← Book details Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 49

Sashe 39

Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kin koma sukuku da ke, idan aka yi magana sai ki ce baki da lafiya alhali
arya ne lafiyarki lau.

Idan wani abun ne yake damunki ki fito ki fadawa mutane, ba wai ki ware kanki gefe kina kunci ba."
an yi shiru, sannan ya ci ga ba, "Ke ce ya kamata ki shige gaba a hidimar nan, kece
anwata kwaya daya tilo amma sai kika koma gefe kika nade hannuwa.

Idan aka yi magana sai ki fake da 'ba ki da lafiya'."
Rumana ta yi shiru kalamansa sun shiga zuciyarta fiye da yadda ta zata.

Idanuwanta suka cika da hawaye.

Hawaye na zubowa daga idanunta ta ce, "Why are you doing this to me?

Na ce ban da lafiya ka
aryatani."
Da karfi ya ce, "
arya kike lafiyarki
alau.

Yarinyar nan Jidderh
anwarki, saboda ke ta zo bikin nan amma sai kika watsar da ita, kika watsar da bikin.

Saidai da Farida na ha
ata, jiya a gidan Hajjo ta kwana wajen Farida wanda ko na rantse ba zanyi kaffara ba akan cewa ba ki san a can ta kwana ba."
Ta sauke kai kamar yana a gabanta ta ce, "To ka yi ha
uri."
Junaid ya girgiza kai zuciyarsa har lokacin cike take da takaici, "Ha
urin shi ne ki shirya mu wuce dinner, kafarki kafata."
Ta yi shiru na
an lokaci kafin daga bisani ta ce, "Gashi kuma ban shirya tafiya cikin gungun maza ba."
Junaid ya ware idanu cikin mamaki da
an haushi ya ce, "Kato kike son ki ce min?"
Ta girgiza kai da sauri, cikin sauri ta gyara maganarta da fa
in, "Ba haka na ce ba, anyway tunda ba za ka je ba ka hutar da mutane, sai ka kira ka ce na ce ba zan je ba don haka kaima baka je ba."
Ba tare da jira amsa ba, ta tsinke kiran.

Junaid ya tsaya yana kallon wayar zuciyarsa gaurayen da jin haushi da mamaki da kuma wani irin nauyi da ba ya iya fassara shi.
******
Rumana ta dungure wayar na mintina biyar kafin daga bisani ta kira lambar Abdulmajeed ana picking ta ce, "Yaya Abdulmajeed... ya aka yi?

Ya shirya ko har yanzu taurin kan yake nunawa?"
Muryar Junaid ta ji yana fa
in, "Ina nan, ban shirya ba na fiki taurin kai."
Ta sassauta murya ta ce, "To Allah ya huci zuciyar ranka ya da
e... yanzu zan shirya."
Junaid ya ce, "Da ya fiye maki, haka kawai kina neman mayar min da aure sansanin damuwa ba tareda kwakwakwaran dalili ba."
Da sauri ta ce, "To Allah ya bada ha
uri." Ta tsinke kiran.

Ta mi
e ta rage kayan dake jikinta ta
aura towel ta wuce bathroom, ta jima a cikin bathroom
in fiye da yadda ta saba, ruwan dake zuba yana saukar mata da nauyin dake zuciyarta, tana
arin wanke damuwar da ta kasa fassarawa.

Bayan ta gama, ta fito a sanyaye, ta tsaya gaban madubi na lokaci tana kallon kanta, tana son gano wani abu a cikin idanuwanta amma ta kasa.

Ta za
aya daga cikin dinkunan bikin da ta yi, leshi ne mai kyau da aka yi mata
inkin doguwar riga wacce ta zauna a jikinta tamkar an halicceta ne domin ita.

Launin leshin ya fito da kyawunta, amma duk da haka, babu walwala a fuskarta.

Ta yane kanta da kallabi sannan ta
ora mayafi a saman kafadunta, saida ta tabbata komai ya yi dai-dai kafin ta juya ta fita.

Ba ta bi ta babbar
ofa ba, ta bi ta backdoor kamar yadda ta saba yi a
an kwanakin nan musamman idan tana son gujewa hayaniya ko tambayoyi.

Gidan cike yake da mutane da shirye-shiryen biki, yayinda ita kuma a lokacin babu abun da zuciyarta take bu
ata da ya wuce nutsuwa.

Ta isa parking space, ta bu
aya daga cikin motocinta wacce bata ta
a amfani da ita ba, ta shiga ta ja
ofar, ta kunna motar, amma kafin ta jata sai da ta jingina bayanta da kujera ta lumshe idanu na
an da
u, tana jan lumfashi a hankali.

Sai kuma ta bu
e idanunta, taja motar ta fice daga harabar gidan ta nufi hanyar gidan Aunty Hajjo, zuciyarta cike da tunane-tunane iri-iri, wasu da take
arin mantawa, da wasu kuma da suka
i barinta.

Akan hanyarta ta bu
e gilashin motar iska mai sanyi yana bugawa a fuskarta amma hakan bai rage mata nauyin da take ji a zuciya ba.

Duk da haka akwai wani
aramin fata a zuciyarta cewa watakila zuwa gidan Aunty Hajjo zai ba ta nutsuwar da take nema.

Tana tu
i cikin nutsuwa duk da cunkoson tunanin da ke ranta, ta
auki wayarta ta kira Abdulmajeed.

Bai jima ba aka
aga kiran.

Ta ce, "Waye akan layi?"
Junaid ya ce, "Nine."
Ta murmusa ta ce, "To na shirya yanzu haka ina akan hanyata ta zuwa gidan Anti Hajjo.

Ni mace ce don haka tawagar mata zan bi, ba ta maza ba."
Kafin ta
ara cewa wani abu, ya tsinke kiran, bata kawo komai a ranta ba kasancewar hankalinta baki
aya yana akan tu
in da ta ke yi.

Babu jimawa wayarta ta sake haskawa video call ne daga lambar Yaya Junaid.

Ta kalli wayar dake akan phone mount sannan ta
aga kiran, ko kallon fuskar wayar bata yi sosai ba, idanuwanta suna manne akan titi, hannuwanta ri
e sitiyari da
arfi tana driving.

A can ta
ayan
angaren, Junaid yana
arin kallon cikin idanunta amma sam hankalinta baya a kansa, idanuwansa cike da wani irin yanayi da ba zai iya fassara ba, ya ce, "Kinyi kyau, Didi, Didin Junaid."
Ba tare da ta karkata hankalinta daga titi ba, ta amsa da, "Na gode.

Tunda na shirya kaima ka daina taurin kai ka shirya ka tafi ayi shagalin bikinka tare da kai."
Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Didi sai yanzu na san za'ayi biki da za ki je."
Daga nan fuskarsa ta
an murtuke, ya
ara da cewa, "Me kike nufi da tafowa ke ka
ai?

Ko har yanzu kina kan bakanki na cewa zakije dinner tareda katon gardi ba?"
Ta girgiza kai har lokacin idanuwanta suna akan hanya ta ce, "A
a, ban ce wa kowa kato ba.

Kawai dai bikin mata daban ne da na maza, don haka a matsayina na mace sai na tafi
angaren mata."
Ya na
e hannuwa ya "Idan kuma na ce ba zan je Dinner
in ba fa?"
Ta murmusa ta ce, "Sai in je in wakilce ka.

Didi ba bakuwar tsanani ba ce ba."
Bai
ara cewa komai ba, har sai da ta isa gidan, san
nan ya tsinke kiran.

Ta fito daga motar tana gyara mayafinta cikin nutsuwa, ta nufi ciki zuwa
angaren da amarya Khaleseert take.

A hanya ta ha
u da Jidderh tare da Farida.

Ta murmusa ta ce, "
an mata, adon gari."
Farida ta ce, "Sai yau ake ganinki?"
Ta saki murmushi mai
auke da gajiya ta ce, "Sai yau na samu sau
i shi yasa."
Ta juya ta dubi Jidderh da
an zolaya a muryarta ta ce, "Shine kikayi mamu kaura aka barni ni ka
ai da hayaniyar
an biki?"
Jidderh ta
aga kafa
a ta ce, "To rashin lafiyar da kike kirawa kanki ne ban gane kansa ba, shi yasa na tattaro kayana na taho nan domin in cinye bikin sosai."
Ta ce, "To ai shikenan," sannan ta wuce.

Ta wuce wajen amarya Khaleseert, Leeserh tana ganinta ta fa
a da murmushi, ta ce, "Ga manyan ba
i, ga amara kirjin biki."
Ji tayi kunya ta kamata, ta sunkuyar da kai ta ce, "Rashin lafiya ne ya kawo min tsaiko, yanzu ma yaya Junaid ne ya tattagoni."
Leeserh ta ce, "Aiko ya kyauta da ya saka kika zo.

Mutane suna ta tambayarki, wasu idan suka yi wa Jidderh magana ta ce bata ganesu ba, sai suce kece kike masu wulakancin naki."
Rumana ta girgiza kai ta ce, "Ayyerh, to Allah ya ba su ha
uri, ya matsa na zo kuma na ga amarya don haka yanzu dakin Aunty Hajjo zan nufa in yi kwanciyata.

Ai dai bazai bini har can ba."
Ba tare da ta tsaya bata lokaci ba, ta juya ta nufi
angaren Aunty Hajjo.

Da ta shiga parlour, ta samu mata
an biki zaune suna hira, ta gaishesu sannan ta wuce ciki, zuwa bedroom
A can ta tarar da Aunty Hajjo tare da Hajiya Maamaah zaune.

Ta gaishesu, suka amsa da kulawa.

Aunty Hajjo ta ce, "Ya jikin?"
Rumana ta langwa
e kamar wacce take fama da ciwon gaske, ta ce, "Da sau
i... yanzu ma yaya Junaid ne ya fatattakoni wai dole in je dinner.

Shine na gudu nan, in sha barci a dakin Aunty Hajjonmu."
Aunty Hajjo ta yi murmushi ta ce, "Yi kwanciyarki diyata, Allah ya
ara lafiya."
Rumana ta cire mayafinta ta ajiye, ta sauke handbag
inta gefe, tabi lafiyar gado ta lumshe idanu, babu
ata lokaci bacci yayi awon gaba da ita.

Can cikin barci, ta ji ana jijjigata, ta bu
e idanu a kasalance, tana
arin tantance inda take, idanunta suka sauka a kansa, ta warosu da mamaki ganin Junaid tsaye a gabanta.

Da sauri ta tashi zaune tana dube-dube, amma babu Hajiya Maamaah, babu Aunty Hajjo.

Ta sake kallonsa da mamaki ta ce, "Ta ya ka shigo?"
aga gira da murmushin gefen baki ya ce, "Ta yadda kika shigo."
Ta dafe kai tana fa
in, "Nazo nan ma ban tsira ba.

Allah tunda nike ban ta
a ganin marar kunyar ango kamar wannan dake gabana ba, ka taho har dakin surukarka."
Ya dage kafa
a ya ce, "To ai Aunty Hajjo ce.

Idan nayi laifi tsaf zata zaneni kuma babu mai tambayar dalili."
Ta jinjina kai da yar dariya tace, "Haka ne."
Ya nuna doguwar rigar da ke ajiye a kan gado ya ce, "Ki watsa ruwa ki shirya mu wuce."
Ta ce, "To shikenan, kaje ina zuwa."
Ya girgiza kai da sauri, "Ai kafarki kafata."
Ta sake waro idanu, "Kana nufin a gabanka zan shirya?"
Ya jinjina kai, "Eh, ai ba yau kika fara shiri a gabana ba.
Chapter 39 · 0% Book details