← Book details Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 49

Sashe 47

Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Taji zaman gidan ya fita kanta, gashi tana jin da
in zaman sosai, kasancewar babu takura, babu tsawa, babu wanda zai tashe ta da sassafe ya ce ta shiga kitchen.

Sai ta tuna gidan Ammi, inda kullum da safe ake tashi da ita da wuri, a saka ta girki da gyaran gida kamar wata
ar aiki, nan gidan Alhaji Baffah ya fi mata sau
i da nutsuwa.

Wasu lokuttan sai ta ji kamar ta tattara kayanta ta koma gida kawai, ta huta da wannan drama
in nasa, amma da zarar wannan tunanin ya zo, ta san idan ta tafi, a zuciyarsa zai
auka ya yi nasara ne, ya karyatata, watakila yayi gadarar ya koreta daga gidan, wannan tunanin ne yake saka tsayawa.

Ta ce a ranta, "Ni in gudu saboda shi, Never."
Ta cigaba da zama kamar babu abun da ke faruwa.

Ranar tana yawo a compound, kunnenta ya kama hirar Aunty Nauwara da Aunty Anisa.

Ta tsaya a gefe ba tare da sun ganta ba, tana sauraro.

Aunty Nauwara ta ce, "Gaskiya Uncle Al'ameen ya dace da ita.

Shekaru goma sha biyar kenan da rasuwar Aunty Zeenatu, tun daga lokacin bai
ara kula wata mace ba sai ita."
Aunty Anisa tayi dariya tana fa
in, "Wannan
ar girman kan ita a dole sai ta tunawa mutane a London tayi rayuwarta."
Normally bata cika gaishe dasu ba amma don su fahimci tana kusa, sai ta
arasa da zummarta, ta ce, "Ina wuni?" Ba tare da ta jira amsa ba, ta wuce fuu kamar iska ta bar su da kallon juna.

Takaici ya kai mata ta
auko kofi ta cikashi da ruwan omo ta ajiye tana dakon dawowarsa Uncle Al'ameen, tana jin
arar shigowar motarsa tayi wuff ta zuba ruwan omon a kan tiles
in da yake shirin takawa.

Da ya taka, sai ya sulale ya fa
i rijib! ya fasa ihu.

Rumana kuwa ta fashe da dariya tana ri
e ciki.

Ta ce, "Ka
an ka gani!"
Duk da yana kwance yana jin jiki amma bai bayar da kai bori ya hau ba, ya ce da
yar, "Babu kom
ai... duk cikin sone...

MATAR UNCLE..."
Ta fusata ta ce, "MATAR UNCLE my foot," ta mi
e fuu ta wuce sama, ya bita da kallo yana dafe da kugu a lokaci guda yana dariyar yadda ta haye bene fuu.

Washegari tana saukowa daga bene ya biyo bayanta yana mata ma
e, yana son sake tsokanarta.

Ta juya cikin sauri, zuciyarta cike da zafin wasan, ta saka masa
afa.

Bai ankara ba sai ya wulwulo
asa har kasan bene, ya buga jiki ya fasa ihu.

Fatima, ta fito da gudu tana fa
in, "Wayyo sannu Daddy!"
Rumana ta tsaya cak, idanunta suka fa
a.

Ta ce da mamaki, "Ke yanzu wannan yaron kike kira da Daddy?"
Uncle Al'ameen kuwa yana
asa yana ta 'wash wash ashhh' da ihu, bai ma iya magana sosai ba.

Fatima ta yi rau-rau da idanu ta ce, "Babana ne."
Rumana ta
an karkatar da kai, ta ce da wata irin murya, "Wannan ne babanki?

Tab... ashe tsohon kashi ne."
Ta fashe da dariya tana tafa hannu, "Tab amma
antahalikin nan ya kasheni, don kuturun wulakanci mutum mai
ar da ta kusa kai shekaruna yace yana sona, an shani ba ka
an ba"
Uncle Al'ameen na
asa yana dafe da kugu yana fa
in, "Rumana kin kasheni..."
Fatima ta juya ga Rumana da kallon tuhuma ta ce, "Mi kikayi mashi?"
Rumana ta ware hannuwa, ta ce, "Tuntube yayi da kafata."
Kafin a fara tambaya ko rantsuwa, ta riga ta juya ta wuce dakinta.

Washegari da safe ta ha
a meeting a bangaren Alhaji Baffah domin kawo karshen wasan banzan da Uncle Al'ameen yake mata.

"Na lura wasu suna
aukar maganar da Uncle yake yi akan cewa yana sona da gaske, to, wasa yake, beside ya yi min tsufa, na yi masa tsa
a, kudin karatuna kawai sun fi
arfin tattalin arzikinsa."
Uncle Al'ameen da yaga jar wuta jiya, ya jinjina kai ya ce, "Haka ne."
Tun jiya yayi wa kansa fa
an fita harkar yarinyar, yadda take ramakon gayya idan ya biye mata sai ta kassarashi, har lokacin kugunsa ciwo yake masa, da
yar yake takawa, lokacin da ta saka mashi kafa akan bene har wuta ya hango
Rumana ta
age gira ganin ta yi nasara.

Aunty Nauwara ta ce, "Dama akan wannan ne kika taramu, ni na saka ko daidaita junanku kukayi." Rumana ta ce, "Daidai juna as in aure," sai kuma ta fashe da dariya ta juya ta
ara juya ta ce, "Dubeni da kyau ai hanyar jirgi daban da ta mota." Ta fice fuu.

Hajiya Attuwa, Hajiya Murya, Hajiya Rabi, Hajiya Rahama da Alhaji Baffah suka bita da kallon mamaki.

Aunty Anisa ta ce, "Ikon Allah sai kallo."
Rumana ta koma
akin da ta sauka, ta fara tattara kayanta, kafin ta gama, wayarta ta fara ringing.

Ta duba, Ammi ce.

Tana
agawa, muryar Ammi ta zo kai tsaye, babu
ata lokaci, "Komai kikeyi ki dawo gida yau, wato saboda ki gujewa kitchen da ayyukan gida shine kika tsaya a nan, to a yau ba gobe ba ki kamo hanyar gida.

Gobe
ar uwarki zata fara koya maki girki."
Rumana ta zaro idanu, "Koyon girki kuma?

But sati mai zuwa zan koma London makaranta."
Ammi ta ce, "Abbanku ya soke makarantar.

Ya ce wanda kikayi ya isa haka."
"Na'am?" Rumana ta fa
a a razane.

Ammi bata
ara ce mata komai ba sai, "Ki kamo hanyar gida."
Kalmar ta tsaya a kunnenta kamar
arar
aho.

Jikinta ya yi sanyi, ta tattara abun da ya rage, ta yi sallama da mutanen gidan, ta kama hanyar gidan Ammi zuciyarta cike da ru
ani.

Da ta isa gida, kai tsaye ta wuce
akinta, ta zauna tana jiran dawowar Abbi.

A ranta tana saka ran watakila idan ta same shi cikin nutsuwa ta ro
e shi, zai saurareta, ya barta ta koma London ta
arasa karatunta.

Bayan cin abincin dare, ta nufi study room
insa.

Ta tsaya a
ofar ta ce, "Abbi, barka da warhaka."
ago ya ce, "Yauwa."
Ta yi shiru na
an lokaci, zuciyarta na bugawa.

Ya kalle ta ya ce, "Miye?"
Ta ha
iye yawu, ta ce, "Makaranta zan koma London..."
Kafin ta
arasa, ya katse ta, "Na soke karatun."
an matsa gaba ta ce, "Amma Abbi..."
Bai jira ba ta furta abun da take furtawa ba, ua nuna mata
ofa da hannu, "Ki fice na riga na yanke hukunci, bana magana biyu."
Jiki a sanyaye ta juya, ta fita daga
akin.

Tana isa
akinta ta
auki waya ta kira Umma.

Tana jin muryar Umma ta fashe da kuka.

"Rumana?

Miye?" Umma ta tambaya cikin damuwa.

"Abbi ne ya hanani komawa makaranta..." ta fa
a cikin kuka.

"Please kiyi masa magana..."
Umma ta yi shiru na
an lokaci, kamar tana tunani sai kuma ta ce, "Ki kyaleshi, gobe zan wuce Dubai, udan na dawo kai tsaye Katsina zan nufo, zan kawo dalilin da zai saka zamanki ya koma
ashin mu amma ba irin wancan zaman zamuyi ba.

Dole ki fara koyon girki da ayyukan gida."
Rumana ta shiga gya
a kamar kadangaruwa, "Eh, zan yi."
Tun daga wannan ranar ta fara kirga kwanaki, tana
ididdige lokacin dawowar Umma kamar wata mai jiran ceto, zuciyarta cike da
uncin hanata komawa London da Abbi yayi.

Shekarun da ta shafe tana karatu, burin da take da shi a rayuwa idan aka katse su a wannan lokacin, ba a yi mata adalci ba.

Amma dole ta jira domin wani lokacin, jiran lokaci shi ne ya fi kowace gardama
arfi musamman naci bazai saka ayi mata abun da kake son ba.
***********
Ranar talata wajen
arfe tara na safe, Rumana tana baccin safe ringing
in waya ya tashe ta.

A hankali ta janyo wayar ta sa a kunne ta ce, "Uhmm..."
Wayar na kunnenta tana kwance a gadon idanuwanta a lumshe cikin ragowar barcin da bai ida sakinta ba.

Daga
aya bangaren Junaid ya ce, "Kina bacci ne?"
Ta ja numfashi kafin ta amsa da, "Ehhh kiranka ne ya tayar da ni." Ya ce, "Guess what?" Ta juya jikinta a kan gadon ta gyara murya tace, "Ina jinka."
Ji ta yi ya ce, "Yau zan shigo garinku, zan tafo da maki da shopping da kikayi tare da kayan gara."
Jin haka ya saka ta farka sosai.

"Car or flight?" Ta tambaya.

Ya ce, "Flight, ki yi min girki, na yi kewar girkinki didi,
anwata tawa ta kaina."
Murmushi ya subuce mata duk da kasalar jikinta, ta ce, "Anything for you?" Ya yi shiru kamar mai tunani sannan yace, "Alright, let me think...

Sunasir...

Sakwara da miya..."
A take Rumana ta mi
e zaune ta zaro idanu waje ta ce, "Duk ni
aya?" Ya yi dariya a
aya bangaren ya ce "Kika ce anything for me... uhmm...

Didi..."
Ta ce, "Okay, zanyi."
Ji ta yi ya ce, "Kuma zakiyi min dambun kaza, ki aiko min da shi."
"Yau zaka koma ne?" Ta tambaya.

Ya amsa a ta
aice, "Ehh." Tace cikin kulawa, "Safe trip, Allah ya kawoka lafiya." Ya amsa da, "Amin Rumana...

Aww Didi..." Ta mi
e zaune tana kallon agogon bango ta ce, "Tab akwai aiki babba a gabana."
A tare sukayi dariya, ta mi
e ta wuce bathroom tayi wanka tare da shiryawa cikin doguwar riga marar nauyi ta rufe kanta da hula ta fito.

Tana saukowa parlour ta ci karo da Uncle Al
ameen, kallo
aya tayi mashi ta kawar da kai sai kuma ta juya ta ce, "Ina kwana?"
Uncle Al
ameen ya dubeta da mamaki yace, "Sabon salo, yau kece kike gaidani."
"Naga kana amfani da hakan ne kana shiga harkata shiyasa and I don't want anything that have to do with you."
Uncle Al
ameen ya ware idanu yace, "O really.

Alright then.

Morning, how are you?"
Tayi murmushi kamar wacce aka yi forcing tace, "I'm fine Baba Aminu." Ya waro idanu ya ce, "Waye Baba Aminu?" Ta ce, "Kai mana, kana da
iya wacce ta kai tsayina ai dole in kiraka da Baba, tsohuwa mai ran karfe." Sai kuma ta fashe da dariya.

Ta wuce hanyar kitchen tana tafiya a nutse, kitson guda
aya da tayi wa gashinta yana lilo a bayanta.
Chapter 47 · 0% Book details