← Book details Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 49

Sashe 14

Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta fito balcony ta ja kujera ta zauna tana turo baki tana kwafa idan ta tuna abun da Al'ameen ya yi mata a garin Katsina sai ta ji kamar ta fasa ihu, tana ta kwafa ita kadai har Umma ta lura ta tambaya, "Miye?"
Zuciya ta kawo mata wuya tabbacin yadda abun yake kona mata rai, ta yi subul da baka tace, "Da mi yake takama da har zai yi min magana da gadara," ta
arashe maganar da karaji.

"Waye?" Umma ta tambaya.

Rumana ta yi kwafa a karo na adadin da ita kanta ba ta sani ba sannan ta ce, "Wannan saurayin wanda na hadu da shi a garin katsina, dukkanin lokacin da na tuna abun da ya yi min sai in ji ban iya kyalewa, har yana da karfin halin da zai iya duban tsabar idona ya yi min magana da gadara yana cewa in durkusa a kan kafafuna in rokeshi."
Umma ta daka mata tsawa, "Ke!

Ba na hanaki magana a kan dukkanin abun da ya shafi wannan abun ba." Rumana ta yi baya da sauri ta ce, "Amma ya raina min hankali ne, ya yi min magana da gadara." Umma ta fusata ta daka mata tsawa a karo na biyu ta ce, "Ke wacece da ba za'a raina maki hankali ba, ke wacece da ba za'ayi maki magana da gadara ba, kika wuce sakarai, banza, wofi.

Idan kika
ara maganar da ta danganci abun da ya faru a katsina sai na zaneki."
Rumana ta yi rau-rau da idanu kamar za ta yi kuka, Junaid ya fito yasha gayu ya kure kyau yana baza kamshi, yana daura wristwatch ya ce, "Umma, na tafi." Umma ta ce, "Allah ya kiyaye hanya." Ya maida dubansa akan Rumana dake faman ta
e baki ji take kiris ta fashe da kuka, ya ce, "Waye ya ta
a min ke?"
Za ta yi magana, Umma ta daka mata tsawa a karo na ukku ta ce, "Ki yi min shiru a nan tun ban mareki ba, sai in yi kwallo da ke a wajen nan." Junaid ya ce, "Subhanallahi, mari kuma?" Umma ta fusata ta ce, "Ehh ko kana da magana ne, yanzu in fara buga misali a kumatunka ta gani ganin idanunta."
Junaid ya ware idanu, lallai abun babba ne, Umma ta murtuke fuska ta ce, "Ta
ara yi min maganar ta gani idan ban rufe kofa ba nayi mata
an banzan duka na barta a kwance ba, mu gani idan kai da ta ke takama da kai idan ka isa ka yi magana ka gani idan ban ha
a da kai nayi maku shegen duka ba."
Junaid ya yi shiru domin abun ya fi karfinsa, Rumana tayi rau-rau da idanu ta ce, "Yaa Junaid zan bi ka mu tafi tare tun kafin ka barni da Umma ta rufeni da duka tunda ta daina sona, magana ka
an sai ta ce za ta yi min duka." Junaid ya mi
a mata hannu ya ce, "Ta so mu je dama wajen Leeserh zan je."
Rumana ta warware mayafi dake a saman kanta ta yi lullubi da shi, ya kama hannunta suka fita zuwa parking space, yana tuki yayinda ta kwantar da bayanta a kujera ta lumshe idanu ta yi shiru tana kitsa yadda za ta rama abun da Al'ameen ya yi mata, har suka
arasa gidan ba ta sani ba tana can ta lula a duniyar tunani tana tukfa da warwara, sai da ya ta
ota sannan tasan sun zo gidan, ta
alle murfin motar ta fita ta zauna a kan bayan motar tana buga game, ya tsaya kusa da ita, yana leken wayar yana mata hira suna dariya.

Katon gida ne sosai, wata kyakykyawar budurwa
ar kimanin shekaru ashirin da hudu ta fito daga cikin gidan, kalar chocolate ce, doguwa mai kyawun jiki samfurin slender, tana sanye da umbrella gown, ta kashe
aurin kallabi, mayafinta a kan kafa
a, tana tafiya tana baza kamshi da kyakykyawan murmushi akan fuskarta, khaleesat kenan wacce Junaid zai aura.

Junaid ya juya tare da kafeta da na mujiyarsa yana kallonta ba ya koda kyaftawa da murmushi kwance akan fuskarsa, yana kallonta tana
ara yi mashi kyau a idanu har ta
araso tana fa
in, "Rumana
ar gatan yayanta game kike yi?"
Rumana ta
ago ta ce, "Ehh Aunty Leeserh, da girman kujerarki amaryar next month." Daga haka ta maida dubanta akan majigin wayarta.

Leeserh ta ce, "Yau kin yi mashi rakiya kenan?"
Hankalinta a kan game da take bugawa ta gya
a kanta tana fa
in, "Kinga na manta ban gaishe da ke ba.

Ina wuni?" Leeserh ta amsa da, "Lafiya lau." Junaid da neman magana ya ce, "Amma da muka tashi da safe ni baki gaidani ba, kuma da sha biyu ya yi baki gaidani ba."
Rumana ta
ago ta ware manyan idanunta a kansa na tsayin lokaci sannan ta ce, "To ina kwana?

Ina wuni?" Daga haka bata
ara magana ba, ya lakuci hancinta yana fa
in, "Yauwa ta wajena, Didin yaya Junaid, kamota-kamota."
Leeserh ta ce, "Ki shiga wurin Hajjo kusha hirar yaushe gamo." Rumana ta girgiza kanta ta ce, "Kai, a'a gaskiya, don ba ni da gaskiya, ranar ta yi min fa
a a kan saka hijab kuma ban saka ba, ku tafi abunku ina nan ina buga game abuna."
Khaleesat ta girgiza kanta ta ce, "A'a muje." Ta wuce lambun gidan, Junaid ya kama hannun Rumana suka bi bayanta.

A nesa da su ta ja kujera ta zauna, Allah ya kamata Aunty Hajjo ta fito ta ganta aikuwa tasha fa
an da sai ta yi dana sanin biyoshi da ta yi.

Aunty Hajjo ta murtu
e fuskarta ta ce, "Na ce ina hijabinki, a mota kika mantoshi ko kuma tun daga gida kika fito haka kidigai-kidigai."
Rumana babu bakin magana saida idanu ta yi tsuru-tsuru kamar ka ce kyit ta gudu, Aunty Hajjo ta daka mata tsawa ta ce, "Ba da ke nike magana ba, ko nima gadarar taki zaki nuna min."
Rumana ta ce, "Uhmm."
Aunty Hajjo ta tusata a gaba har falo tana tambayar ba'asi fitowar da tayi babu hijab babu mayafi.

Rumana ta yi rau-rau da idanu tana fa
in, "Ayyerh Aunty Hajjo ki yi ha
uri." Aunty Hajjo ta kwalawa Farida kira ta ce, "Farida zo ki
auko min dorina in nuna mata na fi ta taurin kai."
Rumana tana jin zancen bulala ta mi
e zata gudu, Hajjo ta ce, "Dawo ki zauna ko kuma kina fita in hada har da shi Junaid din da yake daure maki kugu in zanneku."
Jin za'a zane Junaid Rumana ta dawo ta zauna tayi tsuru-tsuru da idanu ta ce, "Ayyerh ban dinka ba, waccen da kika bayar ya yi min yawa na baiwa mai aikinmu."
Aunty Hajjo ta cika da al'ajabi, "Saboda ban isa in sakaki kiyi ba shiyasa kika dauki hijaban kika bayar saboda ki nuna min ban isa dake ba."
Rumana ido ya raina fata ganin Farida ta kawo dorina, gashi dai za ta ci duka ga shi babu mai cetonta.

Tana yarfe hannuwa tana hawaye ta ce, "Ayyerh na tuba bazan
ara yawo da
aramin mayafi ba."
Aunty Hajjo ta ce, "Ni dake shege ka fasa
an halak sai yanka tunda har ita Aminar ba zata iya maki tarbiyyar ba sai ni inyi maki da kaina."
A LAMBU
Tunda Aunty Hajjo ta shiga da Rumana ciki hankalin Junaid kacokam ya koma a can, har Leeserh ta lura ta ce, "Ba fa dukanta za ta yi ba." Ya ce, "Ba dukan ba, idan ta sakata kuka akwai daru." Leeserh ta gumtse dariyar dake neman kufce mata na yadda yayi tsuru-tsuru da idanu kamar shine aka tutsuye, ta ce, "Ko muje in rakaki kayi rescuing dinta." Ya ce, "A'a fa, ranar da na shiga tasowa tayi da bulalarta a hannu zata ha
a da ni ta zanemu."
Leeserh ta fashe da dariya tana fa
in, "Kai Hajiya Hajjo tana shigar maku hanci ta kudundune kuma babu yadda kuka iya da ita, duk garin nan ita da Hajiya Kaka ne kawai suke ta
a Didi a zauna lafiya ba'a yi wallahi tallahi ba."
Ya yi yake ya ce, "To ya muka iya?

Fa
an da ya fi karfinmu ai dole muke mayar da shi wasa." Ta gyara zama ta ce, "Amma sun fi ku gaskiya ya kamata ana kwa
arta ba wai komai ta yi a mayar da shi daidai ba."
Junaid ya
ata fuska ya ce, "Yarinya ce fa, duka-duka nawa take." Sanin ba amsar shawarar zaiyi ba sai ta ce, "Haka ne kuma, da wannan don wannan."
Daga haka ta sauya hirar tun basuyi bara-baran akan lamarin Rumana ba.

A PARLOUR
Aunty Hajjo ta juya ta mayar da dubanta inda Farida take ta ce, "Farida
auko min sabbin hijaban da aka dinko maki." Rumana tana jin haka ta yi karaf ta ce, "Zan yi wa yaya Junaid magana sai a dinka min akan hanyarmu ta komawa gida."
Ita a dole ta yi mata dubara don kada ta amshi hijabin a yi mata fa
an ba ta sanya ba, Aunty Hajjo ta yi mata banza.
*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*
*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*
Taku Har Kullum Aysher Angel (Matar Aliyu)
*ZANE A KAN RUWA*
_(Mai Wahalar Gane Kamanni)_
*NA*
*AYSHER ANGEL*
Page 5
Free Page
*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*
*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*
Babu jimawa Farida ta kawo leather cike da hijabai wadanda yawansu zai kai goma, Rumana ta amsa tana zuba godiyar dole.
Chapter 14 · 0% Book details