi
e ta shiga madafa ta fito ta tarar da ya fita, ya dawo ya
ara shiga
aki ya tattara dukkanin wani abu da ya ke mallakinsa ya fito, da mamaki take kallonsa har ya gotata sai kuma ya dawo ya dauki jikkarta ta makaranta da ke akan tabarma ya fiddo littafi ya yagi takarda ya yi rubutu, ya mi
a mata, da damuwa akan fuskarsa ya ce, "Amina na sakeki saki
aya."
Hawaye suka zubo mata tana kallon takardar da ya ajiye mata, ya juya ya fice ba tare da ya waiwayo ba, Suleiman yana matu
ar sonta ta yarda da hakan domin shine gaskiya, tana mamakin dalilin da ya sa ka ya saketa.

Tana kuka ta shiga
aki ta zaro idanu ganin wayam babu Baby Meemah babu dalilinta, ta tabbatar da a
aki ta barota tana barci, hankalinta ya tashi ta fita makota tana tambaya ko yara sun shigo sun daukota amsar ita ce a'a, tashin hankali wanda ba'a saka masa rana mutanen da suke a waje sun tabbatar mata da cewa sun ga lokacin da Suleiman ya fito da yarinyar ya bayar da ita ri
o ya koma gida ya fito ya amsheta ya wuce.

Kafafaunta suka kasa daukarta, ta yi zaman durshen a zama tana kuka kamar ranta zai fita daga gangar jikinta.

Baabaa Hadiza tana jin abun da ya faru ta suri mayafi ta wuce ruggarsu ta kwashe
arya da tuggu ta sanar da Baffa, ta yi haka ne domin ta fitar da kanta tana gudun tonuwar asirinta na rufeshi da ta yi ya aurar da Amina wa Suleiman da kuma abubuwan da suka faru ta
oye gaskiya ta saka aka tilastawa Amina komawa gidan Suleiman duk da wahala da take sha na dukanta da ya ke yi mata.

Amina ta sha kuka ta gaji, j
ikkarta ta hannu kawai ta dauka ta fita ta nufi Bali ganin zaman nata babu amfani tunda yarinya ce ya riga da ya tafi da ita.

Babu abun da ta ke yi sai kuka tana tafiya tana faduwa tana tashi.

Maganar Baffa ce ta dawo mata na gargadi da ya yi mata a yajin da ta yi na karshe, ta yi turus tana raba idanu, abubuwa suka hade mata, sakinta da Suleiman ya yi, tafiyarsa da diyarsu Maryam wacce ta matu
ar shaku da ita da kuma abun da zata tarar a wajen Baffa.

Hango Baabaa Hadiza tana dawowa daga Bali a mashin ya saka gabanta faduwa ta tabbata zuwa ta yi ta ha
a tuggu da makirci domin ta rufe laifinta akan dukkanin abubuwan da suka faru, Baffa ya yarda da Baabaa Hadiza yana ganin
ar uwarshi ce ba za ta cutar da jininsa ba sai dai abun da bai sani ba shine Baabaa Hadiza ba ta ha
a kudi da komai ba.

A kofar gida Amina ta ci karo da Baffa, muryarta tana rawa ta ce, "Suleiman ya sakeni." Ta sanar da shi duk da tana da tabbaci akan Baabaa Hadiza ta sanar da shi maganar sakin.

Baffa ya murtuke fuska ya ce, "Kin san yadda mu ka yi da ke, tunda kin nuna taurin kai kin kashe auren sai kije ki nemi wasu uwayen, na yafekiwa duniya, babu ni babu ke, ko dangina kika nufa ban yafe ba."
Amina ta fashe da kuka tana
arin sanar da shi gaskiyar abun da ya faru, ya katseta, "Kwara ki juya ki wuce idan ki ka janyo min hankalin mutane zan yi mummunan furuci a kanki."
Tana zubar da hawaye ta juya ta fara tafiya, lokacin wajen karfe sha
aya na safe ne.

Ta yi tafiya sosai har ta gaji sannan ta samu achaba ta hau, ya fiddota bakin titi, "Ina zan saukeki?" Ya tambaya.
Chapter 27 · 0% Book details