← Book details Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 49

Sashe 8

Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Trust me, wannan ita ka
ai ce hanyar da za mu bi Umma ta barka ka tafi da ni Katsina."
Ya yi jim yana nazari, ta marairace fuska, ya juya inda mai aiki take tsaye ya ce, "Ki ce mata mun koshi."
Ta juya ta koma ciki, Umma da ke zaune a parlour ganin basu dawo a tare ba ta ce, "Baki gansu ba ne?" Jamila ta rusuna ta ce, "Sun ce sun koshi."
Umma ta rasa bakin magana, ta ce, "Okay, ki je." Ta janyo ta wayarta ta kira numbar Junaid bugu
aya ya dauka, da kakkausar murya ta ce, "Junaid ka sameni a parlour yanzu."
Jim kadan ya shigo kansa a kasa yana sosa
eya, ta ce, "Ka
ago ka kalleni da kyau, saboda na ce Rumana ba za ta je katsina ba shine kuka tsiri yin bore a kan abincina, to shikenan babu komai ka je da ita, amma ina san ka sani ina fa
a maka da babbar murya idan har aka samu damuwa ka kuka da kanka domin ba zan yi maka da sauki ba.

Junaid idan wani abu faru da ita ka yi kuka da kanka, Junaid idan aka samu damuwa za ka ga
acin raina, kuma a lokacin ne za ka tabbatar da baka ta
a ganin
acin raina na gaske da gaske ba."
Jikinsa ne ya yi sanyi ya ce, "A'a Umma tunda baki so a bar maganar." Umma ta
an kalleta ta ce, "Sai ka je ka fa
a mata hakan." Har ya mi
e ya nufi waje sai kuma ya dawo da baya ya ce, "Zan je da ita."
Ta jinjina kai ba tareda tace kanzil ba, a sanyaye ya haye sama maganganunta suna damunsa, Anya kuwa sunyi mata adalci?

Babu abun da ta ragesu da shi a rayuwa, sai yake ji abun da su ka yi mata basu kyauta ba, a haka Rumana ta sameshi tana tsallen murna ta ce, "Umma ta ce ta barni mu je Katsina tare."
Ya yi murmushi wanda iyakarsa a kan labbansa ne kawai, ya ce, "Na tayaki murna, mu je mu ci abinci."
Sai da suka sauko sai kuma ya ji kunyar Umma ta kamashi sun ce sun koshi amma bayan ta yi masu abun da suke so sun sauko su ci, maganarta ta fito kenan akan bore su ka yi wa abincinta.

Umma ta dubesu kamar ba za ta yi maganar ba sai kuma ta ce, "Kuka ce kun koshi." Rumana ta yi karaf ta ce, "Saboda kin ce ban zuwa katsina na yi fushi da abincin shima yaya Junaid na hanashi ya ci."
Ji Junaid ya yi kamar
asa ta tsage ya shige jiki saboda kunya, ya kasa
aga idanu ya kalli Umma, yana zaune shurum kamar wanda ruwa ya ci.

Umma ta dubeshi ta girgiza kai kawai ta ce, "Mutane sun yi gaskiya da suka ce na sangartaku da yawa tunda ga shi a yau na zama diyar ku kuma uwayen." Ta mike tabar wajen ranta a
ace.

Junaid ya mike yabi bayanta yayinda Rumana take zaune tana kwasar gasar girki abunta, ya biye mata ta barshi da kunya.

Ya samu dakin Umma a kulle, ya kwankwasa ta yi mashi banza har ya gaji ya juya ya koma parlour.

Rumana ta yi digging abinci ta kai bakinsa ya amsa yana mata murmushi, ta ce, "Ina ka je?" Ya ce, "Umma na je in ba hakuri." Kanta tsaye ta ce, "Ka rabu da ita, anjima za ka ga ta dawo tana shiri da mu, tana kaunarmu bata iya fushi da mu."
Har washegari da suka tashi tafiya daga Rumana har Junaid babu wanda yaga fara'ar Umma, har Rumana sai da tasha jinin jikinta kamar za ta yi kuka ta ce, "Yaa Junaid tun jiya Umma bata yi mamu fara'a ba, tunda ta tashi yau bata yi murmushi ba, mu je mu bata ha
uri." Ya ce, "Ki bari idan muka dawo sai mu bata ha
urin." Ta fashe da kuka ya yi rarrashi har gaji amma taki matsawa ta shiga mota har sai sun je sun ba Umma hakuri, dakyar ya rarrasheta ta hakura suka tafi.

Suka dauki hanyar garin Katsina, a jirginsa ya yi nufin tafiya amma Rumana ta matsa a kan su tafi a mota tana mararin doguwar tafiya a mota (Ni MATAR ALIYU I was like samun gari, dadi ne ya yi wa Rumana yawa).

Ko da Umma taji labari a wajen shugaban masu bashi tsaro bata ce komai ba, ta dai ce su kula mata da yara.

Mota ce sabuwa dal mai tsadar gaske, Junaid ne yake jan motar yayinda take zaune a bangaren mai zama hakanan tana kallon hanya da garuruwa da suke wucewa tana murmushi wannan shine karon farko da ta yi doguwar tafiya a mota.

Motoci ukku ne sukayi masu convoy idan aka ha
a da motarsu guda hudu kenan, motocin iri
aya ne sak ta yadda babu yadda za'ayi mutum ya iya tantance wacce suke ciki.

Sun shigo cikin garin katsina a daidai wajen roundabout na liyafa, Junaid ya yi parking daidai wani katon shagon zamani ya ce, "Didi Ina zuwa?" Ta gya
a kai, ya
alle murfin motar ya fita zuwa ciki.

Ta fito ta jingina da motar tana kallon garin Katsina wanda wannan shine
aro na farko da ta shigo cikinsa, wani saurayi ta hango ya zuba mata idanu ba ya ko kyaftawa, ta turo baki tana gyara mayafi da ke akan kafadarta, gani ta yi ya nufo inda take har
aya daga cikin security da suke tare zai dakatar da shi ta yi mashi alama akan ya barshi.

Ta jinjinawa tsaurin idanun saurayin tana so ta ga iyakar tsaurin idonsa duba da yadda ya ke kallonta daga sama har kasa, ta kalli kanta tana sanye ne da tsadadden leshe dinkin umbrella gown, ta rufe kanta da kallabi sai dai jelar gashinta ya fito a waje yana reto a gadon bayanta, ta yafa mayafi a kan kafada yayinda kafafunta suke sanye da takal
ma masu tsini, powder da kwalli ne kawai a fuskarta kasancewarta ba ma'abociyar chaba adon fuska ba, ta zuba gold wuya da hannu, tana zuba kamshi mai sanyi.

Ta ta
e baki tana kallonshi daga sama har kasa, chocolate ne
an duma-duma mai saje yana sanye da brown kaftan, da hula dara a saman kanshi, kafafunsa rufe da takalma slippers, ya
araso inda take yana kallonta da mamaki a kan fuskarsa ya ce, "Jidderh!

Jidderh!!

Jidderh!!!"
Sai da ya kira sunan sau ukku sannan ta tamka, "Jidderh kuma?" Ta ce tana mashi kallon kaskanci.

Ji ta yi ya ce, "Jidderh mi kikeyi a nan?

Garin ya kika saka wadannan kayan kika fito da su?" Rumana ta girgiza kai tana wani shegen murmushi ta ce, "Kai kuma salon da kake amfani da shi kana tsara (toasting)
an mata kenan.

Daga ganin mace mai kyau har ka zo ka yi badda kama kana kirana da suna Jidderh.

To ina mai bakin cikin sanar da kai wasanka bai yi kyau ba a nan don haka ka
ara gaba tun kafin in saka security dina ya yi maka daukar kayan wanki ya watsar a kwatamin kwatar can."
Da mamaki yake kallonta ya ce, "Jidderh hankalinki
aya kuwa?" Idanunta a tsaitsaye ta ce, "Zaka ware ko kuma sai na saka anyi maka da yaren da zaka fi fahimta." Ta
arasa maganar tana yafito
aya daga cikin securityn ya
araso, ta ce, "Idan ya
ara dakiku talatin bai
ace min daga gani ba, ka
aurashi a kafa
a ka watsar a kwatamin kwatar can."
Ya dubeta ya dubi katon da ta kira, juyawa ya yi ya koma wajen motarsa yana tafiya yana waiwayenta fuskarsa dauke da matu
ar mamaki akan abun da ya faru, idanunsa Jidderh suka gani muryarta da komai ita ce amma abun da ta yi mashi ba halinta ba ne ba.

A daidai lokacin ne kuma Junaid ya iso ya kama hannunta ya ce, "Mu je." Ya bu
e mata
aya bangaren mai zaman hakanan ta shiga sannan ya zagaya bangaren direba ya ja motar suka wuce, suka bar saurayin sake da baki, ya bi motar da kallo cike da matu
ar mamaki.

Bai yi
asa a gwuwa ba ya zaro wayarshi ya kira wata number ya yi jim sannan ya ce, "Imran.

Shin Jidderh tana gida?" Daga
aya bangaren Imran ya ce, "Eh tana gida." Mamakinsa ya
aru, "Tana kusa da kai?" Ya tambaya domin ya tabbatar da gaske tana nan.

Imran ya ce, "A'a ina balcony tana dakinta." Ya ce, "Ka je ka dubata." Imran ya wuce dakin Jidderh ya sameta zaune a kan darduma tana karatun Al
ur'ani.

Muryarta da ya jiyo a cikin kira'arta mai dadin saurare tana rera karatu a cikin Suratur Rahman ya tabbatar masa da ba ita bace wacce ya gani, kansa ya
aure shin idan ba ita bace to wacece ya gani domin kamannin sun yi yawa, tsayinsu, muryarsu, kamannin fuskarsu da komai iri
aya ne sak babu banbanci ko ka
"Uncle In bata wayar?" Muryar Imran ta katse mashi tunani.

Ya ce, "A'a ka kyaleta." Ya tsinke kiran yayinda mamaki ya bayyana
arara a kan fuskarsa, ta tabbata wacce ya gani ba Jidderh bace.

Amma tambayar ita ce tunda ba Jidderh bace, Shin wacece?

Mi ya saka take matu
ar kamanni da Jidderh kamar kobo da kobo that har ya kasa banbancesu?
(Wannan kenan, mu koma ainihin labari)
**********
KATSINA
Rumana ta mi
e tsaye tana bin dakin da kallo, hoto dake a kan bedside table ne ya dauki hankalinta ta daukeshi tana kallo, da mamaki kwance akan fuskarta take kallon yarinyar dake cikin hoton ganin kamarsu
aya sak kamar kobo da kobo.
Chapter 8 · 0% Book details