← Book details Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 49

Sashe 37

Zane Akan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuma kinyi kyau sosai."
Ya ware idanu ya ce, "Yaushe kika koyi
aura zani?" Da wannan don wannan ita fa tunda aka fara
aura zanin har aka gama bata fahimci ta inda aka fara ba, ta ce, "Jidderh ce ta
aura min, har rikeshi nikeyi ina ganin kamar zai kwance amma kuma har yanzu bai kunce ba."
Ya yi dariyar wautarta ya ce, "Kuma yayi maki kyau."
Ta kama hannunsa ta jashi suka shiga ciki, tana like da shi tana hira suna dariya, ya kalli hannunta da yake ri
e da hannunsa, ji ya yi murmurshi ya su
uce masa.

Ammi ce ka
ai suka tarar a parlour, ya zauna tare da gaidata ta amsa da sakin fuska.

"Ya shirye-shiryen biki?"
Ya amsa da, "Alhamdulilahi." Kanshi a kasa alamar kunya.

"Allah ya bada zaman lafiya."
"Amin."
"Na girka maka abincin da kafi so, yana a kan teburin cin abinci," Rumana ta fa
a tana murmushi.

Ya dubeta da zaulaya ya ce, "Miye teburin cin abinci kuma?"
Bata gane zaulayarta yake yi ba ta ce, "Dinning table shine teburin cin abinci."
Ya ce, "Wow." Ya kai hannu zai dafa kanta ko mi ya tuna sai kuma ya sauke hannunsa da sauri ya daburce kunyar Ammi ta kamashi.

Rumana da bata san abun da yake wanzuwa a gareshi na kunya ba ta kama hannunsa zuwa dinning table, ya cire hannun ya ce, "Zan bi ki ai."
an dubeshi ta ce, "Miye don na rike hannunka?" ya yi kasa kasa da murya ya ce, "Ammi tana kallo fa."
Da karfinta ta ce, "Ko tana kallo sai mi, ina ce hannun yayana na ri
e, kai fa muharramina ne."
Maganarta ta farko kunya ta sakashi ita ce ta fa
a amma shi ta bari da kunya domin yana da tabbaci a kan Ammi ta jiyota.

Sai dai a kan furucin da ta yi daga baya, abun ya dakeshi ba ka
an ba, ita kuwa ko a jikinta wai an tsikari kakkaura.

Yana gaba tana biye da shi tana murmushi, ya ja kujera ya zauna, ta saka plate a gabansa da fara'arta ta ce, "Dambu ne da wainar shinkafa da miya.

Wanne zaka fara ci?"
Ya murmusa yana binta da kallo ya ce, "Wanda Didin Junaid ta zuba man."
Rumana ta yi murmushi, ta zuba mashi dambu wanda ya ji kayan lambu, tunda daga kamshin abincin yasan dole a tashi kansa da wannan girki, ya yi loma
aya yayinda yanayin fuskarsa ya sauya ya kafeta da kallo, ta yi tsuru-tsuru da idanu tana tarabbabin ka da abincin ne bai yi
i ba kuma tayi wujiga-wujiga idan girkin baiyi
i ba sai taja Allah ya isa.

Junaid ya murmusa hakan ya saka hankalinta ya kwanta, abincin ya yi dadi kenan, ya ce, "Kin tabbata da kanki kika girka dambun nan?"
Ta kama hannunsa tana murmushi ta ce, "Da kaina na girka."
Ya ware idanu ya ce, "Kai, Kai, Kai, To Allah ya karo zakin hannu, ya yi dadi sosai, ki saka min waigi kafin in fara santi."
aura hannu a kan hular da ke a kansa ya karyata ya ce, "Didin Junaid abincin nan naki ya yi dadi na karya maki hula."
Rumana ta fashe da dariya, yana santi tana mashi dariya, ya kafeta da idanu yayinda kyawunta yake kara bayyana a gareshi, bai taba mata kallon gane kyawu ba sai a wannan ranar kuma ya yarda ita din mai kyawu ce ajin karshe, kyau ma
urar ha
uwa.

Ta ja kujera ta zauna tare da zuba mashi idanu tana kallon yadda yake cin abincin cike da nutsuwa yana lumshe idanu, yana cin rabi ta kwace farantin sanin ba zai iya cin abun da ya haura plate
aya ba, ya dubeta ya ce, "Miye haka?" Ta ce, "Wancen zan zuba maka." Ya waro idanu ya ce, "Amma ban koshi ba kuma ya yi dadi." Ta ce, "Masar zan zuba maka itama ta yi dadi."
Ya lumshe idanu ya bu
e ya ce, "Allah ya yi maki albarka, zuba min inji idan shima ya yi dadin sai inci tunda ba'a san maci tuwo ba sai miya ta
are."
Ta zuba wainar shinkafa da miya har da kaza, yana ci yana ha
a wa da naman kazar da ya yi dadi yana mata santi tana dariya, suka lalace a dinning table sai da ya ji babu waje sannan ya kora da zobo.

Rumana ta saka rigimar sai dai ya bata da kansa, sai da ya leka yaga Ammi bata falon sannan ya yarda ya bata abincin sai dai shagwa
a da ta ke yi yana sakashi a wani yanayi.

Har da Jidderh za su tafi, Ammi ta rakasu har wurin mota, masu aiki suka saka masu kaya a booth, Ammi ta ce, "A kula, Allah ya tsare hanya."
A tare suka amsa da, "Amin."
Jidderh ta bu
e gidan baya ta shiga yayinda Rumana take a bangaren mai zaman hakanan a gefen Junaid, suka kama hanyar airport.
*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*
*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*
Taku Har Kullum Aysher Angel (Matar Aliyu)
*ZANE A KAN RUWA*
_(Mai Wahalar Gane Kamanni)_
*NA*
*AYSHER ANGEL*
Page 12
Free Page
*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*
*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*
Rumana ta koma sukuku.

Ba wai tana jin wani takamaiman ciwo bane amma zuciyarta cike take da wani yanayi da ta kasa fahimta, tana jin kamar akwai abun da ke damunta amma kuma ya
uya, ya
i bayyana ballantana ta nemi maganin maganceshi.

Ta rasa abun da yake mata da
i, ta kuma rasa abun da ke saka mata damuwa.

Komai ya rikice mata.

Junaid da ke zaune a gefenta ya dade yana kallonta, yana lura da yadda ta yi shiru.

Ya matsa kusa da ita, ya kirata a hankali, "Didi."
Amma shiru ba ta motsa ba, idanunta a rufe kamar wacce take barci, amma a zahiri ba barcinta ta ke yi ba, hankalinta yana yawo a wani wurin daban.

Ya sake cewa cikin damuwa, "Didi, mi yake damunki ne?

Ko hira ma kinki
i yi min?"
an motsa lebenta ka
an, amma ba ta bu
e idanunta ba.

Murya a raunane ta ce, "Haka nan nike jina wani iri."
Amsarta ta saka Junaid ya
ara shiga damuwa.

Rumana
anwarsa yarinya ce mai fara'a da annashuwa, wacce kullum take cike da dariya da raha.

Yanzu kuwa kamar an sauya ta, an
auke mata walwalarta an bar mata damuwa.

Jirgin yana ci ga ba da tafiya, amma a gareta kamar lokaci ya tsaya, tunani kala-kala yana yawo a zuciyarta, amma babu
aya da take iya kamawa ta fahimta.
arfe biyu na rana jirginsu ya sauka a garin Kaduna.

Convoy suka tarar motoci masu tsa
a sai she
i su ke yi suka tarbe su.

Rumana ba ta damu da komai ba, ba ta damu da tsaron da ke zagaye da su ba, ba ta damu da gaisuwar da ake musu ba.

Ta kutsa kai cikin mota, convoy din motocin su ka yi escorting dinsu zuwa gida.

Motocin suna parking a harabar gidan, direba bai gama parking ba, ta bu
e murfin motar da sauri ta fito kamar wacce ake bi, kai tsaye ta nufi cikin gidan da gudu tana faman kiran, "Umma!

Umma!!

Umma!!!"
Muryarta tana rawa, cike da tashin hankali da ita kanta ba ta san dalilinsa ba.

Ta shiga falon, idonta na yawo kamar wacce take neman mafaka.

Zuciyarta na ayyana mata watakila idan taga Umma ta samu sassaucin abun dake damunta, watakila ganin Umma
in zai iya kawo mata nutsuwa, ya warware mata wannan
aurin da ke damunta a zuciya.

Ta rungume Umma tare da fashewa da kuka tana fa
in, "Na yi kewarki Umma."
Umma ta share hawayen da suka zubo mata ta ce, "Nima na yi kewarki Rumana."
Junaid ya shigo tare da Jidderh, Jidderh ta gaishe da Umma, "Umma Ina wuni?"
Umma ta amsa da, "Lafiya lau." Ta dora da fa
in, "Ya hanya?"
Jidderh ta amsa da, "Alhamdulilahi."
"Ya kuka baro mutan gidan?"
"Lafiya lau."
Umma ta maida dubanta akan Rumana ta ce, "Rumana ki wuce da ita dakinki ku yi wanka, zan saka masu aiki su kawo maku abinci." Rumana ta gya
a kai.

Umma ta ce, "
ata Jidderh, Allah ya huta gajiya." Jidderh ta amsa da, "Amin."
Suka haura sama, Rumana ta fada akan makeken gadonta tare da sakin murmushi ta ce, "Gida, Gida ne, duk wanda ya bar gida, gida ya bar shi."
Sai da Jidderh ta yi wa gidan kallon nutsuwa sannan ta gane mahaukacin girman da ya ke dashi da zunzurutun dukiyar da aka kashe a wajen ginashi, a yadda gidan yake da girman gaske za'a iya dauko gidansu a saka a gidan ba tare da gidan ya rage filin azo a gani ba.

Washegari aka fara gudanar da hidimar biki, gida ya cika makil da
an uwa da abokan arziki, kowa na ta hidimarsa, ana kai-komo, ana dariya, mata suna ta rangada guda ana farin ciki amma duk wannan annashuwa ba ta shafi Rumana ba.

Duk irin burin da ta dade tana yi a zuciyarta game da bikin yaya Junaid, duk yadda ta yi mafarkin wannan rana da yadda za ta shiga ta fita ta yi rawa ta nuna farin cikinta amma sai gashi yau komai ya sauya.

Wani irin yanayi ne ya lullubeta wanda ita kanta ta kasa fassara shi.

Ba ciwo ta ke ji kai tsaye ba, amma zuciyarta cike take da wani nauyi da damuwa marar suna.

Tun da suka iso, ta killace kanta a cikin daki.
Chapter 37 · 0% Book details