← Book details Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 49

Sashe 44

Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jidderh na ta gaishe shi cikin ladabi da girmamawa, "Ina kwana Uncle?" Ya amsa da, "Lafiya lau daughter."
Ya maida dubansa akan Rumana ya
age gira yana fa
in, "Ke baki iya gaisuwa bane?"
Rumana ta karkatar da kai tana mashi kallon tara saura kwata ta ce, "Na iya mana, Ina kwana ko ina wuni ake cewa."
aura kafa
aya akan
aya yana kallonta da kyau, ya ce, "To, gaida ni."
Ta saki siririyar dariya mai
auke da rainin wayo, ta ce, "To sannu, marassa lafiya na gida da na asibiti, Allah ya basu lafiya."
Imran dake gefe ya juyo da sauri, fuskarsa ta cika da
acin rai.

Ya daka mata tsawa yace, "Hauka kike neman ki manna mashi ko mi.

Ki gaidashi tun kafin jikinki ya gaya maki."
Ta turo baki kamar
aramar yarinyar da aka yi tsawa, cikin
an ja da baya, ta ce, "Aminu ina kwana?"
Uncle Al'ameen ya zaro ido da gaske a wannan karon, mamaki ya bayyana a sararin fuskarsa ya ce, "Aminu kuma?"
Ta jinjina kai babu alamar nadama.

"Ehh, shi aka rada maka ai."
Ya girgiza kai murmushi ya bayyana a gefen bakinsa, yana mamakin halin yarinyar.

"Uncle Al'ameen za ki ce."
Ta ta
e baki, zuciyarta cike da haushi, amma dole ta bi ko don kada Yaya Imran ya sharara mata mari.

Ta gyara murya ka
an ta ce, "Ina kwana Uncle Al'ameen?"
aura kafa
aya kan
aya cikin isa, ya ce, "Ban ji ba."
Ta rumtse idanu ta sake maimaita gaisuwar, wannan karon da
arfi, "Ina kwana, Uncle Al'ameen?"
Ya ce, "Lafiya lau, daughter."
Ta juya gefe tana gunguni a
asa-
asa, muryarta
asa sosai har kusan ita ka
ai ke ji, "Daughter my foot."
Ta juya ta nufi staircase
in, tana tafiya da irin takun nan na nuna ko oho, sai ta ji muryarsa a bayanta, "Rumana."
Ta tsaya na
an lokaci kafin ta juya a hankali.

Ta ha
a hannuwanta a kirji, ta ce, "Uncle Al'ameen."
aura kafa
aya akan
aya yana karkadata a hankali, sannan ya ce, "Dauko min ruwa."
Ta nuna kanta da yatsa, da alamun mamaki a fuskarta ta ce, "Ni zan dauko maka ruwa?"
Bai sauke kallonsa daga kanta ba ya ce, "Eh.

Ko ban isa in saka ki yi ba?"
auke ido gefe, tana murmushin rainin wayo ta ce, "Kusan haka."
Bata jira ya sake magana ba.

Ta juya da sauri, ta
aga murya ta kiran mai aikinsu, "Marka!

Dauko bottle water ki ba Uncle Al'ameen."
Da gadara ya ce, "Ke na ce ki dauko min."
Har ta bu
e baki za ta musa, sai kuma ta ha
iye maganar.

Ta juya a hankali ta nufi fridge, wani makirin murmushi ya bayyana a gefen bakinta.

Ta za
i ruwa mai sanyi sosai ta dawo ta dungure masa a gabansa.

Cikin gadara ya kalleta ya ce, "Zuba min a cup."
Ji take kamar ta fasa ihu amma fahimtar so yake ya fusata sai ta shanye fushinta, ta juya ta
auko kofin tana kitsa yadda za ta koya masa hankali cikin ruwan sanyi, ba tareda hayaniya ko wallahi tallahi ba.

Ta sunkuya ta cika kofin da ruwan da yake da matu
ar sanyi.

Ta rusuna ta mi
a masa cikin ladabi shi kuwa gogan ya mi
a hannu zai kar
a, cikin dabara ta karkatar da nata hannun, ruwan ya zube a jikinsa.

Ya zaro idanu jikinsa yana karkar da sanyi.

"Rumana, miye haka?" ya fa
a cikin firgici.

Ita kuwa ta nuna kamar ta firgita da gaske, tana rawar murya tana fa
in, "Sorry Uncle...

Ayyah, sorry Uncle!"
Da gayya ta buge bottle water
in dake hannunta akan table ya
are ya zubo masa a jiki gaba
aya.

Ta
ara rikicewar
ogi tana ta, "Ayyerh!

Bari in dauko maka towel."
Ta juya ta
auko towel ta dawo ta mi
a masa.

Yayin da take mi
awa ta matso kusa, ta sauke murya
asa sosai, ta ce a hankali, "Aminu idan kana cin
asa ka kiyaye ta suri.

Rumana na fi
arfinka, idan na fara wasan ba
ar wahala zaka sha."
Sai ta ja baya kamar babu abin da ya faru, ta juya ba tare da ta sake kallonsa ba, ta nufi staircase
in ta haura sama kamar babu abin da ya faru.

Ta barshi a zaune a wajen, shiru cak, cike da mamaki, har ya kasa cewa komai.
*****
Washegari, ita da Jidderh suka je gidan Alhaji Baffah.

Da suka isa, saida suka fara shiga sauran sassan gidan suka gaishe dasu kafin daga bisani su nufi bangaren Hajiya Attuwa.

A can suka samu Uncle Al'ameen zaune yana kallo.

Rumana ta kalleshi ta ta
e baki tareda kawar da kai.

Jidderh kuwa ta gaishe shi, "Ina kwana, Uncle?" Ya amsa da fara'a, "Lafiya lau, daughter.

Allah ya yi albarka."
Kasancewar Hajiya Attuwa a wajen ne ya saka Rumana ta daure ta gaishe shi, ba don ranta ya so ba.

Ta ce a ta
aice, "Ina kwana, Uncle?"
Ya kalleta ya ce, "Lafiya lau, daughter.

Kina lafiya?"
Ta amsa a takaice, "Lafiya."
Ya gyara murya yana kallonta ya ce, "Lafiya lau ake cewa."
Ta ce, "To, na ji."
Da wata irin gadara ya ce, "Je ki zubo min abinci."
A ranta kuwa ta ce, "Allah ya sa miya ce in
arar maka da ita a kaya."
Da zummarta ta nufi kitchen, zuciyarta tana
ara kitsa mata shirinta na indai miya ce sai ta huce haushinta akan farar shaddar da yake sanye da ita.

Tayi sa'a ta samu masa ce da miya, ta zubo miyar da yawa tana
ara kitsa yadda za ta sakar masa ita a farar shaddar dake jikinsa.

Amma abin da ba ta sani ba shi ne shima yana da nasa shirin a
oye.

Ta fito da zummarta tana tafe cikin
wazo domin aiwatar da shirinta saidai afin ta ankara, ya saka mata
afa, tayi taga-taga ta yi zaman da
aro a
asa kwanon yayi sama ya juye miyar ta watsu a saman kanta da jikinta gaba
aya.

A take ta rikide, kai da fuskarta sun
aci da miya ta koma kamar wata
ar cartoon.

Uncle Al'ameen ya fashe da dariya, yana nuna ta da yatsa.

Ya sunkuya ka
an, ya rage murya ya ce, "Na fi
arfinki.

Ni da ke sai dai ki ci bakar wuya."
Ta cije le
e, takaici na cin ta a zuciya, amma ba ta iya cewa komai.

Ya mi
e ya fice yana dariya.

Hajiya Attuwa ta bishi da kallo tana fa
in, "Shi wannan lafiyarsa kuwa?"
Jidderh tana dariya a
asa-
asa ta ce, "Wadannan da kike gani, ko Tom and Jerry basu kai su dirama ba."
Rumana ta rasa abin cewa, zuciyarta cike da takaici da kunya a lokaci guda.

Ta mi
e ta bar falon ba tare da ta sake cewa komai ba.

Ta wuce dakin da suke sauka, kayanta sun
aci gashi bata zo da wasu ba, ta dauki wayarta ta yi order din abaya ta zauna a gefen gado tana kwafa fuskarta kawai ta goge sauran miyar na nan.

Uncle Al'ameen ya turo mata text message, 'Ki tuba kawai don ban sakaki kuka da hawaye ba.'
Tayi mashi reply, 'Wait and see, idan ban rama abun da kayi min ba sunana ba Rumana bane ba.'
Ya turo mata emoji da dariya ta ta
are ta fasa ihu, Jidderh ta shigo da sauri tana fa
in, "Sis lafiya?" Rumana ta murtu
e fuska ta ce, "Lafiya lau, idan an kawo abayar da nayi order ki ajiye min akan gado."
Ta mi
e ta wuce bathroom, ta sakarwa kanta shower tana wanke miyar da ta
ata jikinta tana kwafa kamar wacce aka ci wa zarafi.

Takaicin da take ciki ya hana ta nutsuwa ko da na
an lokaci.

Ji take idan bata rama ba ba zata ta
a samun kwanciyar hankali ba.

Ta fito
aure da towel ta samu gown akan gado ta
auka ta saka, ta zauna tayi tagumi tana kitsa yadda zata rama kafin tabar gidan, ramakon gayya sai muguwar tsadar da sai ya gwammace kida da karatu.

Takaici ya cika mata zuciya har ya hana ta samun sukuni.

Ba tare da
ata lokaci ba ta
auki waya ta kira Yaya.

Da ya
aga, cikin zafin rai ta ce, "Yaya Junaid so nike ka zo garin nan ka ajiye takalma idan Uncle Al'ameen ya tsallaka ka saka security
inka su yi masa
an banzan duka idan ya so daga baya ka ce baka sanshi bane ba."
Yaya Junaid ya ware idanu cikin mamaki ya ce, "Mi ya faru kuma?"
Ta hura hanci ta ce, "Gadara yake yi min, jiya ya ce in
auko masa ruwa har yana da zarrar cewa in zuba masa a kofi sai kace wata boyi-boyinsa, yau kuma yace in kawo masa abinci, sannan ya saka min kafa na zubar da miya a kaina.

To wallahi ka kira ka yi masa warning kada inyi masa
an banzan duka azo ana wallahi tallahi dani."
Yaya Junaid ya ce, "Amma dai yaro ne ko?"
Ta amsa da sauri, "Saurayi ne."
Nan take ya fashe da dariya yana fa
in, "To amma sai yana barci zakiyi dukan ko?"
Ta yi wani shegen murmushi mai cike da shirin ramuwar gayya, ta ce, "Wait and see
kuma a dawo min da security dina."
Yaya Junaid ya girgiza kai yana dariya, "A'a, ba zan dawo dasu ba.

Ki saka su
arya kawunki azo ana wallahi tallahi da ni."
Ta ce, "Mantawa zan yi da shi kawuna ne sai na saka sun kir
eshi kamar sakwara a turmin daka sannan daga baya in ce tuna fuskarsa ke ban yi ba."
Yaya Junaid ya
ara darawa sannan ya ce, "Allah ya huci zuciyar Didi, sarauniyar zuciyar yayanta."
Ta rausayar da kai ta ce, "Sai na rama tukunna zuciyar zata huce.

Wait and see."
Daga nan ta tsinke kiran, zuciyarta na tafarfasa tana kitsa shirye-shiryen yadda zata rama abun da Uncle Al'ameen yayi mata.

Ta yi kwafa ta ce, "Yau a gidan nan zan kwana, gobe in aiwatar da shirina a kansa sai ya gwammace kida da karatu."
Da marece, Jidderh ta fara shirin tafiya gida, amma Rumana kuwa ko a jikinta, zaune take abunta.
Chapter 44 · 0% Book details