← Book details Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 49

Sashe 28

Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta ce, "Ka kai ni tasha."
Yana sauketa tasha ta bashi kudinsa ta shiga ciki ta samu waje ta zauna tana tunanin inda za ta dosa, kudin mota ba damuwa ba ne, kudin da Suleiman yake ba ta idan za ta je makaranta tana kashe wasu ne tana ajiye wasu don haka tana da ku
e, mi
ewa ta yi ta toshi wata mota da taga ta kusa cika ta ba tare da ta damu da garin da motar za ta je ba, dama saura mutum biyu suka rage, jim kadan wani mutum ya shigo, suka hau hanya.

Sun yi tafiya sosai, tana kallon hanya cike da damuwa, tana kallon yadda take
ara nisantar danginta da asalinta, gudu motar ta ke yi sosai, tafiya su ke yi kamar ba zamu kai inda za su je ba, daga karshe suka shiga wani gari mai yawan gine-gine tare da ci ga ba, motar tana parking a tasha mutane suka fara fitowa, itama Amina ta bi ayarin mutanen, ta fito bakin titi ta yi tsaye ta rasa inda za ta dosa, addu'o'i ta fara karantawa tare da neman agaji a wajen Allah madaukakin sarki.

Daga bayanta ta ji muryar mace tana kiran sunanta, "Amina." Da sauri ta juya tana kallonta da mamaki, Hajjo ce
ar asalin ruggarsu wacce take auren wani mai kudi a
aya daga cikin jihohin arewa, itama da mamaki take kallonta ta ce, "Kuma ita ce.

Tare da wa kike?" Ta tambaya.

Amina ta rasa bakin magana sai kuka da ta fashe da shi, Hajjo ta yi shiru tana kallonta kawai, wata katuwar mota ce ta tsaya a kusa da su, direba ya fito yana kwasar gaisuwa ya bu
e baya, Hajjo ta dubeta ta ce, "Ki shiga."
Katon gida ne sosai, ta yi sororo tana kallon katon falon da suka shiga, ta ce, "Ki zauna bari in saka a kawo maki abinci." Mai aiki ce ta kawo mata abinci ta ci ta koshi ta yi wanka ta huta.

Hajjo ta sameta, "Amina ki fa
a min gaskiyar abun da ya baroki daga gida?" Amina ta fashe da kuka tana kuka ta mai sanar da ita komai akan abubuwan da suka faru.

Hajjo ta girgiza kai ranta ya
aci sosai ta ce, "Banda abun Malam Muhammad ina aka ta
a yin haka, wani satin za mu je in mayar da ke." Amina ta fashe da kuka tana girgiza kai, "A'a, idan na koma zai iya fa
ar mummunar magana a kaina, ban son komawa har sai gaskiya ta bayyana.

Baabaa Hadiza ta ha
a tuggu da makirci ta yi asiri ta hana kowa magana."
Hajjo ta ce, "Torh shikenan, nima dazu na je amso sako ne a tasha, daga can aka aiko min sakon."
Daga nan zaman Amina ya dawo gidan Hajjo, tana jin dadin zama gidan sosai, tana da
iya guda
aya sunanta Ramlerh sa'ar Amina, cikin
anin lokaci shakuwa ta shiga tsakanin Amina da Ramlerh, Amina ta waye ta koma
ar birni (lols
), ta yi kiba ta
ara haske ta yi bulbul abunta hutu ya zauna a jikinta.

Wata rana suna zaune a compound, Hajjo ta yi kiran Amina ta sameta a parlour, ta ce, "Na yi maganarki da mai gidana, zamanki haka ba zai yiyu ba, zan sakaki a makarantar boko da Islamiyya sai ki rin
a zuwa tare da Ramlerh."
Ji ta yi hawaye sun zubo mata ta ce, "Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi." Ta ce, "Amin, ta shi kije, wani satin sai ki fara zuwa makarantar."
Ranar litinin Amina ta fara zuwa makarantar boko tare da Ramlerh, makarantar masu kudi ne sosai, aka sakata aji biyar that's Ss2 two a ajinsu Ramlerh, Ramlerh ta gabatar da Amina a wajen
awayenta a matsayin
ar uwarsu da ta zo daga Taraba, a wajenta Amina ta san Zainab (Aunty Zaynerb) wacce ita ce babbar
awar Ramlerh kuma
iya a wajen Hajiya Kaka abokiyar kasuwancin Hajjo.

Amina ta kammala sekondire da sakamako mai kyau kasancewar tana maida hankali sosai akan karatunta sosai, ita da Ramlerh suka jona school of nursing yayinda Zainab ta wuce london a can ta hadu da Omar wanda
an Nigeria ne kuma
an asalin jihar katsina.

Hajjo ta aikesu gidan su Zainab su kaiwa Hajiya Maryam sako, sun fito daga mota za su shiga ciki, Abdurrahman yana zaune a compound, Ramlerh ta gaida shi ya amsa da fara'arsa, Amina ta dan kalleshi ta ce, "Ina wuni?" Yana kallonta ya ce, "Lafiya lau."
Suka shiga ciki ya dan juya yana kallonsu musamman Amina wacce kallo
aya ya yi mata ta tafi da shi, su ukku ne a wajen mahaifiyarsu Abdurrahman, Zainab sai autarsu Husnah, tun daga lokacin Abdurrahman ya fara bibiyarta tun bata kulashi tana ganin ba sa'an aurenta bane, that ya fi karfinta, that soyayyarsa YA FI KARFIN ZUCIYARTA, har ya yi nasarar cusa mata soyayyarsa, ba ta
oye mashi komai ba, ya yarda zai aureta a hakan, bayan sun kammala school of nursing aka yi auren, a rana
aya aka daura auren Amina da Abdurrahman, na Ramlerh da kuma na Zainab.

Zaman lafiya suke cike da farin ciki, Abdurrahman ya hanata aikin gwamnati amma ya bata jari tana kasuwanci, a takaice bayan shekara biyu ta haifi Junaid wanda kamarshi
aya sak da mahaifinshi kamar kobo da kobo, yaro ya ci suna Junaid, Junaid yana shekara biyu Abdurrahman ya matsawa Amina har sai da ta yarda da tafiyarsu Taraba, suka shirya sukaje ruggarmu ita da Abdurrahman tare da Hajjo.

Baffa ya yi nadamar korar Amina da ya yi, sun nemeta sosai, bayan ta baro garin gaskiya ta bayyana wanda hakan ne ya yi sanadin mutuwar auren Baabaa Hadiza gashi tana matu
ar son mijinta tana fama da rayuwa, ga ciwo ta koma wata iri, tana kuka tana ba Amina hakuri.

Tana kuka tana fa
in, "Amina kiyi hakuri ki yafe min, na zalunceki na cutar da ke, nasan waye Suleiman da halinsa na shaye-shaye amma son kudi ya rufe min idanu na saka aka aurar mashi da ke, kika sha wahala amma ban tausaya maki ba, a karshe ya gudu da diyarku, na dauki alhakinki na cutar da ke, ki yafe min."
Sai da Amina ta yi mata kuka ganin yadda rayuwa ta mayar da ita, ta koma abun tausayi, "Na yafe maki, Allah ya yafe mamu."
Sai da suka kwana biyar a Bali suka zaga dangi sosai sannan suka juyo zuwa kaduna, tun daga haihuwar Junaid haihuwa ta tsayawa Amina ga shi tana matu
ar sha'awar haihuwar
iya mace tana kewar diyarta Maryam, idan ta tuna da ita sai dai ta ji hawaye suna zubar mata, tana son haihuwar
iya mace ta yi mata kwalliya, ta tabbata dukkanin lokacin da ta samu haihuwar
iya mace za ta ga gata a rayuwarta.

Sai da Junaid ya shekara sha biyar a duniya sannan ta
ara samun wani cikin, a koda yaushe fatanta shine ta haifi
iya mace, gab da lokacin haihuwarta rashin lafiya ya samu Zainab sun je Katsina dubiya haihuwa ta kamata, ta haihu a asibiti ta haifi
iya mace sai dai yarinyar ta koma, bayan ta fahimci hakan ne ta yi musayar
iyar da ta haifa da wata.

Ranar suna yarinya ta ci suna Rumana amma Junaid yana kiranta da Didi, sun tashi cikin shakuwa da son juna, komai Rumana za ta ce Yaa Junaid, tana samun gata babu abun da ta nema ta rasa, suna kiran Amina da Umma yayinda suke kiran Abdurrahman da Abba, shekaru ukku da su ka wuce Allah ya yi mashi rasuwa a sanadin hatsari, kafin rasuwarshi ta sanar da shi komai akan Rumana.

Junaid ya yi karatun likitanci a London bayan kammala karatunsa mahaifinshi ya bu
e mashi private hospital, saidai soyayyarsa da kasuwanci ya saka yake cigaba da kula da kamfanonin da mahaifinsa ya bar masa.

Satuttuka kadan ne suke rage aurenshi da Khaleseert Jikar Hajjo, Rumana kuma a London ta fara karatunta tun daga kindergarten har zuwa Jami'a da zata fara."
**************
Umma ta dubesu hawaye na kwaranya akan fuskarta yayinda muryarta ta dusashe ta ce, "Abun da na yi muku ban cancanci a yafe min ba amma duk da haka ina ro
onku da girman Allah ku yafe min.

Alfarma
aya ce kawai nike nema a wajenku wata mai zuwa ne auren Junaid.

Don Allah ku barta ta zo.

Bayan an gama bikin sai ta dawo.

Rumana ta zaro idanu da firgici.

Ta kalli Umma ta kalli Junaid, cikin rawar murya, ta ce, "What?

Umma kika ce in tsaya a nan?

A'a ba zan zauna ba, I can't survive here."
Umma ta girgiza kai hawaye na ci ga ba da zubo mata ta ce, "Rumana dole ki zauna tare da iyayenki."
Rumana ji ta yi kamar an caka mata wu
a a zuciya, ta fasa
ara.

Da sauri ta mi
e ta shige jikin Junaid, ta makalkale shi da
arfi tamkar rayuwarta ta rataye ne a kansa.

Kuka ta ke yi sosai har lumfashinta yana yankewa.

"A'a babu mai rabani da ku!

Yaya Junaid don Allah karka bari ku tafi ku barni.

I can
t survive here, ba zan iya rayuwa a cikin wannan akurkin gidan nasu ba, ba zan iya ba."
Hannunta na rawa tana ri
e da shi kamar wacce take tsoron kada ya
ace daga gareta.

Junaid bai ce da ita komai ba, ya saka hannu ya banbareta daga jikinsa, ya juya ya nufi hanyar fita.

Ta dur
ushe a wajen jikinta yana rawa, tana kuka mai tsuma rai, tana kallon bayansa yana nesa da ita tana jin tamkar ana
auke mata komai na rayuwarta ne a lokaci guda.

Har ya kai bakin
ofa, sai kuma ya tsaya cak, ya juyo.

Idanunsa suka sauka a kanta, ya kafeta da na mujiyarsa yana jin sautin kukanta har cikin zuciyarsa.

Lebensa suka motsa ka
an amma kalmomin da yake son furtawa suka makale.

Daga
arshe ya ha
iye su ya juya aka bu
e masa
ofa ya fita.

Convoy na motocin suka fice daga gidan suka kama hanya cikin yanayi na shiru.

Ya jingina da kujerar mota, ya lumshe idanu yana neman mafaka daga tunaninsa.

Tun daga lokacin da suka bar gidan ya kasa samun nutsuwa.
Chapter 28 · 0% Book details