← Book details Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 49

Sashe 19

Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har mintina goma sha biyar suka shu
e babu Rumana babu Junaid, Umma tana kiran lambar Junaid ba ya
agawa ta mi
e ta haura sama ta samu wayam babu Junaid babu Rumana.

Ta fita ta samu mai guard inda ya tabbatar mata da sun fita, hankalinta ya tashi tana kiran lambarsa ba ya
agawa, ta dafe kanta ta rasa wani tunanin za ta yi, shin mi ya sa suka yi haka bayan ita dasu sun san da cewa shure-shure ba ya hana mutuwa haka zalika ranar wanka ba'a
oyon cibi.

Ta koma falon inda Ammi da Abbi suke, ta rasa abun da za ta ce masu daga baya ta karfafi kanta ta ce, "Ku yi ha
uri amma yaran nan sun tafi kuma ina kyautata zaton London za su wuce, watakila ku ga kamar na yi amai na lashe sai dai lamarin ba haka yake ba, kamar yadda na fa
a a
azu Rumana diyarku ce, tabbas haka zancen yake, Rumana diyarku ce, kuma zan maido maku da ita sannan zan sanar da ku yadda aka yi, amma ina son ku bani lokaci in daidaita komai sannan in je har London in tafo da su sai mu zo har nan gidanku a Katsina in kawo maku ita kuma in baku labari akan YADDA ABUN YAKE."
Abbi ya jinjina kai ya ce, "To shikenan babu damuwa." Ta ce, "Amma ku bari ku kwana a nan washegari sai ku wuce." Ammi ta ce, "A'a duk dare nafi son in gani a Katsina." Saida Umma tayi insisting sannan suka yarda suka kwana, washegari suka dauki hanyar Katsina, Umma taso ta saka direba ya kaisu amma suka
iya.

Ammi da Abbi suka sauka Katsina basu zame ko'ina ba sai gidansu Ammi wajen Alhaji Baffah, suka taru a falon Alhaji Baffah, ita, Abbi, da kuma Hajiyarsu Ammi wato Hajiya Attuwa.

Ammi ta kwashe dukkanin abun da ya faru ta sanar da iyayen nata, Hajiya Atuwa ta cika da tsantsar mamaki ta rasa bakin magana saidai jinjina kai kawai da ta ke yi.

Alhaji Baffah ya ce, "Allah mai iko, kenan ita yarinyar diyarku ce." Ammi ta jinjina kanta ta ce, "Eh haka ta ce." Sai a lokacin Hajiya Attuwa ta saka baki ta ce, "Idan haka ne, ya aka yi ban ganku kun tafo da ita ba."
Abbi ya gyara zama ya ce, "Ko labarin yadda aka yi yarinyar ta zama
iyarmu bata fa
a mamu ba saboda yayan yarinyar ya dauketa sun gudu ta tabbatar mamu da babu shakka London zai wuce da ita amma za ta je ta tafo da su tazo har nan Katsina ta sanar damu komai sannan kuma ta damka mamu diyarmu."
Alhaji Baffah ya jinjina kai ya ce, "Na gane amma kai baka ganin kamar akwai rashin gaskiya a lamarinta, sai nikega kamar tana so ne ta yi amai ta lashe, ma'ana ta hadiye maganarta ta hanaku yarinyar."
Hajiya Attuwa ta
ora da fa
in, "Idan kuwa haka ne ya kamata hukuma ta shiga lamarin, ai babu wanda ya fi karfin hukuma."
Ammi ta yi saurin fa
in, "A'a ba na jin hakan take nufi, ina ganin tunda har ta nemi mu bata dama to mu bata damar mu gani idan ya so idan daga baya ta nuna alamun rashin gaskiya sai mu saka hukuma a ciki."
Abbi ya jinjina kai ya ce, "Nima abun da nike ganin ya kamata muyi kenan, a yadda na fahimta ita kanta bata jin
in abun da yaran suka yi ba, ta nuna damuwa
arara akan lamarin."
Alhaji Baffah ya ce, "To shikenan sai mu bata damar mu gani abun da za ta yi." Suka cigaba da tattaunawa akan lamarin sai wajen karfe biyu sannan Ammi da Abbi suka koma gida.
****************
Tunda suka
auki hanyar Abuja Rumana take kuka, ba irin kukan shagwa
a da sangarta da ta saba ba, kuka ne mai
auke da tsoro da damuwa da kuma wani irin
unci da ya cika zuciyarta har ya kasa samun mafita.

Lumfashinta yana fita a hankali, idanunta sun kumbura sun yi ja saboda tsabar kukan da tasha, hannayenta suna rawa kamar wacce aka tsorata da wani abu mai firgitarwa.

"Bazan iya rayuwa a wani gidan da ba gidanmu ba," ta fa
a cikin rawar murya, tana ri
e hannun Junaid kamar wacce take jin tsoron kada ya ku
uce.
ara sautin kukanta tana fa
in, "Bazan iya rayuwa da wasu ahalin da ba kai da Umma ba... bazan iya ba... wallahi bazan iya ba..."
Ta girgiza kai tana sake fashewa da kuka, hawaye na zuba daga idanunta kamar ruwan sama, tana jin kamar an cire ta daga duniyar da ta sani aka jefa ta cikin wata sabuwa mai cike da duhu da rashin tabbas.

"Mu gudu daga Nigeria tun kafin Umma ta tilasta min rayuwa dasu," ta
ara cewa, muryarta na rawa.

Junaid ya juyo ya kalleta yanayinsa cike da tausayi da damuwa, kalamanta bana wasa ba ne, tsoro ne yake ragargazarta a zuci har ta kasa shiru.

A hankali ya matsa kusa da ita, ya
ora hannunsa a kafa
arta yana
arin kwantar mata da hankali.

"Ki kwantar da hankalinki," ya fa
a cikin sanyin murya, yana kallon idanunta kai tsaye domin ta fahimci gaskiyarsa.

Ya ce, "Didi ki kwantar da hankalinki bazan ta
a bari hakan ya faru ba.

Ina tare da ke kuma ba zan ta
a jefa ki cikin wani hali da ba ki so ba."
For once kalamansa sun saka taji sanyi amma tuna cakwakiya da turka-turkar dake cikin lamarin ya saka ta koma gidan jiya, damuwarta ta koma sabuwa yayinda kalamansa suka zame mata tamkar iskar da ta ratsa kunnuwanta ba tare da ta zauna a zuciya ba, tsoron da take ji a wannan lokacin ya fi karfin kalamansa su kwantar mata da hankali.

Motar na ci gaba da tafiya yayinda hanya take ja kamar ba ta da
arshe.

Gari yana sauyawa a gefensu daga
ananan kauyuka zuwa manyan gine-gine.

Ta yi shiru ba don ta daina kukan ba sai don kawai lumfashinta ya gaji.

Sai kuma ta sake fashewa da wani sabon kuka, mai
arfi fiye da na baya.

Tana share hawaye da bayan hannunta tana fa
in, "Ba zaka fahimta ba.

Ni ban saba da su ba... ban san su ba... ni ina son zama daku ne kawai... ni ina son mu zauna mu uku ne kawai...

Ni, da kai da kuma Umma."
Junaid ya ja lumfashi a hankali yana jin kalamanta suna dukan zuciyarsa.

Wannan ba
aramin abu ba ne a gareta, wannan canjin rayuwa da ake son tilasta mata kamar ana so ne ta manta da duk wani abun da ta sani ta fara wani sabon shafin rayuwa ba tare da shiri ba.

Ya ce, "Zaki iya amma ba ta tilas ba.

Zamu yi komai a hankali.

Ba zan bar ki kisha wahala a rayuwa ba hakazakila ba zan barki ki rayu a inda baki so ba."
Ba ta amsa shi ba, ta juyar da kanta gefe tana kallon waje amma saidai ba ta ganin komai, hawayen da suka cika idanunta sun rufe mata magannan.

Lokaci na wucewa daga seconds zuwa minutes zuwa hour amma halin da take ciki bai sauya ba.

Kukan zuci da na zahiri ya zame mata tamkar abokin tafiya, yana bin ta a duk inda motar ta dosa.

Har suka fara shiga birnin tarayya Abuja kogin hawayenta bai kafe ba, shigowarsu Abuja bai
auke mata hankali ba.

A gare ta, komai sabo ne, kuma duk abun da yake sabo a wannan lokacin yana
ara mata tsoro ne.

Har ya kama hanyar gidansa yayinda take faman share hawaye da sauri-sauri, can kuma kamar wacce ta tuna da wani abun tsoro, sai ta
ago kai da gaggawa tace, "A
a, a
a, zata iya binmu har can gidan naka ta amsheni ta mayar masu... don Allah muje hotel... don Allah..."
Muryarta a wannan karon ba kuka kawai ba ne, akwai ro
o a ciki, akwai firgici na wanda yake neman mafita.

Ta
ara matsawa jikinsa, tana ri
e shi da
arfi.

Junaid ya ja lumfashi yana kallonta da mamaki.

"Hotel kuma?" ya maimaita cikin
aramin murya a lokaci guda kuma yana
arin rabata da jikinsa domin yadda take shige masa da yadda take manne masa yana jefa shi cikin wani yanayi da bai ta
a tsintar kansa a ciki ba, wani yanayi mai rikitarwa tsakanin tausayi, kulawa, da kuma wani abu da yake
arin dannewa a zuciyarsa.

Amma duk
arinsa na son ja baya, sai ta
ara matsowa kamar
aramin yaro da ke neman mafaka daga abin da yake tsoro.

"Eh... hotel..." ta sake fa
a, tana girgiza kai.

"Don Allah... kada ka kai ni can... bana jin zan iya rayuwa da wadancen mutanen... don Allah mu gudu..."
Ya yi shiru yana kallon fuskarta da ta cika da hawaye da tsoro da kuma wani irin rashin tabbas da ya saka zuciyarsa take jin tausayinta.

A hankali ya juya idonsa ya kalli hanya yana tunani cikin sauri.

Bai shiryawa wannan lamarin ba, koda ya biye mata suka gudu bai shirya abun yayi tsawo har haka ba, bai yi tsammanin abubuwa zasu juya haka ba.

Amma a wannan lokacin, abun da ya fi muhimmanci a gareshi shi ne yadda zata samu nutsuwa, ko da kuwa na
an lokaci ne.

Ya sauke numfashi a hankali, ya
an jinjina kai.

"Okay," ya fa
a a ta
aice.

Ya sauya akalar motar zuwa hotel mafi kusa da su, Rumana ta sassauta ri
on da ta yi masa, amma har lokacin tana manne da shi, kamar yaron da ake
arin rabawa da Innarsa.

A hankali kukan nata ya ragu, amma ba duka ba, saidai ya koma irin kukan nan ne na shiru mai
auke da ajiyar zuciya da lumfarfashi.

Yayinda suke ci gaba da tafiya, kan Junaid ya cunkushe da tunani: shin me ke jiransu a nan gaba?

Shin wannan shawarar ta hotel
in zata zama mafita... ko kuma wata sabuwar matsala ce zata bu
ofa?

But for now ya ajiye komai a gefe.

Abun da kawai yake ji shi ne rawar lumfashinta a jikinsa da kuma yadda ta ri
e shi kamar shi ne ka
ai mafakarta a wannan duniya.

Da muryarta wacce take tsinkewa saboda kukan da tasha tace, "Ina...

Ina son...
Chapter 19 · 0% Book details