← Book details Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 49

Sashe 35

Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kanta tsaye ta ce, "Bana iya cin abun da kuka girka, idan ba za'a barni in siya ba sai in zauna da yunwata tunda shi aka za
ar min."
Ammi ta girgiza kai tana al'ajabi yadda aka yi sakaci da yarinya har ta girma haka ba tare da tasan lafazin da ya kamata ta fitar ba, ba tare da ta kalli inda take ba ta ce, "Kije ki girka da kanki."
Rumana ta ce, "Ko ruwan shayi ban iya ba, beside ban yi kama da
ar kitchen ba, koda yake ta kwana gidan sauki tunda gidan ne ba'a shigowa da abincin saye sai mutum ya fita ya siya."
Imran da ya shigo parlorn ya ce, "Babu inda za ki je, idan yunwar ta yi maki illa kin ci." Ta kalleshi ta watsar tana fa
in, "Amma naga da kudina zan siya."
Imran ya ce, "What!."
Sai dai ji ta yi ya kwasheta da mari, ta fasa
ara tana fa
in, "Mi nayi maka kake cin zalina?"
Ya murtuke fuska yana nuna mata kitchen, "Ki tashi ki wuce kitchen wurin
ar uwarki ki tayata aiki."
Duk da marin ya shigeta amma taurin kai ya hana bakinta mutuwa, ta ta
e baki ta ce, "Idan kuma na ce ba zan yi ba fa, to bari ka ji ko a gidan mu ban shiga kitchen ba ballantana a gidan nan."
Imran ya
aga hannu zai
ara mata wani marin, da gudu ta yi hanyar kitchen, ya ce, "Ammi idan ki ka yi mata da wasa raina kowa za ta yi a gidan nan."
Abbi da ke tsaye a kan matakalar bene wanda akan idanunsa komai ya faru, ya ce, "Hajiya Balki daga yau Jidderh da Rumana ne za su rin
a girki a gidan nan.

Kai kuma Imran ka rin
a yi mata da sauki, ta tashi ne babu kwa
a shiyasa ta ke yin haka."
Rumana ta shiga madafar tana turo baki a lokaci guda tana share hawayen da ke akan kumatunta, Jidderh ta juyo ta ce, "Adda Rumana ke da wa?"
Sai da ta juya ta harari kofar madafar sannan ta ce, "Wannan mugun yayan naki ne azzulumi macuci, ya mareni wai inzo in koyi girki."
Maganar ba ta yi Jidderh
i ba amma sai share ta ce, "Kinga ni kuma ina matu
ar son girki.

In tambayeki mana, wasu iri kalolin abinci ne yaya Junaid ya fi so?"
Sai da ta yi jim sannan ta ce, "Wainar shinkafa, dambu, sunasir da zobo sannan kuma yana son kunun gero, sai kuma wannan abun da kukayi jiya da dare."
Jidderh ta yi dariya ta ce, "Wai tuwo." Rumana ta harareta ta ce, "Ke kuma miye na fa
in sunan ai nasan sunan naki fa
a saboda jinsa kawai yana tayar min da zuciya."
Jidderh ta ce, "Ba wannan ba, duk wadannan girke-girke da kika lissafa na iya sarrafasu, ki rin
a tayani girki, ni kuma zan koya maki yadda zaki girkasu, kinga idan kikaje kaduna sai ki bashi mamaki ki girka mashi yana ci yana maki santi."
Rumana ta ware idanu ta ce, "Kina nufin idan na koya na girka mashi zai yi dadi har ya yi sati." Jidderh ta ce, "Sosai ma, idan har kika kware a girki kowa ma idan ya
ana sai ya yi santi."
Rumana ta yi jim tana nazari, ba koyon girkin ba, ita wahalar girkin ne ba za ta iya ba, can sai ta ce, "That's good idea.

Mi zan yi maki yanzu?"
Jidderh ta nuna mata kayan lambu da ke a gefe ta ce, "Bari in nuna maki yadda zaki wanke min su."
Tana wankesu tana mita a ranta, don ta baiwa yaya Junaid mamaki ne kawai shiyasa ta hakura za ta koya.

Ji ta yi Jidderh ta ce, "Uncle."
Tana juyawa taga Al'ameen ne, kallo
aya ta yi mashi ta kawar da kai ta cigaba da wanke kayan lambun kamar yadda Jidderh ta nuna mata, tana ji Jidderh tana gaida shi.

Ya dubeta ya ce, "Ke baki iya gaisuwa ba."
ago tare da sakin wani shegen murmushi ta ce, "Na iya gaisuwa amma sai dai inda kayi rashin sa'a shine wanda ya dace na iya gaidawa, don haka ka fita harkata, ni ba sa'ar yinka bace ba."
Al'ameen ya shafa gemunsa ya ce, "Kai, Haba."
Takaicinsa ya kawota makoshi, ta harari inda yake ta ce, "Bani da lokacinka domin kai kanka idan aka yi maka kudi sai in siyeka da duk wani abu da ka mallaka ba tare da na girgiza ba don haka idan wani abu ne a ranka a kaina shiyasa kake shige min to kayi ta kanka domin na fi karfinka."
Daga haka bata
ara cewa komai ba ta ci ga ba da abun da ta ke yi, ji ta yi ya ce, "Kadangare."
Bata san lokacin da ta fasa ihu ba ta daka tsalle ta yi baya, ya fashe da dariya yana fa
in, "Wasa nike, matsoraciyar yarinya." Kafin ta yi magana ya juya ya fice.

Ta rasa bakin magana, takaici ya kawo mata wuya, tana tsaye kawai tana luguden la
a ta kasa furta kalma ko
aya, ta yi kwafa tana ayyana sai ta rama.

Jidderh ta yi dariya ta ce, "Ke da uncle kuna drama."
Rumana ta yi kwafa tana fa
in, "Sai ya yi nadamar shiga hurumina sai na rama abun da ya yi min, yadda ya razanani nima sai na razanashi."
Har ya fita basu sake haduwa ba, suna gamawa Rumana ta wuce sama ta yi wanka ta sauya kaya ta kwanta a kan gado tana jin baki daya jikinta yana mata ciwo.

Da dare tana kwance a dakinta ita
aya, ta janyo wayarta ta yi wa yaya Junaid video call, ta fashe da kuka ta ce, "Shine ka wuce ka barni a gidan nan bayan ka san ba kaunata su ke yi ba, tun a gabanka ake barazanar dukana, shine don nace zan sayi abinci aka hanani kuma wannan mugun macucin ya ce dole sai na shiga kitchen na koyi girki."
Kukanta yana sakashi a damuwa, ya ce, "Didi kiyi hakuri kinji, ki daina kukan kada kanki ya yi ciwo, kina tada min hankali."
Tana cigaba da kuka ta
ara kawo wani ba'asin, "Kuma Abbi ya ce ni da Jidderh zamu rin
a girkin gidan, ka ji wani danyen hukunci, a yaushe ne na zama kalar shiga kitchen." Sai kuma ta ja fasali tana goge hawayen da ke a fuskarta ta ce, "Amma ka san mi?"
Junaid ya yi murmushi ganin ta saki fuska ya ce, "A'a sai kin fa
a min."
Da fara'arta ta ce, "Jidderh ta ce za ta koya min kalolin girkin da kafi so idan nazo Kaduna in yi maka."
Ji ya yi ranshi ya yi sanyi ganin babu damuwa a ranta, ya ce, "Ah haba, kice in shirya cin girkin Rumana mai
an karen
Ta saki dariya tana fa
in, "Kuma ta ce idan kaci sai kayi santi."
Ya ware idanu ya ce, "Ahh, haba."
Ta ce, "Haka dai ta ce." Sai kuma ta yi rau-rau da idanu ta ce, "Na gaji da zama gidan nan ka dubi dakin da suka bani kamar akurkin kaji, mutane sai zuwa suke ganina, kuma naji suna cewa gobe za mu je gidansu matar gidan, nifa na gaji da gidan nan." Ta
arasa maganar tana mai fashewa da kuka.

Damuwa ta bayyana a kan fuskarsa ya ce, "Rumana babu yadda zan yi saboda sun fini iko a kanki.

Rumana ke ka
ai ce
anwa da nike ita.

Ina cikin damuwar rabani da ke da aka yi, idan ina ganinki a damuwa
ara min zafi kikeyi, Didi ina kike so in saka kaina ne.
azu na ce zan zo in daukeki saidai komai zai faru ya faru amma Umma ta hanani."
Shi kanshi da ya yi maganar yasan
arya yake domin kunyar da ke tsakaninsa da Ammi ba zai iya zuwa ya ce zai dauketa ba.
ora da fa
in, "Amma ki bari bayan biki Umma za ta je Dubai idan ta dawo zanzo in rabaki da gidan nan, kiyi ha
urin zama da su kafin cikar lokacin."
Ranta bai so ba amma babu yadda ta iya, ta gya
a kanta ta ce, "To shikenan."
Islam ta shigo ta ce, "Adda Rumana zan yi bacci." Rumana ta nuna mata kusa da ita ta ce, "Okay zo kiyi bacci abunki."
Washegari, Ammi, Jidderh, Islam, da Imran ne tsaye a harabar gidan suna jiran Rumana, Jidderh tana jingine da mota sanye take da dogon hijab har kasa, Rumana ta fito tana sanye da atamfa dinkin half gown da skirt, ta
aura mayafi a kan kafa
Ammi ta murtuke fuska ta ce, "Koma ki ajiye wannan mayafin ki saka
aya daga cikin hijaban da kuka dinko." Ta juya inda Jidderh take ta ce, "Jidderh ki jirata ta fito
sai direba ya kaiku."
Rumana ta kalli kanta tana
arin fahimtar miye illar shigarta da har za'a ce ta koma ta saka hijab, tana tsaye turus tana al'ajabi.

Ammi da Islam suka shiga mota Imran ya jasu ya rage daga ita sai Jidderh, ranta a
ace ta koma ciki ta fa
a a kan gado tana turo baki tana ayyana ta fasa fitar baki
aya, wayarta ta yi ringing alamar shigowar kira koda bata duba ba tasan waye kasancewar ringing dinsa na daban ne, ta
aga kiran ta kanga a kunne ta ce, "Yaa Junaid."
Daga daya bangaren ya ce, "Didi har kun tafi?"
Ta girgiza kanta kamar yana a gabanta ta ce, "A'a." Ya ce, "Mi ya faru naji muryarki wani iri?"
Ta ta
e baki ta ce, "Ammi ce na shirya na fita ta ce in koma in saka hijab kuma atamfa na saka half gown da skirt."
"Sai aka yi ya?"
Ta harari kofar dakin ta ce, "Sun tafi bayan da ta ce direba ya kaimu tare da Jidderh ni sai dai inje da motata."
Yana ji yasan akwai wani abun da bata fa
a ba, ya tabbata hakanan kawai Ammi ba za ta ce ta saka hijab ba ta ce, "Amma hala da kayan kawai kika fita babu mayafi."
"Da mayafina na fita."
"A kan kafa
a?" Ya tambaya.
Chapter 35 · 0% Book details