← Book details Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 49

Sashe 30

Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Aunty Zainab ta yi sororo tana kallonsa, "Karfe goman daren za ka je gidan mutane, to ba dani ba, maza juya ka koma inda ka fito." Ya sosa
eya ya ce, "Taki cin komai ne, ya kamata inje ko don kada ta kwana da yunwa ko kuma ta kasa barci, bata saba da mutanen ba, a tsorace take, damuwa ta yi mata yawa."
Aunty Zainab ta nuna mashi matakalar bene ta ce, "Babu inda za ka je ita kuma ya rage mata ta
auki kaddara ta zauna da ahalinta lafiya ko kuma taci ba
ar wahala ta zauna da su ta dole ai a irin tarbiyyar da Hajiya Amina ta yi wa Rumana na tabbatar da dole sai an samu damuwa, babu wacce nike ji sai ita wacce aka baiwa aiki a yanzu, tarbiyyar yarinya kamar wannan a yadda ta girma babu kwa
a babu
yara ai dole akwai kabulabe babba, yarinya ta girma amma kun zuba mata idanu ko ruwan zafi bata iya dafawa ba, wani namijin ne zai juri zama da ita da wannan lalacin da kuka koya mata."
Har ya kai matakalar bene sai kuma ya dawo da baya ya ce, "Ayyerh Aunty suya zan sawo." Ta koma ta zauna tana fa
in, "Okay babu damuwa." Har ya fara murna zai je wajen Rumana sai ji ya yi ta kira waya tana sanar da direba ya siyo suya ya kawo masu.

Ta dubeshi ta ce, "Ina ce baka san wajen masu siyar da suya na garin nan ba don haka na hutar da kai fitar, direba zai siyo ya kawo maka idan kuma zaman gidan ne ya isheka kaje compound ka jirashi idan ya kawo sai ka shigo."
Daga haka ta rabu da shi ta kunna TV tana kallon wa'azi ya karaci tsayuwarsa ya fita compound ya ja kujera ya zauna ya kira numbar Rumana.

Daga
aya bangaren ta saka mashi kuka tana fa
in, "Wayyo cikina, yunwa za ta kashe maka ni."
Fuskarsa ta cika da damuwa yana tarabbabin halin da
anwar tasa ta tsinci kanta a ciki na rayuwa da wasu mutane daban a rana tsaka ba tare da ta shiryawa hakan ba.

"Basu baki abinci ba ne?" Ya tambaya.

Daga
aya bangaren ta ta
e baki tana hararen kofa ta ce, "Sun bani nace na koshi kuma ni gaskiya ba zan je ince su bani a yanzu ba."
Yasan za'a rina shiyasa hankalinsa yake tashi akan zamanta a wannan gidan, ba haka ya tsara rayuwar
anwarsa kwaya
aya tilo ba, ya tsara ne sai ya nemo mijin da zai yarda da sharuddansu kafin ya aura mata, wanda zai kula da ita kamar yadda suke bata kulawa saidai kafin aje ko'ina rayuwa ta yi masu juyin waina ta kaita inda yana ji yana gani bata jin dadin zaman amma babu yadda ya iya domin wadanda take tare da su sun fishi iko a kanta.
aya bangaren ya ce, "Ki kaiwa Jidderh wayar." Ta yatsine fuska tana son ta tuna waye Jidderh sai kuma ta tuna ashe macece, ta yatsine fuska ta ce, "Waye Jidderh kuma?" ta yi maganar da murya irin ta shagwa
un yaran da suka tashi basu san komai ba sai abun da ransu yake so.

Ya murmusa ya ce, "Wacce kuke kamanni?" Ta turo baki ta ce, "Cewa zaka yi wannan mai saka dogon hijab kamar matar Malam,
azu fa makota za ta shiga amma haka ta zuba dogon hijabi kamar wata mai takaba,
ar kauye ce nike gaya maka."
Junaid ya ce, "Rumana." Ta rausayar da kai ta ce, "Na'am." Da murya da ke nuni da rarrashi ya ce, "Kije ki kai mata wayar kinji." Ta
an waro idanu tana fa
in, "A wani dalilin zan kai mata wayar ai sai dai tazo da kanta ta amsa, ajina da matsayina ya wuce inje inda take in kai mata waya salon su rainani su
auka
aya nike da su don kawai sun yi garkuwa da ni, kuma gobe tunda safe zan je police station in shigar da korafin kidnapping domin babu makawa kidnapping dina su ka yi."
Juniad ya yi dariya yana jinjina wautarta, "Didi ban da ke da abunki ta ina za ta san ina son magana da ita har tazo ta amshi wayar kuma kinga ba ni da numbarta amma idan kina da ita ki bani." Sarai yasan bata da numbar, ya yi maganar ne domin ya lalla
ata ta yarda ta kai wayar domin ya yi maganin damuwar da yake fuskanta na magance yunwar da ke nukurkusarta.

Ta ta
e baki kamar yana gabanta ta ce, "Numbarta a wayata kuma?

Ni kuwa miye zai saka in ajiye numbarta a wayata, kawai ka ha
ura da maganar da za ku yi."
Ya ce, "A'a, please kin ji, ki je ki bata wayar ki yi domin ni."
Ta ture wayar tana tura kafafu na shagwa
a, "Oh Oh sai dai ta zo da kanta ta amsa." Ya murmusa ya ce, "Didi tawa ni ka
ai kije ki kai mata wayar sai ki dawo abunki zan saka ta maido maki wayar har inda kike kinga shikenan bata rainaki ba."
Sai da ta gama daru kafin ya lalla
ata da
yar ya samu ta fita ta sauka parlour ta samesu suna kallon wa'azi, babu wanda ta kula ta isa inda Jidderh take ta dungure mata waya ta juya ta haura sama ba tare da ta ce komai ba, suka bita da kallo.

Yadda ta shigo falon da gadara da yadda ta fita da gadara ya saka jikin Ammi ya yi sanyi, tabbas akwai aiki babba a gabanta na yi wa yarinyar irin tarbiyyar da yaranta suka tashi da shi, icce tun yana danye ake tankwarashi, a lamarin Rumana iccen ya riga ya giga don haka abun ba mai sauki ba ne ba.

Jidderh ta kalli wayar da aka dungure mata taga kamar kira ne da aka yi saving numbar da MY LIFELINE
ta saka hannu ta
auki wayar ta kanga a kunne tana mai fa
in, "Barka da dare.

Ina wuni?"
Daga
aya bangaren ya ce, "Lafiya lau Jidderh.

Ya gida yasu Ammi?"
Ta amsa da, "Suna nan lafiya lau."
Junaid ya ja fasali sannan ya ce, "Junaid ne yayan Rumana wanda ya daukoki daga daji da kika gudo daga wajen masu garkuwa da mutane."
Jidderh ta ce, "Na gane, na gode sosai da taimakona da kayi min, a wancen lokacin ru
anin kirana da ka yi rinkayi da Rumana ya saka a lokacin ban samu zarafin yi maka godiya ba."
Ya ce, "Babu komai, dama taimako nike son kiyi min."
Ta yi jim tana tunanin wani taimako kuma sai kuma ta ce, "Ina jinka yaya Junaid, Allah yasa bai fi karfina ba."
Ya ji dadin kiransa da ta yi yaya Junaid da kuma girma da ta bashi, ya tuna da mutuniyarsa Rumana wacce idan ta
arar ta tashi gatsarai take kiran sunansa kuma idan ya yi korafi ta hau fushi tana kukan babu gaira babu dalili, Rumana akwai daru, shagwa
iyar kanwarsa mai abun ban dariya.
*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*
*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*
Taku Har Kullum Aysher Angel (Matar Aliyu)
*ZANE A KAN RUWA*
_(Mai Wahalar Gane Kamanni)_
*NA*
*AYSHER ANGEL*
Page 10
Free Page
*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*
*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*
Junaid ya ce, "Jidderh please ki zuba abinci ki kai mata dakinta kada ta kwana da yunwa."
Jidderh ta yi jim sai kuma ta ce, "Amma da bakinta ta ce ba za ta ci ba har tambayarta nayi idan akwai abun da take so in dafa mata amma sai ta kada baki ta ce ita tafi karfin taci abun da aka girka a wannan akurkin kajin."
Yasan za'a runa, an ari zanen mahaukaciya ya
ata aikuwa dole a siyo mata irinsa idan anyi sa'a ta amsa sai kuma ta kahe ta ce sam bata san zancen ba sai dai a nemo mata nata a nan kuwa aiki ya samu wanda ya yi gigin aron zanin.
Chapter 30 · 0% Book details