← Book details Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 49

Sashe 12

Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta samu Ammi da maganar tare da sanar da ita shawarar da ta yanke akan maganar, Ammi ta yi jim tana nazarin maganganun Jidderh sannan ta ce, "To shikenan amma ki je ki samu mahaifinku ki ji ra'ayinsa tukunna."
Jidderh ta gya
a kai, "Yana Ina?" Ta tambaya.

Ammi ta ce, "Yana dakin karatu." Jidderh ta mike zuwa study room inda ta sameshi yana karanta jarida, ya fa
a fuskarsa da murmurshi ya ce, "Daughter."
Ta zauna tana mai gaishe da shi ta dora da fa
in, "Abbi barka da warhaka." Abbi ya ce, "Barkan mu." Sai da ta yi jim sannan ta ce, "Abbi dama akan wannan yarinyar ne wacce aka kawo a madadina a watan da ya wuce."
Abbi ya ajiye jaridar da ke a hannunsa ya maida hankalinsa kacokam a kanta ya ce, "Miye a kanta?" Ta gyara zama ta ce, "Kamanni da mu ke yi da ita abun dubawa ne, ina ji a jikina kamar za ta iya kasancewa tsanin da za mu bi mu hadu da ahalinka wanda saboda nemansu ne ka baro Morocco ka shigo Nigeria."
Abbi ya lumfasa, shima abun yana ci mashi tuwo a kworya sai dai ba ya da hanyar nemanta shiyasa bai tada maganar ba.

"Kin tuna gidan da aka kaiki ne?" Ya tambaya da saka ran watakila ta tuna gidan da aka kaita ne shiyasa ta tado maganar.

Jidderh ta girgiza kanta tabbacin ba ta tuna ba, ya ce, "Idan haka ne babu abun da ya rage mamu da zamu dauka a matsayin madafa da za mu yi amfani da shi domin cimmata."
Jidderh ta ce, "Ba zan iya gane gidan ba saboda lokacin da aka kaini bana a cikin hayyacina sannan lokacin da na fito ina a ru
e, amma Ammi ta ce min Uncle Al'ameen ya ce ya ta
a haduwa da yarinyar tun kafin faruwar wannan lamarin, ina so in je in sameshi in gani idan zan iya samun karin haske daga gareshi."
Abbi ya yi shiru na tsayin lokaci kafin daga bisani ya ce, "Babu damuwa ki je, Allah ya yi maki albarka, yadda kike
arin ganin kin faranta min kema Allah ya baki wadanda za su faranta maki." Jidderh ta amsa da, "Amin." Tana mai jin
in wannan addu'a da mahaifinta ya yi mata.
ewa ta yi ta koma dakinta ta yi wanka ta shirya cikin atamfa dinkin riga da zane, ta tattare gashinta ta yi mashi gammo, ta
aura kallabi, ta zura doguwar hijab har tana sharar kasa, ta sauko parlour ta samu Ammi tana kallon wa'azi.

Ta ce, "Ammi zan wuce." Ammi ta ce, "Amma direba ba ya nan." Jidderh ta ce, "Babu damuwa sai in hau kekenapep." Ammi ta yi jim sai kuma ta ce, "Alright, Allah ya kiyaye hanya.

Ki gaida min da su Hajiya." Jidderh ta ce, "Za su ji."
Tana fita bakin titi ta samu kekenapep ya sauketa a wani katon gida, ta wuce cikin gidan tana tafiya a nutse yayinda dogon hijab da ke a jikinta yake sharar kasa.

Bangare biyar ne a katon gidan, ta shiga bangaren da ke a farko, wata tsohuwa ta samu a zaune a cikin katon falon tana kallon wa'azi, Jidderh ta shiga da sallama, ta zauna tana mai gaishe da ita, "Hajiya, Ina kwana?" Hajiya Attuwa ta amsa da, "Lafiya lau.

Ya mutan gidan?" Jidderh ta ce, "Suna lafiya lau.

Suna gaidaku."
"Kin shiga sauran sassan kuwa?" Hajiya ta tambaya.

Jidderh ta girgiza kanta ta ce, "A'a, ina so in fara ganin uncle Al'ameen tukunna sai shi shiga gaishe-gaishen ya biyo baya, wai ina yake ne tunda na shigo ban ji duriyarsa ba."
"Yana a haraba ta
aya bangaren," Hajiya ta sanar da ita.

Jidderh ta ajiye jikkarta ta fita compound ta sameshi zaune a bayan motarsa hankalinsa kacokam akan wayarsa yana latsawa, ta
arasa tare da dafa motar, ya dago da murmushi akan fuskarsa ya ce, "Hauwa kuluwa inji Alhaji, yau
aya na ari bakinsa na ci masa albasa na
ana sunan matar mamman."
A tare su ka yi dariya, ya ce, "Kin ce kina son ganina.

Ta samu ne?" Ya karashe maganar da barkwanci.

Ta rausayar da kanta ta ce, "A'a na zo gaisuwa ne da kuma neman iri." Ya
an ka
lleta ya ce, "Na amshi gaisuwar saidai irin ne ban sani ba, na gya
a kike so ko masara ko na maiwa."
Ta yi dariya ta ce, "Akan Rumana ne." Ya maimaita sunan da mamaki yana
arin tuna wacce take nufi.

Ganin bai gane ba ta ce, "Wacce Yaa Imran ya kawo gida yana zaton ni ce." Tunawa da ita ya saka shi sakin murmushi da bai san dalilinsa ba ya ce, "Mi ye a kanta?" Jidderh ta ce, "Ina tunanin watakila tana da alaka da ahalin Abbi shiyasa nike kamanni da ita kamar kobo da kobo.

Kuma na samu labari a wajen Ammi cewa ka hadu da ita tun kafin wannan lamarin ya faru."
Al'ameen ya gya
a kansa ya ce, "Tabbas hakane babu shakka sai dai babu wani abu da na sani a kanta da ya wuce wannan.

Idan akwai bai wuce kasancewarta diyar masu kudi na sosai da sosai ba domin har matakan tsaro take tare da su a lokacin da na ganta sannan tana da girman kai da gadara."
Jidderh ta ce, "Alright amma please idan ka tuna wani abu ka kirani." Ya ce, "Babu damuwa matar mamman."
Dariya ya ba ta ta ce, "To shikenan kawun matar mamman.

Ka gaida min da Fatima." Ya ce, "Za ta ji." Ta juya ta ce, "Na wuce sauran sassan in gaidasu tun kafin in koma ciki Hajiya ta koroni da mita."
A tare su ka yi dariya, tana fa
in, "Wannan tsohuwar rigima ne da ita, daga shigata ko ruwa ba ta ba ni ba ta fara tambayata idan na shiga na gaishe da su." Ta nufi sashen da ke kusa da wannan.

Ya bi ta da kallo yana murmushi yana son tuna wani banbanci na kamanni dake tsakaninta da waccen yarinyar saidai babu wani banbanci.

Banbancin da yake tsakaninta da waccen na shigar suruta a bayyane yake, Jidderh ta kasance ma'abociyar saka dogon hijab har yana sharar
asa yayinda waccen mayafi kansa akan kafa
a take daurashi a yadda da shi da babu duk
aya.

Sai da marece sannan ta fara haramar komawa gida ta yi sa'a Uncle Al'ameen yana nan ya sauketa har gida, ya shiga suka gaisa da Ammi, ta ce, "Ka tsaya ka ci abinci." Yace, "A'a na koshi." Jidderh ta ce, "Ko a zuba maka a cooler?" Ya ce, "To shikenan, shukran Matar Mamman." Ya yi wa Ammi sallama ya fita zuwa motarsa.

Har ta mota ta kai mashi cooler ta ce, "A gaida min da Fatima." Ya ce, "Za ta ji." Ta juya ta koma ciki yayinda ya
anna horn mai guard ya wangame mashi ya
anna motar waje.
*******
A BANGAREN RUMANA
Tun daga ta koma kaduna ta
asa mantawa da abun da Al'ameen ya yi mata ba, musamman inda yake cewa ta durkusa akan kafafunta ta rokeshi idan ta tuna ji take kamar ta fasa ihu, 'How dare him' har ita zai ce ta durkusa ta rokeshi.

Bayan tarin dukiya da gata da take da shi amma har ya dubeta ya yi mata wannan maganar cike da gadara, ji take ba za ta iya hakura ba har sai ta rama sai dai tana tsoron tada maganar tana gudun fushin Umma ya sauka a kanta.

Tsaye take a gaban iccen flower tana tsalle tana son ta tsinko furen amma ta
asa kasancewar tsayinta bai kai ba, Junaid ya duba parlour bai ganta ba ya fito compound nemanta ya hangota, ya yi murmushi yana tako sadaf-sadaf ya nufo inda take kamshinsa ne ya sanar da ita zuwansa sai dai ba ta yi yunkurin
ata mashi bazatar da ya yi nufin ya yi mata ba.

Ya kama kugunta ya yi sama da ita ta tsinko furen, ya sauketa yana sakar mata murmushi ya ce, "Didi mi za'ayi da fure?" Ta kalleshi sanye yake da yard mai tsa
a dinkin zamani fitet wanda ya zauna a jikinsa ya yi mashi kyau, yana baza kamshin designer perfumes, ta mi
a mashi furen ta ce, "Ka yi kyau."
Ya amsa ya dora akan hancinsa yana shakar kamshinsa ya lumshe idanu ya bude ya ce, "Kkoch gomawo." (Na gode da furen flower).

Ta ware idanu ta ce, "Yau kuma yaren Korea ka koma." Ya gya
a kai yana gyara mata gashinta da yake reto yana rufe mata fuska.

"Eodi ga?" (Ina zaka je).
an kalleta ta ce, "Hala baka gane ba." Ya dai yi shiru yana murmushi.

Ta gya
a kai tana gyara mashi hular dara dake a saman kanshi.

"Ina zaka je?" Ta tambaya da yaren hausa a wannan karon.
Chapter 12 · 0% Book details